Advertisements
Chapter 10 Reading Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   10 / 87

27K to 30K   out of 258.3K words

fadin ni kenan
zan zubawa kai na ko.
Mikewa nayi nabi bayan shi zuwa falon yana zaune na zuzuba mai komai harda
gaiyya nayi wurin zubawan amma duk haka sai da ya lasheshe kaf.
Ya mike ya dan shiga daki zuwa can ya fito ina jin lokacin da ya fita ya bar
gidan.
Fitan shi gidan yasa ni sauke ajiyan zuciya namile nafito na fara dan gyaran
gidan na murda kofan dakin shi na jita a kulle nace kai ka sani.
Naga komai na dawo falo na zauna ga tv amma inajin tsoron kunnawa yazo yace
wayace in taba mai kaya.
Kewan gida ya dawo min a rai na zauna ina tunane ina kukan rashin yan uwana da
nayi kusa dani.
Na saba a gidan mu in gari ya waye hayaniya kawai ya isheka tun safe har dare
ihun yara ne zai tare ka a gidan.
Gashi yanzu nazo nan garin da bansan kowa ba ina zaman kadaici duk da unguwa guda
muke dasu gwago na sin amma har dare yayi babu wanda ya sake zuwa wurina bayan yaya
saad duk da kuwa tana da yara yan mata zasu girmay ni ga shekaru.
Ko da yake nasan wanan sana, a da takeyi bazai basu lokacin samun zuwa yawo ba
ko wani lokaci.
In gari ya waye tun karfe hudu idan ta tashi bata da lokacin komawa kuma yi wanan
sauke wancen har dare .
Jama, a sai shige da fice suke a gidan wanda akasarin su hausawa mazauna lagos da
ke zuwa sayen kayan iri na arewa da babu shi a can.
Yaran ta mata ko wace nada aikin da zatayi nata cikin sana,a da take suna taimaka
wa uwarsu dashi.
Suma mazan kakani ba a barsu a baya ba wurin bada nasu taimakon in ba haka ba
yaro ya gane kuren sa ta hana mai kudi.
Yau ma kamar jiya bai dawo ba ina jin barci na ja kofan dakin da nake ciki na
rufe kwantawa nayi na makure a wuri daya cikin tsoro.
Karfe biyu saura naji ya dawo gidan a cikin mayen shi da yasaba ina jin shi yana
ta surutain shi da banke banken kaya ban dai fito ba balle.
Can nabar jin motsi haka yasani n yayi barci kenan Allah ya kyauta nace tare da
gyara kwanciyana dakyau sai dai babu barcin kwarai gare ni.
Da asuba na fito in yi gyaran falo sai ganin shi nayi tirim kwace tsakiyan falon
yayi amai da fitsari ya bata wurin dashi.
Take idanuwa na suka kawo hawaye nasihan da akai min ne yazo min a rai a hankali
na juya zuwa ciki na dauko abin kwashewa na fara gyara wurin da ya bata nai nisa
da gyara motsina ya tayar dashi.
Daga barcin naga ya mike kata kata zuwa ciki nan naji dadin tsabtace wurin da
kyau ina yi ina kuka da addua a cikin bakina hawaye nata zuba min.
Nagama na shiga na dora girki abin da zamuci don nasan da ya tashi abinci zai
nema in banyi kuma iyayyena su sha zagi.
Har nayi na gama ban ji motsin shi ba na shige nai wanka na fito bayan na gama
gyaran jikina na fito do in debi abinci in ci ga dai abincin na diba sai na tasa
shi a gaba na kasa cin koda cibi daya ne.
Nai zurfi ga tunane najiyo motsin shi daga dakin shi lokacin har karfe takwas da
rabi saura na safe rana ya soma fitowa a gurguje ya fito yana sauri.
Ina kwana nai mashi ya amsa a dakile kamar wanda baya son amsawa bani abinci na
yace dani ya nufi wurin cin abincin kai tsaye a ranan nasan wai ashe yana aiki ya
makara saboda ya bugu a daren jiya.
Nidai na zuba mai na koma daki yana ci ya fice a gidan ban sake jin duriyan shiba
kuma har rana ina zaune ni kadai a gidan nace barin leka waje inga yanayin uguwan.
Uguwa ne irin mai jamma, a din nan da yawa kowa na harkan gaban shi ba ruwan
wani da wani kowa tashi ta fisshe shi din nan.
Na dan duba yanayin na koma ciki tare da jan kofa na rufe kwantawa nayi sai barci
ban tashi ba sai biyu da rabi.
