Advertisements
Chapter 39 Reading Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   39 / 87

114K to 117K   out of 258.3K words

suka fita neman magani anyi saa an
samu a wani shago sai dai shi yaya sani yana ganin yawan kudin don dubu ashiri da
wani abu suka kaso .
Ya dawo yana fada min nace mun yi arziki ai tunda an samu tun cikin dare akaiwa
baba aluran da bashi maganin sai gashi ya samu barci sosai ranan.
Washegari nacewa driver ya wuce sai yake cewa ai sunyi waya da maigida yake cewa
ya dan tsaya don zirga zirgan mu ya taimaka muna naji wani iri a raina sai dai a
fili cewa driver nayi anya ayi haka bazamu takura maka ba ?
Haba madam aini a kan aiki na nake daganan har ki gama banda damuwa ko kadan
Allah dai yaba baba lafiya.
Nai mashi godiya sosai yace babu damuwa hajiya ai mu aikin mu ne naga kuma oga ya
damu sosai da ciwon na baba murmushi nayi kawai.
Sai na tuna ban kirashi ba tun jiya kamar yadda yace in kirshi din don ya anshi
wayana yasa min nombashi da zamu wuto.
Gefe na koma saida na tattara natsuwa na wuri daya sanan nai dialing din nomban
na shi ringi na uku ya daga wayan yana cewa.
Safiya yaya ai na zaci bazaki kirani ba kin ga mutanen gida kin manta da kowa.
Murmushi nayi nace wallahi ba hakana bane ya dan kwaikwayeni yace to yayane nace
kawai dai jikin babane ya tsoratani jiya da na samay shi jikin ba dadi wallahi.
Amma yanzu ya samu lafiya sosai don maganin da aka rubuta mai da allurai tunda ya
sha su ya samu barci jiya sosai.
Yace masha Allah haka akeso to yaya mutanen gida nace suna lafiya sai nai shiru
kusan tare mukai magana ina cewa kuma har da wani dawai niya haka mai yawa.
Yace bake nai wa ba iyayyena da kanne na naiwa tsaraba ki basu godiya na fara mai
yace haba na fada maki bana son haka nifa iyayyena ne yanzu koba hakana bane ?
Murmushi na danyi yake cewa yanzu dai hankalin ki ya dan kwanta ko baba ya samu
lafiya sai na sauke ajiyan zuciya nace hakane amma da hankalina a tashe yake so
sai.
Don mu din tallakwa ne na karshe indan baba ya kwanta wa zai dube mu shi kaga
hankali na ya tashi sosai.
Yace karki manta da cewa Allah ne mai yi ba wani ba yanzu bagashi ya samu sauki
cikin yardan ubangiji ba nace haka ne kuma.
Yace idan ya tashi ki gaida min shi zan shiga meeting yanzu dama don baki kirani
ba ne yasa ban kiraki ba yanzu kuma naji dadi alama ya nuna na dan samu karbuwa ke
nan.
Kai nace haba uncle kabar wanan magana tukun yace na bari as you wish ganin zai
kashe wayan yasa nace sai kuma driver yace kace ya tsaya damu.
Yace eh haka na umurce shi don idan ya wuce ina zaku samu abin yin zirga zirga
shine nace ya dan dakata har muga yadda hali yayi.
An gode na kara fadi zan shiga godiya naji ya kashe wayan shi kit na dubi wayan
ina murmushu na shiga dakin da aka aje baba din har lokacin yana barci naja kujera
na zauna tare da kafa mai ido.
Mama tana zaune a kasa saman tabarma tana karyawa da abincin da na sa yaya Sani
ya sayo muna don bamu da kowa a garin.
Na dan dade a zaune sai ya motsa da sauri na dago ina cewa sannu baba yaya jikin
ina dan gyara mashi kwaciya yace Safiya ke ce yaushe kika dawo ?
Nace a sanyayye jiya na dawo baba yaya jikin yaya jikin baba ?
Yace jiki da sauki Safiya na gyara mashi kwaciya yace baiyi sallah ba da tai
makin mu nida mama muka kamashi ya kewa yayi alwala.
Bayan ya idar da sallah ne yake cewa nan ina ne mama ne ke fada mashi ai asibitin
birni aka zo dashi jiya da dare da safiya ta iso.
Yace Allah sarki sannu Safiya nagode nagode ubangiji yai maki albarka yasa ki gama
da duniya lafiya nace amin baba mama tace yau ga ranan diya mata mun gani a gidan.
Don badon Allah ya taimaka ba da bamu san yadda wanan alamarin zai kaya muna ba
kana zaune a gida ciwo zai halaka ka babu yadda muka iya .
