Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
hado min mai yawa babu abunda babu na fannin girki da ba a hada min
ba niki niki na dawo gida da kayana.
Taimin alkawarin zata dinga zagayowa akai akai tana dubani nai msta godiya ina
kuka tace nayi hakkuri ta kawo kudin ta kara min ta wuce zuwa wurin aikin ta.
Ban bata lokaci ba na shiga kawar da kayan kafin mugun ya dawo gidan ya tar dasu
ya samu na min iya shege a kan su.
Komai na adana su tsab ba abin da na bari a fili na dawo falo na zauna can ko
kamar ta san zai dawo sai gashi ya shigo gidan ina zaune a falo.
Ko kallo ban ishe shi ba ya shige dakin shi fuskan murtun kamar na yan high
killer marasa imani dasu jin kadan ya fito ta sake fice wa na nisa tare da fadin
macuci azzalumi kawai ta Allah bataka ba.
Kashi dai karfafa ne gashi da tsayi da saje ya kewaye masa fuska a ido kamar
kamili idan ka gashi amma duka halinsa ba na saye.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , ,
1🧕🏿717
1️⃣
1️⃣
7️⃣ 7️⃣
YAR UWA WANAN NOVEL DIN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU
PLEASE, ,
Gani ina gida ya sa ya juya ya fita nasan ba komai ya dawo yi gidan ba abincin da
na dauko tun na safe gidan maman biyu shina yini ci a cikina.
Mugun bai dawo gida ba sai da magariba ya shigo da leda biyu a hannun shi na
dauka wani abu ya sayo ashe wai garin kwaki ne.
Dayan ledan kuma kayan break fast din safe da zai karya dashi ne ya sayo ce na
dauki garin ni ya sayowa na aje mai kayan tea din shi da safe zai karya dashi.
Na dauka nakai saman fridge na aje ashe yana kula dani ban sha ba yace ke garin
bazaki sha bane a dakile nace na koshi a harzuke yace kin koshi may kika ci ?.
Nace komai atakaice.
Kamar zaiyi magana sai ya fasa ya sai ya mike zuwa dakina yana bincike baiga komai
ba a dakin ya fito yana kutawa.
Yace idan ma baki sha ba ke kika sani ni dai hakkina zaki bani ba ruwa na da
rashin cin ki wanan ke ya shafa.
Banko dago kai na kalle shi ba na kurama tv da ta shigo ya samu ina kallon super
story.
Tashi nayi zuwa sallah inshai don lokaci yayi ban fito ba ina gurin da na
sallama sallah zaune sai gashi ya shigo daga shi sai gajeren wandon boxes a jikin
shi.
Kallo daya nai mashi na kawar da kaina don bani son ganin shi a irin siffan nan
yace ke bake nake jira bane.
Nai dabur dabur na rasa abinda zanyi gashi ya tsure ni da idanuwan shi jajaye
kamar garwashi wuta.
Yace a dake ki samay ni a dakina ina jiran ki gabana ne ya fadi badai wanan dakin
matataran karuwan shi da mashayan giya yau zai ce na samay shi ciki.
Dan jin nayi na dan wanj lokaci tunane ya hana zuciya na shakat a lokacin ta shi
nayi na bude kaya na na ciro turaren jiki duk na mulke jikina dashi hijjab dina na
sallah na cire na nike a saman gado na canza zanin jikina.
Ina tsaye ina kara kintsawa sai gashi ya dawo kamar maye yaso kurwa yace yana
zazzare ido wai ashe bake nake jiraba ne.
Tare da tsura min ido kamar zai cinye ni danya nace gani zuwa ina gyarawa ne
yaja tsuki ya fice daga dakin nace kaji dashi dai kazami ko wanka baiyi idan za a
kwanta dashi.
Na shiga dakin da sallama na yana kwace dadaya saman gadon dakin ga abin taba
nan ko ina sakin birjit warwatse a kasa sai kwalaben dake wani gafe a ajiye.
Ina shiga ya kalle ni sama da kasa yace mallama dallah zo konji ina da abin yi
tun dazu kin shanya ni ina jiran ki.
Dan matsawa ni bakin gadon zan zauna sai ko naji ya sa hannuwan shi masu kama da
na karfe ya hankado ni saman gadon sai na kai kwance.
Tun takwas da wani abu nake dakin bani na fito ba sai daya da wani abu na dare
ya koro ni koshi nasan giya zai hada dashi.
