Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
wai na ko gode ashe idan na koma gida inna sai bakin ciki ya
kashe ta.
Tsab muka fito bani ba ba yaran ba ban bari anty ta jiramu ba don a gagauce na
shirya simple makeup nayi a fuska na duk da hakan ba karamin kyau nayi ba sosai.
Duk sun fito nice karshen fito wa a tare da su yan biyu muka fito kowan mu in ka
gan mu basai an fada ma cewa ga inda zamu ba a lokacin.
Nan ko su Fati aka sako min ido take kowan su ya daure fuskan su, don basu san
da rigan da na saba na gani amma nai kamar ban gan su ba.
Nan dai babu tsatsayawa muka fice gidan har da funke gaba dayan mu ba a bar kowa
a gidan ba mota biyu mukai tafiya dasu inda nida yara da fati muka shiga mota guda
sai anty da faiza da funke a dayar motar.
Da kamar ba za tai min magana ba sai naji tace wai yaya kika ga shiga na ne
Safiya na fito kuwa ?
Nace kai ai duk kin fimu haduwa wallahi kin ko ga yadda ki ke wani haskawa wurin
nan ashe akwai wanda zai kai ki haduwa a wurin.
Taji dadi ta washe baki tace ina yinki safiya wancan yar bakin cikin cewa tayi
wai in saka dayan rigan nan don ta san baikai wanan din haduwa don ta fini fitowa.
Nace ke kyale ta don Allah ita Faiza bata taba fadawa mutum gaskiya ai tace da
sauri ashe kema kin gane ta yanzu ni shiya bani shiga harkanta .
Mun isa wurin ba kowa sai anty damu muka karasa duba aikin da akayi bayan wuce
wan mu nan muka shige wani daki muka kara gyarawa kafin a fara.
Ni dai kwance nake sai su ke ta heleke su da gwale junan su kamar wasu kishiyoyi
can nidai murmushi kawai nake ta masu sai anty ne ta shigo dakin take cewa ai an
bude wurin yanzu za a fara don Allah tana son kowan mu ya natsu muyi abu a hankali
kada mu bada ita.
Bamu fito ba sai da taro yai taro muka fito muna mara ma anty baya tare da wasu
yan uwan su da suka zo daga bauchi sai yanzu na gansu.
Sulaiman din ya fito tare da abokan nan nashi na dazu wanda na fahinci sune dai
abokan shi na shakiki na kusa.
Mun fito wurin ya dauki tafi don mc na bayani akan Sulaiman din da dalilin
haduwan a nan wurin ni dai biye kawai nake dasu kamar ace in sheka in ruga da gudu.
Don yawan mutanen dake wurin naga anty ba abinda ya damay ta sai walwala take
tana ta gaisawa da mutanen wurinta saka wasu matarial sai walkiya take yi a gurin.
Ana ta bayanai akan ki shi din wanene tare da manufar shi na bude company da yayi
nan wuri ya dauki tafi rafrafraf .
Sulalewa nayi na fice daga dakin taron na fita waje wani iska mai sanyi ya dake
ni na shaka sai naji ina son in dan kadaice ni kadai a wuri daya.
Wani dakali na hango a gefen don haka na nufi wurin na zauna ina kallon masu
shige da ficen wurin.
Nace a raina idan mutum na cikin wayan nan har sai ya manta da halin da yake ciki
ya shagala da rudin duniya dan dai ma ita anty mace ce mai kula da addinin ta.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , ,
3️⃣6️⃣3️⃣
3️⃣
🧕🏿 6️⃣6️⃣3️⃣
YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDINE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU
PLEASE DON BA A YAFE BA DAKE DAKE TURAWA MUTANA DA SU DAKE KANRATAWA DUK ALLAH ZAI
KARBAN MIN HAKKINA A GUN KU, , , ,
Hankali na ya tafi ga kallon yadda wani miji da mata suka shigo ririke da junan su
a wurin har zuwa cikin holl din dadin kallon su yasa ban dago kai inga ko waye a
kusa dani ba yana waya.
Gama wayan shi yayi daidai da kare kallona don sun zo sun shige har ina ajiyan
zuciya naga mai shi ya zauna a saman abinda nake zaune.
Sai na dago da sauri ina kallon shi yace dani sun baki shaawane daidai da yake
zama sai a lokacin na gane shi, yinayi kamar banji abinda yake fadi ba don yadda
yai maganan baiyi shi akan zan iya jiba.
Da sauri na matsa mai sai dai ban tashi ba don wurin nada girma ko mutum huda
zasu iya zama akai ya sake cewa hayaniya yayi yawa a ciki ko ?
