Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
a lokacin zama yayi yake cewa mommy bata fito bane
har yanzu nace ina ga shiryawa take zata gidan su yaya Saadu tace .
Baiyi magana sai jawo plate dayayi a gaban shi ganin duk a sabule nake a lokacin
sai lokacin na natsu na mike na fara zuba mai arish din a plate.
Sai da ya fara cin abincin yace zasu tafi can lagas din ke nan yau da sauri nace
ban sani ba don bamuyi maganan haka dashi ba.
Wayan shi ne yayi kara yaya saadu dine yakirashi a lokacin yake fada mai rasuwan
dan uwan nashi yace eh ai daka bugo mata muna tare Allah ya jikan shi yasa ya huta.
Zaka tafi lagas din ke nan yace eh da yau nake son mu shirya mutafi da iyalina
mota zaku bi ko jirgi yace ina ganin mota zamu bi don mu uku ne.
Bari kubi jirgi zaifi ku isa da wuri zan fito yanzu zan biyo ta gurin ku kafin in
wuce ni dai sauraren maganan su nake yi banyi magana ba.
Sai dai zuciya ta ba dadi a lokacin don mutuwa ko na wanda baka sani ba yana
shiga ranka balle ga wanda ka sani din.
Har ya gama yana min sai ya dawo ban iya cewa dashi zan tafi gidan yaya Saadu in
mai gaisuwa ba don kada ya fassara min magana da wata manufa kuma.
A dawo lafiya nake yi mashi har yakai kofa yace idan mommy ta shirya sai ku tafi
tare ki sauke ta ki masu gaisuwa.
Na gode nace mashi ya fice gidan na sauke ajiyan zuciya mikewa nayi zuwa dakina
ko kayan ban ita kwashe wa na soma shiri nima.
Sai da na sauke kannena a makaranta muka wuce gidan mun samay su har sun shirya
da ganin yaya Saadu kasan yayi rashin dan uwa a lokacin .
Don ya fita hayacin shi sosai kan mutuwan da akai mashi din samira ke fada muna
ai Uncle yazo yanzu ya wuce shine ma ya biya muna kudin jirgi zuwa lagos din.
Nayi ma yaya Saadu gaisu nace idan sun je ya mika min gaisuwa ga sauran yan uwa
yace zasu ji safiya .
Yace Ahmed dai ya rasu bai samu rokon ki gafaran abinda yayi maki ba har ya mutu
nace babu komai yaya na gafarta mai.
Allah dai yayi mai rahama yasa mutuwa hutu ne gare shi yace amin safiya muna
gidan har suka shirya muka raka su zuwa airport muka sauke su a can muka dawo gida.
Ranan dai haka na wuni jiki ba dadi zuwa rana samira ta kirani tana fada min sun
isa lafiya yanzu haka suna gidan ma ana batun kauda shi ne.
Wani iri naji a raina na kara mata gaisuwa tace ga sadiya mu gaisa sai da na
gyara na fara amsa mata gaisuwan tana kuka sosai a lokacin ni dai hakkuri na basu
nace ta gaida min da gwago ina mata gaisuwan rashin da akayi din.
Sai yamma ya dawo a daki na samay shi muka gaisa na hada mai ruwan wanka na fita
bayan ya fito falo ne yana cin abincin dare nake mai godiyan abin da yayiwa su yaya
Saadu din.
Yace halin shine yasa nai mashi hakan din don yana da rikon gaskiya da amana a
tare dashi banda abinda zan saka mai dashi in ba haka din ba.
Shiru nayi shima bai kara magana ba ya gama ya mike yana tambaya na mommy nace
suna daki basu fito ba yau.
Bamu dade ba muka shige ciki nikan kwanciya nayi don har lokacin jiki na ba
karfe don mutuwan ya shige ni sosai ranan.
Sai dai ina kokarin ganin bai fahinci hakan ba don gudun zargina zai sa yace na
damu aiko ban tsira ba sai jin muryan shi nayi yana fadin yau dai kamar kina cikin
damuwa ko ?
Da sauri nace damuwa kuma uncle akan may kuma zan damu an maki mutuwa yau mana
uban diyar ki ya rasu.
Naji zafin maganan nashi amma a fili cewa nayi mutuwa ko na wanda baka sani ba
kana tausayawa mamaci ai balle wanda ka zauna dashi a baya .
Ko ba komai kuma ai dan uwana ne shi kaga dole inji mutuwar a raina wanda nima ba
komai nake tunane ba sai tawa makomar a yanzu.
Naga alama yace yana gyara kwanci ba tare da ya kara magana ba muka kwanta hakana
ba wani abu daya shiga a tsakanin mu ranan.
