Advertisements
Chapter 81 Reading Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   81 / 87

240K to 243K   out of 258.3K words

na haye gadon na kwanta a bayan
shi.
Haka barci ya kara daukan mu sallah asuba ya fita yi don jin jikina yadda ya
gashe kuma ina rawan sanyi yasa shi fita bai tayar dani ba.
Har yaje massalaci ya dawo ina kwance sai kaduwa jikina keyi ina wani irin sam
bato hakorana suna kadawa da yan uwan su na kasa.
Hawowa yayi saman gadon tare da dan tallabo ni yana fadin tashi muje asibiti
hakana .
Kasa tashi nayi dakyat ya samu na tashi nace kuma zanyi sallah kina iyawa yace
dani kai kawai na gyada mai na shiga ban dakin ya biyoni ciki har nayi alwala na
gama na fito ya miko min hijjab dina.
Da kyat na sallamay bai saya jiran komai ba ya dagani muka fita daga dakin da
kanshi ya toka motar muka fice a gidan bayan ya buga ma mommy zamu tafi asibiti
tace jikin ne har yanzu ?
Eh kawai yace ya fice bamu dawo gida ba sai da suka bani gado suka kwantar dani
likitan shi ne a kaina sai wasu dakan dan shigo sun debi fitsarina da jini zasu
auna su gani.
Alluran da akai min yasa ni barci sosai fita yayi ya kira yaya Saadu ya fada mai
anbani gado ya kashe ya kira Aisha tace gata nan zuwa da ta sauke yara makaranta.
Gida ya kira mommy ya fada mata don hankalin ta ya kwanta shigowan yaya Saadune
da samira na dan falka ban dade ba na koma barcin don karfin alluran da akai min
din.
Zuwan su samira yasa shi komawa gida don anan suka barsu a tare dani sai barci
nakeyi hankali kwance ga ruwa daure a hannu na .
Aisha ta zo nan suka hade wurin suna dan hira mummy da zai dawo bayan yara sun
tafi makarantane yazo da ita don ance sai sha biyu result zai fito na test din da
akayi.
Bai shigo dakin ba amso result din yayi suka hade da likita bayan ya karba
yafita sai ya dawo dakin da nake kwance din sun gaisa dashi ya nufi wurin gadon
yana tambaya ban falka ba har yanzu ?
Samira tace na dan falka dazu ban dade ba kuma na koma barci ya dade tsaye a
kaina ya juya ya fita sai suka hade da likitan.
Hannu likitan ya mika mai yana fadin congratulation sir madam.cikine gare ta har
five week shine ya jawo mata ciwo haka kuma kasan yanayin jikin nata gashi kuma
bata dade da haihuwa ba strees yayi mata yawa ne.
Wani irin lumshe ido uncle yayi tare da dan rike hannun likitan yana fadin ya
gode kamar shi ya bani cikin.
Takardan magani ya mika mai yace asamo wanan maganin idan ta tashi zata samu
sauki sai tasha don jikin nata ya samu dan karfi don yanayin ta.
Bai dawo dakin ba don mata sunyi yawa a ciki yake gani wurin sayen magani ya tafi
daga can ya wuce office ya duba wasu bakin da yayi sai bayan la,asar sosai ya shigo
asibitin.
Lokacin ina zaune ina tauna Apple din da nace yaya Saadu yazo min dashi idan zai
zo gaishe sukayi ya amsa a duduke ba tare da ya kalle su ba.
Bakin gadon ya karaso yana tambayana yaya jiki da sauki kawai na iya bashi amsa
ya kalle ni duk na ramay na fada a lokaci guda kamar na dade ina ciwo .
Fita suka fariyi a dakin kamar wa yan da ya kora bansan may sa suke shakkan shi
idan yana wuri har samira bata sakewa takan ce dani mijin nan naki kamar ustazu
yake baya kallon mutane ko kana gaida shi sai ya dinga yi kamar yana tsoron mata.
Muryan shi naji yana ce min cin fruits din ya tashi ko da sauri na kalle shi sai
kuma na sadda kaina nayi kasa .
Sai kuma na dago nace dashi ciwo yasani ci idan bashi na dan ci ba banjin dadin
baki na yace aifa yanzu banda sauran wasa da saye fruits .
Haba uncle daga ciwo kuma sai in buge da shan fruits ko yaushe murmishi yayi yana
gyara zama da kyau yace yanzu yaya kike ji naji sauki na fadi a hankali kamar
banson magana.