Na tashi ina salati don makaran da nayi wurin yin sallah na dade zaune ina adduoi
na neman tsari da mafita ga Allah.
Na tashi nafito duk da akwai dan sauran abinci amma sai da na girka wani na
rufe.
Don ina gudun ya dawo ya hauni da masifan don ni yanzu tsoranshi nake ji sosai
gani nake zai zo ya samay ni da duka idan ya je ya shawo.
Na gyara gida na dawo falo na zauna can dai nace barin kuna tv in kallo ina
kunnawa yana a wani tasha da aka badala iskancin filin Allah maza da mata.
Da sauri na kashe karshe ma a mike daga falon na koma daki na zauna ba wani aiki
a gareni sai na tunane.
Sati na guda a kidan muna wanan zaman in ya fita run safe baya dawo gida sai dara
ya raba idan zai shigo kuma a buge zai dawo gidan.
Tun ina tsoro har na fara sakin jikin na na saba da zaman kadaci ba mashigowa
nima bana zuwa wurin kowa.
Duk da zaman da muke yi dashi tun ranan da yai mai da fitsari nakwashe ta rage
zagina da tattara sai dai ba sakin fuska ko kadan a wurin shi.
Nima dai hakan ne a wurina daga gaisuwan safe zan ja bakina na tsuka sai kuma
wata goben in Allah ya kamu lafiya.
Yau ma zai fita na gyara gidan nake rokon shi da ya kunna min tv zaman kadaici ya
isheni har zai yi magana komay ya tuna sai da ya gama jan rai ya hada ya nuna min
yadda zanyi.
Ya fita ina zaune ko ina zaune ni daya kallo ya dauke min hankali wani indiya ake
yi mai ban tausayi kofa naji ana bugawa.
Nai mamakin jin bugun kofa a lokacin na tashi na saurara kofan ake bugu a hankali
na bude kofan.
Sisters din shine su biyu tsaye a kofan na tare su da mutunci sai naga suna
amsawa dakyat suna wani yamutse fuska.
Nace sai yau anty ?
Naji sadiya tace min tauuu,
Na sake cewa ina su gwago suna lafiya ?
Ta amsa da lafiya kalau.
Nace dasu ku zauna mana.
Sai naga sun kalli junna su kamar ba zasu zauna ba sai dai suka zauna din
kitchean na wuce na fito da cups da goran ruwa na kawo masu.
Ita dai habiban ko magana bata son yimin nace dasu bissimillah ga ruwa sai naga
sun kalli juna sun tabe fuska .
Sadiyan tace bar ruwanki dama mu hanya ya biyu damu nan muka ce bari mu biyu
magani ko yaya yana gida mu gaisheshi.
Nace yana wurin aiki sai daren ya shigowa habiban tace ke sadiya mu tafi don
Allah hakan haka auka fice nabisu da idanuwa cike da mamaki yan uwan nawa kenan
kuma yan uwan miji na.
Da wani zanji a raina wai da nashi ko da nasu tsiyar da naga sun fara nuna min
ina ce wurin su zan ji dadi ashe abin ba hakana yake ba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , ,


9️⃣
🧕🏿


DON ALLAH YAR UWA KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA DON BA A YAFE BA DON ALLAH KI
YI HAKKURI DA HAKKIN WASU, , ,



A kwana a tashi zama yai tafiya saida babu wani jin dadin aure a gare ni kullun
zaman hakkuri nake yi garama da zaman gidan mu mai wahala da wanan zaman ukuban da
nake cikin sa yazu.
Ko ba komai a gidan mu ina ganin iyayyena ina jin dadi da yan uwa na nan ko haka
zan wuni banyi magana da kowa ba na tsawon kwanaki.
Sai da na cika wata biyu cur a gidan ranan yace in shirya zamu tafi gidan su da
farko murnan zuwa nayi sai kuma na tuna da abinda yan uwan shi sukai min sai murnan
ya koma ciki.
Don yanzu ma ban san abinda zanje na sama a gidan sai dai nasa a raina cewa zan
kama kaina da sha, anin su a rayuwa na.
Na shirya cikin cotton lace light green mai yan duwatsu kanana sai hijjab dina
da na saka a falo na samay shi yana jiran fitowa na.
Simi simi na fito tare da cewa gani yaya mikewa yayi yana mai kare min kallon
muka fita nasan kwalliya na ne bai kashi ba.
Don shi indon ta nashi ne baiki ace na fita ba hijjab a jikina ba ko na yafa dan
gyale a kafada na mu fita yafi son na fito yar bariki sahihiyar ta amma ni na kasa
yin hakana.
