Advertisements
Chapter 31 Reading Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   31 / 87

90K to 93K   out of 258.3K words

ma inna ne a gidan tafi dason in zauna in wulkanta
tana min gori ko yaushe a gida ?
Yanzu dai ai ya dauki mataki a kanta don da wuya ta sake maganan ki kuma ai a
gidan nan yadda suka kwasa dashi abin ba dadi wallahi.
Nan dai muka sha hiran mu kan matsalan gidan namu da ita karshe nai mata sallama
na tashi don gyaran daki sam bani barin dakin da kazanta ko kadan.

********* ********* *********
Faiza na shiga dakin anty tace ta samu wuri ta zauna sai da ta kai zaune tace da
ita yanzu yaran nan ke fada min abinda ya faru da bana nan.
Shi nake son ki fada min komai nan ta fara fadi yaran na tuna mata wani abin har
ta kai karshen zancen ta.
Tace wanan yarinyar sai na fito mata ta bayan gida zamu zauna lafiya bata kara
furta wani abin ba sai faiza da ta mike ta fice daga dakin tana masu yan biyu wasa.
Hankalina yanzu akwace yake babu abinda ke damuna araina Fati ce kawai matsalata
ban kuma kulata bayan gaisuwa da yama kamar na dole a tsakanin mu babu abinda ke
hada mu da ita.
Nayi wani haske na kara kyau sakamakon mayuyukan da Anty ta sayo min in dinga
amfani dasu a maimakon vesiline da nake shafawa da.
Wanda ko vaseline din ban damu da shafawa da don oilyskine din da nake dashi sai
dai ina da dry face amma haka nake barinsa ba gyara.
Nan ko anty ta maysa min son ita yar son kwaliyane taki jinin taga mace bata
gyara fuska ba ko jikin ta tun ban iya ba dole na kowa duk kowa da ba inda nake
zuwa daga gida sai gida.
Duk wanan halin da nake ciki nakan tuna da halin da rayuwa na yake ciki zamana
kenan ba karatu ba aure tare da ni.
Duk da anty na iya bakin kokarin ta wajen ko dayaushe takan muna nasiha da
gargadin mai kyau da nagarta .
Babu irin wanda batai muna badon komai ba ba sai don jin tsoron Allah takance ku
kama kan ku daga duk wani nauin shiga tarkon shedan
Takance duk kanku amma kuke a wurina don haka ba zan yi sakaci da tarbiyan ku ba
don baku gaban iyayyen ku.
Ta kuwa sa a don duk kan mu babu wanda baya daukan nasihan ta dan dama Fati wani
lokaci sukan kwasa wajen saka tufafi sai taso tace zata saka irin na kabilu nan
sukan kwasa da yar nata.
Bayan ita bata da wani matsala da kowan mu gashi yanzu zuwa na zatafi hankalin ta
kwace don tasan yaran ta zasu samu kulawan da ya dace ko bata gida.
Don ni dama haka nake dayara kona waye sai kaga atake yaro ya lake min a jiki bai
damu da uwarsa ba koda na zauna gida akwai yar makwaciyar mu data lake mun duk safe
da an mata wanka zata zo gidan mu sai da yamma indan dare yayi zan maida ita gida.
Amma naiyyanar ciwon dake jikina sai uwar ta hana yarinyar zuwa wanda nasan aikin
Inna ne don dama tana jin haushin hurdana da matar.
Dadine gashinan sai abinda mutum bai so a gidan anty mijin ta kuma baya kasan tun
zuwa na wai yaje US wani aikin suna sojoji amma kwanan nan naji antyn tana maganan
dawowan shi kasan.
Don haka muke yi yadda muka ga dama a gidan babu mai takura muna amma naji Faiza
na fadin yanzu yaya zai dawo gidan zai koma ba dadi don in yana nan babu wali a
gare mu.
