Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
shi ina kallon yadda ruwan da ake kara mai yake shiga jikin
shi.
Yaya Saadu bai dawo wurin shi ba haka yasa na dauka ko ya wuce office din sune
ashe yaje ya sawo wani magani ne da fruit da dai wasu abubuwa.
Da ido yaya saadu yayi min magana na biyo shi muka fito daga dakin a falo muka
tsaya ya juyo yana fuskanta na tare da cewa ki kwantar da hankalin ki.
Insha Allahu zai samu lafiya zazzabi ne mai karfi yadan bugeshi kin san mijikin
baya hutu sai irin haka ya kasance dashi.
Kamata yayi ace ya ware wasu ranaku da zai rika zama gida ya huta don jikin
nashi bai maison wahala bane ko kadan don Allah ki san yadda zaki kawo mai wanan
shawara nima zanyi nawa kokari inga na fahintar dashi.
Nace na gode yaya yace shi zai tafi don suna da aiki akwai kayan da zasu shigo
masu daga waje zai je yaga komai ya kammala a wurin.
Na sake mai godiya yace ba komai wanan ai duk ya shafe mu har zai tafi sai ya
juyo yana fadin don Allah kada a tasheshi idan ba shi ya falka da kansa ba.
Mummy tafito jin muryan yaya tana fadin zaka tafi ke nan yace eh zai koma wurin
aiki sai dai an jima zai dawo ya duba jikin nashi.
Bayan mun dayi magana da mummy na koma dakin wanda har lokacin ya sharar barci
sai dai dan hannushi da ya dan karkace mai na gyara mashi a hankali hakan bai sa ya
falka ba daga barcin da ya samu din.
Zaune nake na kura mai ido daga saman kujeran da nake zaune zuciya sai faman sake
sake take min a kan shi ban sani ba har barci ya dauke ni a wurin mai nauyi nima.
Ban san tsawon lokacin da na dauka ina barcin ba shi ya fara falkawa ya hangoni
zaune nake barci tausayi na bashi.
Don yasan wai gadin shi nake a haka barci ya dauke ni a gurin ya dade kwance yana
kallon yadda nake barci a wahalce daga zaune.
Ga ruwan dake makale a hannun shi saura kiris ya kare a ledan jin kamar motsi
yasa na zabura shi na gani a zaune yana cire roban ruwan a hannun shi.
Da sauri na mike na isa wurin shi ina fadin ka tashi yaya jikin na ka ina kokarin
taimaka mai da ledan ta hanyar rataye ledan da allura sama.
Sai da ya dan dade zaune ba tare da yayi magana ba sai ya mike zuwa ban daki ya
dan jima ya fito tare da dauro alwala zai yi sallah.
Nace dashi lokacin sallah yayi ne yace kina barci ina zaki san lokaci yayi anya
haka ake jinya mai jinya barci mai ciwo barci ni dake wazai dubi wani a haka.
Murmushi nayi ina shimfida mai abin sallah tare da cewa wallahi ban san lokacin
da barci ya daukd ni ba a haka zaune bai magana ba sai murmushi ganin ya tada
sallah na nufi dakina don nima in gabatar da nawa sallah.
Na dade zaune bayan na idar ina kai kuka na ga Allah yabamu lafiya ni da mijina a
wuri san nan na mike na fito abinci na fara hada mai nakai mashi.
Har lokacin yana zaune yadan kara jikin shi da bangon dakin kamar yana tunane na
shigo dauke da abincin na zauna bayan na aje mai a gaban shi.
Ya dago kai yana kallona tare da da fadin zan ko iya cin abincin nan da dai fruit
kika hado min watakila zan iya dan sha.
Nace uncle kayi ko two spoon ko three zaifi ka zauna bakaci komai duk yinin yau
hakan zai iya jawo ma wani matsala kuma don Allah kadan daure kaci ko kadan ne.
Baiki ba na zuba mai ganin baya son ci yasa na karbi cibin a hannun shi ne debo
nakai mai a bakin shi.
Murmushi yayi ya bude bakin ya karbi abincin yaci nima na debo nakai bakina don
dai ya danci Alhamdullahi na samu yaci yakai cibi hudu yace ya koshi.
Mike nayi na kwashe kayan sai ya riko ni yana fadin ke ba zakici ba kin san fa
kin finu lalura sosai kada kije ki haifa muna baby ba kosasshe ba.
Murmushi nayi nace nima fruit din zan sha idan na gyara hakan yasa shi ya kyale
ni na fita da kayan nakai kitchen nan na tsaya na hada muna fruits salad.
