Advertisements
Chapter 65 Reading Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   65 / 87

192K to 195K   out of 258.3K words

bell din gidan na kuka alaman ana sallama ke nan.
Mummy ce ta fita zuwa duba ko waye goye da yaron a bayan ta don takan goyashi
kafin mu kwata don tace idan yaro yasha baya kafin ya kwanta yafi dadewa yana barci
da dare.
Shiru bata dawo dakin ba yasa ikilima fita ta dubo ta sai gata ta dawo tana
fadin Safiya maigidan ki ne fa ya dawo.
Gadunan dasu yaya saadu a falo ana shigo da kaya cikin gida wani iri naji gaba na
ya amsa min mummy ta dawo ta sauke yaron dake bayan ta tare da kiran ikilima suka
fita.
Ya shigo dakin a daidai lokacin da nake aje kofin tea saman dan drower dake gefe
na dago kai nayi ina kallon shi.
Yaja yayi tsaye daga kofan dakin yana kare muna kallon cikin shaawa daga nesa
tasowa nayi zuwa gare shi .
Take ya ware min hannuwan shi na shige ciki ya mayar da hanayen shi ya rungumay
ni tare da matse ni cikin jikin shi.
Ajiyan zuciya kowan mu ke saukewa a lokacin babu abin da nake tunawa sai haihuwan
wahalan danayi na farko babu muji babu aike shi.
Allah mai yin yadda yaso ga bayin shi na furta a raina yanzu gani gidan akwai
gidan mutunci inda akasan daraja na da kimana ana tarairariyana kamar kwai.
Sake juna mukayi tare da jana zuwa wurin gadon da yaron yake kwance yana barci
acikin net din jarirai .
Hannu na ya sake ya duka ya dauko yaron dake ta barcin shi hankali kwance ya
rugumay shi a jikin shi.
A hankali bayan yagama mai adduan da yake mai a duka bangarorin jikin shi ya dago
yana kallona inda nake zaune a bakin gado na zuba masu ido.
Sannu madam yace tare da sake min murmushi mai ma,anoni da yawa a zuciyar shi
nima murmushi nayi mai kamar yadda yake min.
Yace wanan katon baby haka yaya kika iya haihuwan shi a gida nace da taimakon
Allah da na nurse Lidia na haife shi uncle.
Zama yayi da yaron a hannun shi yana mai kura mai ido babu ko kiftawa nace uncle
shine baka fada muna zaka dawo yau ba mu sani a shirya ma abinci.
Yace aini akoshe nake ganin ku ya kosar dani da komai yanzu ya sake dago kai yace
sannu safiya ubangiji ya raya muna wanan yaron yasa mashi albarka a rayuwan shi kin
min komai tunda kin haifar min baba na a yau.
Nace sunan Abba ke nan zaici yace ba dole ba Safiya ina matukar son mahaifina
shima yana sona amma mutuwa ta raba mu alokacin da muke jin dadin junan mu.
Allah ya gafarta masu na furta yace amin yau ki dawo min da tsohona dana rasa
wanda har yau cikin yan uwana babu wanda ya taba min kara yace zai saka sunan shi.
Nace ai gashi Allah ya baka yanzu ka huce haushin hakan yace wallahi na dade ina
jiran wanan ranan a raina har da na cire tsaman sumun shi a rayuwa na.
Sai gashi a lokacin da ban taba zato ba ubangiji ya dawo min dashi a rayuwa
safiya zan so yaron nan kamar yadda nima mahaifina yaso ni a rayuwan shi ki taimake
ni ki tayani sin shi don Allah.
Nace har ma zan fika ni da yake babana kuma sukina ina kewar rashin shi a
lokacin da muke bukatan shi a tare damu a lokacin da ya kamata ya kasance dakai
yaji dadin haihuwan ka.
Mummy ne ta leko dakin tana fadin Alhaji ga abinci can an hada maka yace mummy
sannu da kokari ina jin labarin kokarin da kikewa babana sosai a wurin safiya.
Murmushi mummy tayi tace masha Allah tsohon gida ne ya dawo ashe?
Ya na aje yaron yake cewa baba na ya dawo mummy ku tayani farin cikin samun
wanan daman da ubangij yayi min .
Ya aje yaron yana kallona yace zan je in watsa ruwa sai da safe idan Allah ya kai
mu don naga kuna shirin barci ne yanzu.
Nace barin taso in hada ma ruwan wanka don ban hada heater ba yace na hutar dake
yi zaman ki sai da safe ma hadu ai mummy sun kawar da komai yadda ya dace.
Yana fita mummy ta shigo dakin tana cewa kin ga kyautar ubangiji watau sunan
tsoho yaro ci ubangiji ya raya muna shi nace amin mummy.
