Advertisements
Chapter 32 Reading Ku Dube Mu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ku Dube Mu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   32 / 99

93K to 96K   out of 295.8K words

itama "su waye zasu ganmu Daddy?"


" 'Yan tawayen mana"


Kasa magana tayi ta tashi ta koma dakin Innarsa tana kuka. Har yaushe zasu kare
rayuwarsu a wannan yanayi? Dama haka ake auren sojan ko kuwa kaddararsu ce haka?


Sauki babu sai daga Allah. A wannan yanayin Gambonsu Mami da mijinta Harun da a
wurin Alh Baba suka zo daga Germany inda yake aiki a gidan rediyo a matsayin mai
labarai.


Sunyi bakincikin yadda rayuwa ta mayar da 'yan uwansu shine Harun ya shiga newarwa
Major da Mami visar tafiya. A cewarsa zai kai dan uwansa asibiti ne tunda babu wani
cigaba a gida. Iyayensu dai sun kyaleshi ne amma a iya tunaninsu asarar kudi zaiyi.


Abu na Allah sun tafi Germany a shekara ta uku bayan rasuwar Zayyan. A can ne
bincike ya nuna Major yana fama da Post Traumatic Stress Disorder (PTSD). Lalura ce
ta kwakwalwa da a lokacin ba'a waye da ita sosai a bangarenmu na Africa ba. PTSD
tana samuwa ne ga mutanen da suka yi gamo da mummunan yanayi ko al'amari kuma tana
tashi ne idan suka samu kansu a yanayin da zai iya tuna musu da wannan abu. Yawan
mafarkin da yake yi da kuma ji ko ganin kamar yanzu abin yake faruwa duka
alamominta ne.


Mami tambaya take ba haukacewa yayi ba aka ce mata ba hauka bane sai dai masu ita
suna bukatar tsantsar kulawa daga makusantansu don idan abu yayi yawa wasu har
kashe kansu suke yi.


A gidan Gambo suka zauna har zuwa lokacin da ya fara jin sauki. Mami ta jajirce
sosai wurin kula dashi. Daga baya ta fara tunanin kada su zame musu nauyi tace
Harun ya nema mata aiki. To aiki a wata kasar ba'a samunsa kai tsaye. Ta bukaci ko
yaya tana son neman kudi kafin su koma saboda kusan karkaf sunyi. Komai nashi ya
kare an fara shiga aljihun dangi.


Aikin nanny ya samar mata har yana tsoron fada mata sai ta basu mamaki wurin karbar
aikin hannu bibbiyu. Gidan wasu 'yan kasa take zuwa daga bakwai na safe zuwa bakwai
na yamma. Tayi su shara, wankin toilet da sauran ayyukan gida hade da raino.

Mutane da dama suna zaton da ance ka fita waje watayawa kake. Aikatuwa take
bilhakki mijinta yana kukan nakasa a gefe. A hankali masu gidan suka yaba da
kwazonta sai aka basu wani dan bangare karami a gidan.


Cikin shekarsu ta biyu Harun yaje gida abinda ta hada ta bayar aka dauko musu
'ya'yansu sauran kuma ta aika Sakkwato wurin sojan da Major ya rubutawa sako cewa a
bawa su Mairama. Shekara guda cif cikin kudin aikin Mami ake dibarwa Mairama.


Sako ya riskesu daga karyar Maikudi cewa tayi aure sannan dan cikinta baizo da rai
ba. Hoton Alheran Radhiya kuwa da suka bukata cikin dakin Jume ya dauko wani da aka
yi musu da yaransu gidan wani zuwansu da sallah. Murna sosai ranar da suka amshi
hoton.


Cikin ikon Allah sai ga Mami da ciki. Allah Ya bata 'ya mace Major ya saka mata
suna Zayyanatu. Dariya tayi da taji sunan yace idan haihuwa goma zata sake Zayyan
da Zayyanatu zaiyi ta saka musu.