Mun shiga kwanan gidan tun daga nesa muka hango jama , a masu sayen abinci sun
cika wurin sai ya dan ja ya mota ya tsaya nesa da gidan na su.
Yace cikin wani murya ke ki saurare ni kiji may zan fada maki dakyau hakan danaji
yasa na natsu ina sauraren shi.
Yace bani son naga kin fito waje inda suke sana a ar su din nan kuma ki tabbatar
kina saye da wanan abin har mu fito cewa hijjabin kenan.
Duk kika yarda na ganki wurin wanan sana an ran ki zai baci ki kama kan ki da
dabiun wurin nan a sanyaye na amsa da to yata da mota muka karasa gidan.
Maza da mata a waje sai cin abinci suke yi tuwon shinkafa miyar ganye da agushi
sai kamshi ke tashi.
Tunda muka tsayar da motar mu yan wurin suka sako muna idanuwan su da kallo maza
da mata yan duniya.
Nan aka fara yi mai kirari da sunan shi na tan bariki nidai daga kafa nakeyi amma
ji nake kamar zaa ce ke in sheka da gudu.
Wani rumfa muka nufa inda gwagon nawa take ciki ga yan matan ta nan gefe daya
suna kidayan kudi sunci kwalliya sun kure adaka.
Duk yawan taron nan dake ciki bai hana ni zuwa gaban ta na durkusa ba in gaishe
ta sai cewa tayi yau kun ga daman zuwa ku gaida ni koda yake baki da laifi ai ga
mai lefin nan gaban ki.
Bai bata amsa ba wata maidan buje tazo ta run gumay shi sai yaja hannun ta sukai
waje suna rike da junan su.
Nauyi da kunya suka kamani tace tashi ki zauna dan duniya ya hadu da mashiririta
yan uwan shi.
Na juya inda sadiya take ina gaishe su don ko banza sun girmay ni ga shekaru.
A dakile ta amsa mim gaisuwa sai ga wata yar fara mai dan buje tazo da hausa ta
gwargwari tana cewa a wanan ne amaryan tamu.
A gaskiya hardguy ya iya zabe mace Allah yasa a zauna lafiya amarya sai hakkuri
da mutumin fa don naganki yarinya karama shiko gashi tsohon tazuru.
Cikin wani murya gwago tace da ita salima me i no wan dat wooo sai salima tace
sorry ma.
Nace ashe su gwago tsofin bariki ne har da turancin go and come an iya a raina
nake fadar hakan wata yar baka mace tazo ta katse min tunane da cewa.
Wai ki shiga ciki inji hardguy saina rashi na bi bayan ta ina jin habiba na
mata magana sai dai ban fahinci may take fadi ba.
Ina nan zaune sai gata ta dawo tana cewa may za a kawo maki ne murmushi nayi
nace a a barshi na gode a koshe nake ai.
Sai mamakin wanan rayuwan nake mace da auren ta tara kananan yaran mata a gida
ana shar holiya wai da suna neman kudi.
Zuwa can ta dawo dauke da abinci a cikin tire tana cewa yace in kawo maki wai kin
dade baki ci abincin hausawa ba ta sauke tire din naga tuwon shikafa ne da miyan
alaiyahu ya ji agusi da naman shanu tace dani ko baki sin wanan akawo maki na
yauki.
Murmushi nai mata nace a, a barshi kawai ko wanan ma na gode ai sai ta kashe
murya tana dan waige waige tace mijin kine ya saya maki indon hajiya ne har kizo ki
tafi bazakici komai ba a nan.
Kin santa da shegen son kudi koda yake ke bakuwa ne a gidan baki san komai ba
tukun tun tafiyan ta ina zaune ni kadai ban kuma taba abincin ba duk da ina son ci.
Can sai gata ta dawo dauke da kwalban coke a hannuta mai sanyi ta dire min tace
kina nan zaune ke kadai ba, yi hakkuri dan Allah hajiya bata tasowa yanzu sai ta
rarage cinikin ta.
Ina nan zaune sai ga sadiya ta fara shigowa gidan cikim gidan daga wurin sanaar
su tace a, a kina nam zaune na ashe.
Murmushi nai mata kawai sai ta dan fara rage kayan jikin ta zuwa can ta kai kallo
ga abincin dake aje a wurin sai take cewa a, a baki ci abincin bane.
Aikoda kin ci abincin ki don mijiki yau yana can ya samu yan matan club suna
sharholiyan su dama ya dade baizo ba sai yau.
Wani irin naji a raina amma na dake a fili cewa nayi abin da suka sabayi ne yin
hankan ya zamay masu jiki ko.