Nan mummy tazo ta samay ni ina gap da gamawa take tambaya na yaya mai jikin nace
da sauki mummy har ya danci abinci yanzu.
Tace a da sauki ke nan in dai ana cin abinci ai zai zo da sauki ciwon da ba a ci
ba a sha ai yafi wahala ga mai jinya.
Nace muje ki duba shi mana mummy tace a bana shiga dakin mijin ki ba nace haba
muje dai ai ba a kwance yake ba.
Ina gama mummy na bayana na shigo dauke da bowl din dana hada salad din daga kofa
mummy ta tsaya take gaida shi ya amsa da mummy ne shigo mana.
Bata dai shigo har cikin dakin ba ta tsaya daga kofa tana mashi yaya jiki ya amsa
da mummy naji sauki sosai tace Alaji ka dan dinga hutawa mana haba ga kunan kullun
cikin aiki ba hutu.
Murmushi yayi yace mummy ai aikin nawa mai sauki ne da wanda ke yini a cikin
rana ko yaushe jikin dai ne dama ba lafiya gare shi ba.
Tayi mashi sannu ta fita daga dakin ya mata godiya tana fita na zauna a kusa
dashi tare da fara zuba mai yana zaune ya kura min ido kawai har nagama na miko
mai.
Yakarba tare da fadin thanks gefe na koma na zauna tare da tsura mai ido da ido
yayi min alaman in diba mana sai na kada mai kai tare da fadin ban jin sha.
Yau din baki shan fruits din nace na koshi ne sai naga ya debo ya mika min ba
yadda na iya dole na bude baki ya zuba min amma sai naji yau abincin nawa ya koma
min kamar madaci.
Da kyat na iya hade wanda ya rage min abaki na sai na samu kaina da tura kaina
cikin kafafuna na dunkule a waje daya ina kuka.
Ji na ya kamoni zuwa jikin shi tare da dan bubuga min baya a hankali ba hana ni
kukan ba sai da nayi may isa ta ya mika min ruwa in sha.
Ban ki na karba na dan kurba na aje kofin shidai yana zaune ya kukara min ido
muryan shi naji ya katse min tunanen dana fara yi a lokacin wai may kike ma kuka ne
haka.
Na bude baki nace Uncle bani son in rasaka cikin wanan halin da nake ciki kaine
uwa da uba a gare mu idan na rasaka yaya rayuwa zata koma ?
Sai na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciyan mai sauraron ta kamoni yayi zuwa
jikin shi ya lalashi na wayan shine yayi kara a lokacin hakan ya dakatar damu da
maganan da mukeyi.
Ji nayi bayan ya amsa wayan yana fada min ga yaya Saadu nan yadawo duba jikina
yana falo.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/28/20, 11:45 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , , ,
6️⃣6️⃣6️⃣
6️⃣
🧕🏿 6️⃣6️⃣
Barci mai dadi ne ya dauke ni bayan sallah azahar inda na sallamay sallah a wurin
na kwanta saman ties sai barci.
Muryan mummy nake ji sama sama a cikin barcin nawa take fada min ga dan uwan ki
nan yazo da kyat na bude idanawa na ganta tsaye akaina.
A cikin idon barci nake magana da ita nace mummy kina magana ne tace eh dan
uwanki ne yazo daga gida.
Da sauri na mike zaune don nasan da zuwan yaya sani din a lokacin na dan jama
zaune bayan mummy ta fita daga dakin .
Na fito yana zaune yana cin abincin da mummy ta gabatar a gare shi cikin jin dadi
da ganin shi ina murmushi nace yaya sani kaine a garin yau?
Shima murmushi yake da gani na yace wallahi nine Safiya ai tun jiya naso zuwa to
nakai su babane da ummi wurin alluran mahajta shiyasa na bari yau na taso.
Nace Allah sarki kuna kuna shirin tafiya zaku taka kasa mai tsarki abinku yace
wallahi kin ga ikon Allah ke nan Safiya.
Ai maganan baba kullun yanzu akan mijin ki yake yana yawan cewa bai san itin
adduan da zaiwa bawan Allah nan a rayuwan shi ga gida kuma ga makka kusan lokaci
guda.
Nace haka abin Allah yake sai yazo ma ta inda baka zata ba a rayuwan ka na fadi
ina zama kusa dashi.
Yace wai naso ummi taga yadda Safiyan ta ta koma kamar wata irin hajiyan birnin
nan wallahi safiya haka kika koma yanzu.
Dariya nayi mai nace kai yaya sani ho yau kuma yar kaunar taka kake zolaya
haka ?
