Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
mace ce wata ukun da aka bamu mu koma baiti ba har kin shiga goranta
ma wata halin da take ciki ki bari a san makomar yar taki tukun san nan ki samu
abin fadi.
Dama Inna bata son zancen komawa asibitin nan don ko yaushe tsinewa likitan
takeyi akan yace su koma a sake auna ta.
Nan ta shiga cewa insha Allahu babu abinda zai faru da ita sai alheri na gane
kaima so kake wani sheri ya faru da ita a gidan nan su zama daya da yar ka.
Tai ta sababi ba wanda ya sake kulata har tayi ta gaji ta koma dakin ta tana mai
zuba mugun addua ga masu fyaden da masu zagin yar ta.
********* ********** *********
Ranan ina waki tufafin mu da rana naji anyi sallama muryan dai ta wace na sani ne
amma kuma may zai kawo ta nan.
Naji tana tambayan ina nan da sauri na dauraye hannuwa na fito daga inda nake
wanki mama biyu ne tare da yan tagwayen ta.
Sun girma sun kara wanj irin kyau dasu da uwar su baki daya ban san lokacin da
nai cikin suba da murna na sai fadi take alhamdullah.
Naji dasin yadda na samay ki alamu ya nuna min kina ahan maganin ki ke nan mun
shiga dakin mu na rasa ina zan sakata.
Na fara gabatar ma mutanen gidan mu da ita suka shiga gaisawa da ita suna
tambayaan ta yara da maigida nan na fito na aika a sayo masu fanta kwalba da ruwa
mai sanyi.
Tace no ki barshi ashe garin naku yana da nisa haka ne yanzu zamu wuce dama nayi
alkwarin zanzo na duba ki ne tunda ke kin yada mu.
A kunyace nace ban yada kuba anty yanayi dai ne yazo da hakan mun dan taba hira
tamike tace zasu wuce don dare yayi yau zasu koma dama buki tazo yi arewa shine
tace bari tazo ta gane ni.
Ina ta rawan jiki na rasa may zan basu tace huta abinki bashi ya kawo ni ba tunda
nagan ki alhamdullahi.
Ta kawo kudi tace in bawa ummi na ga tsaraba mai yawa da ta kawo muna a cikin
buhu ta fito tsakar gida taba su inna dubu ashirin su raba.
Takawo wani tace aba baba in ya dawo nafita na rakata bakin motar ta anan take
cewa dani idan na samu lokaci indan leko wuein su ina kuka ta rungumay ni tana
share min hawaye.
Nan dai suka tafi suka barni cike da kewar au gani nike abun kamar a mafalki wai
anty ce a garin mu yau.
Mun koma naji inna na fadin tunda nike ban taba rike ko dubu biyar ba na kaina a
rayuwana yau ga bakuwar arziki ta zo mun dashi.
Ban tsaya ba na shiga dakin mu na bude tsaraban da ta kawo min turmin zani guda
uku da sauran tarkace ne a ciki nai murna sosai tare da yin hamdala.
Mun dade muna hiran ta ina fadawa ummi irin taimakon da tai tayi min acan
lokacin da nake cikin bukatan aimin din.
Ummi tace Allah ya saka mata da alheri daga waje naji mama na fadin mukan ai
Safiya kin jawo muna arziki har gida wannan abin arzikin da may yai kama.
Baba ya dawo gida ummi ta bashi kudi da akace a bashi din ya shiga murna da saka
mata albarka.
Yana ta godiya yace haka Allah ke ikon sa yau na tashi tun shekaran jiya banda ko
kobo a aljihun nan yazu ga kyauta na samu daga sama.
Kwana biyu ana facali a gidan mu kafin su kare nidai ina kallon su kawai ba kunya
ba tsoron Allah a tare dasu.
Haka rayuwan yake gudana dan dama yanzu bakin Inna ya mutu ko tayi ma sai a bayan
mu don da ta fadi ummi take mayar mata.
Sai dai indan wani abin can na kishi ya hadasu daban amma dai ba gori ba don yar
ta na gida kamar mujiya da ta fita sai a kama nuna ta.
Wasu ma harda kari wurin bada labari zancen nata suke karawa don maganan yai
dadin fada shiyasa Saaden bata son fita ko ina koda yaushe tana gida zaune.
Yaya Saadu yazo diba mu bayan kamar wata shida da tafiyan maman biyu shima yazo
muna da abin arziki kamar yadda ya saba kawo muna idan zai zo.
Sai dai wanan karon da wata yazo yarece dai amma yace matar sa ce da ya aura ya
kawo muna ita taga gida.
