Advertisements
Chapter 59 Reading Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   59 / 87

174K to 177K   out of 258.3K words

ne ga bawa.
Tace matan yaya ban san abinda yasa yaya ya kasa fahinta na ba har yanzu maganan
shi guda koda yaushe akan miji nima inda nasan haka tun farko aida ban aure shi ba.
Hakkuri nake ta ba ta tare da fadin ki shirya driver zai dawo ya kaimu mu duba
kayan yanzu na juya wurin yaranta ina tambayar su ko sun koshi.
Kada kai sukayi alaman sun koshi din nace to ku tashi kutafi wurin anty Zarah
tana dakin ta kuyi mata fira sai lokacin take cewa zarah na gidan nan ne ?
Nace tana nan dakin ta bata fito bane sai bayan fitan yaran ne na samu magana da
ita inda mukayi magana na fahinta nake kara bata hakkuri tabar bari yaran suna jin
damuwan ta da mijin nata ko yaushe.
A karshe dai driver yazo na muka fita gidan bayan na rufe ko ina na gidan Nura
kawai muka bari a gidan tana aikinta.
Mun tafi wurin mun kuma duba suna da kaya sosai a wurin mun zabi mai kyau cikin
mafi tsada da daraja har labulen da za a saka mun zaba bayan mun gama muka kirashi
mukai mai bayani.
Yace mu bashi shugaban wurin suyi magana dashi nan na bashi matar sukai magana ta
fada mai kudin kayan sun tasan ma milayan daya da dari biyar yace ta bashi account
din su.
Mun dawo gida a gajiye don dan zakayawan da mukayi a wurin akarshe falo muka
zube duk mun kwaso gaji a tare damu sai Nura ce ta kawo muna ruwa da abinsha muka
dan sha ga abinci ta gama mukaci muka tafi sallah.
Aisha ganin abin takeyi kamar a mafalki sai maganan takeyi duk zaman da mukayi
daki na bude mata don ta shiga da yaranta su huta a ciki inda nima na wuce nawa
dakin don yin sallah.
Bayan na idar da sallah na zauna ina tunanen ratuwan Uncle da yan uwanshi na
rasa gane may ye matsalan shi da su haka.
Gashi ni yana iya yiwa yan uwa na dama wasu lalura ba tare da jin kyashin komai
ba a ranshi amma nasa kafin yayi sai ya ja masu rai zaiyi.
Koma may watarana tunda ina cikin su zan ji ko may ye matsala da inda abin nasu
ya samo asalin faruwa.
Ita ko Aisha tana shiga dakin dana bude masu wanda yake gyare komai akwai a cikin
sa gashi kuma kullun a gyare yake duk da ba kowa a dakunan.
Wayan ta tadauko a cikin jakkan ta ida ta kira mahaifiyar ta bayan sun gaisa take
cewa hajiya maganan ki ya fara tabbata gaskiya.
Yau yaya yasa mun fita da matar shi muje in zabi kayan dakin da nake so a wani
shago nan dai take fada mata duk yadda akayi a wurin da kuma fadan da yayi mata
kafin ya fita.
Murmushi mahaifiyar tayi tace kamar yadda nake fada maku wanan yarinyar zata
zamay muna alheri a cikin mu sannu a hankali zamu samu ta canza muna shi amma fa
sai kin bita a sannu komai zai daidaita.
A hankali tace kwarai hajiya aina ga alaman hakan tun yanzu gashi yaya har da
zuwa gida na yayi ta dalilin ta nan dai take fada mata son canza mata wurin zaman
da yake son yi ma,ana ya raba masu gida da kishiyar ta.
Wanan maganan mahaifiyar taji dadin din shi sosai inda tace Allah yasa Aisha su
kuma Allah ya saka masu da alherin sa.
Ki barshi da mijin naki ai kar tasan kar shi da shi, shi yasan ta inda zai fito
mashi da maganan a tsakanin su har ya yarda da maganan a saukake.
Bayan la,asar muka fito nan falo muka zauna muna hira sai gashi ya dawo gidan
yaranta dake waje suna wasa ya shigo dasu rike a hannun shi.
Sannu da zuwa mukeyi mashi amma hankalinshi na ga hiran da yaran suke yi mashi
sai dai da kai yake iya amsa muna gaisuwan da muke yi mashi.
Ina zaune rakube ina kallon yadda yakewa yaran tausayi ya bani don nasan yadda
yake tsananin son haihuwa a wanan lokacin.
Ido na zuba masu sosai daga inda nake zaune tashin hankali na da uncle yanzu
shine haihu wata shidda kenan cur a gidan shi ba bu wani labari ciki a gare ni
shiko yanzu ba abinda zai farauta mashi rai kamar ya ganni da ciki.