Ni dai dama ba sanin shi nayi ba don haka ban damu ba don koda yana nan ba ruwa
na sai in fake ma daki inda har yana gida baiko ganin giccina a gidan nace a raina.
Muna zaune falo da anty take cewa wani sati maigidan zai dawo kuma tana ganin
shida sulaiman zasu dawo.
Faiza tai saurin cewa harda shi zai dawo anty tace ba dole ba yana zuwa ya zauna
a kasar mutane gashi arzikin shi sai kara habbaka yake yi yanzu ai gara dai ya dawo
gida asan abin yi kan case din shi.
Kamar yadda anty ta fada hakane satin da muka shiga bamu da hutu a gidan don
shirye shiryen taron maigidan da kanin sa da zasu dawo kasan.
Kusan aikin nice a gaba don banda kasala akan aiki duk yadda yake kuwa kafin wani
lokaci mun hada komai yadda ya kamata muyi.
Sai a wanan lokacin naga Fati na rawan kafa don har takan dan saka hannun ta ga
aikin da mukeyi ayi tare da ita.
Tai ta faman murna tace ance harda Uncle sulaiman zai dawo ashe gidan namu zai
cika ke nan kwanan nan.
Da yake ba hira muka saba yi da ita ba babu wanda ke kulata har tayi ta gama
sukiburutsun ta ta bar wurin.
Don ba sabawa tayi da irin haka ba don haka bata da jimirin dade wa tare damu a
falon ranan da zasu dawo kuwa tun safe muke murzan aiki sai yamma muka gama kowa
yaje yai wanka kafin shigowan shi.
Tun da nai wanka na jawo dogon rigata na saka a jikina na koma nabi gado na haye
don dama a gajiye nake don mun sha aiki sosai.
Ban fito ba ina jin ana ta hayaniya a gidan nasan matafiyan namu sun iso kenan
zuwa dare anty ta leko daki na tana cewa najiki shiru ga bakin mu sun iso gida
lafiya har sunci abinci baki fito ba ke .
Nai murmushi nace sun iso lafiya anty tace kalau suka iso nace da safe indan sun
huta mu gaisa dasu ai wani kallo tai min.
Tace amma Safiya baki ko kyau ta min ba in kin ce sai gobe mutum ya kwaso gajiya
na mike zubur nace tuba nake anty ta dan harare ni tace ke kika sani ai.
Tace ai har uncle din yara ya tafi abishi don shi dama bai son yawan magana na
fita da zumbulelen hijabina yana shirin tashi sai gani shi kadai na gani a wurin
sai anty da yaran ta har kasa na kai ina cewa daddy barka da dawowa.
Ya juyo da sauri tare da amsawa yana kallo na yace Safiyar taki ke nan ashe ma
karamar yarinya ce haka yace mun samay ku lafiya nace lafiya kalau.
To yaya hakkurin abinda ya faru aita hakkuri haka duniya yake dama ba komai ne ke
zuwa wa mutun daidai ba a sanyayye nace nagode a huta gajiya don har idona ya kawo
kwalla ko.
Na juya zan tafi naji anty tace dani Safiya a rage kayan nan daga wurin nan na
juyo na fara kwasan kayan ida ba wani cin abincin sukayi ba sosai dan tabawa sukayi
suka barshi duk uban wahalan da mukaci na aikin yin shi.
Na saka na fridge a cikin sauran kuma na adana su inda ya dace a jiye su san nan
na koma dakina na rufo Asuba ta gari indan tunane ya barni nai barci yadda ya
kamata
Yar uwa ina zaki da hakki a kan ki na mutane ance ba a yafe ba baki barin turawa
kina daukan nauyi a kan ki,
Karatun nan fa ba dole bane kiba kanki lafiya mana da daukan nauyi don neman suna
kike turawa ko don kina ganin haka ba komai bane.
To nace Allah yai min gagawan isa ga mai fitar min da novel waje .