Ga magani likita ya rubuta yace a sayo dazun sai kin ci wani abu zaki sha don
haka barin fita in kira Aisha ta zuba maki kici sai ki sha ido na lumshe a hankali
tare da fadin bazan ci abinci ba zan dai sha koko da mummy ta damo min.
Yace ok kisha din sai ki sha maganin ya mike ya fita ya kira Aisha tazo ta zuba
min ya dawo ya zauna inda ya tashi yana zaune har na gama sha ya bare maganin ya
bani na hadiye na koma na kwanta.
Kwana daya nayi aka sallamay muka koma gida ba laifi don na samu lafiya sosai sai
dai jikin nawa ba karfi har lokacin su Maimu da hindatu keyi wa Abba wasa ina zaune
na kura masu ido kawai banjin dadin hayaniyar nasu amma kuma ban iya tsawata masu
su bari.
Mummy ne ta fito tana masu fada daga dakin ta lokacin uncle ya shigo gidan zama
yayi nan falo inda muke mommy ta gaida da dawowa.
Bayan ya tambayeni jikin yana yi ma abba dan wasa ya leke mai wai ya dauke shi
yace tafi wurin uwar ka maimu zan dan watsa ruwane a jikina.
Ya mike ya shiga dakin shi ya jima a ciki na tashi na bishi dakin nashi don ban
iya jure hayaniyan da yaran ke yi haka kawai nake jin haushi komai ba gaira ba
dalili.
Shiga nayi na kwanta saman gado har ya fito ya samay ni a nan nan kika dawo kuma
nace haniyan yaran nake jin shi har cikin raina wallahi.
Sai da ya gama shirin shi yasa jallabiya ya fesa turare a jikin shi haka yasa
nasan bazai fita ba ke nan yau kuma don baya fita hakana.
Takowa yayi inda nake din yazo ya zauna safiya naji ya kira sunana a hankali na
dan bude idona da suke lumshe na sauke akan shi tare da dan kakaro murmushi a
fuskana kadan.
Kin san kina dauke da ciki a jikin ki na wata daya da kwanaki da sauri na daga
daga kwanciyan da nake ina fadin na shiga uku.
Kin sha uku akan may safiya ban taba zaton jin wanan furucin daga bakin ki ba
domin ko abin farin cikine ya samay mu bana shiga uku ba.
Uncle abi fari ciki fa kace yaro na yana da wata bakwai uncle
zakace wai abin farin ciki ya samay mu ?
Kallon da yake min ne yasani natsuwa na farga da katobaran da nake shirin yi a
gaban shi a yadda na san shi da son haihuwa yanzu.
Yana yawan fada min shi haihuwa yake so yayi yanzu yana son ganin yara sun cika
mai gida kamar sauran gidajen yan uwan shi da abokai.
Sai gashi ina shirin yin baranbarama da albishir din da yake min na dan cikin da
ke jikina wanda ashe shiyani zazzabin nan da nake yi duk dare.
A hankali na koma na kwanta tare da lumshe idona ina mai jin zafi a raina da
samun wanan cikin na jikina a wanan lokacin da ban tsamace shi ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/21/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , ,

8️⃣4️⃣8️⃣
🧕4️⃣8️⃣4️⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU


Fita yayi daga dakin batare da ya kara magana komai ba nima komawa nayi na kwanta
ina jin zuciya na yana min zafi maikon in ji farin ciki a raina.
Ba don komai ba sai irin surutun da mutane zasu dinga yi ga haihuwa na a kai akai
da nake yi kowa zai fassara min shi da wata manufa ta daban.
Na dade a wurin kwance ban motsa ba shi kuma bai shigo dakin ba har wanan
lokacin barci ne ya dauke ni wanda na dade ina yi sai a zahar na tashi don sallah.
Ko da na fito nasamu bai gidan sun fita da yaran zuwa shan ice cream dakina na
nufa ban iya yin wani abuba a dakin sai kwanciya da nayi.
Ina nan kwance sai ga hindatu ta shigo da Abba dauke a hannun ta maimu na bayan
ta dauke da ledan tsara da ya sayo masu.
Suna zuwa suka fada min a jiki gaba dayan su na dan lumshe idanuwa a hankali ina
jin su a jikina kun dawo nace dasu anty kin ga abubuwan da baba Abba ya sayo muna
yakai mu mun ga biri da zaki abubuwa da yawa muka gani inji hindu.
Murmushi nayi nace su bude kayan in gani ba komai bane sai tarkacen kayan lashe
lashe na yara dasu yought din robobi nace sai kuje wurin mummy kuyi ta sha ai.