Da safe ne yaya Saadu ya kirani wai zamu gaisa da gwago na dan jim nayi na karbi
wayan muryan ta na rawa cikin gurbatacen hausan ta da ya gauraye yanzu tace Safiya
ke ce yaya gida yaya maigidan naki.
Nace muna lafiya gwago yaya akaji da hakkuri tace hakkuri ya zama dole Safiya
Ahmed ya rasu yana fadin a rokar mashike ki yafe mashi don Allah.
Nace gwago ni na yafe mashi tun tuni ai dan uwana ne sai naji ta kama kuka dole
na kashe wayan don ban iya jimirin sauraren kukan nata a lokacin.
Nima kukan na kama a wirin sai dai nayi saurin share hawaye na kafin kuka yayi
min yawa don ta bani tausayi sosai sai dai shedan na rudina ina tuna irin cutar da
sukai min a lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/24/20, 5:48 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA , , , , , , , , , ,
8️⃣8️⃣8️⃣
🧕8️⃣8️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Haka rayuwa ke ci gaba da gudana a gidan uncle watarana mu tashi a farinciki har
dare wata rana kuma haka kawai zai daure fuska gare ni ba gaira ba dalili yayi ta
fushi dani ga laifin da ban san nayi ba.
Ga dai ci da sha da sutura wadatace a gidan amma banda kwanciya zuciya a
gurin uncle ga fargaban ciwon dake jikin mu yau kaji ance babu wani a cikin masu
irin lalaurar mu gobe kaji ance wata ta rasu akan laluran nan.
Ga ciki yayin wani irin girma a jiki saikace cikin tagwaye na dauka wanda bai san
halin da nake ciki ba sai ya dauka ai ina cikin daular duniya ne ina cin ta da
tsunki ba abinda ke damu na.
Sai dai da zan zauna dake in fada maki ciki na zaki fahinci rayuwan da nake yi a
yanzu wanda zan iya kira maki shi da BAHAGGON RAYUWA .
Daga bakin ciki na fito na fada rashin kwanciyan hankali a gidan uncle don
kullu a fargaba nake dashi kada yace ga laifin da nayi mai a gidan.
Amma idan yana cikin dadin rai idan ka ganmu saika dauka ba wanda ya kaimu soyewa
a duniya a yanda muke daga bakin rayuwa zuwa haske da mai kumshe da magana a
zuciya🧕🏿🧕.
Cikin wai a hakan ina jin yan uwan shi na fadin wai ya rage a cikin halin shi na
baya sai nakan tuna da maganan da Faiza ta fada lokacin muna gidan anty a lagos.
Dadi na guda shine akwai waddata kuma yana taimakawa yan uwa da nashi da duk
wanda yake rabe damu kodan wanan abin dole in yi hakkuri tunda na saba da irin
rayuwan shi yanzu.
Su baba da mama sun tafi lagos gaisuwa sun kara tula ma gwangon mu nayi a ka
wanda ranan da ta gansu taji kunya sosai ba kadan ba.
Baba yace ai zumunci bai yake ba don Saadu bai yarda zumunci ya lalace ba a
tsakanin mu idan ma ke da Amadu bakuje ba ai shi yatafi gurin mu kin ga ko dan shi
mazo wanan gaisuwan tunda bai yar damu ba ya dauke mu da muhinmaci sosai a rayuwa.
Mama kuma ta saka gwago a gaba tace yanzu n saboda son kai kika zabi wanan
rayuwan a tsakanin kina ganin kin kyautawa kanki ne a hakan da kukayi.
Kun cuci yar mutane badon Allah ya kawo mata mafita ba a rayuwa da anmanta da
rayuwan wanan yarinyar a duniya.
Da yake Allah bai barin bawan shi haka ya tabe sai ubagiji yayi mata dubaiya ya
saka mata da miji yau itace ke rike damu da yan uwan ta baki daya duk ko da bakin
cikin da ta fuskanta da farko a cikin mu bai sa yanzu da ta samu ta watsar damu ba
ta jawo mu ta rungumay mu a jikin ta.
Kuka gwago keyi sosai na nadama mama ta gagaya mata magana masu zafi tace kiyi
kokarin ganin ta ki roketa gafara zai fi.
Cikin ikon Allah na haifi dana lafiya asibiti don uncle yana gari a lokacin don
haka a asibiti na haihu lafiya.
Bai samu gani na ba sai da aka fito dani dakin hutu suka shigo dakin ina kwance
shida yaya saadu da mommy dasu samira .
Tunda mommy ta mika mai yaron ya rungumay shi a jikin shi bai yarda ya mikawa
wani ba ya dade yanawa yaron addua.