Baba yace ikon Allah kayi aure bamu sani ba a gurina matar tashi ta sauka don
bata jin hausa munyi dan hira da ita kwanan su biyu damu sukai muna sallama suka
koma.
Kafin ya tafi yake min maganan aure wani iri naji don bayi zaton zai min wanan
maganan ba ya kula da kaduwan da nayi sai yace.
Safiya ki daure ki samu wani mai irin matsalar ki ki aura hakkuri zaki yi bawai
don kina so ba sai dai don kare mutuncin ki.
Nai shiru na dago kaina idona na zubar da hawaye nace ni yanzu yaya ina zan samu
miji a haka yadda nake kowa fa garin nan ya san zance na ba inda inna bata kaini ba
.
Yace ai kinji abinda na fada mai irin matsalar ki zaki aura acan gurin ansan
maganin zasu iya hada ki da wani mai wanan lalurar idan hakakin ki ya kwanta sai ki
daure ki aure shi.
Hakkuri zaki yi da almarin kaddarane kuma yadda kikai tawakkali yana dakyau sosai
haka ake son musulumi dayi.
Shima Ahmed yana can ciwon yakai shi kwance sosai sai da nazo ne na kaishi
asibiti da yana gida kwance yana karyan wai sammu ne.
Nai dariya nace shida yace baida shi yaya akayi haka kuma yace kyale su don Allah
wai saida muka je asibiti ya baiyana yanzu ne mummy ke fadin an cuce ki.
Da wani ido zata kalli baba dashi bayan duk wahalan da kika yi bata zo ta dubaki
ba har yau yanzu dai suna can na barta dashi ban san yadda zasu karata ba nidai na
kaishi asibiti yadan samu sauki yanzu yana nan gida.
Allah ya sauwa ka nace yace ko zaki hakkura ki koma mai kiyi hakkuri ku zauna
hakana.
Nai saurin cewa Allah ya sauwa ka yaya ida bakai ka fada min haka ba yau da sai
an raba mu amma kaine ban cewa komai.
Yai dariya yace Allah da zaki hakkura ki koma yanzu ai yayi nadaman abinda yai
maki ya koma yana daya sani ita ma Lilliya naji ance an kwashe ta zuwa garin su
okene.
Nace yaya don Allah mu bar hiran su kazo zamu rabu da dadin rai kuma kana son ka
bata tsarin nace ai zan shigo lagos indan anyi daidai kana nan sai na karasa wurin
ku naga mazaunin ku.
Yace yaushe kenan nace idan baba ya barni sabin wata nake son zuwa nake fada mai
zuwan maman biyu da tace in dai je in mata kwana biyu yace idan zaki zo sai ki
sanar dani tunda ga waya.
Nan suka kama hanya suka tafi ya barmu cike da kewar shi yaya Saadu mutum ne
wanda yasan kan sa yasan hakkin zumunci.
Yanzu fa zuwa yayi ya kawo muna matar da ya aura wai taga garin su da yan uwan
shi don tasan yana da asali.
Rayuwa yaci gaba muna a gidan dadi ba dadi haka muke hakkuri mu zauna a cikin sa
anyi bukin yar wurin mama salin alin mun sha buki inna na kallo ita da tasha
alwashin yar ta zatayi aure.
Sai gashi Allah yai nashi ikon a kan ta ba maganan aure gare ta sai in Allah ya
kawo mijin nasan dai ba a karkaran mu ba kan don ba inda zancen ta bai kaiba har da
makwabtan garin mu.
Dole muka koma fita tare da ita tun uwar na fada har ta gaji ta saka muna ido don
yanzu haka muka koma kamar aminai da ita.
Sai dai ban yarda tasan sirina don su ba abin yarda bane ga mutane sherin su yawa
gareshi don ta gado uwar ta da hassada sosai.
Idan wata ya zagayo sai in tafi amsan magani acan wani ya leke min wai shi sona
yake yi har da zuwa gidan mu.
Ranan da ya fara zuwa kin fita nayi sai da yaya sani ya shigo na fita bayan wuce
wanshi nace da yaya sani ni ban yarda da shi bane.
Don da ganin shi manemin mata ne sosai don tsarin shi ya tabbatar da hakan yana
magana yana wani iri.
Niko yanzu ba zan yarda na koma wa wala ba bayan na fito gare shi yace ki dai
kwantar da hankalin ki ki bishi sannu mu gani.
Ni dai a raina nasan abinda na yanke shawara a kai so nake baba ya yarde min in
tafi wurin maman biyu sai ranan da suka gane ni.
