Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
Tace kin san girman laifin da kika aikata kuwa yar nan ai sai baka son namijine
kake gudun haihuwa dashi nace shima yasan ai bada wata manufa nayi ba mommy kawai
dai lafiya na nake jawa .
Amma ni ba wai don ban son haihuwa dashi bane kawai dai haka Allah ya nufa sai ya
faru a tsakanin mu yaki yarda ya saurari manufata kuma.
Maza fa a sannu ake binsu diyar nan don Allah ya riga ya basu girma a kan mu ki
lalaba mijin ki ku zauna lafiya yadda kuke yafi.
Hindatune ta shigo daukan Abba a lokacin ban koma daki ba na nufi kitchen don
shirya ma hajiya abinci sai dai ban san ko su nawa zasu zo ba kuma.
Kafin su dawo nayi nisa ga aiki sosai don da Nura muke aikin abinci nagama
abinda zanyi na fito kara gyara gidan su maimu na taya ni.
Mun hada komai zuwa hudu hudu da rabi suka iso gidan yafita a lokacin dakin da
aka gyara masu na kaisu ita da anty suwaiba sai yan matan ta biyu da tazo dasu.
Mun gaisa na tambaye su sauran yan uwa suka ce duk suna lafiya abinci na gabatar
masu sai da sukai sallah suka zauna ci .
Ban koma wurin su ba na barsu su dan huta don sun kwaso hanya mai nisa dakina na
koma na dan kwanta kadan don na gaji a lokacin.
Cikin yan matan da suka zo da su ne daya tazo ta kirani.
Na samu har sunci abinci ko na shigo dakin dayar yarinyar naa kwashe kayan
abincin daga dakin tana kaiwa kitchen baaba yaya gajiyan hanya nace bayan na kai
zaune kasa gefen gadon.
Garin nan naku akwai nisa yar nan shiyasa ban sa kaina zuwa ba tun farko ko yanzu
don naji ance kinyi fama da jikine har kin kwanta asibiti koda yake ke da ke da
mijin nake ba fadar ciwo kukeyi ba.
Ko sannu akace maku ai an rage maku ciwo a daidai lokacin uncle ya shigo dakin
yana fadin sannu ku da zuwa naje dan nesa shiyasa ban shigo da wuri ba.
Bata fasa maganan da takeyi tace idan shi bai fada min ba aike kya gaya min
tunda muna waya kusan ko yaushe dake.
Zaune yakai kasa shima don mika gaisuwa ga mahaifiyar ta shi cikin girmamawa ta
amsa mashi tana ci gaba dayi muna fadan rashin fada mata matsalar mu da baya yi.
Yace aiyi hakkuri baaba ai ta dade da samun sauki dama ba wani matsala bane
sosai ke damun ta a raina nace ka fadi hakan mana tunda cikin ba ajikin ka yake ba
ai.
Allah ya sauwaka tace muka amsa da amin tace Safiya kije ku bude tsaraban nan kada
su lalace a saka a fridge nace baaba har da dawainiya aka zo muna kuma ?
Kin jiki da magana ina dawainiyar yake anan ni mai gida na nayowa tsaraba dama ba
ku ba yar uwar ku dai ta kawo maku tsaraba.
Ina mikewa nake fadin baaba ba a zo da maryam na dai tace maryam din nan tana
fama da laulauyin ciki bata iya zuwa ai taso ta biyo mu hakana hanata nayi.
Nace Allah sarki ashe zamu sha suna idan rai ya kai mu lafiya tace a toh zaku sha
kan don wanan cikin ma ya zo mata da matsala sosai wallahi ba kamar wanda take a
baya ba.
Yace dama ai haka ciki yake ko wani da kalar tashi zuwan fita nayi daga dakin na
nufi inda kayansu yake yan matan na zaune falo da su maimu suna hira.
Da dare na shirya bayan na idar da sallah na shiga dakin nasu suna ciki dukan su
muka gaisa na samu wuri na zauna muna fita da anty suwaiba hajiya na lazimi saman
carpet din sallah har lokacin.
Ya shigo cikin jallabiya baka sai kamshin turare yake yi yace ke kije ki kama
yaron nan haka na yau mommy bata jin dadin jikin ta.
Mikewa nayi na bar dakin ba tare da nayi mashi magana ba zuwa kama Abba din dake
ta kuka a dakin mummy baaba ne ta shafa ta juyo gare shi tana fadin kullun ina fada
maka kabi yarinyar nan a sannu.
Ji yadda kake faman daure mata fuska babu walwala a tare da ita duk tabi ta fige
ta koma wata iri jikina yayi da bayan shi a bango yana fadin ni bani na fige ta ba
baba halinta ne ya fige ta.