Kai kawai na kada mai alaman eh sai yake cewa dani yana kallon wayan dake hannun
shi
Bana son yawan hayaniya don haka na fito waje na sa driver yazo ya dauke ni yanzu
zan tafi .
Saurin kallon shi nayi sai naga shi bai ko kallon inda nake gashi dan zaman da
yayi kusa danu duk a takure nake a wurin.
Yana yi yana kallon agogon hannun shi akai akai nasan lokaci yake diba na zuwan
driver shi nace sai naji yace bakiji tsoron zama a nan ke kadai ?
Karamar dariya nayi sai wanda ya saurara zai iya jina tare da nuna alaman ina jin
nauyin sa wanda hakan ya zamay nin jiki ga kowa indan muna magana.
Sai kuma naji ya sauke wani murmushi shi ma yace koda yake bai kamata na katse
maki yanayin da kike ciki ba na son ki kadaita kan ki ga mutane,
Kin san ku mayya sai a hankali bai kamata na katse maki jin dadin din ki ba wa
wanan lokacin yar gajeran murmushi na sauke har yanzu akwai alaman jin kunya a tare
dani.
Shiru ya biyo baya na runtse idona ina dan fidda ajiyan , gabana yaci gaba da
bugawa don gani nake kamar a mafalki na shiga tambayan kaina shin may ya fito dashi
waje a wanan lokacin da aka hadu don shi a kumayace zai wuce ya barsu
Sauke ajiyan zuciya na yi don ina mamaki hali iri na uncle sulaiman da ga mutum
shiru shiru mai kyakyawan halitta da kyakyawan hali.
Jin shi da nayi yana jan dan tsiki akai akai kuma yana yi yana kallon agogo har
yanzu lokaci zuwa lokaci.
Dagani ba sai an tambaya ba don mutum zai fahinci a gajiye yake a lokacin gana
haka sai kawai na miko mai goran ruwan faro dage gefena ajiye wanda na fito dashi.
Nai mamaki dana ga ya amsa yana min godiya tare da kafa kai bai sauke ba sai da
ya zuke ruwan goran duka.
Ya wurgga da goran yana kara min godiya dai dai nan abokin shi hamza ya isa wurin
yana fadin kai ana can ana neman ka kuyi photo ashe kana nan ka boye.
Sai lokacin ya farga dani a wurin nima sai tsarguwa nayi a yadda ya samay mu
kamar masu wani hira.
Saurin gaida shi nayi don kada ya zargi komai a tsakanin mu sai ya dago yana ma
sulaiman din wani kallo mai kama da zargi yaya haka kuma ?
Baka da hankali yai mashi alama tare da mikewa yana shirin barin wurin nidai
gyara zama na yi ba tare da na kalle su ba sai naji hamza yace a a zaka tafi kabar
ta kuma a nan kawai barin koma dama bamu gan ka bane shine na fito in dubaka.
Yama rasa abinda zaicewa hamza din sai sauran biyun sun fito suna cewa hamza yaya
sai hamza din yace yeh na gangashi ashe yana nan ne.
Dukkan su suka karaso ida muke, naji dayan na cewa kai muna can muna neman ka
harda madam ashe kai kana nan hamza ne yai masu nuni da hannu cewa su duba sugani.
Sai duk suka juyo inda nake zaune wani dariyan shakiyan ci gudan ya dauka yace i
see mutafi kawai inda ka gama mutane na jiranka kuyi photo a ciki .
Basu tsaya ba suka wuce suna ce mai sai ka shigo kenan girgiza kai yayi tare
dadan jan tsuki ya juya yana dubam ida na tare da cewa ba zaki shiga daki ciki ba ?
Nace nan di yafi mun dadin zama akwai isaka mai dadi a wurin, shigewa yayi ba
tare ya sake juyu ba yabar ni zaune na sauke ajiyan zuciya tare da lumshe idona.
Na dan dade zaune a wurin babu abinda nakeyi sai tunanen abubuwan da nake gani
sai ga funke an aikota ta kirani ban dauki lokaci ba na koma ciki tare da ita take
ce min mu fara ba mutane abin gift din kamar yadda aka tsara fon uban gaiyyan kan
shi yace ya gaji sai da aka nemo muna shi waje ,
Wai da wata yarinya tana fadi batare da ta kalle ni ba take naji gabana ya yanke
ya fadi ya kuma ci gaba da bugu uku uku don kada anty ta gane nice muke waje ince
mata may .
A tare muka je dakin da kayan suke sai da muka shiga ta fara bayani san nan na
sauke ajiyan zuciya tana mun bayani gabana yaci gaba da fadu.