Amma ban fadawa ko ummi na ba na bar zancen a raina don naga ko ita tayi aman na
da zuwan mutumin wuri na su ala dole na samu mai sona da halin da nake ciki in dai
yi aure ko yaya ne su nasu kawai kenan garesu.
Basu tunanen hali na gari ko wani irin rayuwa zan je kuma na tarar ga ciwo ga
taulalin miji a kaina.
Shi yasa na yanke wa kaina shawaran barin gari salin alin batare da kowa yasan
manufana ba a gidan.
Don in sun sani ba zasu yarda in yi nesa da suba ko kadan shiyasa na bar abin a
raina ni kadai.
Sai in lokaci yayi su san manufana idan kuma basu gane ba a tafi a hakana duk
inda nake sarin kaya a birni tare da kanina nake zuwa don ya iya ya saba dasu don
ko na tafi bazai sha wani wahala ba ya iya.
Harkan kasuwan ci na tare dashi muke yi yasan kan komai da yadda muke aje uwar
kudi mu fidda riba daban duk ya iya.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , ,
2️⃣
8️⃣
YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU
PLEASE..........
Matsala na yanzu Inna ce tabi gari tana bada labari a kaina wasu har zuwa suke yi
ganina a gidan mu.
A cikin gida kuma ita da yaran ta ne suka tsan gwamay ni a gidan ko zama nayi a
wurin sai sun share ko su goge zasu zauna.
Idan na taba ubu bazasu taba ba koda sunyi niyar taba abin sai su fasa.
Ga sake habaici a tsakar gida wai an kwaso cuta an zo za a lakaka masu sudai an
cuci rayuwan su wallahi.
In naji su na kan yi murmushi kai a fili amma cikin raina nakan ji zafi da dacin
zuciya ya kama ni.
Wani lokaci kuma idan sunyi man nakan shige daki inyi ta kuka sai ummi na tai min
nasiha nakan yin shiru ko inji dan dama da sanyi.
Har aikin da kan taya ummi sai suka tsani cin abinta idan na dan taba wani abu
daga ciki ko ta gama ta basu sai kaji ana kiran almajiri a juye mashi.
Da na gane hakan sai inyi zamana kawai a daki bana fitowa taya ta aikin ita ummi
ta fahinci manufa na sai tace min ki zaman ki a daki yafi maki har kiji sauki.
Ranan ina daki kwance ina karatu akai sallama ina jin bakuwar suna gaisawa da
mutanen gidan mu.
Sai take tambayan Safiya tana nan kuwa aka nuna mata dakin mu ta nufi can suka
bita da kallon mamaki yar gayu da ita zata zo wuri.
Jin ta ambaci suna na yasa ni saurin tashi ina da sauri ina daga labulen dakin mu
don in ga ko wacece take nema na din .
Bakowa bace sai Amina kawa na da mukayi karatu tare da sauri na sake labule na
nufo ta muka rungumay nuna da ita sai yan gidan mu sukai tsaye cirko cirko suna
kallon mu.
Na san ba komai bane suke ma mamaki sai yadda ta rugumay ni ne su gashi suna
gudu na agidan suna gwada min kyama a fili.
Muka shiga dakin mu nan na aika ka sayo mata pure wata mai sanyi tana cewa a a
nace ta dai bari a sayo mata bayan yaron ya fice sayen ruwan ne.
Tace dani ashe kuma haka abin ya kasan ce dake alamarin yazo da matsala haka
Allah ya nufa Safiya kiyi hakkuri nima da na shigo jiya mama na ke fadamin abindake
faruwa.
Safiya jiya da naji maganan nan ban iya barci ba amma kuma danaga masu shi yanzu
ba a gane su a fuska sai na barwa Allah alamari .
Gaskiya naji dadi yadda nazo na samay ki baki gala baita ba gaki har jikin ki na
dawo naji dadin haka kwarai da gaske.
Nan na fara bata labarin abinda ya faru tun farko sai cewa take subbahanallahi
amma wanan mutum baida tausayi baida imani ko kadan.
Tana share hawaye tana fadin Safiya Allah ya duba maki alamarin ki ya tausaya
maki wanan BAHAGGON rayuwan da kika taso a cikin shi.
Nace da ita amin don yanzu idona ya kyan kyashe da kukan nayi nayi nagaji sai
dai na kasa daurewa ganin tana kukan nima kukan nake yi.
Sai ummi ne take bamu hakkuri tana cewa haka Allah ya nufa ba yadda banki auren
nan ba amma mahaifinta da matan shi suka nace da sai tayi.