Dan kallon shi tayi kamar harara tana fadin wani hali ke ga wanan yarinyar banda
kai dake son takura mata a kullun hakan da kake wallahi tun tana tsoron ka na fada
ma zata zo ta daina ne.
Wani matsi ai bai da kyau wallahi idan yayi yawa ya danbala mutum ko ya hinjira
shi murmushi yayi yace yanzu kuma wani matsi nake mata.
Yarinyar da take gani ban isa da ita ina fadi tana fadi tace ba zan taba yarda da
wanan magana duk da karya ba haki ka bane a baya.
Hajiya yanzun haka ciki ke gare ta na kamata tana yunkurin zubar wa nayi magana
tason tayi min rashin kunya kuma.
Kira min ita suwaiba tace anty suwaiba ta tashi zuwa kira na muna kitchen muna
hira a can ta samay ni .
A daki kuma ce mata yake hajiya ban san may take nufi da yunkuri zubar min ciki
da take yi ba ka zauna kunyi magana ta fahinta da ita ka saurare korafin da yayin
hakan da tayi niya ?
Lokacin na shigo dakin nuna min wuri tayi alaman in zauna nakai zaune jiki a
sanyaye sai da taja dan lokaci tace min.
Safiya yanzu mijinki ke fada min wani magana da banji dadin jin shi ba sam na
dukar da kaina kasa sai haaaye tace Safiya may zai sa kiyi yunkurin zubar da cikin
jikin ki kuma ?
Har kin sa zargi ya shiga tsakanin ki da mijin ki yana zaton kin yi haka ne don
baki son shi ko baki son haihuwa dashi ?
Da kyat na dago kaina ga nauyi ga kunya dake cina nace ba hakana bane baba yaki
ya fahinci manufata ne a hankali na kora mata bayani na da dalilin daya sa nake
yinkurin cire cikin da farko.
Tace banda abinki ai komai na Allah ne Allah daya baki shine kuma zai raba ki
dashi lafiya ai kowa da irin tashi kaddaran rayuwa.
Sai kiga ke kin haife komai ba zai samu ba cikin hukuncin Allah wani kuma sai
yasha bakar wahala haka abin yake ga Allah.
Kinyi kuskure babba don kisan kai kika so kiyi ba don Allah ya gyara kin fahinta
daga baya ba kiba mijin ki hakkuri ban son irin yadda na samay ku din nan sam.
Ana maku kallon sha,awa daga waje a ciki kuma baku da jittuwa tsakanin ku abin
bai yi kyau ba wallahi kuna zaton wani bai san halin da kuke ciki ba to kirana
akayi aka fada min abinda kuke ciki a gidan.
Da sauri kowan mu ya kalle ta da mamaki tace eh ba dole bane in fada maku wanda
ya kira amma dole tasani tasowa in zo don in tsawa ta maku.
Dan shiru ne ya biyo dakin cikin sanyi murya nace uncle nayi kuskure ka yafe min
don Allah babu komai yace a takaice.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/22/20, 8:13 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , ,
8️⃣7️⃣8️⃣
🧕7️⃣8️⃣7️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Bayan baaba ta shirya mu ne abin ya danyi sauki sosai tsakanin mu kwanan baaba biyu
tare da mu a gidan bata tafi ko ina ba suka shirya komawa bauchi.
Ko gidan Aisha da kyat na samu ta tafi bamu dade ba muka dawo sai sahad store da
muka shiga ta dan duba abinda take bukata ita da anty suwaiba da yan matan ta.
Kudin da uncle ya basu shi suka sawo yan kayayankin fashion dashi a cikin saukin
farashi washe gari zasu tafi don haka bamuyi barci da wuri ba a gidan.
Da safe kuma na tashi nayi sakkon dora masu abin karayawa kafin su wuce saida
suka karya suka dauki hanya anan suka barmu cike da kewan su a gidan.
Sai gidan ya koma muna tsit bayan wucewan su zuwa azahar na shiga kitchen na hado
masan da nayi warming da miyar kassa na dawo falo na zauna kasa saman carpet ina
ci.
Mommy ta shigo falon masan takai ma kallo daga inda nake zauna ina ci a hankali
ina kallon tv take fadin wai ni na rasa yaya mutanen nan ke masan su yafi na ko ina
dadi ?
Nace da ita suna tsaya su gyara ne ko ke a gidan ki mommy idan zaki tsaya ki
gyara kamar yadda sukeyi zai koma ki.