Ina fita ruwan zafi na samu nai wanka tare da gassa jikina dashi san nan na samu
barci sai dai barcin sama sama nake yin sa.
Da safe na tashi duk jikina yana min ciwo amma don rashi imani sai da yasa na
dafa mai ruwa tea ya zauna yasha ya sha ya koshi bai ko kalli gefen da nake ba.
Nima sai harkan gaba make yi ban kula abinda yake sha ba a lokacin har ya gama
ya fice na sauke ajiyan zuciya.
Golden morn na hada na karya dashi na mayar maboya na boye sauran inda bai gani
na sama yan kitso sun zo min don haka nake busy da jamma, a wata mata ce ta gwada
min inda ake sayar da wake da bread a area namu.
Shi na sayo na ci abanicin rana na sai shan ruwa ya biyu bayan har na gama ma
mutun biyar kitso bai dawo gida ba na lissafe in kudina na na soke na gyara wurin
kamar banyi ba.
Bai ma dawo gidan ba sai dare koda zai shigo a buge ya shigo gidan ranan ko
matsin haukan shi baiyi ba.
Washe gari sai karfe goma saura ya tashi sai ya hauni da fada wai yaya akayi ban
tashe shi ba har yakai rana.
Badon na gudu ba da ya dake ni son ranshi da naga yana da niyar bugu na bude gida
na gudu sai da ya fita na dawo gidan.
Na samu yai baja naja da kaya na yana neman kudi a ciki bai samu komai ba sai
dari biyar da na aje canji ya gani ya dauke .
Nagyara kayana tare da mayar da komai inda yake ma dafa abinci naci na koshi na
dan kwanta falo in huta sai barci masu kitso suka tayar dani kai biyu na kama ranan
kawai.
********* ********* *********
Ina sauri in shirya in tafi gidan su gaida gwago na dake fama da kafa kwana biyu
bata ko iya tashi.
Tsaida ni yayi wai sai na dafa mashi ruwan zafi a gurguje na dafa mashi don an
dauke wuta na zube mai ya kewa ya na fito kada ya hana ni in yi laifi gun ta.
Yau basu sana a duk yan matan gidan su nan kowa da abinda take yi sai dai masu
hira da maza cikin su sunfi yawa.
Na shiga duk suka bini da idoban kula su ba na shiga dakin gwago din na bada
baya naji sun kwashe da dariya.
Na shiga naga gwagon nai mata sannu da jiki tana amsa min da kyat inda ciwo har
da hali kamar bata son ansa min.
Muka dan zauna tsawon wani lokaci a dakin shiru itace ta kawar da shirun da fadin
shi yana gida ne ko ya fita aiki ?
Nace yana gida na barshi zai fita yanzu kaita kada min can ta sake cewa ke har
yanzu babu ko batar wata sai aukin akawo maki ki juye a masai.
Shiru nayi ina wasa da yatsun kafana ta sake cewa idan har kin san wani abu kike
yin don karki samu ciki idan na gane ki bazaki sha da dadi ba gare ni.
Teema tashigo dakin wanan yarinyar da muka taba haduwa da ita a gidan farin zuwa
na tana gani na sai ta washe baki tana min dariya.
Duk naje gidan mukan dan kebe da ita muyi hira wani lokaci takan ziyarce ni ko
taje nai mata kitso a sace.
Yau ma mun samu mun killance take cewa dani ashe kin zo nace eh kwana biyu ban
ganki ba tace kin san mutanen namu sai a hankali.
Kwana ki hajiya taji natafi wurin ki taita sababi dani ta kar na sake zuwa gidan
ku idan na koma duk abinda tai min nina ja wa kaina.
Nace o o zuwan kuma da kike yi an maishe shi tsegumi tace ai basa so na je ba don
suna ganin zan fada maki abubuwa gamay da mijin ki.
Tsaki nayi nace in dai wanan mijin nawa ne mai zaki fada mi wanda ban sani ba
tai saurin jiyowa gareni tace akwai shi amarya kedai baki sani ba kawai.
Wata sabuwar fuska naga ta fito daga wani daki tana wani shan kamshi tana wani
yamutse fuska ta dube mu a wulkance tafita daga gidan.
Da ganin ta goggace takwarai yar barikin gaske ce don basai an fada maka ba
tafiya ma tana wani girgiza jiki goggagan karuwa da ita.