Ko bata fahinci may nake nufi bane sai naji tace min bari in debo mai zafi nazo
muci tare tunda naga kina jin kunyan ci.
Nace aida kin bari naci wanan din bata saurare na ba ta fita sai gata ta dawo da
wani abincin wanan karon miyar danyan kubewa ne ta debo muna.
Tare muka zauna muna cin abincin muna hira sai na fahinci bata da matsala ita
har take cewa dani tankan so zuwa gidan mu amma sai take tsaro kamar nace mata
tsaron mai sai dai na kyale ta kawai.
Nan na taya ta sance kanta da ya tsufa da kitsu nai mata wani kitsun duk wace ta
shigo ta samu muna kitsun sai ta yaba da kyan kitsun da nai mata.
Nan sukai ta fadan zasu zo in masu kitsu a gidan suma habiba dai ko kallo ban
isheta ba sai
A wurin ta nake jin wai yaya saadu yai tafiya dama shi ba mazauni gida bane yana
zuwa kasa ibom neman kudi ne a can.
zuwa can gwago na tashigo daka ciki lokacin ina masu shara son ko lokacin gyaran
wuri basu dashi.
Kullun ana aikin naiman kudi a waje koma nasu kaca kaca a gidan yake nai ma wurin
tas na kama na wanke wa na wanke.
Saida ta samu wuri ta zauna a dakin nata wanda na share kale kale take bin dakin
dashi ta kwala min kira ina bakin famfo na amsa nazo.
Nazo na durkusa gabanta sai tace dani kwanaki na aika yaran nan gida ku kikai
masu rashin mutunci su da gidan dan uwan su.
Ni har na aika a dibo min dana kice wai barci yake baki tashe shi ke har yaushe
kika san dadin miji kega mai miji.
Sai sadiya tace mama na fada maki fa ba haka tace ba tace da sadiya ke rufa min
baki yar uwar takine zatai mata karya ko may ?
In dai zurian Rabi ne wani irin tuggu ne basu iya ba matar da kullun cikin kullin
sheri takewa kishiyoyin ta ta hana su shakat a gidan.
Na dago kai na kalle ta don jin kallaman da ta fadi gamay da mahaifiyana sai tace
eh mana.
Ko kina nufin bansan shirin da kukayi akaina bane dashi kan cewa zaki shigo ki
mallake min da sai a baninda kuka ce da ke da uwarki a kan shi.
Na dukar da kaona hawaye na tsiyayo min a fuskana ganin ina kuka tace a hasale
karya na fada ke nan ko kina nufin nai maku sheri.
Nace haba gwago wallahi tallahi bansan komai ba akan haka, sai habiba tace
wallahi karya kike yi an ina jin ki ranan daurim auren ku wai suna maki huduba
Ita ta fada habiban ta fada haka suka sani a gaba da zagi kamar ba yar dan uwan
ta nake ba shi babana yai mata halarci ita kuma tai mai son ranta
Kwasan ya fado dakin kamar wanda aka turo ganin yadda nake nake kuka da rantsuwa
a gaban mahaifiyar shi da habiba nata yanka min zagi.
Cikin mamaki yake kallon su ya kalle ni yana son jin abinda ya faru haka suke min
masifa ina kwasan kuka.
Sadiyana ta fara mashi bayani sai uwar ta katse ta jikin shi yai sanyi ganin
yadda nake kukan da rantsuwa sai zagi suke zubamin.
Ke tashi muje hakana yace dani ya dubi uwar yace muzamu tafi don banga amfanin
yin hakan da kuke yi ba .
Simi simi na miki na jawo hijjab dina dake rataye ga igiya na saka ina fadin sai
amjiman ku itako gwago sai faman fada takeyi tana cika tana batsewa.
Nan ya biyo ni baya ranshi yana mai suya yasani sarai safiya ba zatai wa yan uwan
shi haka ba sheri yaran suka kulla min wurin uwar su tun ranan da yazo ta fada mai
ya samani da maganan nai mashi bayanin komai ya yarda
Nika sai faman kuka nake ina tunane a raina wanan wace irin kiyayya ne haka may
ne mata a rayuwan ta take shirin nakasa ni.
Har muka isa gida tunanen maganganun su nake akaina may nai mata a rayuwa na take
son gani na a cikin ukuba can na nisa nace Allah ya fata duk abinda ya shirya zai
samay ni babu makawa sai ya faru dani .
Na share hawaye na na mike zan shiga wanka ya shigo dakin yana fadin may ya hadaki
da su habiba ne na ce babu komai nidai a rayuwa na.
Sai yai min wani

10 / 87