Na samu na iza su suna fita na sauke ajiyan zuciya har wani lokaci banji motsin
uncle da banyi ba yasa banji dadin haka ba a raina nasan idan na biye mashi fushin
nan nashi ne zai wakana a tsakanin mu kwana biyu.
Haka yasa na dan mike jiki ba kwari na nufi dakin shi don bai falo a lokacin
dakin shi na nufa na tura da sallama yana ciki zaune ya tasa laptop din shi a gaba
yana aiki dashi.
Jin sallama na da yayi ya dago kai ya dan dube ni kadan ya mayar da kan shi
ga abinda yake yi a hankali na karaso inda yake zaune nace.
Uncle sannu da aiki kun dawo yau kasha kiriniya da rawan kai wurin su maimu ya ce
na kaisu shan iskane da Abba don kin san farin cikin yara shine nawa a yanzu.
Nasan magana ya fada min a fakaice cikin dakewa nace Allah ya raya muna su ta
farkin addinin musulunci yace amin kawai ba tare da ya dube ni ba.
Gyara zama nayi da dakyau a kusa dashi na dan dora kaina saman jikin shi ajiyan
zuciya naji ya sauke a raina nace su zuciya manya.
An fara sauka ke nan don naji ya sauke ajiyan zuciya karo na farko shiru ba wanda
yayi magana a cikin mu har na wani lokaci sai aiki yake yi wanda nake gani sako
yake turawa a lokacin.
Gajiya nayi da kwanci haka na na sai na dan juya ina kokarin jawo filo in kwanta
sama muryan shi naji yana fadin kin ci abinci kuwa nasha koko nace mashi.
Koko ba abinci bane kin dai ji likita yace ki dinga cin abinda zai gina maki jiki
ko yaushe uncle zan ci nace a takaice.
Rufe laptop din yayi ya mike ya fita sai gashi dauke da abinci yazo ya aje a
gabana yana fadin oya tashi ga abinci ki ci na kai duban ga abincin .
Sakwara ne da miyan gaye yaji agushi sai manja da tayi amfani dashi da nama
manyan yanka da ta saka sai kamshi ke tashi a gabana.
Take naji warin abincin ya nashe ni har amai na son taso min a lokacin amma don
dai kawai in farauta mashi rai haka na daure nayi loma biyar da kyat har nayi kusan
rabin plate din dake gaba sai dai ban kai ko ina na ba koda ya dawo mayar da kayan
abincin ya samay a bayi ina haraswa sosai.
Na galabaita abinda yasani barcin yamma ke nan ranan sai magariba na falka jina
na shiru da mommy tayi ta tambaya lafiya nake kuwa ?
Murmushi yayi yace mummy jikin nata yanzu sai a hankali ai don lalurar juna biyu
sai a hankali.
Murmushin jin dadi mommy tayi tana fadin masha Allah nikan nayi tunanen haka
yadda naga ta koma kwanan amma naji dadi jin haka wallahi .
Maganan mummy wanda yasa shi jin dadi har cikin ranshi yace mummy na gode kwarai
don Allah a tayani kulla da ita a gidan idan ban nan.
Kada kaji komai suriki wanan ai farin cikin mu ne mu duka Allah dai ya raba
lafiya ya bamu masu albarka rayulayyu masu tarbiya yace amin mummy.
Dana tashi don sallah magariba da yayi na dawo dakina na yi ban fito ba har
ishai sai da mayi wanka na fito falon bai shigo gida ba har lokacin.
Mommy tazo ta samay ni a falon zaune wuri ta samu tana fadin ayya safiya ashe
abin arziki muka samu da sauri na kalleta tace mun zamu samu karuwa .
Murmushi nayi na sadda kaina kasa don kunya tace wanan abin yayi dadi wallahi da
sauri nace haba mummy.
Dudu fa Abba yanzu wata na bakwai yake shiga ko fafiya bai fara ba kuma ace na
samu wani ciki a jikina.
To may ye naji ta katsani yo mai shege ma ta goya balle ke naki da ubansu zaki
wani ce bai yi ba ai indan ma wata uku uku zakiyi kina haihuwa ba wani matsa bane a
hankan yanzu.
Don ko uban su na da halin kula abin shi yanzu ai gara mutum yayi ya gama da wuri
wanan haihu mai wahala na yanzu.
Shiru nayi ina nazarin maganan ta sai kuma na tuna a garin mu matar da tai ciki
da goyo har waka ake mata da shagube bata da sauran shakat a rayuwan ta kuma.
Ummi tayi haka lokacin goyon hindatu ta samu cikin autar mu har girkin ta inna
tace basu ci a gidan wai tayi kazanta tayi abin kunya don bakar jaraba.
