Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
Allah ya bani lafiya sosai dana samu kwarin yin abinda ya kaimu
kasan mai tsarki ranan da aka sha ruwa washegari muka fara shirin komawa gida .
Ban samu zuwa sayayya ba shida wani abokin shi da matar shi suka tafi sun ko
sayo muna kaya masu kyau koni naje da kaina iyakar abinda zan sayowa kaina ke nan.
Jirgin mu ya sauka lafiya a Abuja inda su yaya saadu suka zo taron mu da dawo
kallo daya mutum zai min ya fahinci na samu sauyin rayuwana.
Na murje na zama wata katuwa na kara girma da cika ta ko wani sassan jikina
haskena na asali ya fito sosai a jikina.
Rigar dake jikina ya biye cikin jikina sai may kaifin tunane ne zai gane hakan
gare ni da sauri amma wanda bai san ciki ba sai yace na samu lafiya ne kawai.
Na dan jirkita don zaman jirgin da nayi don haka hutu kawai nake bukata a lokacin
don tafiyan dare mukayi muka iso da safe.
Don haka muna shiga gida sallah na gabatar sai na samu wuri na kwanta sai barci
da zazzabi mai karfi ya rufe ni ga samira da su Aisha duk gidan amma ban samu zama
dasu ba a ranan.
Sunzo sun fahinci banda lafiya haka yasa jikin su yayi sanyi sai kuma aka shiga
yi min sannu ina dunkule a cikin bargo shi yashi ya bani magani na sai barci ya
dauke ni.
Ni dai har suka watse gidan ban sani sai mummy maman samira da yarta aka barmin
so zauna dani a gidan sai da nayi kwana biyu sannan na samu zazzabin ya sauka min.
Na fito falo da yamma na zauna don jikin nawa ya dan kara sake min sosai ya shigo
gidan anan ya samay mu zaune muna dan hira jefi jefi dasu.
Zama yayi a kusa dani yana gaida mummy da gida sai ya juya inda nake yana fadin
jiki ya jikin madam ?
A hankali irin mutum ya tashi ciwo yadda yake ji nace mai naji sauki tare da
lumshe idanuwana a hankali.
Mummy dake gefena zaune ta nisa tare da fadin amma sai ina ganin kamar wanan
madam din ta samu karuwa ne don tun ranan da kuka dawo nake ganin haka a gareta.
Uncle yayi saurin dago kai ya kalleni na dukar da kaina kasa yace mummy na magana
dake fa.
Nace aiba dani take magana ba dariya yayi ya gyara zaman shi yana fuskantar
mummy din sai dai ina ga in jikin bai bari ba zuwa gobe sai mu koma asibiti.
Da sauri nace mashi ai naji sauki ba gashi na fito ba yace kin ci abinci nace kai
nake jira ka aika a sayo min fruit in sha.
Mummy tayi saurin cewa bana fada maka ba wanan ciwon nata da walaki a cikin sa
mutum yace baicin komai sai diyan icce kawai yake dura ma cikin shi.
Ya dan kalle ni yayi murmushi yace mummy ko acan shine kawai abincin ta duk
abinda taci sai ta amaye shi shi kadai take ci a zauna lafiya.
Mummy ta sake cewa ai duk wanda yasan ciki ya kalli Safiya yasan tana da ciki
ubangiji ya raba ku lafiya yaba rayayye mai albarka ya amsa da amin da sauri.
Mikewa yayi yana fadin barin in sa a sayo maki yanzu ki samu kisha ko jikin zai
kara sakewa yace mummy dai ta gano abinda kike boye masu.
Murmushi nayi kawai idan yaso wasa sai ya juye kamar ba shi ba a gidan amma indan
yan kai na saman kan shi zaifi sati daya yana dunkulan baki rai bai magana da kowa
bayan gaisuwa.
Ni yanzu na saba da halin shi don haka duk irin yadda ya juya nasan yadda zan bi
dashi a zauna lafiya masan mun dawo gida yanzu halin zai tashi mai.
Don a can ko yayi fushin bai jimawa yana yi zai sake mu koma daidai amma da zaran
naga ya fara daure fuska nima sai in kama kaina dashi.
Washe gari ne mukayi baki daga bauchi inda yan uwanshi ne mata zallah hajiya
baaba taba mota wai su zo su dubani su kuma ga sauksn mu.
Basu fada muna suna tafe ba sai ganin su mukayi Allah ya taimake ni mummy na
gidan kafin wani lokaci tayi masu abinci mafi sauki don har Nura ta tafiko yamma
yayi.