Gashi daga zuwan mu jiya jiya har mun ga haske gashi yau ubagiji ya nufa ka bude
ido nace baba don Allah ka rage yawan tunane don likita yace tunane yai maka yawa
har zuciyar ka ya kumbura.
Murmushin karfin hali yayi yace yaro yaro ne tune ne ai dole mai rai yayi shi
balle ni da gidana yake batun fin karfina inda rai na kuma don may bazanyi tunane
ba safiya ?
Nace baba hakkuri za a yi abar ma Allah komai ubangiji yana sane da komai da
bawa ya gani yanzu dai may zaka iya ci a sawo ma ?
Yace ban jin cin komai sai barcin da nake bukatan komawa don idon nan nawa kamar
asa min abu mai nauyi nake jin shi.
Nace baba ka daure kasha tea mai dan zafi ko hajin ka zai warware ka kara samun
karfin jikin ka.
Yace dadai kune ne kila zan dan iya sha da sauri nida mama muke cewa ga kunu nan
an sawo bari a baka yaya sani ne suka shigo shida driven nan suka shiga gaida shi.
Bai sha wani abin kirki ba ya koma barcin muka sauke ajiyan zuciya muna kallon
yadda yake sauke numshi a wahale wai ma cikin yaji sauki ke nan.
Sama sama muke hira da mama ina fada mata irin zaman arzikin da muke yi da anty
da yan uwanta tace Safiya haklin ki ne ya ja maki .
In dai baka dauki kan ka da fadi ba Allah yana taimakon bawan sa ta ida bai zata
ba Allah ne ya kawo ta cikin rayuwan ki don ta taimaka maki.
Gashi tun yanzu muga haske badon Allah ya kawo ki ba wanan alamarin yaya zamuyi
kena da haka zamuyi ta kallon shi a gida babu mai taimaka muna.
Shiyasa nake ganin haukan innar ku da bata da kalamin alheri sai na tsiya akan
yayan mutane duk da wanan abin da ya cika dasu kuwa.
Murmushi nayi nace banga ranan da inna zata daina halinta ba ita haka Allah ya
halicce ta da hassada don bata bar kowa ba a gidan.
Tace bata fa dainawa don dubi abinda tayi jiya Sani ne kawai mai taka mata burki
don badon shi ba jiya ba karamin tashin hankali za a yi ba.
Nace niko ban ga Saadatu ba ma tace tana nan daki bata jin dadin jikin ne don
duk da malam ya hana a zubar da cikin jikin ta amma bai hana uwan bata abubuwa a
boye ba.
Nace na shiga uku mama karfa ta kashe ta tace in ma ta kashe ta ai ita ta sani
waya ci baya ina mahaifiyar ki data rungumi kaddara ba ga abin yazo mata da sauki
ba.
Mu dai fatan mu ubangiji ya baki miji ki aure ki huta da zargin cewa zaman banza
kike yi a can na ce ai Allah yagani mama.
Ban yi ba da sai yanzu da lalura a jikina zanyi in cutawa mutane ko mai tace ai
bata gane hakan ita don idon ta ya rufe ko.
Motsawan da baba yayi yana fadin a bashi ruwa yasa mu tashi muka ce yayi hakkuri
an daura mai ruwa nace barin fita in nemo likita a fada mai.
Naje gun nurse din ward din mu na fada mashi sai yazo ya duba baban ya fita kiran
likita sai gasu sun dawo tare da likitan yadan duba baba din tare da zare mai ruwan
da suke kara mashi din.
Yace a barshi ya dan huta zai daina jin kishin da yake ji nan dai suka kara
taruwa a kasa suna mashi gwaje gwaje irin nasu na likitoci.
Yaya Nura suka iso shi da su ummi da mama da rana nan suka samu yana barci bayan
gaisawan da mukayi dasu ne mama take masu bayanin halin da baba din ke ciki yanzu.
Nan dai muka wuni dasu sai zuwa yamma sukace zasu tafi drive nan dan arziki yace
in bari ya mayar dasu sukace ya bari zasu shiga motar kasuwa inna sai baza ido
takeyi wirin kalle kalle a asibitin.
Ya kwashe ya wuce dasu hankalin gida zai kwanta yanzu da suka zo suka gan shi dan
da basu zo ba duk wayan da muke yi dasu basu yarda a yadda muka fito dashi gida wai
ya samu lafiya yanzu.
Baba yana samun kulan da ya dace sosai dashi sannu a hankali yake samun sauki na
shigan shi yana dan dada murmurewa .
A kwana na uku ne driver da ya kawo ni yace zai koma gida na bashi kudi yaki
karba amma sai naba yaya Sani ya bashi idan sun fita.