Ya dago kai yace yaya Saadu kaga baiwan da Allah ya karamin kaunaka taso ta min
bakin ciki ga hakan da Allah ya azurtani a dan lokaci kankanni ?
Murmushi yaya Saadu yayi yace yallabai ai mata hakkuri ta tuba murmushi yayi
kawai ya mikawa yaya Saadu yaron.
Sun dade a dakin ana muhawaran wa yaron yabiyo cikin ni da uncle mommy tace wanan
duk fuska gidan su suke daukowa Abba zai koma watarana don da ubansu suke da kama
sosai.
An sallamay mu mun koma gida bayan dan wani lokaci sai dai ciwon kai da jiri da
ke damu na akai akai wanda ya hanani walawa mun koma asibiti washe gari ba abinda
likitan mu ya bani sai cewa yayi hutu jikina yake bukata kawai.
Kaina yana rike da hannuna na dafe goshina da hannu daya yana tuka mota muka
nufo gida magana yake min amma ban iya bashi amsa a lokacin.
Har muka shigo gida ban tsaya ba na shige daki na kwanta maganin da aka rubuta
min ya sayo na sha na samu barci mutane na shigowa amma ban sani ba.
Sai bayan karfe hudu na falka daga barcin da nakeyi kewayawa nayi sai dai daga
ban dakin sai da mommy ta kamoni na dawo daki.
Uncle ta kira take fada mai abinda ke faruwa dani yace gashinan zuwa gidan dole
ya baro aikin ya nufo gidan da sauri a ranshi yana fadin kardai yar mutane ta mutum
dama abinda take gudu ke nan gashi kuma yana shirin faruwa da ita.
Gudun da yakeyi ne yasa shi isowa gida da wuri dakina yayo derict ina mai da
numfashi guda guda ina fadin mommy kaina kamar zai fashe min nake jin shi.
Turo kofa yayi da sauri ya shigo dakin yana fadin Safiya har yanzu kan bai bari
ba na dago idona da suka kade sukai min ja sosai gaban shi ne ya fadi yadda dan
lokavin gadan na sauya nayi wani irin baki sosai.
Gashi na ramay lokaci daya kamar bani ba rike min kan yayi yana addua yana
yarfarwa gefe ya dago yana tambayan mommy ko naci abinci tace ban ci komai tashina
ke nan na shiga bandaki acan na tashi faduwa sai da ta kamoni muka fito.
Mommy hada mata tea mai kauri sosai ki kawo madarar ruwa da tomotor da gwagwanin
maltina in fara bata da sauri mommy ta juya ta dauko abindaya lissafa mata ta shigo
dasu take a wurin ya hada ya bani na sha.
Ta kawo tea din nace mata na koshi ba zan iya sha ba suka matsa min nasha rabin
cup din nayi getsa sai ga zufa na karyo min lokaci daya na koma na kwanta tare da
lumshe idona.
Ya dade a wurin tsaye ganin na samu barci yasa su fita su barni dakin ni daya
mommy na goye da jiririn abayanta kallon mommy yayi yace ina ganin jinin da ta dan
rasa ne a jikin ta yake haifar mata da ciwon kan haka.
Mommy tace dama shine fargaban ta a kullun wallahi ko haihuwan Abba tayi ciwon
kai sai dai bai kai haka din ba gaskiya.
Yaron dake goye a bayan mommy ne yayi kuka ta sauke shi tana dan jijiga shi
ajiyan zuciya ya sauke yace ina ganin kamar a kira gida gwago tazo ko khadija su
taimaka maki don abin yayi maki yawa ke kadai haka.
Tace don dai abin yazo da akasi ne amma ai bai da matsala don ga yan matan tana
suna taimaka min da kula da Abba idan suna gida.
Naji dadin kamun kan da yayi min don shi ya lafa min da ciwon kan da nake ji a
baya sosai dana falka cikin dare ni da kai na nemi a bani abinci inci.
Na dauka dare yayi a lokacin sosai ashe wajajen karfe tara na dare muke a lokacin
don ganin su maimu da nayi basuyi barci ba na tambaya mummy ke fada min time.
Ganin na tashi ne sukazo kusa dani suka zauna hindu na goye da jariri maimu kuma
ta goya Abba.
Ido na lumshe a hankali tare da tunanen yanzu duk yaran nan nawane gasu kamar
tagwaye don ba wani tserayan kirki a tsakanin su tunda Abba ma bai wuce goyo ba.
Uncle ne ya shigo dagin ya ganmu shiru sun tasani a gaba ba mai magana cikin mu
duk da yawan rakafi su yau sun natsu sanadin rashin lafiyan da suka ganni ciki.
Wuri ya samu ya zauna a kusa dani yana ce masu kune yan jiya naga kunyi cirko
cirko a dakin mommy dake zuba min ruwa ina wanke hannu tace dashi ba dole ba.