Dole na mike haka na ba dadi jikin nawa muka shiga hidimar baki a gidan ya dawo
ya samay su don sun fita da yaya Saadu a lokacin .
Yayi murnan ganin su sai dai tunda suka gaisa ya shige dakin shi bai sake fitowa
ba sai da naji shi shiru ne na leka shi dakin nashi.
Na samu ya fito wanka yana saye da jallabiya a jikin shi haka yasa na gane zai
fita sallah ne a lokacin yana gani na yace ashe baki gare ki haka gidan ?
Murmushi nayi don jin abinda ya fadi nace wallahi aisun yi kokari da suka zo
dubamu don basu taba zuwa ba sai wanan karon.
Gashi kuma naji suna fadin wai gobe zasu koma baaba tace dasu lalai su dawo a
gobe din yace kai haba ai ta bari su dan kwana biyu dai.
Nace to sai kayi masu magana ai suma zasu so hakan wallahi don akwai gajiya a
jikim su.
Tare muka fito ya wuce massalaci nikuma na koma daki na don inyi shirin alwala
sai da na bi ta wurin su naga basu bukatan komai na wuce bayan sun dan jani da wasa
irin ta kannen miji da akeyi.
Naji dadin kansan cewar mummy a gidan don tana da matukar kokari sosai bata jin
nauyin jikin ta ko kadan kamar ba ita ta haifi Samira ba, don samira bata kaita
kiza kiza ba.
Bayan na idar da sallah nan dai na dan kai kwance don yanayin jikin nawa da bai
gama sake ni a lokacin wanda nasan gajiyan aikin da mukayi ya dan tambaye ni da
zaman jirgi.
Yar uwa riban da kike samu wurin fitar da novel dina sai ki shirya dake da masu
karatun novel din sata don taki ta samay ki a rayuwa muje zuwa in dai kin ce wasa
da kallaman Allah kike yi .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/25/20, 10:38 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , , ,
6️⃣4️⃣6️⃣
6️⃣
🧕🏿 4️⃣4️⃣6️⃣
NOVEL DINA NA KUDI NE IDAN KIN FITAR ALLAH ZAI FITAR MIN DA HAKKINA AKAN KI IDAN
KUMA KIN KARANTA KI SAN HAKKINA NA KAN KI.
Yar uwa na fadi zan sake fada ban yafe ba idan kin fitar min da novel waje Allah
yabi min hakkina akan ki don bayan yafe ba.
Idan kin karanta min novel baki biya ba ubangiji ya kwato min hakkina a gunki
cikin gagawa.
Bakin mu sun tafi cikin dadin rai muka rabu dasu lafiya suna ta farin alherin da
dan uwan su yai masu da zasu tafi koni nayi mamaki don a yanda uncle yake bakacewa
yana da tarin arziki irin haka a rayuwan shi.
Kyaunta yamun dadi har cikin raina don yadda ya dauko yiwa yan uwa alheri ba
karamin alheri bane agare ni don na fita zargi daga bakuna su.
Yadda nake jin suna zagin anty kan ta kakace komai da karshe akaina zagin zai
dawo sai gashi ya sauya gaba daya wanda suke ganin wai nice na sauya shi hakan.
Ko yan uwana bai bari ba don kullun aiken shi na hanya zuwa wirin yan uwana da
iyayyena sai dai inji sun bugo waya suna min godiya abinda ya aika masu din.
Gashi dana fara mai godiya zai daga min hannu alaman ya isa haka na sai da yayi
dana gode mai bani fasawa.
Ba abinda ke mun dadi kamar yadda mahaifan mu ke sa mashi albarka har nima abin
ya shafe ni don da hajiya baaba da babana ida sun fara mai addua idan ina kusa sai
na lumshe idona don jin dadi.
Sai dai halin shi na fushi yanzu ya rage don baya wuce kwana daya yana fushi
dani ko don cikin dake jikina ne yake raga min ban sani ba.
Don Uncle akwaishi da saurin fushi abinda baka dauka abin fada ba yanzu zakaji ya
juye ya koma fada gare shi.
Sanin halin shi da nayi yanzu na gane bai son kana magana yana yi sai in ja
bakina inyi shiru sai ya gaji ya kyale don kan shi.
Abin da kan yawan hada mu shine fita a dade duk da ba fita nake yi ba don bai
bari na mami kowa a garin ba sai yan uwa tsiraru da muke dasu ko nafita sayen wani
abu da zaran ya kira nace ban koma gida ba ya ishe shi jidali har wani lokaci.
Ya hana mummy komawa gidan yaya Saadu wai ta zauna dani har in kara jin karfin
jikina don acewar shi ban gama warwarewa ba har yanzu.