A yanzu Major ya sami aiki a wani kamfani shima sannan Awwab ya sami scholarship
saboda kwazonsa a makaranta. Harun da Gambo sun koma Nigeria da 'ya'yansu uku
Ghazalatu, Hafsa da Imam. Su Mami kuwa zaman jiran kammaluwar karatun Awwab suke su
koma su ma. Sun sami rufin asiri daidai gwargwado kuma sai Major yayi watanni
lalurarsa bata tashi ba sai anyi zancen Nigeria ranar zai kwana hankali a tashe
yana tuna aikin da ya yiwa kasarsa ya kaishi ga wannan rayuwa


**********


HADUWAR ALKHAIRI
[02/11 7:30 AM] My 2nd Mtn: 19. Max, Anna da Liam sune 'ya'yan da suka tashi a
hannun Mami. Suna ganin shigowarsu lawn din suka taho suna murna. Idanun Anna jazur
taci kuka tun safe take abu daya.


Rungume Mami tayi "bana so ki tafi Naanaa" tace cikin yaren jamusanci.


Da yaren Mami ta maida mata "kiyi hakuri Anna, watarana zan zo ziyara ko ke kizo
mana Nigeria ko"


"Zaki zo aurena next year?"


"In sha Allah"


Hawaye Anna take ta rinka sumbatar kumatun Mami ita kuwa sai dariya. Liam da Max
hannuwanta suka rike suka kaita tsakiyar wurin suna nunawa jama'a Naanaa dinsu. Mai
aiki ce amma wadda take a inda aka san darajar masu aiki har masu gida suke karrama
su.
Ta sami kyaututtuka da yawa daga abokan aikinta da abokan arziki.


Frau Marie Schmidt ta kawo envelop da kudi a ciki ta bata sannan ta bawa Fauziyya
da Zahra wasu setin dankunne da sarka 'yan ubansu wai su saka da bikinsu. Zayyana
ma an bata katon teddy kusan kansu daya. Tana ta murna Mami a ranta tayi dariya
kawai. 'Yan kasarmu ina muka wani san darajar teddy.


Hotunan tarihi suke dauka Major ya daga waya yana fadin inda suke. Ko minti biyu
ba'ayi ba sai ga matashin saurayi kyakkyawa wankan tarwada mai cike da kwarjini da
haiba ya shigo wurin sanye da uniform dinsa na matukin jirgin KLM mallakar kasar
Germany. Jacket da wando ne navy blue sai farar shirt a ciki kansa sanye da hula
irin ta Captain din jirgi. Mata hudu ne a gefensa hagu da dama air hostess kowacce
da uniform riga da skirt sky blue suna rike da flowers masu kyau.


Shigowar tasu ta kayatar da mutanen wurin bare iyayensa. Yana shigowa kai tsaye
wurin Major ya nufa ya rungume shi. Mami ta saki baki sai kuma ta daure fuska cikin
wasa.


"Awwab, yau din ma?"


Sai da yayi mata dariya sannan ya rungume Maminsa a kunnenta yana cewa "sorry
Mamina"


'Yan matan da suke abokan aikinsa kowacce ta mika mata flower da dan gift suna mata
fatan alkhairi.


Awwab ya fiddo tickets biyar daga aljihun sa ya mikawa Major.


"Daddy ga nawa gift din...Captain M.A Mustapha shine zai ja jirginku zuwa birnin
Abuja. Sai da na duba schedule dina na sayi ticket. Tafiya ta dawo nan da sati
biyu. I hope it is okay"


Zayyana tayi tsalle ta dane shi tana ihun murna. Mami sai murmushi kawai na
jindadi. Major kuwa tsokanarsa yake yi wai bazai shiga ba kada ya zubar dasu a
teku.


An gama party lafiya suka koma gida tare dashi. Shirye shirye ya kankama inda suka
hada ya nasu ya nasu sai gida Nigeria.


***********


Iyayen Zainab sun sakata a gaba kowa da abinda yake cewa tun da ta sanar musu cewa
a yiwa iyayen Hadir magana akan aurensu.


