Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
dauke da leda da lemo da ayaba a ciki ya nufo dakin ya shigo ya
samu na farka.
Ina zaune ina dan matsa kafana a hankali don haka likita yace dani nayi sai gashi
ya shigo dakin babu kunya babu alamunta ya samu wuri ya aje ledan dake a hannun
shi.
Yazo ya zauna a kusa dani ga mamakina sai naga ya fara wade ayaba a hankali ya
miko min sai na girza kaina alaman a a yace likita yace abaki abin gina jiki saboda
haka kici wanan nan.
Yayi niyar wai bani har a baki don yaudara sai na ki karba sai dai ya wade min na
karba nakai a baki da kyat.
Naci kamar kwaya uku da kyat don bakina bai da dadi nace ya ishe ni sai ya mayar
da ledan ya aje gefe daya ina zaune na langabe kaina a karfen gadon da nake kwance.
Sai naji ya kamo hannun da yafi mun ciwo na dan matsawa a hankali sai da nai
kara, yana fadin ai sannu zai warke ya bar ciwo da yake na zugi.
Ban kai ga bashi amsa ba sai ga matar da nake cewa maman biyu mutumiyar kirki ta
dawo niki niki da su flask da ledoji da wata yar budurwa bayan ta.
Suka samu wuri gefen gado na suna aje kayan da suka shigo dashi din tana cewa a
she kin falka sannu yaya jikin ina sauri karki falka babu abinda zaki ci anan.
Yana zaune ya dukar da kanshi kamar maijin nauyi da kunyan ta sai can tace wanan
ne mijin naki ko sai lokacin ya dago yake cewa da ita sannu da zuwa.
Yana kokarin mikewa tsaye ya fita tace dashi No zauna abinka ai tafiya zanyi don
ba dadewa zanyi ba dama wanan kayan na kawo sai yarinya da zata dan zauna da ita
don naga kaunar bata son zama da ita.
Ya dai mike yana cewa zan dan tafi nan bakin get ne na sayo abu sai ya fice
tabishi da harara tana cewa mara mutunci kawai sai ta ja tsuki nasan haushin sa
take ji har cikin ranta.
Tace wa yarinya Nafisa dan zauna anan bakin gadon barin zuba mata abincin nan
kadan ta danci.
A sanyaye nace nakoshi maman biyu tace da sauri may kika ci da kyat na bude baki
nace ayaba naci sai ta kalli wurin ledan ayaban da ya aje tace ina wanan bawan da
nagani shi kika ci.
Na kada mata kai alaman eh,
Sai take cewa idan kika biyewa wanan mijin naki mara mutunci kina tunane sai
ranki yai ta baci ga banza.
Nan ta zuba min ta jawo kujera a gabana ta zauna ta debo min zanyi gardama tai
min jan ido dole na karba.
Ina ci ta jefo min tabaya akan auren mu ina bata amsa a hankali har na dan ci
abincin kamar spoon biyar zata karo nace na koshi.
Bata ce dani uffan ba ta aje plate din tare da mikewa tana gyara gyalen kan ta
tana cewa barin koma yara suna gida na barsu.
Sallama tai muna ina mata godiya ina share hawayen dake zuba a idanuwa don tun
tana tambaya nake kuka.
Ta fice tare da jawa yarinyan kuna akan ta kula sosai idan da matsala ta kirata a
waya.
Tai muna sai da safe ta fice daga dakin na dade ina kuka bayan fitan ta dakin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , , , ,
1️⃣
2️⃣
1️⃣
🧕🏿
1️⃣ 2️⃣
2️⃣
INA MAI GODIYA GARE KU YAN UWA NA GODE DA KAUNAR KU A GARENI ALLAH YABA HAKKURIN
ZAMA DA JUNA NAGODE.
YAR UWA NOVEL DAI NA KUDI NE BA YARDA KI KARANTA BA INDAN BAKI BIYA BA DON BA A
YAFE BA, , , ,
Tsaye yake ya jingina jikin shi da motan shi yana busa cigari sai busar da hayaki
yake sama da alaman tunane yake yi a lokacin.
Har ta tako zuwa inda yake tsaye yana shagalin shi bai farga da zuwan ta ba sai
da tai magana ya dawo cikin hankalin sa.
Tace dashi wanan abinda kake yi ba dabian diyan hausawa bane komai na ba haushe
ansa shi ne a cikin kawaici da alkunya.
Murmushi yayi ya jefar da taban dake hannun shi kasa yana takewa a cikin kasa.