Ina jin dadin zaman mummy don mace mai dadin zama ga sa mutum hanyan daya dace
yabi na alheri ga kuma bata jin kiuya ko kadan aiki ba sha mata kai ga tsabata
gidan nan ko yaushe kwal yake don tsabtan ta.
Hakan yasa ya yanke sharan bata albashi duk wata da farko taki karba wai ai an
zama daya don yaya saadu yana kokari dasu.
Sai uncle yake cewa ta karba ai duk wanda ke karkashin shi haka yake masu shine
dalilin karban kudin ta duk wata.
Yaya Saadu da matar shi samira sunzo kan hakan da yake yi sai cewa yayi shi in
son samune ma mummy ta zauna damu tunda ba komai take yi ba acan.
Idan tana son zuwa ganin yaranta ba zai hana ba taje tayi kwanakin da zatayi ta
dawo don shi hankalin shi ya kwanta da ita don ko na haihu dole ne ya nemo wanda
zai kula da baby din.
Yaya Saadu yai mata magana kuma ta amince mashi din da hakan tunda dama zaman
hakkuri takeyi can yara kowa ya kama gaban shi.
Muna waya da anty don dawowan nan namu na tura mata kudi wanda yake bani duk wata
na hada dari biyar na tura mata don dai a zuna lafiya ni da ita don kawai na fitar
da komai a ranta mu zauna lafiya.
Ranan nasha yabo a gunta take cewa in dan hada da dabara ina rika amsan kudi
idan sun taro sai ta san abinda zatayi min dasu nace anty na gode.
Wanan yasa ko yaushe yanzu muna waya akai akai da ita ba kamar baya ba can da ta
share ni din haka yasa han kalina ya kwanta yanzu don da ina cikin damuwa idan na
tuna halin da muke ciki da ita na rashin shi.
Yau tun safe uncle bai fito ba yana dakin shi bayan na gama karyawa na nufi
dakin shi don in duba shi sai na samu yana rufe yana barci haka yasa nayi zaton
hutu yake yi kawai.
A hankali na jawo mai kofa na rufe sai naji muryan shi yana kirana don haka na
tura kofan na koma ciki karasawa nayi bakin gadon da yake.
Murya ta alaman rashin lafiya yake magana da cewa don Allah hado min tea ki kawo
min nan zan sha magani da sauri na duka ina fadin Uncle baka da lafiya ne?
Kai ya gyada min alaman eh sai nakai hannuna saman laulausar kan shi dako yaushe
bai rabuwa da gashi irin na fulani yayi kwance lup a saman kan shi.
Zafi naji jikin nashi yayi nace subbahanallahi Uncle kuma kake kwance jiki ba
dadi haka a gida gyara kwanciya yayi yace jeki hado min tea din don Allah.
Fita nayi da sauri nan dai na hada mai komai na dauka zuwa dakin har lokacin da
na dawo dakin yana kwance a yadda na barshi na fita.
Bayan na aje ne na dan taba shi ina fadin ga tea din na hado maka Uncle ya dan yi
mika tare da bude idanuwan shi ya sauke a kaina.
Ina tsaye akan shi cikin damuwa na kura mashi ido sai da ya dan jima ya mike
zaune tare don son yunkurawa ya tafi ban daki nasan kewaya yake son yi amma ya
kasa.
Tsoro naji sosai a lokacin nace in taimaka maka ne ka tashi ya dago kai yadan
kallene sai ya girgiza kan shi yace hada min ruwa dai a ban dakin .
Na shiga na hada mai na dawo wurin shi har lokacin yana zaune a yadda na barshi
hannunwan shi na rike sai ya dafa ni ya tashi tsaye da taimoko na ya je ban dakin
ganin ya shiga ya fara tubewa na barshi na fito.
Wayana na dauko na kira yaya Saadu nake fada mai yau Uncle ba lafiya da sauri
yace gashi nan zuwa yanzu ya dan jima ciki ya fito bai ko tsaya share jikin shi ya
dawo saman gadon dana gyara bayan tashin shi.
Kurban tea din yayi bai sha wani abu ya koma ya kwanta tare da dan yin nishi
nace maganin fa yace barin dan huta zan sha ai.
Ina tsaye a kan shi ina kura mai ido idanuwan shi a lumshe ina tunanen lokacin da
yaya Ahmed yayi jinya ina gidan shi yadda yayi tayi mun a lokacin da yadda
hankalina ya tashi gani ni kadai a gida dagani sai shi haka nayi ta jiyar shi har
ya samu lafiya.
Nace kilama lokacin duk yana dauke da cutan yake jiya hakana ni ban sani ba
saboda kurciya da nake dashi.