Munyi yadda ya dace haka mutane sukai ta watsewa don komawa gidajen su don dare
yayi sai mu yan gida kawai aka bari nan wata doguwar mota ta kwaso mu zuwa gida
gaba dayan mu a gidan anty aka sauka.
Sai mazan ne suka sauka gidan sulaima din haka wuri yayi kada dole nida yara muka
koma dakin anty sukuma bakin suka sauka a dakin mu.
Ni dai bayan na tube har nayi barcin na falka anty tana gun bakin suna hira ko
tashi nawa yan biyu ce ta falka da ni wai zata yi fitsari.
Na dawo kaita sai ga anty ta shigo dakin take cewa bumuyi barci bane idona da
sauran barci nake cewa yan husna zatai fisari natashi.
Tace kin ganni sai yanzu muna can muna fira yaushe rabo a kasa na kwanta su suka
hau gado sai da ta fito han daki ta ganni kasa take cewa haba dai Safiya ku kwanta
mana saman gadon da yara nace kasa ma yai min don na sa bargo.
Tace kedai kin huta wallahi shiya sa nake ma Sulaiman gwadayin ya aure ki ai don
rayuwan ki ke simple ne kamar nashi.
Ai yanzu dole in matsa mashi don an fara kawo mai mata wai ya aura ko da kuwa bai
so haka za saka shi a gaba sai ya yarda.
Jin abinda ta fada yasani kallon ta da mamaki tace kina ganin wautana ko kan
abinda nake kokarin hadawa da hankalina Safiya.
Sulaima mutum ne da ko wacce ke mafalkin auren shi kyakyawa mai kyauwon siffa da
hali na gari ga wadatan zuci da Allah ya bashi dana Aljihu mai tattare da illimi
addini da na zamani uwa uba dan karen tsoron Allah kamar yana ganin sa.
Abin da na fadi shu ya dakatar da ita da yabon da take fadi nasa don cewa nayi
anty ni ina ni ina Sulaiman gashi dan masu arziki niko yar tallakawa.
Dama dai Fati dake mutuwan son shi kikai kokarin hadawa dashi don ita yar uwar
kine gashi tana mutuwan sin shi sosai , , , ,
Ke dan Allah rabani da abin haushi koda sulaiman zai iya auren ta ba zan yarda in
hada shi da fati ba don bata da tarbiyan da ya dace da mutum kamar sulaiman a tare
da ita.
Balle aure ita dashi ya haramta gare su don dai sulaiman shima victim ne irin ki
matsalan ku daya dashi.
Da sauri na dago kai na kalleta nace nace a razane HIV anty ?
Tace wallahi Safiya tana hawa gado take cewa matsalan ku daya dashi shima wata ya
aura maishi suka munafunce shi basu fada mai ba sai bayan aure ya baiyyana mata
koda akaje aka duba akaga shike gare ta har yai nisa da aka auna shi aka samu shima
ya samu daga gare ta.
Wallahi safiya daya kiramu yana kuka kamar karamin yaro yake fada muna ranan mun
shiga tashin hankali ba karami ba a gidan nan .
Allah yasa daddy yana nan shi ya shiga jirgi yaje can South African ya samay su
inda ya samu ya shawo kan shi sai dai kafin yaje har ya saketa ko.
Daga baya daddy yayi yayi dashi ya maida ita amma yace ya gama auren ta karshe ma
yace shi ba zai kara aure ba a rayunwan shi.
Daga baya muke jin wai ta gaji da bin shi ta auri wanda yasa mata cutan yanzu
shine kika ga sam baya son ai mashi maganan aure kuma ya koma gudun mata.
Dama can ba damuwa yayi da matan ba sai abin yazo mashi da sauki dalili kenan
kika ga ina son in hada ku don ko banza halin ku zai zo daya dashi.
Yanzu haka yan uwa basu san halin da yake ciki ba don ba afitar da zancen waje
wani yaji ba.
Shine ita mahaukaciyar kika ga tana wanan haukan haka shi yasa ma kika ga bai son
zuwa kasan nan don matsin da iyayyen shi ke mai akan ya kara aure.
Kafin taga bani labarin fuskana har yacika da hawaye fam taji ina kuka tace ke
ko saurin karaya gare ki ai hakkuri za a yi haka wani rayuwa yakan zo wa ba ya zama
BAHAGGON RAYUWA .
Amma in ai yi hakkuri aka rungumi kaddara sai Allah ya duba ma mutum Allah mai
tausayin bayin sa ne akoda yaushe yana ma mutum mafita ta hanyar da bai zata ba.
