Advertisements
Chapter 25 Reading Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   25 / 87

72K to 75K   out of 258.3K words

to waya ja wanan matsalar haka karamar yarinya da ita ta
iya kishin tsiya.
Yanzu ai sai ki koma gida kuje kuyi ta zaman gida ai kin san abinda kika baro
gidan naku ba wani abu ya canza ba.
Tsam anty ta mike tace dani tashi muje Safiya akwai Allah duk wanda ya cuci wani
a cikin ku Allah yana ganin sa ai.
Haka na muka fice gidan muka barta nan tana ta faman fada abin dai zabar kunya
don bai ma faduwa .
Gidan mama biyu nai kwana biyu ta rakani gidan na dauko abinda nake so cikin
kayana washe gari na kama hanyan arewa acikin motar da akai min shata sai gida.
Asubanci mukayi amma sai dare muka kai garin mu lokacin da mota ya tsaya kofan
gidan mu an shiga sallah isha,i .



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , ,


2️⃣
5️⃣


YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDINE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU
PLEASE, , , , ,


Cikin wata daya da nayi a gidan mu cikina ya karasa shiga wata na tara duk da nace
ma ummi da mama bansan ko wata nawa cikin yake ba.
Amma su daya ke manya ne sun gane na shiga watan tara nan aka shiga min jikile
jike ana bani.
Don samun saukin haihuwa wai idan haihuwa yazo vazan wahala ba sosai indan ina
shan abin karya zaki.
Watarana da dadare ina cikin barci na farka da matsanacin ciwon mara da ban taba
jin irin sa ba, wai ashe nakuda ya kamani .
Cikin barci na dinga tada ummi na daga barci ina fadi wayyo ummi bayana marata
ciwo kamar zai fashe min nake jin shi.
Ummi ta tashi a rude take tambayana ya nake ji na fada mata, fita tayi daga dakin
taje ta tada mama sai gasu sun dawo a tare da mama din dakin.
Nan suka fara bani abinda ya dace da akewa mai na kuda da fada min yadda zanyi
abin yazo min da sauki.
Abu wasa wasa har wuraren karfe sha biyu na rana ba labarin haihuwa gashi ina
dan banzan wahala.
Don haka suka yanke shawaran su kaini asibiti don ina wahala sosai na gala
baita matuka na wahala a gida.
Mun isa asibiti aka duba ni suka ce haihuwa ne sai dai bazan iya da kaina ba don
haka za ai min theater ne.
Bani dake wahala ba harda su mama da suka kawoni sai da hankalin su yai matukar
tashi, aka rubuta masu abinda za a sayo kafin theater din.
Baba ya fara fadi tashin neman kudi don ya sayo maganin da sauran kayan aikin don
baida kudin a hannunshi.
A cikin karfin hali na daure nace baba akwai kudi a hannuna a tambayi ummi na
agida ta duba zata gansu.
Allah da ikon shi anshiga dani dakin theater sai Allah ya kawo min saukin haihuwa
na nisa sai abin cikin cikin nawa ya fito.
Ashe abin da matsala ne shiya sa na wahala diya ce mace sai dai tazo da wani irin
halitta na daban likitoci suka taru akan mu suna dibata.
Daga karshe dai hakana dai aka sallamay mu muka koma gida da ita cikin yanayin da
tazo.
Sai dai mama ta hana abawa kowa yar ya gani tana dunkule a raggan zani duk wanda
yaga abinda yarinyar keyi dole ya tausaya mata.
Karamar yarinya da bata dauki alhakin kowa ba a kanta tana bautar Allah cikin
wani yanayi na ban tausayi.
Amma ita inna har kiran mutane take su zo su aga abinda na haifa mutane ko sai
suka fara tururuwan zuwa ganin halittan yar.
Kwana daya da haihuwa Baba ya shigo gida da dadare yake ce min yaya za a yi a
samu su gwago can lagos a fada masu zancen haihuwan nawa.
Na lumshe ido nace baba aida a kyale su kawai, yace aa baki da hankaline yarsu ce
fa suna da hakkin a fada masu ai.
Sai nace sai dai yaya saadu don shi kawai nake da nomban shi wayan shi cikin su
bayan shi ban da lanban kowa cikin su.
Ko shi da yazo ne yaban wayan da zo dashi shine har na samu namban shi din, da
ban da layin kowa a cikin su.
Yaya sani ne yakirashi sai baba ya karba yana fadama mashi zancen haihuwan yayi
murna sosai dajin na haihu lafiya da Allah ya saukeni lafiya ba tare da anmin aiki
ba.
Sun gama da baba yace a bani wayan yai min barka na karba cikin jin kuya nake
karba mai yace da ya kashe zai kira mummy da Ahmed ya fada masu na sauka lafiya.
Hakan ko akayi nan ya kirsu ya sheda masu zancen haihuwan nawa sai dai ba wanda
yai farin ciki da jin haihuwan daga cikin su.
Shima gogan daya kira shi cewa yayi and so what idan ta haihu may kake son nayi
mata yanzu kuma ?
Ashe lokacin suna tare da Liliya ne ya kirashi don haka baida halin nuna farin
ciki da haihuwan nawa.
Nan dai dan uwan yai mashi tas yakuma ce indan baiyi hankali ba sai ya hada shi
da hukuma akan wanan case din.
A haifa ma ya kace min and so what kai wani irin jahilin mutum ne wai kana koda
inmani kuwa kai ?
A cikin fushi ya nufi gidan su yana fada ma mahaifiyar su yadda sukayi da saadu
din wai ya kira shi da jahili.
Tace ai gaskiya ya fada maka dole ne ai a fada muna san nan ai wani abu daga nan
wurin mu kuma ya zama dole mu tafi yace wa ?
Cikin hasala shi ba inda zan tafi indai ke zaki tafi ban hanaki ba amma nikan ba
inda zan tafi tun wuri .
Don nasan a jirace suke damu yanzu kuma sun samu kafar samun mu ke nan don haka
ni ba inda zan tafi final.
Saadu yazo yasa uwar a gaba son su hada abinda zasu sai mu na kayan suna suzo
muna dashi, mahaifiyar nasu tace bata da kudi yanzu a dai tambayi Ahmed din.
Gogan da aka tambaye shi dubu goma kawai suka samu a wurin shi wai baida kudi duk
karuwai sun cinye kudin shi da giya dole yaya saadin ne ya fitar da kudi ya sai
muna abinda za a zo dashi din.
Sun saka ranan tafiya saura kwana biyu suna munyi waya dashi nai mashi kwatancen
gidan maman biyu don yaje ya fada mata.
Ya ko je tayi murna dajin na haihu din ta karbi lanba na a wirin shi ta bashi
abinda zai kawo min sai dai bai gwadawa mahaifiyar ta suba.
Da dare ina zaune a dakin mama don anan nake jegona sai naji wayana na tsuwa