Yace wallahi ba zolaya bane kin koma din ne yace ashe maigidan ya fita waje sai
yanzu nake ji a wurin mummy da nazo gashi kuma shiyace in shigo a cikin satin nan.
Nace ai ina ganin yaya Saadu ne zaka hani don yabar sakon ka a gunshi koda yake
ba,ayi dani ba amma kamar sakon na babane.
Yace kuma dai baba bai sani ba da bai bari nazo ba don sai da yaja min kunne tace
kada in yarda yace zai yimin wani dawainiya gidan zumu ba kasuwa bane.
Murmushi nayi Allah ne kadai zai saka mashi da alherin sa ai amma Uncle yana
dauwainiya dayawa wallahi bamu kadi harda yan uwanshi haka yake fama dasu suma.
Yace haka aike so indan ka samu yan uwanka ma su su san ka samu ba kazo masu
inuwar giginya ba hange daga nesa.
Fitowar Mummy daga daki ne ya katse muna magana inda take tambayan shi Rukkaiya
yace tana can gidan mijin ta ai yanzu.
Nace banko tambaye ka labarin mutanen gida ba mun zauna muna zuba hira yace
cikin dariya kowa lafiya lau yake wallai.
Nan itama ta zauna mukai ta hiran gida dashi yana bamu labarin kasawar shanun
baba da yadda abin yazo mai amma baba ya rabe wa mutane naman duka yace shima ai a
alheri ya samu ya saya.
Sai da akai kiran sallah laasar yafita sallah muma muka kama gaban mu daga can ya
fice gidan ya nufi gurin yaya Saadu.
Na idar da sallah ke nan waya na yayi kara na dauka hajiya baaba ce ke kirana
da ladabi na amsa wayan kamar tana gaba na a lokacin.
Mun gaisa da ita take tambaya muna dai lafiya nace mata lafiya muke tace ashe
shi yayi tafiya ne kuma nace hajiya bai fada maku bane ?
Tace ina zai fada muna don yasan in ya fada bazan barshi ya tafi cikin yadda
tsufa din nan nace ai lafiya nake hajiya tace to aidaiyi ta hakkuri kin dai san
yanayin mijin naki yanzu ba wani don haka zama tare sai da hakkuri nace nagode
hajiya.
Tace yaya wurin su Aisha nace ta kwana biyu bata shigo ba amma dai lafiya take
dai tunda naji shiru munyi sallama har zata kashe wayan naji ta tambaye ni.
Yanzu ke kadai ne a wanan katon gidan naku dariya nayi nace hajiya ai akwai
mutane agidan yan aiki suna tare dani ban yarda na fada mata mummy na gurina don
ban san yadda zata fasara abinba.
Tace hakan yayi ni dai ba zaku ganin ba sai idan Allah ya sauke ki lafiya zan zo
inga jika na tunda nasan ba a nan zaki haihu muna ba.
Nace haka dai ummina tace bazata zo gida na ba sai na haihu tace ai shine mutunci
ina dadi kullun kana yawo gidan dan ka.
Tasan mutuncin kanta ne tunda ta fadi hakan nace indai ummi ne hajiya nasan ba
zuwan zata yi cewa zatayi ga iyayye na da yawa su zasu zo tace wanan shine daidai.
Kada kiga laifin ta dariya nayi nace amma ai hajiya mu bamuki ko yaushe mu ganku
ba in zamu samu.
Ina jin dariyan ta tace bakuma zaku samu ba mudai fatan mu ku zauna lafiya shine
adduan mu kullun akan ku.
Mun gama wayan naji dadin yadda hajiya ke jana a jiki tana nuna min kauna kamar
yar cikin ta ko yaushe.
Wayan na jona charji zan fita daga dakin sai ya koma yin kuka na juya na dauka
anty ce ke kirana saida gaba na ya fadi dam.
Na dauka da sallama muka gaisa tace kwana biyu najiki shiru nace barin in kiraki
nace wallahi anty banjin dadi ne shiyasa ban kiraki ba kwana biyu.
Tayi min yaya na kara ji nace naji sauki ta dora da fadin kodai abin arziki ya
samu ne kin ga ai magana na nafita yanzu sai mu tara kudi da tushe.
Zuwa haihuwan ki mun san abin da muka tanada ba sai dai kawai aga muna bushashan
mu ba da kudi amma kin tsaya kina noke noke.
Ke barin fada maki duk wata mace da kike ganin tana heleke da haka ta tara ga
gumin mijin ta amma ke naga tsoro yayi maki yawa baki karban kudi yadda ya dace ki
tatse shi.
Murmushi nayi nace anty matsalan shi baya bada kudi ne sai dai yayiwa mutum
hidima tace aike zaki koya mashi bayarwan .