Yanzu da wahala ya cika da ita duk sun watse din sa muna ido da ni da ita a daki
sun koma suna kyamatar ta a gidan.
Safiya tace ai wanan jahilci ne ba a gudun mutum sai dai ayi taka tsantsan wurin
yana yin zaman takewa.
Amma in ana gudun mutum tunane sai ya shiga maishi sai ciwon ya samu galaban
samun wurin yin barna da kyau.
Mun dade da ita a gidan nan ta wuni wurina nai mata dahuwa taci zata tafi na
rakata bakin kofan gidan mu.
Zan shigo gida na hadu da Inna ta yafa zata fita ta wuce na shiga gida ashe tabi
bayan Aminan ne ta tsaida ita.
Tace keko yar nan baki san may ke faruwa da Safiya bane nagan ki wurin ta har da
cin girkin da tai maki.
Amina tai murmushi tace kwarai kuwa na sani shine ma ya kawo ni wurin ta ai don
in mata jajen abinda ya faru da ita.
Inna tace baki gudun ki dauki wanan cutar kema a wurin ta don ance saurin yadduwa
ne dashi.
Amina ta girgiza kai tace ba haka bane gaskiya a samun sa ta hanyar saduwa kamar
yadda ita Safiya ta samu daga mijinta.
Sai kuma ta wurin amfani da zera ko masilar kitso ko allura idan jinin maishi ya
shiga jikin ka to kaima kana iya samun wanan cutar bayan haka zaku iya hurda ko
wani iri da mai wanan cutar kamar kowa.
Inna tai mata wani irin kallon rashin gamsuwa da maganan ta tace ni dai na fada
maki gaskiya don naga kamar baki sani bane.
Ashe kin san komai idan iye iyen ki ya kai ki kika dauko ma kanki cuta ke kika
sani ninayi nan.
Amina tace da ita dakata inna sai ta juyo ta tsaya tace da ita wanan abinda kuke
yi ya kamata ku dai na wanan halin da kuke nunawa safiya.
Inna ki sani idan yarki ce ta shiga irin wanan halin yaya zakiyi sai ta tofar da
miyau tace bakin ki ya sari dutse Allah yai ma diyana tsari.
Tace kin gani itama fa ba da son ranta ta samay shi ba kin sani ya kamata ku jawo
ta a jiki kuna kwantar mata da hankali ba ku dinga aibanta ta kuna hattaran ta ba
haka.
Don Allah Inna ku daina wanan abin da keyi sai ta tare ta dacewa mugun halin
uwarta ce ya bisu ai kadan ma suka gani ai.
Allah ya kyauta Amina tace da ita ta wuce tana bakaken magana Amina dai tabita da
kallo tare da girgiza kanta kawai ta wuce.
Inna ta dawo ido mirsisi tana zage zage a fakaice sai kuma ta shige daki suna
magana da diyan ta kus kus kus.
********* *********
*********
Ina zaune a dakin ummi tun safe da na fito van sake leko waje ba ina dai jin
hayaniyar mutanen gidan mu daga waje suna harkokin su na yau da kullum.
Ba abinda nakeyi sai tunane abu biyu ne ya tsaya min a raina na farko in na tuna
muamula na da mutane yadda ya ja baya yanzu.
Sai na biyu yaya rayuwa ta zata kasance a haka zan zauna dakin uwa ta in kare
rayuwa na ba wani abin ci gaba da zanyi wa rayuwana.
Na lumshe idanuwa na cike da takaici take naji hawaye na zubo min ashe ummi ta
shigo dakin ban sani ba tana tsaye a kaina nadan wani lokaci.
Muryan tane yasani bude idanuwa tana tsaye a kaina tana kallo na cikin bacin rai
da ya baiyyana a fuskan ta.
Ta lumshe idanuwan ta cikin takaici ta juya tana neman abinda tazo dauka a dakin
lokacin muryan ta yayi rauni ta fara magana ba tare da ta dubeni ba.
Watau so kike kuma ki jawa kanki sabon matsala a rayuwa baki san ciwon kan ki ba
ana fada maki ko yaushe kiyi hakkuri kibar wa Allah almarin ki.
Amma sai ki zauna a daki ki ta kuka kina tunane ke kadai ana fada maki gaskiya
baki dauka to maye amfanin zama na a gidan kina kara min bakin ciki ?
Ki rungumi kaddaran da ubangiji ya jarabe mu dashi sai Allah ya tausaya maki yai
maki mafita ta inda baki zata ba.
Kuka nake yi sosai nace ummi ba hakana bane in na tuna da irin zaluncin da sukai
min ne sai na kasa