alaman kira ya shigo min .
Na dauka da sallama muryan wace najine ko a barci na falka ina sheda shi maman
biyu ce ta kirani, na dan kwala ihu do jin muryan ta, tace dani.
Ai nayi fushi dake nace anty ba hakana bane wallahi kullun kina a raina ban san
yadda zanyi in kiraki bane.
Don lanban da kika bani ya bata nan dai muka taba hira da ita take tambayana
yadda muka kwasa da mahaifin mu da nazo gida ?
Ta fada mata komai harda zuwan yaya Saadu wurin mu da yadda ya wanke ni a gaban
su baba da sauran yan uwana.
A karshe mukai sallama da ita tace zan ga sako wurin yaya saadu idan ya zo nai
mata godiya na kashe wayan.
Idan na kalli yarinyar tausayi take ban don yadda take wahala matuka taita murde
murde da hannu idanuwa warwaje tana wani irin numfashi a wahalce kace ko zaka je
kadawo kasamu bata da rai.
Mama ce ke kwana wahalce da ita har safe sai a kama mata tadan kwanta da rana ta
runtsa barcin ba wani barci ba take tashi.
Da aka ga wahalan yai ma yarinya yawa aka koma asibiti da ita likita ya tambaye
ni idan na taba mugun faduwa da ciki.
Nace a a yace duka fa kowani buguwa mai karfi sai nai shiru mama tace mijin da ta
aura yake dukan ta da ciki likita yace wanan abun ne ya taba yarinyan tun a cikin
ciki yasa tazo kamar jujartata.
Hawaye na fara yi ina tausayin yarinyar da kaina, magani aka rubuta muna muka
dawo gida rai baci tun a mota mama ke ta zabga fada tana cewa mutane ba imani haka
?.
Yanzu gashi ke ke wahala shi yana can yana barikin shi hankali kwance abinshi.
Mun iso gida mama tana kuka tana ma mutanen gida mu bayani komai da likita ya
fadi.
Allah ya isa yaya sani suke ta ja baba baki ya mutu da har ya fara cewa in gwago
tazo sai in hakkuri in koma dakina.
Wai kada yarinya ta tashi ba uba tare da ita maganin da likita ya bayar a bata
shi ake bata kai da kai sai numfashin ya fara ragewa ya dan fara komawa nomal.
Su yaya Saadu sun taso kamar yadda suka shirya ba isoba sai da safe don tafiyan
dare sukayi.
Tun da ya shigo yagga yadda yarinyar take hankalin shi yai matukar tashi sosai
gwago tun taron da yan gidam mu sukai mata ta shiga tsarguwa.
Mama na kuka take fada masu abinda likita yace a gamay da yarinyar yaya yace
komai akace ya faru ne ba a kyauta ba gaskiya amma ayi hakkuri.
Suka bayar da abinda suka zo dashi wanda ni nasan yaya saadu ne yayi shi don
nidai duk zama na gidan bai taba yin min sutura ba.
An karba da godiya sai gwago tace adai yi hakkuri dashi mama tace ba a dai kyauta
ba gaskiya malam ya bada yarinyar don zumunci ya dore gashi abin kuma baiyi dadi
ba.
Baba sun zauna da gwago ya nuna mata bacin ran shi sosai ga irin rikon da dan ta
yai min acan har da nata laifin ma, sai ta kama kukan munafunci wai yara zasu bata
masu zumuncin su.
Baba yace basu bata muna zumunta don ba su suka hada mu ba balle su yanke muna
zumuncin mu.
Nan ta danji sauki har ta fara aibanta ni wai ban da kirki banda tatali banda
sanin ya kamata ko ita rashin kunya nake mata..
Sai da yaya saadu ya bari ta gama ya kawo matsalnta duk ya fada ma baba da yadda
tabar tarbiyan su ya lalace komai ya fadi.
Sun dade suna magana baba ya san yi mata nasiha har da alkwarin wai zai mayar
dani dakina yace dasu.
Ana gobe sunane sun zo washe gari da safe yarinyar ta koma Allah ya gani banji
bacin rai da rashin ta ba don a halin da tazo da ta rayu wani gwamma ta koma yafi.
Nan dai aka kawar da ita yan uwana sun tausaya min sosai nidai abu ga kurciya ga
bacin rai banji komai ba a lokacin.
Sai gwago ta kebe da yaya saadu da mama wai a rage abinda suka zo dashi tunda
yarinya ta koma nan yaya saadu yai cikin ta.
Yace indon dubu goman da Ahmed ya bayar kike jin zafi ga dubu goma ki mayar mai
da abinshi ban iya abin kunyan da kike shirin yi.
Mama tace wai ko Rakiya kan ki daya kuwa may yasa abin duniya yake rufe maki ido
haka ita yarinyar da tai wahalan haihuwa fa ?
Nan dai suka yi shi baran baran sai da rayuka suka baci masu, washe gari suka
daga suka koma inda suka fito.
Bayan wucewar sune mama ke mayar da yadda suka kwashe da gwago kan kayan nace mama
aida kun mayar masu da abinsu ma.
Don ni bani son komai da ya fito daga wurin Ahmed sai mama tace ai ai a she shi
dubu goma kawai ya basu su kara.
Duk kanin ne yai sauran kayan da kuka gani uwar bata sako komai ba ni bansan inda
Rakiya zata kai son kudin ta ba wallahi.
Nan nake basu labari ai ko zuwa nayi gaida ita bata bani abinci sayarwan ta sai
ansaya mun zan ci.
Kowa yai tir da irin hali nata na son kudi da rashin taimakawa uwan uwa kullun
tazo sai kukan babu takeyi.
Maman biyu ta bugo min waya da dare tana min barka da taro ya watse lafiya ?
Murmushi nace anty ai yarinyar ta koma jiya nan dai nake fada mata yadda akayi da
abinda likita ya fada akan ta.
Tace kin ma huta wallahi Allah ta baki lafiya yasa ita kuma ta huta nace amin nan
dai mukai hira tana tambayana yadda aka kwashe da gwago tazo nake fada mata komai
karshe nai mata godiyan sakon da ta aiko min mukai sallama da ita.
Tun da akai sati na dan watsake ina yin komai sannu a hankali ina mai da jiki na
ina harkokina na yau da kullun sai dai ban fita ko ina ina gida koda yaushe.
Dan dama dama naka dan dauki lokaci in fita ziyaran yan uwa ban dadewa in dawo
gida don ko na fita sai na tsargi kaina don ban son a dauko min maganan zama lagos.
Sana a nake gadan gadan kanena ke fita mun dashi don haka hankali na yadan kwanta
har nakan manta da rayuwan gidan Ahmed din da nayi a baya.
Zan tura kudina wa maman biyu da kudi sai ta sayo kaya ta turo min dashi ta motar
haya a kawo min.
Haka nake har na dan samu nawa sai kuma kyashi da hassada ya shiga zukatan Inna
da wasu yaran gidan namu zaka ji ana sake magana akan sanaa nawa a tsakar gida koda
yaushe.