Ta shiga wani hali a lokacin sosai a gidan mu duk da banda wayo amma na fahinci
halin da mahaifiya na take ciki a lokacin.
Dole kula da hindatu ya dawo kaina sai inda na fita zuwa makaran ta hindatu ke
raban ummi a lokacin inna na bin ta da gori tsakar gida.
Muryan mummy ya katse ni tana fadin ai yanzu mata sun waye da ne can ake daukan
shi wani abu amma yanzu ai ya zama isa ga mace goyo da ciki ikon Allah.
Ni dai murmushi yake nayi kawai taci gaba da fadin balle ke da ba nono ma diyan
ki ke sha ba ai gara kiyi abinki da wuri ki gama ki gyagiji ko taso tare da su.
Dariya ta bani don jin wai in taso tare dasu da tace sai dai banyi magana ba hira
take min uncle ya dawo daga wurin sallah.
Muka gaida shi da dawowa daki ya wuce nasan ruwa zai watsa mu kuma mukaci gaba da
sha anin mu a falon har lokacin da ya fito mommy ta shige ta bar mu da su maimu
dake kallon katun da Abba dake kiriniya ya koyon mikewa tsaye suna ihu su kuma idan
ya mike din.
Zama yayi har lokacin fuskan shi babu annuri a ciki sai dai bai daure sosai ba
zama yayi yana kallon yaran yana murmushi.
Juyowa yayi gare ni yana fadin maimuna na gaida ke takira wayan ki a kashe sai ta
kirani nace ayyah suna lafiya tun da na dawo asibiti ban koma ta wayan nan ba ai
zankira mu gaisa idan na tashi.
Abinci ya mike yaje yaci anan ya barni kwance sai da ya gama ya dawo dauke da
fruits a plate ya aje a gaba hindatu na bayan shi dauke da cup din koko mai zafi
yana tururi.
Kallon shi nayi na yamotsa fuska yace kina nufin haka zaki kwanta da yunwa a
cikin ki dauki cup din nan kisha kokon tunda shi kike so in kin gama ga fruits nan
ki sha.
Ya koma ya zauna yana facing dina dole na dauka na dan kurba ina yamotsa fuskana
ba halin magana ya tsureni da idanuwan shi da kyat na shaye dan cup din kunun ina
sauke numfashi.
Gyatsan haraswa nake yi har na samu ya fada min ban fito ba na koma nakai kance
alokacin komai ban so don jikina gaba daya ba dadin shi nake jiba.
Ashe barci ya dauke ni har yayi kallon news yaran suka shige sai lokacin daya
gama naji yana tayar dani inje in kwanta yace ya rufo min dakina don haka muka wuce
dakin shi gaba dayan mu.
Ba laifi na samu na dan warware don kulawan da nake samu gurin uncle da mummy
sosai suke bani kulawa yan kaina ma ba a barsu a baya ba suna nasu kokarin dani
sosai a gidan har gyaran wuri suke taya mummy da yan sauran aiyukan daba su fi
karfin su ba.
Anty tazo daga lagos gani na da yaran ta har da funke mai aikin ta don ita kadai
ke gidan yanzu su fati da faiza kowa ya koma gidan su da zama.
Naji dadin wanan zuwan na anty da dare muna dakina da ita tace ashe cikine yake
wahalal dake haka amma wanan cikin yazo maki da wahala don kamar bakiyi haka ba
cikin Abba ko ?
Idona ya kawo hawaye nace anty sam banyi tsamanin samun ciki yanzu ba duka duka
fa Abba wata bakwai yake da haihuwa na takwas yanzu yake bidan shiga.
To shine may safiya ga mijin ki shi yana ta farin ciki da samun cikin shi ke fada
min kin samu ciki mai wahala wanan karon cikin yana wahal dake sosai.
Ni gaskiya anty ban son daukan ciki yanzu gaskiya da sauri tace saboda da may
nace kinga wata da muke zuwa amsan magani da ita tayi irin haka.
Sai jinta yayi week kamar zata mutu wallahi da kyat ta sha har an debi tsamani a
gare ta sai likita ya fada mata masu irin lalurar mu bai dace suna saurin haihuwa
ba da wuri haka saboda jinin su dake ragewa suna iya shiga wani hali kan haka.
Shi kuma uncle ya kasa fahinta na gaba daya yama ki bari muyi maganan dashi na
fahinta tace toke yanzu yaya kikeso bayan cikin ya riga da ya samu dole zaki kula
da kanki sosai yanzu.
Shiru nayi ban fada mata nufina na son in zubar ba don naga tana goyon bayan
uncle tace

81 / 87