Ban wasa da shan maganina don dama ina dashi anty tana kaini ansa a sace bada
sanin kowa ba a can lagos din don haka ban da matsala wurin amsan maganin .
A kwana na shida aka sallamay mu nan muka samu motar muka dauka ta dawo damu
gida kowa na ta farin ciki yadda suka ga baba ya samu sauki.
Sai dai an bashi dokoki na ya rage tunane da abincin da ya kamata yaci don ya
samu lafiya muka sayo magani wadatacce muka dawo gida dashi.
Dakin mu na shiga na cire kayan dake jikina don duk warin asibiti duke yi wanka
naje nayi na shirya sai na fito zuwa dakin inna.
Saadatu na kwance duk ta kumbure nace subbahanallahi Saadatu may ke faruwa haka
kina zuwa asibiti kuwa maimakon tai magana sai kuka ne yazo mata.
Zama nayi a kusa da ita nace bari kuka saadatu haka Allah ya nufa damu sai dai
istigifar ga bawa nace kin je asibiti tace wa zai kaini Safiya dan jike jike dai
inna ke bani ina sha.
Nace zuwa zamuyi gidan mau ta dubaki mu gani tace uhumm Safiya ai da na dauka
halin innan mu yasa kin fita batuna ne dan da kika zo baki nemay ba harda kuka nayi
gashi ban iya fita ko ina.
Nace haba saadatu may zai sa inyi fushi dake ke fa yar uwata ce ta jini halin
inna kuma inda sabi ai na saba yanzu sai dai addua kawai.
Da taimako na ta samu ta shirya don inna na dakin baba sai fitowan mu suka gani
kawai take cewa ina kuma zaku haka ?
Nace wiri mau ta duba lafiyan jikin ta don ba a barta haka ba tana wahala tace
ai ita taja wa kanta ina ruwan wani saaden tace dani mutafi kin ji safiya.
Nan muka fice muka barta mashin na tare ta hau nima na hau mukaje gidan an
dubata take muna bayani bata samun kulawa ne sosai an mata allurai don tace akwai
maleria masu ciki a jikin ta do haka tabar bari sauro na cizon ta ta bamu magani
tare da fada mata abinda ya kamata taci kuma ta dinga zuwa ana dubata akaiakai.
Bamu dawo gida ba sai da na sayo mata abin bukatun ta harda gidan sauro muka dawo
gida yamma tayi a lokacin nan ina ta ke cewa .
Yanzu dai anyi kudin da bamu san asalin shi ba anzo ana muna facali a gida indai
tai wari ai maji komai daren dadewa .
Ba wanda ya kulata sai dare muka samu kebewa da ummina nan muka shiga hiran
yaushile rabo da ita nake fada mata duk yadda nake can.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , ,

4🧕🏿141
4️⃣
4️⃣
1️⃣ 1️⃣


Ummi ta nisa bayan ta gama sauraren magana na tana cewa dani anya yar nan baki iya
tsaga fadi ba wanan mutumin bai fi karfin mu ba.
Na ce ummi nima abinda nake tunane kenan amma ita anty bata son ina fadin haka
din tace yanzun dai ki dan kara nazari kafin ki kai ga gabatar dashi nan din.
Fadan inna da mukaji shiya dakatar damu daga maganan da mukeyi din da muka
saurara muka fahinci da saadatu ne take fadan akan daura gidan sauron da muka sayo.
Fada sosai suke yi a tsakanin su nice na fito nayi wa saadatu magana sai take
cewa wai inna tace bata yarda ta daura gidan sauron ba a dakin ta.
Nace haba inna tana da wani daki yanzu a gidan nan bayan naki don Allah ki yi
hakkuri kibarta ta daura daidai inda take kwanci.
Nayi dana sanin fitowa raba fadan nan tsakanin inna da diyar ta don abin karshe a
kaina ya dawo babu irin kazafin da inna bataimun ba ranan kowa najin ta a gari.
Dole naja kafana na koma dakin mu bisa umurnin mama har lokacin bata daina fadan
da take yi ba ta hade mu ta zage tas tana cewa sai dai yawon banza amma badai aure
ba gare ni.
Naje nayi fasikanci na nadawo ina wa mutane sallo sai inyi wa wa yanda basu san
abinda nake yi ba .
Ummi tace da na hanaki fita zakiga kamar ban son zaman lafiya ne ai gashi kin
jawo wa kanki kwana da bakin ciki a ran ki.
Nidai shirin kwanciya nake yi ina kara jimamay maganan Inna datake yawan fada min
a koda yau she magana ya hada ta damu.