"Wai shin idan kin koma soyayya zaki rinka zuba muku a kwano kuna ci? Ke ba aiki
shi a zaune. Ni har yau ban gamsu da ba ke kika kashewa kanki aure ba" mamanta tace
a hasale.


Babanta ne ma mai dan sauki a gareta "Zainab nasan kila ko a wurin Ibrahim kina ji
cewa jikin Hadir babu wani sauki sai na musulunci. Kinje kin shafe shekaru tare da
Musa kin saba da jindadi. Ta ina zaki koma gidansu?"


"Baba na fada muku ya bani gida a Kano sannan ya kara min jari akan wanda ya bani
tun da nake zuwa Dubai saro kaya dashi. Alhamdulillah Allah Ya wadatani Abbansu
Aisha ne sila. Ni zan cigaba da tafiya kasuwancina ne Ibrahim ya rinka kula dashi
idan bana nan"


Mamanta ta kara kulewa "sannu uwar tsari, waro har kin gama tsara yadda komai zai
kasance"


Allah Ya sani tana son iyayenta kuma tana girmama su. Amma wannan karon tana jin
tayi girman da ya kamata a karbi uzurinta idan tazo dashi.


"Idan ba kwa so na komawa Hadir bazan koma ba. Amma wallahi bazan kara aure ba har
na mutu"


Tsam ta tashi daga dakin Baban nata. Sun san Zainab da taurin kai. Anyi sa'a ma
zamanta da Musa Allah Yayi da tsayin kwana. Tufka suke da warwara suna guje mata
matsala a gaba. Karshe mahaifinta yace su barta Allah kadai Yasan dalilin wannan
soyayya da take yi masa.


Bayan kwanaki ana muhawara da 'yan uwa babanta da kansa yaje Kano da dan uwansa ya
gabatarwa Baban Hadir bukatarsu. Sunyi matukar mamaki ace har yanzu Zainab tana son
dansu. Matar da sun sani yanzu ita dashi kamar wutsiyar rakumi ne da kasa. Daga
irin suturun da take yiwa Ibrahim da abubuwan zamani da take wadata shi dasu zaka
san Haj Zainab take don tayi Hajji da Umara albarkacin Musa.


"Idan na fadawa Hadir bazai yarda ya aureta ba saboda lalurarsa" Babansa ya amsa
musu a sanyaye. Hadir ya riga ya karbi kaddarar rayuwarsa.


"Sai kayi shiru mu kulla abinmu a tsakaninmu ba shikenan ba" Kawun Zainab ya bashi
amsa.


Da izinin Allah a ranar basu tashi ba sai da aka mayar da auren Zainab jaruma mai
sadaukarwa da Hadir jarumin kasata da kasar ta dade da mantawa dashi.


Da aka kirata da wannan kyakkyawan labari tayi kukan farinciki sosai. Sati daya aka
diba tariya inda Baba ya sa Ibrahim ya kwashe kayan sawarsu ya rinka maidawa
gidanta da yake Janbulo. Hadir yana kallo bai iya tambaya sai ya sawa ransa ko
gyara za'ayi a dakin.


**********
"Wayyo Innawuro, kiyi min rai....Ummiiiii ki ceceni"


Ihun Radhiya kenan da ya karade gidan tana zaune Emzee ya danneta Innawuro zata yi
mata aski.


Mairama hakuri take bata akan ta bari ayi "idan ba'a magance kwarkwatar nan ba
wallahi duka sai kin shafa mana. Har na gama makarantar kwana ni banyi ba. Ku baku
iya kula da kanku sai kazanta da gayun banza"


Kyabe fuska ta sake yi hankalinta yana kara tashi "zan wanke Ummi harda karkashi in
gumbuda musu gishiri Yasin duk su mutu"


"Innawuro ko za'a bari ta gwada saka karkashin?" Mairama tace a hankali tana jin
kunyar shigarwa 'yarta.