Mommy ko na zubu maki ne na dago kai ina tambayan ta don nasan gwanace wurin cin
masa nawa mai dalili ne cin da nakeyi don saboda ciki nake cin masa yanzu.
Zama tayi tana jawo Abba zuwa jikin ta na fadin Abba bazakaci masan nan mai miya
ba don ruda ma ciki zaiyi nace bazan bashi bani idan kuna so ku debo naku ku dumama
kuci.
Zan jira yan matana suzo ne sai mu dumama muci don suma suna son masan nan sosai
nagani tace dama magana nazo muyi dake yanzu gaki kuma kina cin abinci.
Mommy may nene nace cikin dago kaina ina fuskantar ta ta ce ba wani magana bane
dama gani nayi tunda an kai karshen matsalar ku da maigidan ki .
May zai sa har yanzu baki zuwa gare shi kike baya baya dashi bayan kisan kece mai
laifi kuma an shirya maganan nan a tsakanin ku kuma kon kasa bashi hakkin shi har
yanzu.
Jikina ne yayi sanyi sosai da maganan mommy saboda ban dauka ta fahinci ban
shiga turakar incle ba dama don tana rigamu shigewa dakin ta.
Maganan ta yasani dagowa na sake kallon ta da tace indan kina haka kina cutar da
mijin ki ne da kan ki zamana a cikin ku kima baida wani amfani ke nan.
Nasiha sosai tayi min akan abinda nakeyi akarshe nace na gode mommy in Allah yaso
zan gyara mommy tace ki kulla don Allah diya ta.
Nace mommy ba wai ina share shi bane dama ban san may zai mun bane idan na
kusanci ida yake kin san shi bai iya fishi ya sauka maza ba.
Komai zai maki dole ki shanye don shine gaba dake kece a kasa don haka ki maza
ki shirya tsakanin ku komai ya wuce a tsakanin ku.
Mommy in sha Allahu komai ya wuce zan shanye duk wani abinda zai min kan hakan
koda bai hakkura da hakkurin da mahafiyar shi ta bamu ba zan shaye duk wullakancin
da zai min.
Allah yayi maki albarka da kika fahinci haka komai zai wuce da zaran yaga kin
bishi kin kara bashi hakkuri.
Banki ta mommy ba da na gama na gyara mai daki tsab na feshe da room fresh na
wanke ban dakin na rufo mai na dawo part dina.
Sai yama ya dawo gida lokacin muna falo zaune dukkan mu har mommy muna hira su
kuma suna cin abinci.
Ya shigo da alaman a gajiye yake na mike nabi bayan shi zuwa dakin bayan na kara
gaida shi na wuce ban daki hada mai ruwan wanka na fito ina fada mai na hada mai
ruwa ok kawai yace min yana duban wasu takarda a hannun shi.
Ban tsaya ba na fice a dakin na koma falo na zauna ya gama ya fito cikin kayan
da yake zama dasu a gida da alaman ya rufe fita ke nan yau din.
Gurin cin abinci ya nufa ya ja kujera ya zauna isowa nayi gurin ina kokarin bude
kukolin abincin da aka aje don shi a wurin.
Sai da ja zuba mai tuwon semo da miyar yauki Nura tayi muna na abincin dare ya
wanke hannun domin fara ci .
Daya daga cikin kujerun na jawo na zauna nima a wurin abincin shi yake ci hankali
kwance kamar bai san ina wurin zaune ba a lokacin .
Sai zuwa Abba ne wurin namu ya fara magana yana fadin babana kaci abincin kuwa
banga cikin ka ya cika ba shiko yaron kokarin daukan goran ruwan dake gaban shi
yake yi.
Yace zuba mai ruwa kila kishin ruwa yake ji baida bakin fada na zuba zan ba yaron
ya karba daga hannuna yana kokarin bashi yaron na kawar da kai sai goran yake son
dauka kawai.
Daukan yaron yayi zuwa jikin shi ya dibi abincin ya fara kai mashi a baki tare
da balle goran ruwan dake gefen shi ya kafa mai a baki sosai ya zuki ruwan daga
cikin goran ya cire bakin shi yana mai da numfashi sama sama .
Ina zaune gefe na harde hanayena ina kallon su hankali kance yadda suke yi ba
karamin son yara uncle keyi ba dole ya yi min masifa kan barar da cikin da nake
shirin yi din don ko banza ya kamata ace yana da yaran da suka kai biyar yanzu a
shekarun shi.
Ban ankara ba ashe ya dago yana fadin kin kuwa fara bashi maganin da hajiya ta
kawo mai nace cikin kada kai tun tana nan aka fara bashi sai dai bai son sha idan
an bashi sai da dare idan zai kwanta ake bashi.
