Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
ajiyan zuciya har ina jin shi don na kusa kawowa
wurin shi a raina nace su zuciya manya.
Ashe akwai aiki a gabana dan wanan magana yake ta jawa rai haka anya kuwa zan
iya sai da na gama jerawa nace bissimillah na samu wuri a kasa na zauna tare da jan
plate zan fara zuba mai.
Ganin kayan tare a gaban shi kashi kashi yasa yace min may ye haka yau John ya
girka muna?
Banyi magana ba sai ci gaba da bude warmer din nayi inda na fara ziba mai tuwon
shikafa da miyar shawaka da yaji agusi da manja sai nama manyan yanka da nayi
amfani dashi wurin hadawa da dan man gyada kadan.
Kamshi me ya kaure falon alokacin da na bude ferfesun kifin dana hada wanda nayi
amfani da kayan yajin mu na gargajiya sai ruwa dana zuba da maggi.
Gani nayi ya sauko kasa abin wanke hannu na jawo tare da dauko ruwanda na tanada
don wanke hannun nashi.
A hankali ya miko hannuwa fuskanshi akan tv ina zuba mai ruwan ya na wankewa a
hankali na jaye ruwan gefe guda sai ya kallo ni yace ke ba zaki ci ba nace munci da
gwago da Zarah tun dazun dana gama.
Naga ya kara hade rai yayi bissimilla ya fara ci har ya kare bai yi magana ba ni
dai ina zaune na saka ma tv ido nima kamar mai saurare abinda ake fadi nan ko
zuciya ta tambaya kanta take yi mai ya kawo wanan matsalar haka wai ?
Naji yace amma ba John yayi abincin nan ba eh kawai na bashi amsa dashi na fara
hada kayan ina kwashewa na barshi dana ferfesun yana sha a hankali yana kallon tv.
Bayan ya gama na kwashe na dauko kamshi na bude falon dashi yadda ba za a ji
karnin kifin ba idan an shigo falon.
Zama yayi a kasan tare da jingina bayan shi da kujerar daya sauka a kai tare da
mike kafafuwan shi a kasa yana kadasu a hankali zaman naji shiru yayi yawa don haka
na mike zan leka gwago a dakin ta.
Yace jimana sai na dawo na zauna cikin basarwa yace gwago tayi min maganan zuwa
gida yau da safe don haka nake son ku fita ai mata tsaraba zuwa gobe.
Allah ya kaimu nace sai na juya na wuce bina yayi da kallo komay ya tuna a ranshi
sai yaga bai kyauta min ba sauke ajiyan zuciya yayi may ye laifina a cikin wanan
magana daga tambaya kawai ya dora min laifin dabashi ba.
Nasan nayi laifi na kuma dauka ina binshi don yayi hakkuri ya kasa cire laifin da
bani nayi shi ba akaina.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/15/20, 10:51 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , ,
5️⃣7️⃣5️⃣
5️⃣
🧕🏿 7️⃣7️⃣5️⃣
NOVEL DINA NA KUDI NE IDAN KIN FITAR UBANGIJI YABI MIN HAKKINA A KAN KI/KA.
YAR UWA MAINE RIBAN KARANTA KAYAN ALLAH YA ISA KARATU FA IYAKAR SHI DUNIYA.
Karfe goma saura har lokacin ina zaune dakina na kasa zuwa dakin uncle don ban
san da wani fuska zai karbe ni har nayi kamar in share shi saidai na mike na fara
shirin zuwa wurin shi.
Komai na falon an an kashe alaman dai ya shige tuni dakin shi sai wutan da zai
sadani da nashi part din ne kawai a kunne.
Ahankali na kwankwasa kofar tare da turawa sai najita a bude nasa kai na shiga
dakin can na hango shi tsaye bakin window dake kallon wajen gidan yana tsaye ya
rike labule da alama iskan dake busawa a lokacin yake shaka don yana mai dadi.
Shigowana baisa ya juyo gareni ba har na karasa inda yake tsaye batare da jin
kunya ba na rungumay shi ta baya tare da zagaye hannaye na saman ruwan cikin shi.
Ajiyan zuciya naji ya sauke a sanyayye nace uncle may kake yi anan tsaye kai
kadai batare da ya juyo ya kallene ba ya bani amsa da yanayin yana min dadi ne
madam.
Sake shi nayi nima nakoma gefen shi na tsaya ina kallon waje sai naga motoci
suna wulgaiya jefi jefi ga iska mai dadi na hurowa ta tagan dakin.
Gwaron numfashi na sauke amma a fili na kasa fadin komai sai tsayawa danayi ina
kallon wajen kamar yadda shima yake kallo.