"Kyaleta Mairama don baki ga kan bane. Makero ya cinye keyar sai gashi kadan, gaban
kuma amosani da kwarkwata. Yarinya mai cikar gashi da laushi duk ya lalace saboda
rashin kula. Na fada miki Mairo ta biyo a cikar nan zai tofo da wuri"


"Ayya Ummi ki tausaya min mana" tace a wahale.


Emzee ya sake sakar mata nauyinsa akan cinyarta da ya dora kafafunsa yana dariya.


"Mugu daga ni"


Sake danneta yayi tayi kara Mairama ta kasa hakuri "Karami ka kiyayeni fa, me kake
mata ne?"


Innawuro ya kalla suka sa dariya wai ta tarewa abokiyar fadanta sai ta kama bakinta
ta kunshe.


Radhiya na ganin gashinta ya soma zuba ta soma wani sabon kukan "kiyiwa Allah da
ManzonSa Innawuro ki bar min na zaman falo. Kina ji fa Baffa Gide yace duk aurar
damu zaiyi"


Wannan karon dariya harda Mairama "wanne ne na zaman falo kuma?"


"Wanda zan rinka daurewa da ribbon inyi kwalliya"


Innawuro da Emzee suka cigaba da tunzurata tana ta zuba ana kwashe gashin "ance
miki aure za'ayi miki ne kike neman gashin zaman falo?"
"Aure kuma Innawuro ai kamar habo ne. Yanzu idan kika kwashe gashin nan miji yazo
yay...." shiru tayi da ta ji ana kankarar kan nata da reza.


Wani uban ihu ta saka an gama askin Innawuro tana mata kwaryar molo na gasken da
reza ana kwashe sauran gashin da fatar da makero ya gama cinyewa tayi wani fari da
tudu-tudu.


"Wayyo Allahna na shiga uku na lalace, wayyo, wayyo, wayyo"


Mairamu maficin hannunta ta daga zata kwada mata "wane irin sakarci ne wannan kike
mana ihu kamar wata mara hankali"


Sai da ta tashi ta makawa Emzee harara da daradaran idanunta sannan tayi gaba tana
cewa "dama Ummi wane hankali ne zaiyi saura akan budurwar da bata da gashi ai sai
gyaran Allah"


Baki ta rike tana kada kai "anya yarinyar nan ba dabanci ta koyo a bodin din ba?"


"Ummi gang garesu fa na fitinannu inji wata kanwar abokina"


Daga cikin daki tana kuka ta leko "almunafunfun me ya kaika makarantar mata har ka
jiyo gulma. Ummi ta sani dai SS ne ba wata kungiya ba"


Tsawa Mairama tayi mata akan ta dena amfani da kalmomi irin wadannan ga kaninta.


Innawuro tace "kema kinsan yau tunda da amincewarki akayi askin nan to dukkanmu sai
ta nuna mana fushi take yi. Kai Karami zuba gashin nan a leda kaje ka kona.
Kwarkwata harda ta sayarwa."


Hannuwansa yayi saurin nadewa a kirji cike da kyama "kwarkwatar zan taba? Ashe kowa
zaiyi susa a gidan nan"


Dama Umminsa yake son tsokana ta fara fada yana dariya ya kwashe yaje bakin murhu
ya zazzage. Waje yayi bayan ya wanke hannunsa aka bar su Mairama su kadai a tsakar
gidan. Tayi zurfi a tunani da kwadayin ina ma ace zata iya ganin kamanin yaran a
yanzu da suka kara girma. Alheran da Zayyan dinta suna da shekaru sha takwas da sha
bakwai.


"Radhiya kyakkywa ce kamar wata dan daren goma sha hudu, Karami kuwa yadda kika san
sojan maigidanki ba maraba sai haskenki da ya dauko"


Murmushi Mairama tayi kunya na kamata "Innawuro me ya kawo wannan bayanin kuma?"