Sai naga teema tayi dariya tace dani kinga ta nan nace da ita eh sai kuma tace
bari dai zanzo har gida in fada maki magana baiyi a nan an saka muna ido da yawa.
Ban damu da naji komay zata fada min ba muka dauki wani zancen zuwa can naji gaba
na yana faduwa da farko na zo da suna yini ne a gidan sai kuma naji bazan iya ba.
Nace zan koma gida na leka gwago tana barci don haka na tafi ban sallamay ta ba
Sadiya kawai na sama a gidan
mukai sallama na tafi.
Na murda kofan gidan najishi a bude nai mamaki da har lokacin bai fita ba zuwa
aiki ba na tura kofa a sannu na shiga gidan.
Gaba daya baka jin komai sai nishin su a falon basu masan na shigo ba sai ihun da
suka ji na kurma don gigicewa.
Da sauri ya tashi yana fadin ke ke ke may ye haka maynene zaki tara muna mutane
akai kamar kin ga wani mugun abu.
Ban tsaya saurare shi ba sai na shiga kitchen na dauko yuka na nufo su dashi suna
kokarin shigewa daki na nufosu da yuka gadan gadan nai kan yarinyar da yuka sai ya
tare ni.
Nai cikin su gaba daya suka shige dakin sai da ya kimtsa yafito yaso ya jibge ni
nai tsaye nace wallahi yau idan ka dake ni akan wata mace a gida nan sai nayi karan
ka wajen yan sanda.
Fadin da nayi bai yarda ba sai da taji nace dama maman biyu tace ko harara na ka
sake yi na fada mata ai karan ka.
Jin na ambaci maman biyu yasa ya dakata dako har yana nade belt zai shirin
jibgana dashi yaga banza.
Amma duk da haka sai da ya tureni na fadi gefe na shiga bakina ni kaina naji
mamakin kaina da na dake nai masu yankar kauna a gidan.
Ta fita tana wani taunan chewagun sai lokacin ma na gane ashe wanan yarinyar mai
sallon da na gani gidan su ne wurin gwago.
Ta kalle ni a wullakance tace kin dauki bashi in dai wanan ne a tare kika samay
mu tare kuma zaki barmu.
Ta wuce gaba yaba binta baya suka fice a gidan nasa hannu a kai nace ba shiga
uku nikan nawa ya samay ni.
Dama abinda teema tai niyar fadamin kenan ta fasa naji dai tsna cewa ki tafi gida
yanzu kada ki wuni a nan .
Naso na tambaye ta sai na share kuma don ban gane manufanta ba don tace magana
baiyi a gidan sai dai tazo.
Wanan karon na turza na kafa mashi cin mutunci banji tsoron shi ba yace ke ki
rufe min baki Liliya ta fiki komai ke inba kaddaraba may zai kaini aure ki.
Nace kamar yadda ka zamu min mijin kaddara a rayuwana in badon darajan iyayye ba
mai zanyi da dan giya mazinaci a rayuw, , , ,
Marin da ya kwashe ni dashi yahanani karasa abinda zan fadi ya samay ni ya
mamara awurin yakuma ce.
Auren Liliya zaiyi ko da ita taki shiyasa uwarshi ta aura mashi ni don ya manta
da Liliya.
Nace auren ku bai damay ni ba zina daine bazan yarda ashigo har cikin gida ai min
ba yace tunda gidan ki ne sai ki hanani abinda nake so yi.
Ranan dai munyi shi ba dadi yafice yabar min gidan bai kwana a gida ba washe
gari na shirya zuwa gidan maman biyu.
Na samayta a gida bata fita aiki ranan na bata labarin tace ni wanan mijin naki
na rasa wani iri dan iska ne safiya ai mashaya giya wasun su basu damu da mata ba.
Nace anty shi fa tatirin dan iska ne na gaske tace aiko ba irin ki ya kamata ya
aura ba daidai dashi ya kamata ya samu yar iska irin shi su saje.
Amma ke ai cutar ki zai ta yi a banza don baki saba da abin yan bariki ba ni fa
ina jin tsoron kar ya kwaso maki karuwa su halaka ki.
Nace nima anty abinda nakewa gudu kenan wallahi yau wanan tazo gobe ma wata zai
kwaso duk a mutum daya.
Tace Allah dai ya kyauta ban dawo gida ba sai yamma lis koda na dawo gidan yana
nan kamar yadda na samay shi alamu sun nuna bai dawo ba har lokacin.