Nace oh safiya wai haihuwa bai zuwa a inda ake neman sa ne ga gidan Ahmed da bai
son haihuwan a can Allah ya bani gashi a gidan uncle wanda yasan daraja da kimar
haihuwa shiru kake ji.
Jin yana magana dani yasani dawowa cikin hayaci inda yake fadin may yasa baku
sayo wa boy abinda yake so kuka sayawa amira ?
Murmushi nayi tare da sauke ajiyan zuciya nace uncle rabuda boy din nan rikici
yake ji dai shifa yace a saya masu wanan din da yake ma fushi tun dazu bayan an
sayo kuma wai shi bai so a canza mai.
Ya rugumo yaron zuwa jikin shi yana fadin kyalesu zamu fita in sayo maka wanda
kake so yanzu barin in ci abinci sai mu fita dakai bada su Amira ba.
Abinci na gabatar mashi da kaina ya zauna tare da yaran sukaci suna ta zuba mai
surutu har suka gama suka fice gidan shida yaran.
Aisha ta kalle ni tace ashe yaya yana so yara haka wallahi ban taba sanin yana
kula yara ba ke kuma gaki shiru har yanzu babu labari kodai kina planning ne
safiya.
Ajiyan zuciya na sauke nace nawa na aje da zanyi planning anty wallahi nima nasan
haihuwa yake so Allah dai ne bai kawo ba har yanzu.
Take cewa ki dinga shan miyan kuka tun da safe haka ma idan zaki kwanta barci in
Allah ya nufa zaki iya samu da wuri ki haihu.
Nace aiki na gode kice in samo kuka ke nan in dinga sha don nasan idan hakkurin
uncle ya kure zai kai ga yi min magana nima kuma ina son in ga na haihu wallahi na
kare ina lumshe idanuwa na.
Sai dare ya dawo da yaran idan kafin ya dawo ya kira wayana in fada mata ta
shirya gashi nan zuwa zai maida ta gida na fada mata tare da hada mata tsaraba ya
iso bai ko shigo ba muka fita .
Inda muka samay shi da yaran a mota nan mukayi sallama suka wuce gidan Aishan
dashi koda ya je gidan bai shiga sai cewa yayi ta sallamo mashi maigidan nata.
Tana shiga shiko ya hau ya zugo a wurin kishiyar ta tana sa kafa tana fadin gidan
uban wa kuka tafi har dare haka uban wa zai dafa maki abincin dare a gidan.
Sai dai ku kwana da yunwa ke da yaranki don ba zan bata kudina wurin sayen wani
abu don ku ci.
Shi mai kudin gidan naku da baida moriya kije ya baki abinda zakuci da diyan naki
kishiryarta na zaune gefe da diyan ta suna shan cornflake tace ta aje jaka a gida
mana to ban dafa ba in an dawo acine.
Wani kallo tayi masu tace kaje yana waje yana sallama da kai yace wa cikin zaro
idanuwan shi tace yaya Sulaiman da sauri ya zura sillifas din shi a kafa ya fice a
hanya ya hadu da yaron gidan yana shigo da manyan kwalayen da ya sayo masu tsaraba
wanda dagani har Aishan bamu san ya saye ba.
Kishiyar kuma baki ya mutu ganin kwalayen da ake shigowa dasu gidan ana dire su
kofan Aisha din wani irin kishi ne ya kamata a lokacin.
Ya fita sun gana dashi ban san yadda sukayi ba dai da mijin Aishan can ya dawo
ciki bayan sun dauki lokaci da uncle a waje yana cewa boy yau uncle ya kaiku
shopping ne haka ?
Yana ta faman washe baki namiji dama baida kunya nan yabar kishiryar zaune tana
kallon mamaki shine har da yiwa yara wasa a lokacin.
Uncle bai dawo ba sai tara da rabi ya shigo da ledan kajin da ya sayo wanka ya
shiga sai bayan ya fito wankan ya fito falo yana fadin in bude mai kajin su zai
iyaci kawai yau.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/21/20, 6:24 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , ,
6️⃣0️⃣6️⃣
6️⃣
🧕🏿 0️⃣0️⃣6️⃣


NOVEL DINA NA KUDI NE IDAN KIN FITAR MIN KO KA FITAR MIN BAN YAFE MAKU BA UBANGIJI
YABIN HAKKINA AKAN KU DA DUK WANDA YA KARANTA BAI BIYA BA.


Satii biyu ya rage mu daga zuwa kasar Canada wanda yai dai dai da kwanan kin
azumi baifi kwana goma ba tsaka ni.
Zaune yake a saman gadon ya mai da hankali ga laptop din shi daya tasa a gaban
shi ya mai da hankalin shi gaba daya akan abinda yake yi din.