Ya zama min dole in yarda da bukatar Sulaiman akaina kamar yadda yace bai son
abin ya dauki lokaci don shi yanzu bai ga abinda zamu tsaya jira ba .
Magana ummi keyi dani amma banji ba nayi nisa sai da ta kara daga murya na ji ta
nai saurin cewa ummi kanin mijin anty na ne.
Kuma su suka hada ni dashi don shima irin matsalar mu guda dashi aure yayi matar
ta rufe mai tana da lalura sai da akayi abin ya bayana mata.
Bacin rai yasa ya rabu da ita duka duka watan su shidda da aure suka rabu da ita
tace amma ko bai kamata ya sake ta ba tunda ya dai riga da ya kamu da ciwon.
Nace ai nima abinda nagani ke nan amma sai anty tace dani dama ba sonta yakeyi ba
itace ta like mashi.
Yanzu ke baki ganin akwai matsala idan kika bashi baki akan ya fito nifa ina
tsoron masu kudin nan don da wuya suke rikon aure.
Nace ummi duk wanan tunanen nayi shi kuma na fada ma anty amma sai cewa tayi
nasan dai ba zata kaini inda za a cuce ni ba kin ga banda ta cewa don darajan ta a
gare ni.
Amma dai ni sanin da nai mai baida wani matsala rayuwa sai dai ba a san abinda ke
boye ba kwai ne.
Tace yanzu dai kafin ki koma sai ki shirya kije can gida ki ga baba da yaya Adamu
ki fada masu in ma mallam ya yarda sai mu tafi tare dake mu gan su.
Nace to ummi hakan ya kamata ayi nima dai hankali na bai gama kwatawa ba dashi
amma babu yadda zanyi ne kawai sai ya zama kamar na watsa ma anty kasa a ido bisa
kokarin da takeyi dani.
Haka na muka kwanta kowa da tunanen da yake yi a zuciyar shi sai asuba muka tashi
bayan nayi sallah na fito na share gidan na tara kwanonin da akai amfani dasu.
Ina cikin wanke wanke ne na kusa gamawa sai ga inna ta fito sai cewa tayi dama ko
acan abinda ke yi ke nan anzo nan za ai muna barkadon banza.
Nace inna ina kwana bata amsa min ba ta shiga daki sai gata tafito da kwanoni
masu yawa ta zube min su ashe mama na daga kofan ta tana kallon mu.
Inna ta wuce tana maganganun ta sai mama tace kai wanan balain da may yai kama
don Allah ba a barin mutane suji da abinda ya damay su sai bakin fitina tun da
farin safiya haka.
Wa na hana yadda yake so a gidan nan idan kuma kin saka kan ki ne sai a sayar
maki ba abune mai wuya ba ehhy.
Mama tace in ma zaki iya nan da shekara sai ki tayi bama sayar ba ko kwasa ne sai
ki yi gaki ga wuri ai.
Wanan abu damay yai kama kin kwana fitina kin tashi dashi duk yarinyar nan bata
kula ki ba ba sai kiba kanki lafiya ba wanan ai zubar da mutunci ne gare ki.
Nan dai sukai dan cacan baki tsakanin su ba wanda ya kula ta ni dai na gama na
shige dakina na barsu nan.
Wanka na fito nayi ina cikin gyara jikina sai ga Saadatu ta shigo dakin ummi din
ta samay ni muka gaisa.
Nake tambayan ta yaya jikin ta sai tai murmushi tace jiya na samu barci sosai
wallahi Safiya na gode kwarai wallahi banda abinda zan fada maki sai dai kuma kiyi
hakkuri da halin inna don Allah.
Na yi murmushi nace ai inna uwane fadan su gare mu taki wata rana zai muna amfani
a gare mu dariya ta dan yi tace kayya ke dai kiyi hakkuri kawai.
Muna nan muna dan hira sai jin muryan inna mukayi tana kwala ma saadatu kira
share uwar tayi kamar bata jita ba.
Sai da ta kara kiranta tace tana zuwa ta ci gaba da maganan ta sai da nace taje
taji kiran da inna ke mata ta dawo.
Bayan fitan ta ne na ci gaba da shiri na nace ma ummi gidan gwagon ta zan tafi in
gaida ita tace dani aiko kin kyauta.
Nace a debi tsaraba abawa kowa har da makwabta tace kidai diba sai ki ba mutanen
gidan abasu sai na makwabtan duk ki diban masu.
Dole na tsaya nayi kamar yadda tace inyi din tace haka yayi bayan na raba na
dauki na fanin su gwago aka fita min dashi waje inda zan samu mashin

39 / 87