Na kule gidan na shige dakina bayan na gama abinda nakeyi ne na kwanta can cikin
dare naji dawowan shi na fito na bude kofan ya shiga ciki.
Fuska a daure babu walwala nima haka na daure fuska na ina budewa na wuce zuwa
ciki abina na kwanta.
Da safe kafin na fito yayi sakkon barin gidan duk da yake weekend ne a lokacin
amma sai da ya fita gidan .
Can yan iska irin shi fada ya hada su sukai mashi dukan tsiya akan Liliyan Allah
ya rama min ya dawo gida jina jina dashi.
Nan ya zube min a falo yana kwala min kira na fito da sauri yace taimaka min da
ruwan zafi na gasa kafa na.
Nai kamar kada insa sai na tuna da hadisin da kecewa Aljanan ku na karkashin
kafan majajen ku.
Da taimakona ya samu ya gagasa jikin shi da kyan ya samu barci koshi sama sama da
safe jikin yai masa tsami sosai.
Kwana biyu bai iya ko dagawa nan yan iska suka shiga shigowa gida maza da matan
su wai sun zo gaida shi.
Naga mutane iri iri a gidan wurin dubiya sai na kara tsunke ma alamarin shi a
raina nasan ba karamin dan duniya bane ashe nake zaune dashi .
Harda maza masu kitso mata masu dan buje iya cinya da sauran su inaji harda
shugaban yan giyan lagos yazo gaida shi wasu in sun zo su bani alheri in sun tarar
dani a falon wurin shi don boyewa yake cewa nayi kada su ganni wai yana jin kunya
ace nice matar shi.
Gashi ina jinya shi amma sai zagina yake ba kakautawa ranan sai ga mahaifiyar shi
tazo ankawo ta ta gaida shi nan na dan ji abinda ya faru da kyau wurin ta.
Sun sha sun bugu ne sai wani yazo yaja liliya sai ya hana su kuma suka tarar
mashi sukai mai dukan tsiya sai da aka kwace su.
Abinda yasa bai je asibiti ba yan sanda zasu cisu kudi sosai ne shine akai rufa
rufa yake jinya a gida.
Bayan su gwago sun tafi daki na shige naki fitowa yai kira kamar may naki fitowa
waje da ya matsa min sai na leko nace kira karuwan ka tai jinyar ka mana .
Ita da kaje fada don ta da ya dauka baza iya ba sai yaga na koma daki na rufo
kofana nabarshi zaune a falon.
Zagi kan na sha shi a wurin shi amma baisa na fito ba sai da safe na fito yana
zaune yana gyan gyadi saman kujera yana jin motsina ya bude idon shi da sukai ja
yace don Allah taimaka min nai brushe kafan nan ya matsamin da ciwo.
Nace karuwan da kai fada a kanta bazata tai maka ma bane ai ita ya kamata tai
jinyar ka ba ni ba.
Ya marairaice yana cewa don Allah taimaka min asibiti zan koma a duba min kafar
kamar zan share shi sai dai na taimaka mashi yai wanka.
Ranan harda sallah akayi amma saidai a zaune ya ban kudi wai a sayo abin karyawa
na safe na hada yace na taimaka mashi yaci sai wani cika nake da batsewa.
Yadawa asibiti da rana sai ga yar iskan ta shigo muna gida da kawayen ta nan
suka zube falo ana ta tafka iskanci da iya shege a folon namu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , ,
1🧕🏿818
1️⃣
1️⃣
8️⃣ 8️⃣
YAR UWA NOVEL NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KAR KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,
Satin shi guda cur a gidan yana zaune yana jin ya Lilliya takar itake jinyan shi
kusan ma a gidan take kwana nai magana ya zundumi ubana tun lokacin ban sake kallon
su ba.
Idan dai gari ya waye zan masa ina kwana da yaya jikin idan tana kusa zai amsa
min da kyat kamar baya son gaisuwan nawa.
Sai in bata kusa zan samu ya dan amsa min har yasani wani abin in mashi ranan
maman biyu tazo duba shi ta samu Lillya mane dashi.
Ya dan ji nauyin hakan amma abin su na yan duniya sai bai nuna a fili ba ya basar
ta kasa yin shiru tace wanan fa da take manne dakai haka.
Matar kace ko mai, sai yadan yunkura yana cewa No kawatace take dubani.
Kallon mamaki taimai tace amma kasan hakan ba daidai bane agidan ka wata karuwa
zata shigo