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , ,


3️⃣2️⃣3️⃣
🧕🏿 2️⃣

YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU
PLEASE, , , , ,


Washegari muka hade a falo duk kan mu sai anty dake wurin mijin ta Fati sai faman
murna take yi uncle Sulaiman ya dawo,
Hararan gefen ido Faiza tabita dashi tace wai kina ta murnan dawowan Sulaiman
wanan dan bakin rai jiya kin ga ya dubemu ne ma.
Kai wallahi turai ya karbeshi kin ko ga yadda ya kara girma yai wani fresh dashi
kamar bashi ba don Allah.
Faiza ta watsa mata dan harara tace yanzu ai kanki ake ji shi baki ko isheshi
kallo ba, ta bata rai tana fadin oho dai ko bai san ina yi ba wata rana zai sani
ai.
Mako uku cur da dawon su amma sau biyu naga daddy a gidan haka wanda Fati ke
maganan shi ko yaushe ban taba ganin shi ba kuma sunce yakan shigo gidan wani
lokaci amma Allah bai taba sawa mun hadu da shi ba.
Yau ya shigo gidan anty tai mai tayin abinci yace bai jin cin komai a lokacin
kai ta girgiza tace wai kai har yanzu kana nufin baka fitar da zancan Samira a
rayuwan ka bane ?
Yai murmushi yace kai samiran may can ai ni yanzu in ba lokaci ba ban faye kawo
ta a raina ba sai dai ai kin san yazama dole ba zan taba mantawa da ita bane.
Anty ta nisa tacd dashi Allah ya sauwaka amma don Allah ka rage yawan tunane ka
koma alamarin ka kamar kowa ita fa har naji ance tayi wani aure ko.
Yace nima haka naji gun wani dan uwan su can.
Ta dade tana dan kallon shi sanan ta gyara zama tace na cewa dashi ya kamata ka
manta da komai hakana ka samu wata wace kake zuwa wurin ta ku shirya.
Sai yaneme ya katse zancen sai ta hana shi samun damar yin hakan tace kyale ni
har in gama tukun yanzu sulaiman da hankalinka da ilimin ka da komai kaifa ka iya
sa wani agaba kai mai fada idan kaga zai kauce irin haka.
To yaya za a ce kai da kan ka ke irin haka kuma.
Kar fa ka manta Allah yana sane da komai na bawan sa shekara biyar kenan ka kasa
cire hafsat a ranka sau kace ba musulmi ba ?
Haba sulaiman shi fa musulmi da tawali,u aka san shi saboda hadisi ne ingantacce
daya tabatar muna da hakan imanin dayan ku baya kammala har sai yayi imani da
kaddara mai kyau da kuma akasin hakan.
To what come over you ?
Sulaiman
Da zaka manta da duk wanan a ranka ?
Gaba da daya lamannin shi suka sauya a lokaci guda ciwon da dade yana cin
zurciulyar shi ya dawo mashi sabo fil, wanan dalilin ne yasa dama yake gudun gida
don kowa na shakkun fada mai zancen aure.
Ko ita kanta anty sai daga baya taji dama bata dauko mai zancen ba don kawai
ganin yadda ya sauya alokaci guda.
Ta kalle shi a sanyayye tace sulaiman ban dauko wanan maganar ba don in tayar
maka da hankali amma kayi hakkuri kayi tunane akai.
Kar kaga na dauko ma maganan da kowa yake gudun fada maka nayi hakane amatsayi na
wacce muka shaku dakai don zaman ka a haka yana damun kowa.
Ya mike don bai son maganan yai nisa yace zan fita sai na dawo sai dai ba lalle
ne in dawo kusa ba don ina son in leka bauchi kwanan nan.
Ba damuwa haka na da kyau ai aje gida adubasu yafi amma kayi tunane aka magana na
don Allah shi yafi.
Ya sauke ajiyan zuciya tare da karfin halin fidda murmushi a fuskan shi yace zan
diba madam ni zan tafi tace aiko danafi kowa jin dadi wallahi.
Ta sake cewa yau dai kaki taba abincin gidan na mu ya dan yi murmushi yace mata
yau bana jin yunwa ne shiyasa.
Ya fice a sanyayye tabishi da kallo tausaya mashi daidai lokacin Fati tashigo get
din gidan bai ko kalli inda take tana gaidashi ba yaja motar shi zuwa wurin da ake
masa aiki.
Ta shi go da yar fara an ta a fuskan ta tana cewa ashe uncle yazo gidan sai dai
kuma bai dade ba ya wuce kuma ?
Anty ta kalle ta fuska daure tace ke Fati ki saurare ni dakyau kiji may zan fada
maki naga kina wani rawan kai tun zuwan Sulaima.
To ki kama kan ki don sulaiman ba ajinki bane ya wauce sanin ki ki tsaya a
matsayin ki idan kina son mu rabu lafiya dake ke ina ma kika ga haka zai yuyu dube
ki ki dubeshi ina zaki hada kan ki dashi.
Kuma ni ina auren dan uwan shi ina kika taba ganin an yi hakan sai ta turi baki
gaba tana cewa damay yafini kuma ni ba mace bane halan ?
Ta shige tana kumkumi ta bita da harara har ta bace mata dagani tana sauke ajiyan
zuciya ina fitowa daga daki na.