Shi ya kawar da shirun da cewa na dauka kinyi barci ne dana jiki shiru ai ajiyan
zuciya na sauke nace uncle ina zan iya barci bayan miji yana fushi dani karo na
farko a rayuwan mu tare.
Murmushi yayi tare da sanya hannuwanshi saman kirjin shi yace bada ke nake fushi
ba sai dai maganan ki ce ta jawo min fushi na.
A marairai ce nace kayi hakkuri uncle ban san maganan zai bata maka rai ba haka
da banyi ba ni gani nayi yarinyar tana zaman kane a gidan kuma bata samu sakin
fuska a wurin ka ba.
Naji na gode amma ke bakuwa kike a cikin mu shiyasa zan daga maki kafa ga
maganan yanzu amma indai akan zancen wanan zurian ne bani son daga yau ki kara yi
min shi a gidan nan.
Ki barni da yan uwana ki zauna matsayin ki na matana a cikin su bani son ki zure
masu har su samu kafar shige min haka.
Murmushi nayi na kwantar da kaina saman kafadan shi nace uncle yadda kake so
haka za a yi har kullun a shirye nake da in maka biyayya a rayuwana.
Amma Uncle ina son ka zama mai yafiya ga duk wanda ya zulunce ka saboda kayi koyi
da sunnan mai,akin Allah sallalahu Alaihim wassalam.
Yau uncle in har akwai abinda sukai ma rayuwan ka sai ince ya zama maka taki
ayanzu don hassada ga mai rabo taki ne.
Uncle har kullun sai dai inci gaba da yima addua da fatan alheri a garemu uncle
ba zan boye maka ba bantaba ganin mutum adali irin ka ba uncle.
Sai dai kuma cikar kamalan mutum baya kammals sai ya cika sharudun Allah a kan
shi yanke zumuta dasu don sun taba yi ma rayuwanka illar killa can baya ba shine
mafita ba a gare ka.
Kamata yayi uncle kai ka saka masu da alherin ka barsu da halin su Allah shine
mai hisabi arayuwan biyan sa.
Amma uncle akan may zaka rike gawarshin wuta a hannuwan ka su kona ma aikin na
alheri har ka gamu da fushin ubangiji ka ta sanadin su.
Uncle kafan Allah yana fushi da may yanke zumunci sannan na fahinci baaba tayi
hakane don kawar da wani abu a gare ka.
Sannan Uncle ba, , , , ji nayi ya dora dan yatsanshi saman bakina yace ya isa
haka naji na gode zanyi iya kokarina inga na fitar da abin a zuciyata.
Ina alfahiri da kasancewar ki matana a yanzu don samu mace ta gari yana haifar da
alheri acikin zuri,a dawamamiya.
Ya rugumay ni zuwa bakin gadon shi sai lokacin da ya sauke ajiyan zuciya yace may
kika tanadarwa tafiyan gwago ne ?
Ban bata lokaci ba nace gwago mai za a tanadar mata dayafi jarin kuli da takeyi
ba dare ba rana duk shi ya hanata zama hankalin ta na can wurin masu zuwa sarin
mangyadan ta.
Kai naji yace yanzu kina nufin gwago har yanzu tana irin aikin wahalan nan na
kuli nace da hannunta ko take komai wallahi.
Nisawa naji yayi yana kaiwa kwance nace Uncle kuna waya da anty kuwa ?
Yayi dan guntun murmushi tare da fadin ina jiran sai ta huce da kanta zata
nemomu don yanzun ta hau sosai .
Nisawa nayi nace a kullun idan na tuna irin alherin dake tsakanina da ita ban
jin dadi a raina da haka ta kasance a tsakanin mu.
Baiyi magana ba sai kamomi dayayi zuwa jikin shi muka kwanta anan labarin
ya canza sallon shi.
Washe gari bayan ya gama karyawa ne alokacin gwago na da mako biyar a wurin mu
kamar yadda yace kudi ya dora min saman cinya na yana fadin ku shiga kasuwa da
gwago asaya mata duk abinda take so don Allah kada kibi son ranta a sai mata duk
abinda ya dace da ita.
Dago fuska nayi ina kallon shi ganin yadda ya daure fuska yasa na kasa fadin
abinda nayi niyar fada mai din.
Sai dai da ganin fuskana kasan so nake ince mai hidamar da yakeyi a kaina sunyi
yawa haka gani nayi ya gyada min kai tare da fadin karki ce min komai indai ba so
kike ki bata min rai ba.