"Daga yin abin arziki, godiya kawai zaki yi tunda na faranta miki"
Karamar dariya tayi ta lalubi sandarta ta tashi. Yanzu ta gane hanyar dakunan gidan
ko babu dan jagora. Nasu ta karasa tana mitar wane irin jan kunne zata yiwa Alheran
mai tambotsai. Kwanansu hudu tun washegarin dawowarta daga makaranta wai a saya
mata form din makarantar sojoji. Tun Mairama na daukar abin wasa sai ga zance har
kunnen su Ardo. Shine aka fara zancen aurar dasu. Ita kuma tana da burin Radhiya
tayi ilimi mai zurfi amma bazata iya watsa musu kasa a ido ba. Tunawa da tayi anyi
aski yau gidan kowa mai laifi ne a wurin 'Yar soja ya saka ta dariya ba shiri.


**********



Hadir sai tunani yake yi ina zasu je bayan masallaci maimakon su wuce gida. A motar
kaninsa da yake kaisu sallar juma'a suke tare da Ibrahim. Yau sababbin kaya Ibrahim
din ya saka masa iri daya da nasa, yadi ne mai kyau da laushi ruwan kwanduwar kwai
anyi musu dinki iri daya wanda akayi da zare coffee color. Hatta hulunansu iri daya
ne masu kalar zaren dinkin. Sai kamshi suke bazawa sunyi wani irin kyau. Tarin
tambayoyi fal a zuciyar Hadir tun da aka fara komai. Mai aski har gida Ibrahim ya
kawo yasa yayi masa gyaran fuska sabanin da da yake masa a gida da clipper da
Zainab ta siyo masa.


Sun taimaka sun dora shi akan kujerarsa wheelchair bayan sun shiga gidan. Daga
gefen matattakalar shiga anyi shafen sumunti alamun hanya ta hawa da wheelchair
din. Gangara babansa yayi cikin ni'imtaccen falon da ya wadatu da sanyin AC da
kamshi. Daga nan kanin Hadir yayi musu sallama ya juya abinsa.


Idanunsa na nuni da tashin hankali sai waige yake yi Ibrahim ya barshi ya nufi
bakin wasu steps hudu da za'a taka abi hanyar dakuna. Su ma a gefe akwai wurin tura
kujerar.


Wai kunya ce ta hana Zainab fitowa tana jinsu ta makale a daki. Ibrahim na taba
kofar ta taso da wayoyinta a hannu kamar fitowa dama zata yi.


Wani kayataccen murmushi yayi mata na jindadi "Mama kinyi kyau wallahi"


Irin yadin jikinsu ta saka. Hatta zaren dinkin iri daya ne nata doguwar riga anyi
mata surfani siriri mai kyau adon. Daurinta shima yayi kyau ga sarkar gwal dasu
awarwaro. Haj Zainab kenan mata a gidan Hadir.


Murmushi tayi sai kuma tace "Wuce muje ni"


"Fara zuwa Mama naji cikina yana juya min"


Bai jira ta amsa ba ya fita da sauri ya shige sabon dakinsa ya dire akan gado yana
murna. Abokinsa ne ya bashi shawarar kada ya tsaya musu a ka ya barsu su kadai.


Hadadden kamshinta ne ya fara zuwa hancin Hadir kafin yayi tozali da Zainabu
Abunsa. Rufe ido yayi ya sake budesu a kanta. Wai da gaske Zainab ce kuwa?
A nutse ta iso har gaban kujerar tasa sai ta durkuso ta daidaita fuskarta da tasa.
Hawayen farinciki ne ya sauko mata shi kuma idanunsa sunyi ja ya kasa dauke ido
daga kanta.


Hannu tasa a kasan habarsa ta dago kansa tana masa kallon ido da ido ta sumbaci
bakinsa sannan ta rungumo shi a jikinta tana mai kankame shi sosai ta saki kuka.


Hamdala Hadir ya rinka yi a jejjere a zuciyarsa don ya tabbata abu daya ne ma'anar
kawo shi nan gidan da kuma kasancewarta a cikinsa.