********* ********** *********
Hai huwana da wata uku na dan fara ciwon kai sakuma yawan zazzabi da yake biyowa
akai akai.
Ranan ina kwance yaya saadu ya bugo min waya na mike da kyat na dauki wayan
tare da sallama yanayin murya na da yaji yasa yace baki da lafiya ne Safiya.
A hankali na bashi amsa da wallahi yaya kwanan nan duk kai da zazzabi ke yawan
damu na na rasa gane kan jikin nawa.
Yace subbahanallahi kin kuwa je asibiti nace ban je asobiti ba ina dai shan
magani a gida ne yana min sauki in na sha magani ai.
Yace No kije asibiti a duba lafiyan ki asan may ke damuwan ki yafi sauki da shan
maganin nan da kike yi nace naji yaya zan tafi.
Mukai sallama yace dama ya bugo ne yaji lafiyana tunda suka koma bai samu kirana
ba sai yau nayi hakkuri nace nagode kwara muka sallama yana kara jaddada min akan
in tafi asibiti fa nace zan tafi ai.
Kwana biyu na ji sauki nikan na manta da zuwa asibitin da mukayi dashi naci gaba
da harkokina kawai.
Kamar naji sauki da jikin zai tashi mun sai yakaini kwace kasa nai ta faman jiya
a gida ina zuwa chemist ina karbo magani na dan ji sauki.
Ban san yaya akayi yaya saadu ya samu lanban yaya Sani ba ya buga mai yana cewa
ya kirani wayana a kashe.
Sai yaya sani yake ce mai ai banda lafiya ne kwana biyu kila na kashe wayan ne .
Yace subbahanal lahi kon ka kaita asibiti andubata yace dashi a a ina ganin
bataje asibiti ba yace da yaya sani don Allah akaini a dubani.
Shi zai turo da kudin zuwa asibitin haka ko akayi amma da yaya sani yai magana
gida akace mai dahuwan kassa nakeyi tunda banyi ba da na haihu sai yanzu nakeyi.
Sunyi waya dashi yaya sani ke fada mai abinda akace ya matsa wa yaya sani aka ya
kaini asibiti fa yanzu ba a wasa da ciwo gida.
Har na dan ji sauki kwana biyu kuma sai jikin nawa dawo fiye da farko dole muka
kwasa sai asibiti.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , ,