Nace anty ashe kina zaune nan ban sani ba dana fito na taya ki hira ai tun dazu.
Ta kara sauke ajiyan zuciya tace ai bani kadai bane nida uncle din yara ne yanzu
ya fita daga nan .
Nace ayya aiko da na ganshi kullun muna samun sabani sai ya tafi nake fitowa har
yau ban sanshi ba .
Tace aikuwa da kinga shi yaro mai taken zamani don Sulaiman abin son a san shine
bari rana da ya shigo zan kiraki ku gaisa don yace zai tafi gida ya duba su ya dade
rabon shi da gida.
Nace Allah sarki dan uwanki ne anty ?
Tace a a dan uwan mai gidan ne iyayyen su guda sai dai tasu tazo daya da manjor
ne kawai sai muke dasawa da shi sosai.
Bai iya boye min komai nasa nima haka shiyasa nake son shi da komai nasa don
shawaran shi baya wuce ni shima.
Nan muka zauna tana ta bani labari da irin arzikin da yan gidan su daddy ke dashi
da sauran su har Faiza tafito ta samay mu anan itama ta zauna.
Fati bata fito ba sai da yamma lis ta fito tana jan kamshi Faiza ne tace yau may
ke faruwa da yar mulki ne naga tun dazun take fushi a gidan ?
Anty ta ja tsaki tace rabu da mara wayau kawai bata san abinda take yi bane
shiya sa sai gata ta fito a fusace tana fada wai waya shiga dakin ta da batanan ya
dauko mata hand dryer din ta.
Faiza tace itace don Safiya ta karbi nawa kuma bata bude kofa ba lokacin shiya sa
na dauko naki din.
Nan ko ta shiga fada ta inda take shiga ba nan take fita ba sai da anty ta
dakatar da ita da cewa.
Ke Fati kin ishe ni wallahi haba ke kika saye shi ko ni da zaki saka mutane a
gaba kina masu fada haifan su kikayi komay ?
Don haka ki shirya kayan ki gida zan maida ke nagaji wallahi duk naji abinda
kikewa Safiya tun zuwan ta garin nan ido kawai nasa maki inga gudun ki.
Tun farko ina sai da na hada ku nai maku nasiha amma kika shure magana kina yadda
ran ki yaso dasu a gidan nan.
Wai halan kikai Faiza matsayi ne agidan da zaki dinga hura ma mutane hanci yadda
kike so ya zama dole in mai dake gida don ban iya zama da wanan iskacin naki haka .
Jin anty na ambato gida yasa ta sausauta maganan ta ita ko faiza kai ya fasu jin
ance tafi kowa matsayi a cikin mu sai wani budawa take yi.
Nan dai anty ta kafe akan lallai ta shirya ta maida ta gida sai na shiga ba anty
hakkuri tana ta faman fada da ita.
Ds kyat na samu ta hakkura da zance sai dai tace wallahi ta shiga hankali ta don
ta gaji da ita a gidan
Tun wanan lokacin ta shiga hankalin ta da kowa dama ba mai shiga tsabgan ta cikin
mu don haka bamu damu da ita ba.
Da anty zata dawo ranan sai ta sayo min nawa in huta da aron nasu da nakeyi tare
da yan sayayyen kayan makeup dina.
Zama na a gidan yasa yanzu zaka ga komai a gidan tsab don kai aiki iyakan ta
girki nice ke tsabatace gida kafin duk su tashi na gama komai har in kama mata yin
girkin kuma.
Wanan abinda nakeyi shiya na kara shiga ran anty sosai tana tausaya ma halin da
nake ciki takan kaini amsan magani secretly ba tare da kowa ya sani ba a gidan.
Kuma ban taba jin wani ko ganin an kyan kyankyamayni ba a gidan zama suke dani ba
wani nuna rashin yarda dani gashi bata rage ni da komai ba na fannin rayuwa kuma.
Sati uku da maganan mu ina daki kwance yan biyu ta tashigo da gudu tace wai inji
mummy su inzo .
Na dauki dan kwalina dake saman gado nai rolling din kaina dashi tare da dan
gyara fuskana kartai min kwankwami rashin gyara.
Na fito su biyu na samu a fali sai dai may shi ya hada baya ban iya ganin fuskan
shi a lokacin.
Gasu yan biyu sun na wasa da hannuwan shi sai dai mai shi fari ne soll da ganin
shi yan biyu tana ta jan yatsun hannun shi na iso wurin tace yauwa Safiya ga uncle
yau a gidan.
Sai ya juyo da sauri yana kallon wace akace ma safiya din don bai taba jin sunan
a gidan ba sai yanzu.
Juyo wan shi mukai ido biyu dashi sai da gabana ya fadi don ban taba ganin
namiji hadade irin shi ba nan dai na gaisheshi ciki kunya kunya.
Ya amsa min da lafiya lau kawai ya juya yaci gaba da wasa da yaran dake damun shi
nace anty gani.
Tace shike nan dama kiran ki nayi ku gaisa da uncle din yara da baki sani ba sai
nai murmushi na juya na barsu wurin daya fahinci na wuce.
Sai yace ita kuma wanan din wacece ita anan gidan take itama da zama ?
Tace budurwan da nai maka kamay ke nan yace kai haba madam kikan fara maganan ki
don ki koreni ko.
Tace daga maganan mace zan koreka wai

31 / 87