Ke maimu dauko mai biscuit din shi ko zai ci nace biscuit kuma uncle da daren nan
zai iya saka shi kashi don ruda ciki yake yi.
Ba tare da ya kalle ni ba yace ke ke wankewa idan yayi ko ba za a bashi idan
yana so shiru nayi kawai ina kallon su mommy har ta mike ta shige tun fitowanshi
nasan kallo take a dakin ta.
Ganin ya gama na hada kayan zuwa kitchen sai hindatu ta taso tana tayani kwashe
kayan a wurin anan yake mata ba a tana murmshi.
Yau bai dade a falon ba ya shige sai dana dauki lokaci na gama hada mai blact tea
din shi na ganyen na,ana na samay shi a dakin.
Kamshi ke tashi a jikina sosai a lokacin yana zaune yana aiki a laptop din shi
tsab na gyara komai kafin in kwanta a bayan shi.
Bai daina abinda yakeyi din ba har wani lokaci ya rufe tare da mikewa ya nufi
bayi can ya fito ya zauna yana shan tea da na aje mai a bakin gado.
Sannu a hankali na dago daga inda nake nakai zaune ina fadin Uncle don Allah
kayi hakkuri ga abinda ya faru a baya ba munafata ke nan ba ga abinda kake tuhuma
na dashi.
Har tsawon wani lokaci bai mun magana ba nima ban sake magana ba ina zaune shiru
a inda nake a bayan shi cikin fargaba.
Sai can naji yace yanzu may kike son in ce tunda ke baki son haihuwa dani ni
kuma ina son haihuwa a rayuwana baki min adalci ba Safiya ban cancanci haka a gare
ki.
Baka yarda dani ba ke nan uncle nace akan may zan yarda dake yanzu bayan ba wani
ya fada min ba ni nagani da ido na a lokacin da baki zata ba.
Murmushi nayi nace to shi ke nan na dauki laifina tunda haka kake son ji a
bakina ko nayi kuskure a yafe min daidai yana kaiwa kwance yace min .
Magana daya ne yanzu inga kin haife cikin nan lafiya shine kawai zai sa hankali
ya kwanta dake nace har yanzu kana zargina kenan bai yi magana ba sai kashe muna
wuta da yayi yana gyara kwanciyan shi da kyau.
Nima komawa nayi na kwanta tare da lumshe idanuwa ina tunanen wanan hali na uncle
duk abinda ya kamata nayi dai nayi mai a yanzu.
Ban tsamanin jin hannun daya kai jikina ba a lokacin amma sai tunane na ya
kwance a lokacin may yasa maza suke hakane a wurin wanan fannin basu jin kunyan yin
haka ko wani lokaci suke da bukata.
Washe gari ban koma barci ba don yace yana da tafiya zuwa Niger state sayen wasu
kaya don haka na wuce kitchen don hada mai abinci da wuri kafin Nura tazo aiki.
Ina tsaka ga aiki sai gashi ya biyo ni da wayana a hannun shi da na baro dakin
yace yaya Saadu ne ke kirana a lokacin .
Nayi mamakin kiran yaya Saadu haka da safen nan na karba daidai lokacin daya kara
kirana din na dana wayan ina fadin ina kwana yaya .
Yace lafiya Safiya kin ga na kiraki da safe haka ko wallahi waya aka bugo min
daga gida da dare Allah ya karbi ran Ahmed jiya da daren.
Innalillahi wa inna alaihim rajiun ya rasu yaya yace wallahi safiya da dare jiya
suka bugo min waya yana tsaye daga kofa yana saurare na.
Na dago kaina na kalle shi ya tsure ni da idanuwan shi cikin son jin abinda ke
faru a lokaci a sanyayye nace wai yaya Ahmed ne ya rasu jiya da dare.
Waye haka na yace dani a sanyaye nace yayan yaya Saadu dana taba aura a lagas
Allah yai mai rahama yace yana wucewa zuwa dakin shi.
Jikina yayi sanyi na bishi da kallo dakin mommy na nufa a lokacin don fada mata
abinda ke faruwa damu duk ta rude dataji maganan.
Na dan dade muna maganan na koma kitchen na karasa aikina hakana a dadafe sai
tunanen zaman da mukayi dashi a gidan shi nakeyi.
Nashiga dakin bayan na gama komai na samu yana tsaye yana shiri har yayi wanka a
lokacin ga abin karyawavcan nace mashi sai kuma naja na zauna bakin gado har ya
gama shiri ban yi magana.
Tare muka fito a dakin nashi