Nace da alama akwai shakuwa mai tsanani tsakanin shi da mahaifin shi tace ai da
ganin yadda yake yi akan yaron kin sani kema.
Yanzu aiki ya samay ki yadda yake ji da yaron nan sai ki taimaka ku bashi kulawa
yadda ya dace in kina cire wanan filancin da kike yi yanzu sai ki cire don haka zai
iya kawo matsaka a tsakanin ku.
Murmushi nayi ina gyara kwanciya na nace mummy ai naga alama nasan akwai aiki a
gabana sosai haka ta kashe wutan dakin muka kwanta asuba ta gari yan uwa.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/31/20, 11:07 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , ,


6️⃣8️⃣6️⃣
6️⃣
🧕🏿 8️⃣8️⃣6️⃣


Washegari tunda ya shigo ya duba mu da safe ban sake ganin shi ba sai dare ya dawo
gidan a lokacin na samu kebewa dashi da yaron dauke a hannu na na shiga wurin shi.
Na samu ya fito wanka yana shirin fitowa falo don cin abinci sai gani na shigo
dakin nashi yana goge jiki amma idon shi yana a kan mu har na karaso bakin gado.
Inda na aje yaron saman gado na nufe shi tare da kokarin karban da dan towel dake
hannun shi na fara goge mashi kan shi a hankali.
Murmushi naji ya dan sake tare da rike min hannu ya fara fadin duk da gajiyan da
kike ciki zaki koma wahal da kanki ga waban kuma ?
Nace gajiya ai yabi jiki yace haba in shirya baki wani baban nawa ko hajiya
baaba ke nan da sauri nace kai Uncle sai ana zaune kalau ka dauko maganan da zai
firgita mutum.
To be frank ba wasa a magana na sai ki fara shiryawa nan da kwanaki funda naga
baki gaji ba kin ga sai mu tara zurian mu hankali kwance ko yaya kikace hararan
wasa nayi mai tare da kawar da zancen da ki sa gabana faduwa idan naji.
Nace daddy nazo ne in fada ma ma,aikatan ku sun zo sun kawo muna abin arziki da
baka nan yace yana dan duba yaron Saadu ya fada min sun zo sai dai nayi mashi fada
may yasa ya bari suka shigo min gida.
Nace uncle ai danka ne ya jawo su da ba a haife shi ba aibasu zo gidan ka ba
yace ai sun dade suna son zuwa basu ga fuskan haka bane.
Kila ma sun gama kalle min ke ban sani ba nace ko sun kalle ni nan zasu barni
tunda ba kayan su baca ni ina da kishi sosai fa yace min .
Nace ai naga alama amma ai har da budurwan ka akazo ko itace baka son ta gani
don yar kauye ce ni da sauri ya kallo ni don jin abinda na fada mai.
Bayi magana ya juya zuwan wurin kayan shi ya dauko wani light brown din jallabiya
yana sawa a jikin shi sai da ya gama dakan shi ya dauko yaron dake kwance saman
godon shi ya gyara shi da kyau a kafadan shi yana fadin in kin gama fadin maganan
ki muje inci abinci.
Tashi nayi nabi bayan su har lokacin bai kara yin magana ba sai da zai zauna cin
abincin ya miko min yaro wuce wa nayi wurin su mummy nakai mata yaron.
Ban dawo wurin shi ba sai da ya neme ni na dawo na samu har ya gama cin abincin
nace mai na kewa yane bayi,
Tambayana yayi may kuka shirya na maganan suna ne don nasan gobe gidan nan zai
cika da baki masu zuwa suna duk da nace su huta aiyi buki acan bauchin .
Amma hajiya tace min dole sai wasu sun zo nan idan sun koma zasuyi bukin su
nisawa nayi tare da fadin ni ba wasu mutane nake dasu nan din ba karfin mutanan duk
baki ne da zasu zo daga bangaren mu.
Yace ok na dai sa a gyara masu gidajen da zasu sauka a ciki don nan din ba zai
ishe mu ba sai abinci naso inji shirin da kukayi akai don zan bada aiki a hotel ne
ai muna nace da Aisha da mummy ya kamata kayi maganan don Aishan nan bata wuce ba.
Yace may take yi har yanzu anan nace dashi aiki sukeyi a kitchen shiru yayi sai
can yace yimin magana da mummy din da ita Aishan.
Zuwa nayi na kisu sai gasu sun fito daga dakin zuwa gare shi bayan su zaune yayi
ma mummy yaya gida ta amsa da Alhamdullahi .