Ajiyan zuciya na sauke tare da fadin Uncle ni may zance sai dai inci gaba da maka
fatan alheri Allah ya saka da alherin sa.
Sai dai ba zan iya boye maka ba ban taba ganin mutum irin ka ba a rayuwa na har
tsoro nake ji kada yan uwanka su fara zargina akan haka.
Murmushi nan nashi ya sakar min inda ya fara tafiya yana fadin yau ba zan samu
rakiyan bane ?
Na mike da sauri ina fadin ban isa ba ai a tare muka fito ina rike da yar
briefcase din shi har zuwa bakin motar shi inda iya nan nake tsaya dama.
Sai da yayi kissing din goshina ya fara tuki yana cewa ku fita da wuri don idan
yamma yayi tafiyan ba dadin fita garin.
Na dawo ciki cike da murna a nan falo na samu Zarah ta fito ban tsaya ta kanta
ba na nufi dakin gwago tabi bayana da kallo.
Zaune na samu gwago ta kura ma tv ido ga tasbaha a hannun ta tana ja tayi kyau
ta kara kiba da haske sosai nace kai gwago wanan irin kyau haka karfa ki koma inji
zawarori sun fara zuwa wurin ki.
Dakuwa ta nuno min tana fadin wani shegen bazawari zai zo wurina yanzu ai sunyi
nacin su sun barni nan so sukeyi su dan cinye abinda muka dan gada su barmu muna
leke a gidan wasu.
Don gaskiya gwago batayi tsufan da za a ce bata da aure don kunsan yadda aure
yake a kauye irin auren nan na wuri atara zuria da wuri.
Sai da na zauna kusa da ita sannan na fito mata da kudin na aje a gabanta tabini
da kallo sai kuma ta juya ta kalli kudin dake gaban ta tare da zaro ido.
Dariya nayi nace gwago kidin ki ne yace zamu shiga dake gari a sayo maki duk
abinda kike so kuma ya ce don Allah a saya maki abinda naga zaki bukata indan kin
koma gida.
Zaro ido ta karayi tare da fadin yar nan duk wanan uban kudin duka nawa ne haka
gaskiya sunyiwa ki raba uku ki maida mashi da kashi biyu kice na gode.
Sauran na samu na kara jari ai sun isheni sayen buhun gyada goma nan gaba kin ga
jari ya tasa ke nan nan gaba.
Da sauri nace a a gwago Allah ne ya kawo muna hutu a karkashin shi Allah ya duba
wahalan mu na can baya lokacin da sai kin dauko abinci a gidan ki kin kawo muna
muci da sauran abin amfani.
Don haka ma kin madaiji abinda ya fada wai na kaso maki su duka idan mun fita da
sauri naji tace waneni wanan kudi yai yawa da kashewa yar nan.
Haka dai na lalabata ta shirya driver ya fita damu mu uku da zara muka fita
gwago batayi niyar a sai mata abin kwarai ba so tayi ta dunkule kudinta ta koma
gida dasu.
Amma naki yarda sai da na sai mata abinda naga zasuyi mata amfani idan ta koma da
tsaraban da zata kai ma mutanen gida.
A gajiye muka dawo gidan sai dan abin motsa baki da muka sawo muka zauna nan
mukaci muka kora da drinks zarah ta mike ta shiga dakin ta tare da abinda na sayo
mata a fitar namu.
Bayan mun huta na dora girki na dawo wurin gwago na dubata tare da dan taba hira
na koma ban sake dawowa wurin ta ba saida dare bayan na gama komai kafin ya dawo
don ranan yayi dare bai dawo da wuri ba na fara hada mata kayan ina mata bayanin
komai da wanda na sayo masu mama Jummai zata kai masu tsara da yaran su.
Sulaiman ya dawo gidan da alamun a gajiya ya dawo don tun bai shigo gidan ba ya
rage sassauta tie di wuyan shi tare da balle rabin anineyan gaban rigan shi.
Sannu da zuwa muke mai daga ni har gwago yana amsawa da kyat yana kaiwa zaune
yace gwago ana nan anashiri ko tace kaidai dan Albarka sannu da kokari wanan irin
abin arziki haka mai yawa baka gajiya da dawainiya damu ?
Yace kai gwago ai albarka ku muke nema ko yaushe don abinda muke nema yayi
albarka tace haka nane ubangiji ya kara rufa asiri Allah ya kara daukaka da nisan
kwana .
Ya amsa cikin jin dadi da amin gwago abinda muke nema ke nan gare ku addua da
fatan alheri ya juya inda nake tsaye ina saurare su bayan na gama hada mata kayan.