Dakin na shigo dauke da abinda ya sa in dafa mashi na nauin samun lafiyan maza na
shigo dakin dakin da sallama na.
Har na isa saman dan katamin table din dake dakin na aje tire din da ke dauke a
hannu na da kayan shaye shaye irin na maza mai kara masu lafiya karfi.
Bayan ma aje na samu wuri na zauna a kusa dashi ina fadin uncle ga yanan na gama
hada maka idon shi na akan laptop din shi nima dai ba wai shi nake kallo ba ko da
na zauna hankalina yana ga wani takarda da na gani saman gadon shi a lokacin.
Amma wanan kamar wurin da muka sayo ma Anty Aisha kaya mana, nake cewa dashi
cikin dan, kallon fuskan shi dake duke saman laptop din.
Bai ce komai ba sai ci gaba da abinda yake yi yana murmushi nagama kallon
takardan na aje inda na ganshi tunfarko tare da mikewa zan bar dakin .
Da sauri ya dan riko min hannaye na yana fadin ki dan dakata min in gama please
komawa nayi na zauna tare da dan kai kafaduna saman gadon nayi rigingine.
Bai dade ba naji ya sauke ajiyan zuciya ya juyo yana dubana tare da kokarin rufe
laptop din da yake aiki a cikin sa .
May zaki yi yanzu idan kin fita, yace dani, sai tambayan nashi ya bani mamaki
sai dai ban kai karshen tunane ba naji yace dani zuba min ruwan maganin na.
Na dago a hankali zuwa gaban dan table din na fara tsiyaya mai ruwan ganyen
maganin da ya sa na dafa mai.
Muryan shi naji tana cewa yanzu yaya zamuyi da mutane ga tafiya a gaban mu kafin
azumi wanda ba zamu dawo ba sai bayan sallah insha Allah kin ga ban gida za ai
azumi da sallah ke nan.
Juyowa nayi gare shi dauke da cup ina mika mai nace hakane Uncle a yadda kace za
ai tafiyan ya amshi ruwan maganin dake tiriri a cup ya dan kurba yaji da saura
zafi.
Ya dago ya kalle ni nace da sauran zafi ko kai ya gyada min amsa nayi nadan kada
spoon a ciki ina dan motsawa a hankali yana zaune ya mayar da hannuwan sa baya ya
tokare a saman gado.
Ya kura min ida baya ko kiftawa na dago kai ina cewa dashi sai dan ban san abinda
kake shirin yi wa mutane ba kan azumin da sallah.
Yace in banda abinki yanzu ai wanan a cikin aikin ki yake ni dai kawai idan kin
tsara sai ki sanar dani komai ake ciki da can madam maimuna ce take tsara min komai
indan lokaci yayi.
Na ce a raina akwai aiki gaba na ashe don ban san komai a yadda take shirin ta
amma dai ba matsala zan yi iya kokarina yadda ya dace.
Mika mashi cup din ruwan maganin nayi ya karba ya kafa kai bai cire ba sai da ya
kurbe duk ruwan maganin a lokaci guda.
Ya kare yana ya mutsa fuska da alama bai da dadin sha ya dauki ruwa kadan mara
sanyi ya dan kora a cikin shi.
Gauron numfashi na sauke ina fadin wai wanan maganin may ye haka kake sha kwanan
nan yace ba matsalan ki ba ne yanzu.
Mikewa yayi tsaye yana fadin ke nake saurare yanzu don bani son a makara zan baki
list din last year don ki san mutanen da ake aikawa .
Wurin wani dan drower dake dakin ya nufa yana tono list din ya juyo yana fadin
sai dai ta wajen baba can gida ban san wa yanda kike so aiwa sadakan acan.
At list mutane hamsi maza nake son a raba ma abinci da mata hamsin suma a basu
abin azumi dana sallah haka nakeyi duk shekara daga riban da nake samu na wurin
masana,antan taya na.
Duk bayanin da yake min bai dago kai ya kalle ni ba sai da yake miko min takardan
ne ya kare da fadin ki duba idan an samu kari sai a kara dasu.
Ni zan fita dama maganin nan ya tsayar dani yau akwai aiki a gaba ina son in
kammala komai a yanda nake so shi a cikin satin nan.
Namike tare da daukar mai jakkan aikin shi yana gaba ina binshi baya har muka isa
haraban aje motocin gidan bai dauki driver ba shida kan sa ya tuka motar ya fita.
Nayi ajiyan zuciya na juya zuwa cikin gidan zuciyana fam da tunanen nauyin da ya
dora min akai yau a gidan.