Nasan labarin nan da kika ji ya sa kin tuna da naki matsalan ya dawo maki da shi
sabo sai hakkuri abin ba dadi gaskiya.
Ta haye gado ta kanta tare da kashe wutan dakin ya koma duhu ta barni cike da
tausayin kan mu da ma sairan uan uwa musulmai da suka tsinci kansu a wanan halin
irin namu.
Tabbas Sulaiman idan ya zama mijina zan yi kokari inga na bashi kwanciyan
hankalin da ya dace dashi naji zuciya na ya sami karbuwa dashi dari bisa dari bawai
don kudin shi ba don ni basu gaba na yanzu don ina ganin kwana nawa ma yarage min a
duniyan.
Saboda na sha zama inyi ta nacin rokon Allah da yai min mafita ga matsala ta in
samu miji wanda zan masa biyayya kuma yasan ina yi.
In har abin ya tabbata zan fi ko wata mace sa a a rayuwana amma kuma ban taba
tunanen samun haka ba.
Sai gashi kwatsam Allah na baiyyana min ansan addua na yana batun bani uncle
Sulaiman a matsayin miji a gare ni.
Nasan anty da naci kan abinda take so wanan abinda take shirin hada min da wani
irin godiya zan saka mata dashi don tsabar girman shi da daraja a a gare ni.
Sai dai kuma kash nace a raina anys kuwa shi uncle sulaiman din zai soni kuwa ga
yadda yake baya kallon ko wata mace.
Kuma ma yasan cewa na taba aure har da haihuwa indan bai taba sani ba anya zai so
bazawara kamata kuma yar talakalis.
Wanan sune tambayoyin dana rika yiwa kaina kawai sai jin hawaye masu dumi nayi
sun soma bin kuncina a karo na farko da na furta Allah ya isa ga Ahmed kenan.
Don shi ya jefa rayuwa na a wanan hali dan ma taimakon Allah ya kawo min sanadin
sanin anty a rayuwa na har take kokarin mantar dani halin da nake ciki yanzu.
Na sake fadi Allah ya isa aure na da Ahmed cikin sanyin jiki na gyara kwanciya na
ina ci gaba da tuna ne wanda ban san iya wanda nayi ba a lokacin.
Washe gari mun tashi da baki a gidan don haka tunda nai sallah muka fada kitchen
dani da funke don hada masu abin karyawa.
Koda anty ta tashi har mun gyara gida mun gama hada breakfast din na shiga wanka
ina jin tana fadin yau na shiga uku wani irin barci ne nayi haka mai nauyi.
Na fito ina mata ina kwana tace safiya ai yau kan ban san irinbarcin da nayi ba
ga baki gida ban shirya masu abin karyawa ba har wanan lokaci.
Nace anty fita falo kiga abinda muka shirya masu ko yayi na dai hada ban san ko
zaki soshi na tace kai Safiya ubangiji Allah yai maki albarka yasa mu raka da junan
mu.
Har kin hada abinci ina daki kwance ban sani ba shiyasa nake son kada ki kubcewa
Sulaiman don shi kadai ya dace dake.
Shima kene kika dace dashi sai ku taru ku rufawa junan ku asiri a zauna lafiya.
Murmushi nayi nace kai anty dai kina dai son musa kafan wando guda da fati a
gidan nan don ta mutu akan so uncle din sosai wallahi.
Wai ba zaki rabani da wata Fati can ba ana maganan mutanen kwarai kina kawo min
fati ciki wanan kazama may ta iya banda rashin kunya ita kuma Faiza ragguwa ce ta
karshe bata iya aiwata komai banda kallo da kwanciya ai dai za a yita ta kare ga
yan uwan haihuwan shi ai sunzo
Sai da mukai wanka muka fito falon a lokacin har bakin suma sun fito ko take cewa
kun gani sai yanzu na tashi ba sukace suma basu dade da tashi daga barci ba ai.
Dayan tace gashi har an hada abin karyawa ko tace aikin sarakuwan ku ne wallahi
sai duk suka kalleta matar take cewa sarakuwan mu ta ina tace Sulaiman mana.
Nan suka shi murna da sa albarka ga abin nidai kunya duk ya rufe ni dago kan da
zanyi sai ga fuskan fati tana tsaye kamar ruwa yaci ta.
Uncle ne sukai sallama da sauran mazan da suka kwana gidansa suka shigo da murnan
su sai ya samu suna zuba abinci yace a a madam baku gaji ba har kun iya tashi kunyi
wanan aiki haka.
Bata kai ga bashi amsa ba sai wata tace kaidai ai kayi dace wallahi ga