2️⃣
6️⃣


YAR UWA NOVEL DIN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLESASE,
, , , , , , , , ,
Mun yanki kati muka bi layin ganin likita a tare da sauran jamma a da muka samu a
wurin.
Sannu sannu har layi ya kawo gare mu muka shiga wurin likitan bayan yan tambayoyi
sai ya tura mu wurin yin test.
A can ma mun dan bata lokacin mu a wurin don mutane da sukai yawa masu son ai
masu test din.
Mundan jira suka bamu sakamakon mu koma wurin likita dashi muna zaune a gaban
likita dani da baban mu da yaya sani.
Munyi zaune shiru ya gama rubutun da zai yi ya dago kai yace baba wanan yar kace
?
Baba ya gyara zama yace kwarai kuwa yata ce wanan kuma wan ta, sai likitan ya
sake tambaya tana da aure ?
Baba ya dan kara gyara zaman shi yace eh to ta dai taba auren yanzu wata hudu
kenan da mijin ya sakota da ciki ta dawo gida wata uku kenan da ta haihu goyon ta
koma.
Sai likitan ya girgiza kanshi alaman tausayawa gare ni ya sake tambayan baba
yanzu ina mijin nata yake muna son ganin shi, shi mijin nata.
Baba yace ayya ai ba nan yake ba can Lagos yake da zama da iyayyen shi shiru
likitan yayi yasa biro da yake rubutu a bakin shi kamar mai nazari.
Ya dago yace baba indan ba damuwa su fita waje muyi magana dakai sai baba yace ai
ba damuwa likita duk diyana ne indan kaga wani matsala ne kafadi muji.
Sai

25 / 87