Yanzu dai kin ga kin samu ciki kila don haka sai ki mayar da hankali kafin
haihuwar ki musan abinda muka samu a wurin shi.
Ni dai murmushi nake mata kawai nace anty zanyi yadda kikace din idan ya dawo
tace ina ya tafi nace yaje Spain ne.
Allah dawo dashi lafiya tace tana kara jaddada min in yi kokari ina yagan wani
abu a wushin nace mata to anty tana fadin nan da yan watanin ai mun tara maiyawa
yanzu haka daddy su twins ba karamin karba nake a wurin shi ba kin gani na.
Kokari nake yanzu in fara sanaa in bar wanan aikin nagaji dashi wallahi kullun
mutum baida hutu a rayuwan shi yana hanya aiki.
Nayi mata godiya muka kashe wayan fitan da banyi ba ke nan na zauna ina tunanen
maganan mu da ita yadda zan mu kwashe a karshe.
Don dai ni ban fada mata ina da ciki har ya tsufa a jikina ita da ke maganan nan
da wasu watanen masu zuwa can.
Nidai buri na shine in samu mu rabu lafiya da ita don haka na yanke shawaran tura
mata wasu kudi da ya bar min a gida don kawar da maganan.
Bayan sallah magariba su yaya saadu da yaya sani suka shigo gidan na fito falo
wurin su nan muka zauna muna gaisuwa dasu.
Yaya Saadu sai sheri yake min wai na tsufa sosai na wani kara girma kamar bani ba
kodai biyu na kwaso masu ne ?
Dariya na kece dashi nace aida sai Samira ta dawo gidan nan don ba zamu iya mu
kadai da mummy ba.
Yace kina wasa mummy sarai ta iya rike so akwaita da kokari fa nace ai na gani
wallahi itace ra fito daga daki tana masu sannu da zuwa.
Ta tambaye shi mutanen gidan shi yace suna lafiya yaji suna fadin gobe anan zasu
wuni ai nace nikan ai saidai kuyi hakkuri dani yaya .
Don Allah ya hada ni da miji mai kule yace ai shi yafi Safiya mace mai yawan yawo
ai bata da dadi sai da aiyi hakkuri kawai.
Mummy tace banda samira don ko dazun ta kirani wai suna kasuwa yayi saurin kare
ta da fadin sun je sayayya ne fa mummy .
Don ni banda lokaci shiyasa nake bata kudi ita taje tace kudai zama yan bariki ai
kaida matar taka dariya yayi yana kare matar shi wai ai bata da yawo.
Yaya sani ya kawar da hiran yace Safiya ki ji mijin ki wai ashe shanaye yake
son sai wa baba .
Ido na zaro waje yaya Saadu yace yasan shanun baba ya kasa ne ko nace eh da yaya
sani ya bugo waya muna tare anan yaji amma bai mun magana ba tun lokacin.
Yaya yace ai ya fadi don yace wai kada a fada maki nima next week nake son mushi
wirin su muyi sallama don zuwa wani satin sama zasu fara tashi.
Mummy tace nasan dai kafin su daya suna samun kin haihu nace mummy tun yanzu tace
laila da wuya in ba hakana zai faru ba kan.
Nace wai idan na haihu ummi bata kasan sai yaya sani ya tare ni da cewa ba aikwai
mutane a gida ba sai wayanda ke nan suyi buki mana.
Shiru nayi dan tuna katobar dana so yi a gaban shi nace ai fa akwai mutane kan
dayawa a gida zan dai ga yan gida kan.
Munyi hira dasu inda yaya Sani yace zai bi yaya saadu gidan shi ya kwana
washegari samako yake son yi kada a nemay su baya nan.
Nace wai Alhaji sani ke nan yace bari ke dai Safiya har fa mutane sun fara kirana
da Alhaji wasu ma gani suke da farko kamar karya ne ba zan tafi ba.
Nace wai ina yaya Nura yace yana nan wallahi ai yaso ya bata rai sai da mama ta
fita bayan shi ya shiga hankalin shi.
Nace ya sani ko idan zamu tafi badi in Allah yakai ran mu muje tare yaya saadune
yace dayake shi baida aiki sai kai yan uwan ki makka ba.
Dariya mm ayi tare da fadin yaya Allah ne ya kawo mu lokacin hutu mummy tace don
haka sai a huta kuwa ai lokacin abu ayishi.
Mun dan jima muna hira mukayi sallama suka tafi mummy ta hada min abinci wai inci
ban son ci amma dole tasani gaba dole na ci shi.
Daki daya muke