Sunga yar uwarsu a wani hali da basu saba ganin ta ba yace mommy ina ganin ba zan
tsaya ayi suna ba zan fita da ita waje taje can ta samu hutu na dan wani lokaci.
Tace Alhaji kadai yi hakkuri yaron ya karbi sunan shi a nan don kasan mutane
akwai tsegumi in anyi suna sai ku tafi.
Mommy ban damu da abinda mutane zasu fada ba kan haka lafiyan ta nake jawa kawai
shine muradina, ina gudun kar abinda take gudu ya faru da ita don ta riga da ta
nasa hakan gashi yana shirin faruwa da ita kuma.
Haba dai Alhaji bai kamata kayi saurin saka wanan a zuciyar ka ba don Allah ne
mai yin komai ga bawan shi dama dai tasan irin kalubalin da hakan ke haifarwa ne
tun wuri.
Kaida ayi fatan ta samu lafiya kanfin suna zaifi abar wanan maganan yanzu mu
koma na neman lafiyanta kawai.
Ajiyan zuciya ya sauke mai nuna gansuwa da maganar mommy shine amfanin zama kusa
da maya din da akeso a hankali nace ya kara min adduan da yayi min dazun don naji
dasin shi sosai daya min.
Yaran mommy ta kada kan su zuwa waje dakin ya rage dagani sai shi a lokacin
rugumay ni yayi zuwa jikin shi tare da dan shafa min baya yana fadin Allah ya baki
lafiya matana ina jin da da halin in karbe ciwon nan a jikin ki.
Murmushi nayi nace Uncle ai ciwo kaffara ne ga bawan shi da yardan Allah zan samu
lafiya in koma daidai dama sun fada muna haihuwa akai akai yana haifar da irin
matsalan a gare mu rashin daukan matakin da bayi bane bayan haihuwar Abba yasani
saurin daukan ciki da wuri.
Yace da rabon wanan yaron kuma yazo a wanan lokacin yasa muka manta da yin
plaining a ziciyar mu sai dai yanzu dole a dauki mataki tunda na hango illar yin
hakan yanzu.
Kaina ya kama ya fara min adduan da yayi min da rana sai da ya gama yace ki
kwanta ki huta kinji abinda likita ya fada muna hutu kike bukata da cin abinda zai
gina maki jiki da sauri jinin da kika rasa ya dawo.
Allah ya baki lafiya yace yana kokarin kwantar dani kamar karamar yarinya bakin
ba don zaman dama ya isheni na koma na kwanta .
Da safe da ya shigo yake fada ma mommy ya dage sunan sai sarin mai zuwa har na
kara jin sauki zai dai yankawa yaro rago idan sunan yazo buki sai wani sati.
Shi ida hali ma bukin ba sai anyi ba don in samu in huta a dakina baison azo a
damay ni da hayaniya da yawa don taron suna hayaniyane kawai ba komai ba.
Yadda ya fada hakane ya faru don samira da Aisha sun ta kiran mutane suna fada
masu suna sai wani sati idan Allah ya kaimu za ayi.
Sannu a hankali nake jin sauki har na dan bar jin ciwon kan sai dai yawan jiwa
dake damuna idan na mike shima yana ragewa a hankali.
Haka dai suna yazo lokacin na samu lafiya sai dai a tsatsaye nake har lokacin
akai suna yaro ci sunan uncle din sulaiman.
Na dauka zai min kara ya sa sunan nawa mahaifin sai naji yace wa mommy sunan yaro
sulaiman nayiwa kaina takwara don kada a manta baya.
Yan uwana da nashi sunzo akai buki suka koma gida don ba wani hayaniya tunda ba
lafiya gare ni ba haka yasa ummi na zuwa ita da su mama da babanmu da mommy
mahaifiyar Amina kawata da motan gidan su suka zo.
Suna da kwana uku suka shigo garin da yamma da taimakon yaya Sani wanda yayo masu
jagora.
Ba mu san da zuwan su don haka suka shiri da yamma sai ganin su mukayi suna
shigowa da sallaman su muna zaune falo a lokacin sisters dina suna min hira mummy
kuma na bawa Abba abinci kafin yayi barci.
Matan suka shigo baba sai baba ya tsaya a kofan gida bai shigoba a lokacin munyi
mamakin ganin su sosai da tafiya haka babu sanarwa.
Yaran najin ance da baba akazo yana waje nan suka fice da ihun su suna murnan
ganin shi yace ho yan nema mutan abuja ke nan.
Watau kuna nan kun shige birni kun manta da kowa ko dariya sukayi gaba daya sun
sauya a idon shi sosai yaga sun kara