Yace madam yaya gida yana mikewa tsaye yake fadin haka nace Alhamdullahi yaya
gajiya aiki yace not bad nabi bayan shi muka fita tare har zuwa dakin shi dauke da
briefcase din sa dana karba.
Muna shiga dakin ya zube saman gado gaba dayan shi na aje na juyo ina kallon shi
bayan na aje jakkan a ma ajiyar shi takowa nayi zuwa wurin na duka a hankali na
fara cire mai takalman dake kafan shi tare da safa sai naji ya sauke ajiyan zuci
bandaki na shiga na hada mai ruwan wanka.
Na fito still yana kwance a yadda na barshi ga ruwa can ya hadu uncle na fada
mashi ina kokarin fita dakin don na dora ruwa a kattle.
A lalace naji muryan shi yace madam na juyo da ina kallon shi yace da
wanan yarinyar kuka fita sayayya dazun ?
Nace eh zarah ko ?
Sai naji yayi gajeriyar murmushi yace I know it dama mikewa yayi zaune bai bi ta
kaina ba ya fara kokarin cire kayan shi.
Ya barni tsaye ina jimamay tambayan shi gare ganin baita kaina yasa na fita
dakin naje yin tsabgan gabana.
Bayan ya fito yaci abinci bai dade ba ya koma dakin shi tun bayan gama kallon
news da yayi tare da cin abinci.
Nima sai banyi nawa ba na gama na samay shi a dakin amma yana waya a lokacin ga
yadda na fahinta kafin in shigo fada yakeyi a waya amma ina shigowa sai ya rage
sautin fadan shi tare da fadin na fada maku bazan dauki wanan halin ba.
Wuce shi nayi na dauki flask din na tafi daga dakin har na dawo waya yake na aje
na samu wuri na zauna a bakin gado wayan ya kashe yana mai sauke numfashi tare da
wurga wayan saman gado ya shiga ban daki nikan kwaciya nayi kafin ya fito.
Banji fitowan shi ba sai muryan shi da naji yana fadi daga bayana don may kika
dauki yarinyar na kuka je sayayya da ita?
Na juyo da sauri yana goge jikin shi da towel nace uncle naga zamu barta gida
ita kadai ne yace a harzuke ku barta mana sai may?
Ai dama bari nayi kisan halin su da kanki basai nayi warning dinki ba yanzu kin
ji abinda tayi ta buga waya tana cewa wai kudi nake sakar maki kamar may don ko
gwago da zata tafi wai ba karamin kudi na bayar ba akatafi kasuwa mata sayayya.
Ban san lokacin da na mike zaune ba yace yes dama na sani kadan daga cikin aikin
su ne wanan.
A mairaraice nace uncle wani abu yafaru ne ?
Ya faru mana daidai lokacin da yake hawa saman gadon yace waya tayi gida wai
take fada masu a hankali nace Zarah din yace dama may ya kawo ta ?
Shiru nayi a raina nace wai rufin kofa da barawo ke nan ashe idon su hajiya ce
Zarah ban sani ba ashe da munafuka muke zaune a gida aiko nawa ya ya samay ni.
Tunanen may kike yi dama baki san ma,anan zuwa da ita da uwarta ta matsa ma
hajiya sai munyi da ita ba.
Aisha ta fada min komai tun can hannatu ta fada min komai amma tunda naga ke
kina da raayin zama da ita yasa na kyale sai tayi maki.
Da wanan bakin cikin na kwana a raina na Zarah da safe da na tashi bayan nayi
sallah naje muka gaisa da gwago ban tsaya ba kitchen na shiga don dora breakfast.
Sai na samu har Jonh ya shigo yana yayanka kifin da zaiyi ferfesu dashi don
shine mai muna abinci ni kuma kazantar cin abincin shi nakeyi shiko uncle bai damu
ba cin abinsa yake yi.
Na gaisawa mukayi da shi tare da fada mai ya barshi zanyi baiso ba amma ban
bashi fuskan tsayawa ba ya fita daga kitchen din.
Bai dade da fita ba sai ga zarah tashigo muryan ta naji daga bayana tana fadin
anty ina kwana ?
Dan juyowa nayi ina amsa mata tace dani may zan kama maki anty ?
Nayi mamakin jin tambayan don bata fitowa haka da safe sai idan mun gama tace
barci ne ya dauke ta bata san gari ya wayewa ba.
Yau kuma ko tafito ganin wani abin ne ta sake fada ban sani ba sai nace da ita
ki barshi kawai ba wani aiki mai yawa zanyi ba ai.
Tayi dan jimmm sai naga ta nufi wurin dankali nace ki