Wayana yai kara ne yasa nasan yaya Saadu ya iso ke nan da sauri na juya na fita
zuwa wurin shi yana tsaye falo ko zama baiyi ba.
Ina fitowa ya tare ni yana fadin yana ina nace yana dakin shi bai tsaya ta kaina
ba ya nufi dakin nashi da sauri ina biye dashi a baya nima da sauri nake mara mai
baya hankali na yayi kololuwar tashi da yadda yake kwance sharaf.
Muna isa kofan ya shiga da sallaman shi uncle yana kwance a yadda na barshi ciki
jin muryan yaya daji yasa shi dan dagowa kadan yana amsa sallaman da kyat.
Yaya ya karasa gun shi yana fadin yallabai yau jikin ba dadi ne haka yadan dago
yana dan yake yace Saadu ta taso da kaine kuma ?
Yace wallahi fa na kirata mu gaisa sai take fada min jikin naka yau bakajin dadin
sa sosai ya dan kara gyarawa yace wallahi ai duk kwanan nan karfin hali nake bana
jin dadi.
Nabishi da ido da mamaki cike a fuskana sai naji yaya Saadu na tambayan shi ko
zasu tafi asibiti ne sai yace kasan matsalan ciwon mu da zaran mutum yayi dan
ganganci yanzu ciwon zai bugar dashi ne.
Akwai wani yaro dake zuwa nan gida ya kara min ruwa shima yana da irin matsalan
tare dashi yana kokarin jawo wayan shi dake karshin filon da yake kwance akai.
Yace amma kafin yaron yazo barin in hade magani da zai saukar min da zazzabin
don baa shan maganin sai aci abinci sosai.
Cikin marairai ce murya nace dashi a kawo ma wani abu kaci ne yanzu kai girgiza
min ya bude baki da kyat yana cewa tea dana sha is ok for me.
Drower ya nuna min da hannu yace jawo wancan zaki ga wani dogon roba fari ki
dauko min na isa wurin da sauri na tare da jawo drower din na dauko mai maganin.
Yaya ya karba naje dauko mai goran ruwa mara sanyi ko da na shigo na samu yana
kiran mai kara mai ruwa din a wayan shi.
Jefi jefi yake jefo ma yaya magana wanda nasan don ya kwantar muna da hankali
yake yin haka amma ta yanayin maganan zaka gane yana jin jiki karfin hali ne kawai
irin na maza.
Doctor ya iso idan ya kira wayan shi yaya saadune ya fita don ya shigo da
likitan dakin shi bayan fitan yaya ne ya kalle ni sai yaga ina hawaye a lokacin.
May kike ma kuka madam baki son in mutu in barki ne kai na gyada mai tare da
fadin don Allah uncle kabar wanan magana haka insha Allah bazaka mutu yanzu ba sai
ka tsufa damu .
Murmushin karfin hali yayi yace kaiyya ko daina wanan tunanen daga ni har ke ko
yaushe mutuwa ai zata riskan mu koda ciwo ko babu ciwo don haka addua kawai ya
kamata ki muna shine mafita.
Shigowan su yaya Saadu ne dakin da likita wanda yanayin shi ya nuna kamar kabila
ne shi yake cewa yaya ga kaunar ka nan kuka takeyi wai bata son in mutu in barta.
Murmushi yaya yayi wanda nasan na karfin hali ne shima yace ki kwantar da
hankalin ki Safiya in sha Allahu zai ji sauki.
Jikin dai ne nashi ya dan motsa mai kin san sha anin yau da kullun dole haka ya
kasance ga bawa ko yaya ne don haka ki koma dakin ki kiba likita wuri yayi aikin
shi.
Dagawa nayi jiki a sabule zan fita a dakin Uncle ya kirani yake cewa don Allah
kada ki bugawa kowa waya banda lafiya har Aisha .
Kai na gyada mai na fice daga dakin raina ba dadi don duk na tsarace da ciwon
nashi wanda dan lokacin kadan duk ya ramay kamar ya dade yana jinya akwance.
Ina fito sai ga mummy ganin yanayi yasa take tambayana ko lafiya taga Saadu yazo
gidan ya shiga dakin maigida kuma.
Nace yau baya jin dadin jikin shi ne shine yaya saadu ya dauko mai likita da
sauri tace subbahanallahi da sauki dai ko ?
Ta tambaya cikin son karin bayani nace jikin da sauki mummy nan muka zauna tana
kwantar min da hankali har likitan ya fito dashi da yaya.
Yaya yace in je yana kirana sai dai kafin in isa dakin ya samu barci a lokacin
nan dai na zauna wurin