Yace hajiya har kin fito kenan tace eh dama na kawo abinci ne da yarinya da zata
zauna min da ita don na lura yan uwan nata basu san zama anan gashi tana bukatan
mai taimaka mata wani fannin.
Angode yace da ita har ta juya zata fara tafiya sai kuma ta juyu tace dashi a
gaskiya wanan dukan yayi muni kwarai da an kai ka ga hukuma ba abin da zai hana su
kulle ka wurin su .
Ya kamata ace ka godewa Allah da yabaka mace irin wanan yarinyar dan babu macen
da zaka doka a yanzu irin wanan batai karan ka ba.
Yace sherin shedan ne akasi akasamu haka bazai sake faruwa ba in Allah ya yarda.
Taima shi sallama ta yafi bayan ta bashi dan shawarwarin da ya dace na zaman
takewa a tsakanin zama ta tafi sai sauke ajiyan zuciya yayi kawai koba komai dai ta
rufa mai asiri.
Don irin wanan wayyayun mata ba a shansu a banza amma ita gashi ta rufa mai
asiri.
Sai wani tunane yazo mashi a rai a ina safiya tasan wanan mace ne haka da har
take mata irin wanan taimakon dole ya sani don gaba.
Sai da na kwashe kwaki sati a sibitin san nan suka sallamay ni kudi dai ya sha
kashi sosai na dawo gida har lokacin dari dari nake dashi don nasan mai hali baya
fasa halin shi.
Zaune muke a falon da Maman biyu ta wade min lemon da zan sha sai ta tambaya
labarin auren mu dashi
Ban boye mata komai daga ciki ba na labarta mata sai tace barin fada maki idan
sun tambaye ki ko yaya nake dake ki fada masu cewa ni yar uwan mahaifiyan ki ce tun
a gida akace ki nemay ni idan kinzo nan don zan kula da almarinki kamar yar uwata
ta jini kike a guri na don muna garin da dan uwa ke bukatan taimako juna.
Tace idan Allah ya hada ki zama da miji dan iska sai hakkuri don gaskiya mijin
nan naki yayi nisa da harkan bariki duk na miji da zai iya dauko macen banza zuwa
gidan shi tantiri ne.
Don gaskiya sai kin kwantar da hankalinki sosai kin bi halin shi a sannu ki guji
duk wani abinda kika san zai jawo maku matsala a tsaka don shi zai iya yi bai zama
komai ba amma idan ke kin yi zai iya komawa fitina.
Ki bishi sau da kafa ki guji saka ma alamarisa ido koda yaushe kina jina ko sai
na gyada mata kai alaman eh.
Nace cikin murya mai rauni tare da hade miyau bakin cikina a wuyana nace ina iya
kokarina don ganin na kyautata mashi.
Amma da yake shi wani irin mutum ne mai hali na daban duk abinda nayi baya gode
min.
Sannan abun bakin ciki shine yadda yan uwanshi suka tsane ni sun sani a gaba
kamar ba yar uwan su nake ba sam babu kauna a tsakani na da su .
Sanan shi ya kasa fahintar makircinsu na san ba wani abu yasa suke min haka ba
sai don sun dauki iyayyena tallaka ni ban kai sa,an auren shi ba ga rayuwan da
suke yi a nan don ya banbanta da namu.
Ta katse ni da cewa duk ki manta da wanan yanzu ki kama Allah Allah yana tare da
mai hakkuri ko yaushe.
Za a zo ya wayi gari ya gane gaskiya ya daina su kuma zai fahinci kutungwila da
suke shirya wa a kanki.
Nace mhm anty kenan sai dai don kin ce Allah ya fasan gaskiya wani abin da
biyu yake min shi don kawai ya kuntata ma rayuwa na.
Tunda dagani har iyayyena babu wanda yake shakkan zagi yadda rashi yaso idan yana
jin tsiyan mutumin da kullun a buge yake in baisha da safe ba da dare zai sha.
Amma nai hakkuri da hakan ina zaune shi don bin maganan iyayye in yai amai na
kwashe anty in yasha giya anan inda kike zaune zai bar kofi ko kwalban in dauke.
Haka zai shigo cikin mayen shi yai ta surfa min a shar ya danne ni da karfin
tsiya yayi abinda yake so dani na karasa fadi cikin kuka.
Maman biyu tai tagumi tana saurare na cikin jimamay abinda nake fadi ina kuka.
Zuwa can ta nisa tace sai hakkuri Safiya don zaman aure a yanzu hakana ya kunsa
ko wani gida da tasu lalurar idan kuma kin ga zaman wasu sai ki daga hannu kiwa
Allah godiya ke.