Dakina na wuce sai da na kara yin wanka na gyara jikina na dawo na zauna na fara
tunane gashi yana jaddada min kada nayi mashi delay a tsarin ni yanzu ta ina zan
fara ne.
Anty Aisha ne ta fado min a rai da sauri na jawo wayana ina kiranta har kiran ya
katse na sake danna kiran sai nayi sa a ta dauka.
Mungaisa tare da tambayanta yara da gida ta amsa da suna lafiya kafin ta fadi
wani abu nace Anty Aisha ki taimake ni don Allah banda wani mafita yanzu sai gare
ki.
Tana dariya tace niko matar yaya mai zan taimaka maki dashine haka a rayuwana
nace bari kedai yayan kine ya dora min nauyin rabon kayan azumi da na sallah bana.
Dariya naji ta kwashe dashi tare da fadin Allah mun gode da ka nuna muna wanan
ranan don wanan magana kika tayar min da hankalina da farko.
Ai wanan abin farin ciki a gare ki don dama matar yaya na can lagos ne take yo
mashi sayayyan sai abinda muka gani zata bamu.
Nace to yanzu yaya zamuyi don kawai mu kawar da zancen anty da take son daukowa
nan dai tayi min bayanin abinda suka samu last time sai na kwatanta na gani idan
nabi list din zasu samu abinda yafi haka.
Godiya nayi mata ba tare da na tsaya sauraranta ba tace wai ko kin san kokarin da
yayana yayi min na maganan canza gida nan take kora min bayanin abinda ya kasance
tsakanin shi da maigidan ta.
Tace yanzu tunda aka fara zancen ba zaman lafiya tsakanin shi da kishiryar ta
kullun fitina suke kwasa a tsakanin su ita yanzu ta matsu ta tashi ta bar mata
gidan ta koma gidan ta.
Nace kin ga haka yafi aiyafi ance kazantar daba kagani ba sunanta tsabata shi
takewa bakin ciki yanzu true colour din ta zai fita a tsakanin su.
Kin ga sai yasan halin ta na gaskiya shi take ma gudu dama tace gata ragguwa ko
jikin ta bata iya gyarawa balle na diyanta.
Mun dai dauki lokaci muna magana akan gidan mijin nata a karshe mukayi sallama
nan ta barni ina tunane ai ita tasan tana da kishiya ke nan ni yanzu ban san idan
na dosa don wanan nauyin da ya dora min zai iya saka wani sabon tsana tsakanina da
anty kuma.
Kamar yadda yace duk cikin kwana kin nan abinda muke fita ke nan yi daga sayan
kayan masrufi zuwa tufafi da kayan tea da sauran su .
Ga kuma shirin komawan Aisha sabon gidan ta a wani sati da muke yi a makon nan
muka shiga bauchi inda na samu taro na mutunci a wurin yan uwan Uncle da mahaifiyar
shi don yanzu Aisha ta gama shigar dani a gare su ko.
Saida mukayi sallah muka shiga wurin hsjiya baaba don mu gaida ita tana zaune
cikin kamala duk muka zube kasa a gaban ta .
Da fara,ata take muna sannu da zuwa da yaya hanya daga nan kuma suka fara dan
hira da danta a cikin hiran ne yake mata bayanin tafiyan da zamuyi.
Wanda yasa muka zo kawo masu abin sallah dana azumi kafin mu wuce din tayi farin
ciki da jin haka tace babana kokai fa abinda nake fada ma ke nan da dadewa cewa
samun mace ta gari zai iya canza maka rayuwanka.
Yanzu gashi tun ba a je ko ina ba abubuwa suna canzawa sannu a hankali a wajen ka
wanda wanan kokari ba kowane ya kawo shi ba sai ke mai sunan gwago na.
Na dago kai na dan kalle ta cikin mutunci da nuna alkunya gare ta tace eh a
dalilin ki na samu farin ciki da hadin kan diya na da yan uwan uban su suka watsa
min kawunan su a baya saboda son zuciya.
Yau gashi babana dake zaman yaya kuma uba a gare su ya dawo ya rugumi yan uwan
shi da hannu bibiyu abinda na dade ina fatsn gani a gare su.
Yau ko wacen su tana farin ciki a dakin auren ta ta sanadin ki kin saka ya sauya
masu rayuwan su na kunci don dan abinda suka gada a wurin mahaifisu dama yan uwa
sun ciyen shi kaf gare su basu barsu da komai a hannun su ba.
Fatana gare ku yanzu shine Allah ya baku zuria masu albarka nima in ga jikokina
ta wurin babana in runguma in goya kamar yadda ko wace uwa ke burin gani a rayuwan
ta.
Kaina na dukar kasa don kunyan abinda ta fada a karshe sun dauko maganan da ya
shafi gida don haka na

59 / 87