Yake tambayan ta abinda ake shiri akan suna tare da mata bayanin yadda ya tsara
abin gaba dayan su sukace hakan yayi dama har Aisha na tunanen yadda zasuyi dahuwa
a nan gida .
Yace da sauri a ina zakuyi wanan aiki tace wai da anan mana yaya murmushi yayi
kawai tare da kada kafan shi sunci gaba da tsara yadda abin zai kasance da yar
uwanshi sai mummy da take a bangare ne.
Nikan mikewa nayi na shige na barsu a wurin don na fara jin barci na damuna sai
da na falko ne naga har mummy tashigo ta kashe muna wutan dakin ko na gyara
kwanciya na da kyau.
Washe gari zuwa karfe ukun rana baki sun fara isowa duk na matsu inga masu zuwa
daga bangare na alokacin sai hudu na yamma suka shigo garin inda yaya Saadu yaje ya
taro su a hanya.
Shigowan su yayi daidai da fitowa na daga bayi don tsarkake kaina da nake yawan
yi lokaci lokaci saboda in samu walwala a jikina.
Samira naji tana masu oyoyo yasa nasan sun iso ke nan don haka na fito taron su
falo da shafiu kanina na fara arba da sauri yayo wuri rungumay shi nayi cikin murna
da jin dadin ganin shi.
Don Allah ya hada jina da yaron sosai duk da bashi ke bin mun amma shine abokin
shawara na a dakin mu mama na gani na sake shi na rungumay ta.
Abin mamaki shi har da Inna yau a gidan aure na da kannen ummi na da suka zo
mutum hudu da gwago nan dai gida ya cika alokaci guda.
Zama sukayi aka fara gaisuwa tare da gabatar masu da abinci da na sha wanda har
uncle ya fara odan su a gidan don bakin mu da suka zo.
Yan bauchima sun iso mota biyu suka zo dashi bus cike da mutane gidan sai ya
koma min kamar ba gidan mu ba duk girman gidan inda ka duba jama, a ne tako ina.
Inna ta koma can hanya coridor din shiga part din uncle tayi zaune tana raba ido
tana kallon ikon Allah tana anyanawa a ranta.
Wai yau gidan Safiya ne haka safiyan da taso agida ita da uwarta ko na sabulu
wuya yake masu gaskiya nake ganin kowa na rawan kafa da ita yanzu ashe sun san
abinda suka gani ne.
Tasa hannu ta shafo ties din kasan da ta zauna tana kallo wanda aka malalashi
kamar ruwa da kifaye suna yawo acikin sa.
Mummy ne ta katse ta da cewa aa Rakiya nan kika zo kika zauna hanyan dakin
surukin ki kuma tashi mana ki shiga dakin diyar taki tana can ciki ai.
Tace ummm, ummm aiko nan ma yayi min tace a a taso dai ki shiga wurin ta sauran
jamma, an da kuka zo ai suna can tare da ita.
Janta tayi har zuwa daki inda nake tsakiyan su mamana suna min bayani kan abinda
suka shirya akazo min dashi wanda ummi tabar kudi da zata tafi sai su kuma su kara
tasu a wurin dawai niyar.
Nayi mamakin abunda suka zo min dashi don ba karamin kashe kudi akayi ba kamar
lokacin aure wanan karon ma haka suka hado mi gara mai yawa akazo dashi.
Sai hango inna nayi can daga kofa ta rakube wuri guda tana bin dakin da kallo har
tana dagen kai wurin kallon dakin nawa.
Nace a a inna karaso mana shigo daga ciki ki zauna na mike ina fadin kinci abinci
kuwa na juya wurin khadija kauna ta ina cewa khadiza debo ma inna abinci don Allah
tana fadin anbata abinci ai taci.
Nace jeki debo mata nama ki kawo masu ta karaso ciki ta samu wuri ta zauna nace a
mika mata jaririn dake goye a bayan gwago dake zaune a kasa.
Aka kawo mata nama cike a plate ta karba tana washe baki ina kallon ta ta fakaici
idon mutane ta juye a wani tsohon jakka dake rataye a kafadan ta.
Murmushi nayi don bata ganni ba mama ma tashigo nan suka zauna nace su shiga bayi
suyi alwala a dakina suka fito na mike da kaina na dauko masu abin sallah.
Karshe wasu waje suka koma suka zauna saman fararen kujeron roban da aka baza a
wurin sai ci ake da sha ga ma aikata wuri su Nura sai raba abinci sukewa mutane.
Fitowa nayi zuwa wurin yan bauchi muna gaisawa dasu gungu gungu tare da masu ban
gajiyan tafiya.
Dare yayi yaya Saadu yashigo gidan yana fadin yan bauchi su fito akaisu masaukin
da zasu sauka suka fara fito fogayen mota wurin aikin su Uncle suna waje ciki suka
shiga aka tafi dasu.