Nace a hakan maman biyu har akwai macen da tafini wahalan aure a duniyan nan tace
naki kika sani safiya Allah daiya kyauta zamanin nan.
Nace ni maganan mahaifina da yace idan na neme saki a gunshi da bakina bai yafa
ma haihuwan da yai min ba.
Tace to kin gani ko sai hakkuri karki gaji da hakkuri kuma ki rike ibadan ki kina
yin adduoin da hannun ki bibiyu bada wasa ba.
Ina kuka ina mata godiya tace zata tafi amma zata dawo kwana biyu ta duba ni in
Allah ya yarda.
Nai mata godiya ta tafi ta barni ni kadai a cikin damuwa da tunanen rayuwa mai
kunci da nake ci a gidan.
********* ********* *********
Na mike na shiga daki dakin duk yayi kura na rashin mutum a cikin sa duk da
jikuna da dan sauran tsami amma haka na daure na gyara shi har zuwa falon gidan da
duk yai kura nasan ko sau daya bai taba gyarawa da ban nan.
Sai zuwa marance na gama har da girki da na dora na shiga nai wanka na fito na
gyara jiki na sai yamma lis ya dawo gidan daidai lokacin da nake fitowa cikin daki
ya shigo.
Cike da girmamawa irin na macen da tasan darajan wanda take aure na gaida shi da
dawowa bai takan ni ba sai umhum din da yace dani.
Nan ya zauna saman kujera yana debe takalman kafan shi da safa sai na je fridge
na dauko mashi ruwan sha ban kai ga kawowa ba ya dakatar dani fuska daure yace ni
bance maki ina bukatan ruwa ba.
Da sauri na kalli idanuwan shi kamar zanyi magana amma kuma sai na juyana mayar
da ruwan ida na dauko da farko.
Ya na cire takalman ya shige dakin shi baiyi magana ba nidai ina tsaye daga
kofan kitchen na bishi da kallo kawai.
Abinci na dauko na jera mai saman dan taburin cin abincin dake falon na juya na
shige ciki abina tare da turo kofan dakin.
Can bayan kamar awa daya naji yana turo kofan dakina ya shigo yace ke nazo in
maki kashedine akan fada wa Saadu sirin gidana da kike yi.
Ban taba zaton munafuncin da mummy ke fadin uwarki nadashi ya shafe ki haka ba
sai yanzu.
Da sauri na dago kai don jin abinda ya fada gamay da ummina ina kallon shi cikin
mamaki.
Nace ita gwago tace ummina muna fukane ita yaya akayi ta sani ko ta taba yi mata
munafuncin ne .
Yace karya mummy zatai mata kike nufi komay ?
Nace wai may yasa iyayyena basu da daraja a idon ka baka jin nauyin fada min
magana a gamay da su.
Ya a cikin tsawa wanan ke ya shafa kin dai ji na fada maki in ba haka ba daga ke
har saadun zaiyi karanku ina ce tare kuke kuna cin amana na.
Da sauri na sake dago kai na kalle shi a cikin mamaki abinda ya fada na wai zai
muna kazafi dani da yaya saadu akan muna tare .
Ya ce eh muddin baki daina jawo mani shi a gida ba abinda zanyi maku kenan a
gidan nan ya juya ya fara takawa sai kuma ya juya yana cewa uhmhum dama ina son in
tanbaye ki
Ina son insan wanan matar mai zuwa a inakika santa ne uta din wacece may ye
alakarki da ita da take taimaka maki haka.
Nai shiru ban bashi amsa ba saida ya sake maimaitawa na ce yar uwar ummi na ce
ita a kano take acan tai auri wani babban sojja ita din kuma custom ce.
Da sauri yace mayne ita din da nake gani custom ne ashe no warder take abu a
gadaran ce don tasan abinda ta taka.
Nidai ban tanka shi ba sai shirun da nayi kawai yai huce ya fice daga dakin na
sauke ajiyan zuciya tare da fadin Allah ya sauwa ka.
Kwana biyu ba wani fitina a gidan idan ma zaiyi shedan shi bai yi min a falo
saidai ya shige daka cikin dakin shi ya dadaki giyan shi yayi talil ya lamay a
wurin.
Dan kwana biyu jani shakat a raina ga maman biyu tazo ta kawomin abinci na boye a
dakina duk da shima ya sayo koma amma bata yarda tuban mazuru ba tace indai boye
wanan.
Na kwasa nakai dakina na boye tana shirin wacewa ne ya shigo gidan basu hadu ba
tun ina aaibiti sai yau din nan suka sake haduwa dashi.