**********


Danginsu Major na kusa da na nesa sai tururuwa suke domin ganinsu da yi musu barka
da dawowa. Shekaru a kalla sha hudu ba wasa ba. Anyi haihuwa anyi rashi duk basa
nan. Gidan kullum a cike da baki. Satinsu biyu kafin suka samu damar kai kayansu
sabon gidan da suka rinka turo kudi domin ginawa a GRA. Sun sayi filin tun farkon
fara aikin Mami kafin abubuwa su kara tsada.


Kwanansu biyu suna aikin son ganin gidan ya dau saiti abu yaci tura suka hakura
sai sun dawo daga wurin su Hadir da Mairama.


Wannan Sojan mai alkawari da suke turawa kudin Mairama shine ya binciko musu Hadir
yana Kano gidan iyayensa. Major yayi ta mamakin to me ya same shi yake gida.
Mairama kuma wan Zayyan wato Maikudi tun a baya yace masa tayi aure amma Alheran
tana Sakkwato wurinsa. Da wannan suka yi amfani akayi shawarar Kano zasu fara zuwa
sannan su wuce Sakkwaton.


Basu riga sun sayi mota ba Daddy Harun da yake Abuja yanzu shine ya basu wata bus
fara mai kyau da iyalinsa ke amfani da ita wurin tafiye tafiye tare da dreba.


Doki da fargabar yaya rayuwa ta kasancewa bayin Allahn nan sun cika zukatan su Mami
da Major. Zahra da Fauziyya suna ta kokarin tuna Antinsu Zainab da Ibrahim da suke
fada akan daukarsa. Babu wadda tayi shekara goma cikinsu lokacin. Labaran duka
wanda Mami ke basu ne don babu abinda suke tunawa. Awwab kuma tuni 'yan kwanakin
hutun nasa ya cinyesu a Katsina gashi tsarin aikinsu ba na zama wuri daya bane.


Da tambaya Allah Ya kaisu gidansu Hadir can cikin lungu. Bayan gaishe gaishe da
iyayensa Major ya gabatar dasu. Sai da ta share hawaye tace yau kwanansa ashirin da
shida da barin gidan an mayar da aurensa da Zainab tsohuwar matarsa.


"Bangane ba, da auren nasu ya mutu ne?" Yayi mata tambayar don neman karin bayani.


Murmushi tayi masa ganin hankalinsa ya tashi "Bari dai nasa a kaiku can gidan nasu
sai kuji daga bakinta"
Wayar Zainab tasa aka kira mata bata shiga saboda suna asibiti. Kwanansu biyu da
aure ta mayar dashi asibitin koyarwa na Kano wato Aminu Kano Teaching Hospital.
Gwaji da bincike tasa ayi masa sosai inda aka gano matsalar da ya samu a kashin
bayansa yayin fadawa wannan kwazazzabon a Liberia ita ce silar mutuwar jikinsa
kashi ya danne wane bangaren na lakar bayansa. Rashin magana kuwa Likita ya
tabbatar mata da cewa shock wato firgici ne ya haifar dashi. Da ace tun a baya sun
tsananta dabarun dauke masa damuwa kila da tuni an manta da ya taba dena magana..


"Duk da haka Hajiya mijinki zai iya samun lafiya amma shawara mafi a'ala gaskiya ki
fitar dashi ko da Egypt ne idan da hali. Lalurar ta dade a jikinsa yana bukatar
kwararru a kansa da ingantattun kayan aiki"


Kallon Hadir tayi ta saki murmushi "Doctor ka taimaka ka tayani duba asibiti da
kuma rough estimate na abinda zan bukata"


Bata ankara ba ta bayan kujerar taji an rungumo wuyanta sosai ta sa hannu tana
dukan hannayen Ibrahim "dan gidanku shakeni zaka yi?"


Hadir yayi murmushi suna bashi sha'awa zamansu tamkar kaka da jikanta. Ibrahim
dinsu matashi ne wanda kana kallonsa sai ka sake bare yanzu da mamansa ke kara
wadata shi da kaya sa suka dace da zamani.


Kin sakinta yayi yana kara manna kansa a wuyanta "Mama mungode injini da Babana"


Kwalla taji

32 / 99