Suka dawo aka kwashi yan garin mu aka tafi dasu zuwa wirin da suma akai masu
masaukin su gidan ya rage daga mummy sai gwago da yayan samira da muke zaune sai
Rukaiya da na hana wucewa da Khadija na.
Hira mukai tayi da rukaiya a daki tana bani labarin auren ta da Ado mai mai da
yadda zaman ta da kishiyoyin ta yake yanzu a gida.
Rukaiya tace dani na shigo dakin dada sai kika ga Inna ta biyo mu nace wallahi ai
nayi mamakin zuwan su duka su biyu tace.
Ita fa akace ta zauna gida da yara taki wai sai tazo yaya Sani kuma dama yaja
mata kunne sosai kafin ya tafi.
Nace kai Inna ho har yanzu dai tana nan da halin tace ai dole ta rage yanzu da
kika ganta nan bata dako lafiya tafiyan karfin hali ne kawai tayi inji khadija na
dake gyara ma yaro jiki a hannun ta ya gama shan madara zata kai ma gwago ta goya
shi.
Washe gari kafin wani lokaci aka fara shaanin buki baki da yan gari sun fara cika
gida don haka kowa ya koma busy cikin mu maigidan tunda ya shigo da safe yace zai
tafi unguwa bai dawo gidan ba.
Kowa yasan sunan yaro Abdulrahaman nan yan bauchi suka fara kiran Abbamu ya dawo
yaro yaci sunan tsoho ke nan.
Anci ansha an raba kyaututuka masu ma,ana dake dauke da photo jariri da sunan shi
a jikin kyauntan sai ga wasu mata sun shigo wai mata yan kasuwa ne suka zu taya mu
murna har da yan wurin aikin su uncle wasu sun turo matan su wasu kuma ma,aikatan
su mata ne masu aure suka zo.
Alhamdullahi har dare babu wanin hayaniyar da akayi sai faman ci da sha mata keyi
koma anyi ba mai yawa bane abinda ba a rasawa ne kawai na taron mata.
Na shiga na fita walima mukayi inda wata malama da tazo daga bauchi tayi mu
nasiha akan "ya"ya da hankin uwa akan dan ta.
Nashiga na fita daga suturun da Uncle ya waddatani dasu don fitan buki wanda
daga Dubai wanda duk wanda nasa sai an kalle ni daga ni har yaron.
Ban da abin cewa sai hamdala ga ubangiji subbahanahu wata,ala da ya wadatani
daga cikin ni,imomin shi nake rayuwa kamar banda wani tabo na tashin hankali a
jikina.
Har kishiyar Aisha da abokan aikin ta sunzo mata karan suna da makwabtan Samira
da suke zamar arziki dasu suma sunzo mata kara.
Sadiya kaunan su yaya saadu yasa tazo daga lagos don halartan sunan kawai naji
mamakin ganin ta kwarai da gaske don yaya bai fada min cewa zata zo ba sai ganin ta
nayi kawai da safe da suka shigo.
Mun rage daga mu sai bakin mu suma da dare aka maidasu masauki don a gajiye kowa
yake yana son hutu.
Khadija ne dakin da samira suna nade min kayan da nayi amfani dashi da rana ni
kuma ina zaune bakin gado rike da wayana a hannu.
Ina kokarin neman layin anty mu gaisa Uncle ne ya shigo dakin suka shiga gaida
shi da gajiya dago kai nayi ina kallon shi yana wasa da khadija na.
Yace ke budurwan kauye kin boye kawai abinki a kauye baki ko tuna mutane ta turo
baki gaba tana cewa ai mu yanzu garin mu ba a kiran shi kauye don mun waye.
Yace amma dai zaki dan zauna kwana biyu nan ko don ki kara wayewa dakyau dariya
tayi nayi saurin cewa a a kan tace nima bance zan zauna ba ai.
Nace dama shafiu ne da ko wata nawa zaiyi ban damuwa amma wanan wataran zaka
dawo ka samu tamin dan karen duka a gidan nan.
Tace kai anty Safiya ai dane muna kanana ko tun da muka girma ai muka bar fada
dariya su samira suka kwashe dashi.
Yace au ashe da gaske da kina dukan min mata tace wallahi yaya sherin anty Safiya
ne itace dai mai dukan mu din.
Nace ke khadija ni yaushe nake dukan ku ina kafa kafa kada inna ta cuta maku a
lokacin tace ai kin yi kokari wallahi.
Nan Samira ke fadin munafuka sai gata tazo tana simi simi da ita Uncle yace tazo
ne ita ma khadija tayi

65 / 87