Ya shigo yana ganin ta yadan sake fuskanshi suka gaisa sai a lokacin ya samu yi
mata godiyan dawainiyar da tayi damu a asibiti.
Ta katse shi da haba babu komai ai, adaiyi ta hakkuri koda yake nasan kana yi sai
ka kara kasan safiya yarince karama bazaka hada hankalinta da naka ba.
Ya dan sosa kai yace ba komai komai ya wuce ai na gode kwarai ta mike tana saka
hannu a jakar ta kamar yanzu ne zata sallame ni tace ke kuma karbi wanan kyadan
rike karki dami mijin ki da bani bani.
Zai shige ciki tace ya tsaya shima ta debo ta bashi yana aaa amma ta matsa mashi
ya karba na rakata har waje ta tafi na shigo ciki.
A falo na samay shi tsaye yana jirana ina shigowa ya miko min hannu da cewa na
kawo kudin nan da ta baki nan na dago da mamaki ina kallon shi.
Ya sake fadar miko min su nan nace kuma idan kika kuskura kika fada mata cewa na
karba sai na lalatsaki a gidan nan.
Jiki na rawa na mika maisu ya shiga kirgawa yaga dubu biyar ne nashi kuma goma ya
hada yace sha biyar kenan.
Ya tura a aljihun ya shige dakin shi ya dade da shiga ina kitchen naji muryan shi
yana cewa ni zan fita idan kinga nakai sha daya ki rufe gida bazan dawo ba a xan
zan kwana.
Nace dashi to kawai ya fita ya sha kananan kaya sai kamshi yake nace a raina yau
an samu kudin sheke aya ke nan.
Kamar yadda ya fada bai dawo gidan ba sai safe ko safen sai wuraren sha dayan
rana shigo man har zuwa lokacin bai gama warwarewa ba daga mayen shi.
Ya shigo ido yai mai ja sai zage zage yake zubawa ni dai ina daki ban fito ba
har ya gama ya fada dakin shi ya bingire sai barci.
Bashi ya falka ba sai karfe hudu na rana koshi yunwa ta tayar dashi ba ibada ba
ko wani abu don daren jiyan da yake jin kudi a aljihun shi club yaje suka kwashi
rawan su suka sha giya da matan banza su gama suka shiga sheda da matan a wurin.
Ya fito ya samay ni zaune ina kallon wani film din magic ya samu wuri ya zauna
fuska daure yake tanbayana abinci fa.
Na dago nace dashi babu nama ya kare hakana na dafa abincin don shi baicin abinci
ba abin miya a ciki.
Har zaiyi magana sai yai shiru ya ja tsuki yana fadin zubamin hakana don yunwa
nake ji haka na zubo mashi ya lashe daki ya koma ya kwanta.
Babu batun cika ibada gare shi don ba zance yana cika sallah shi ba don ko da
safe sai ta hantse mashi zai tashi haka kuma da rana ko yana zaune akai sallah baya
tashi yayi sai jefi jefi yakan yi.
Yau ma shirin fita yake a gidan sai naji sallaman yaya saad ya shigo har na taso
da yar fara a ta zan tare shi sai na tuna kashedin da yai min a kansa.
Haka na tare shi kadaran kadaham nai mashi sannu da zuwa yake cewa lalai kauna ta
jiki yai dama ya zauna a saman kujera yana cewa ashe kana ciki a dadaure ya bashi
amsa umhum.
Shika yaya saadu ya share shi ya shiga tambaya na yana kuma min hiran tafiyan su
har kasan togo suka tafi.
Ganin ban saka ba kamar yadda ya sanni sai ya dan shiga tsarguwa a take ya fara
tambayan make faruwa ne Safiya ki fada min ni yayanki ne fa.
Na share kwalla dake fuskana nace dashi ba komai yaya saadu ya mayar da duban shi
a kan dan uwanshi da ya mayar da hankalin shi ga abin da yake yi da waya shi
yace .
May ke faruwa ne bros.
Sai yace ai gata nan ka tamabaye ta kaji abin da ya samay ta din ya matsa min
da tambaya nace don Allah yaya Saadu ka bar zuwa don yaya yace zai kulla muna sheri
ni dakai wai tare muke a gidan nan.
Mikewa naga yaya saadu yayi yana huci yake fadin kaika dade baka kulla muna
sheri ba.
Ban san rashin mutuncin ka ya kai hakka ba sai yanzu don ta na yar uwa nace kaga
ina kula mata inda wata ne can bare ka