Advertisements
Chapter 38 Reading Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   38 / 87

111K to 114K   out of 258.3K words

don duban wasu
aiyuka da ya bayar aimashi tun wancen lokacin.
Washegari anty da zancen nama turkey ta dole shi aka dafa mata nai miyan shi nan
aka taru a falo kowa na kwasan dafuwa.
Sai da anty ta bari sunyi nisa da cin abincin ne take cewa damu aduniyan nan babu
abinda nake kamar wanan namar .
Nan kowa ya shiga fadan albarkacin bakin sa akan naman bandani dana ce ban taba
cin shi ba a rayuwana dariya suke min sosai saka su daddy sun shigo gidan shi da
Sulaima a bayan shi.
Daddy ne ke muna kallon mamaki ganin irin dariyan da sukeyi din yake tambayan
maiyai maku dadi haka irin wanan dariya.
Fatine ta iya bashi amsa da cewa wai Safiya ne ke fadin ita bata taba cin naman
turkey ba shine tabamu dariya sai daddyn ya mayar da kallon shi inda nake yana zama
a kusa da matar shi yace.
Kauna na kada ki damu da dariyan su watarana sai kin ci abinda duk kan su basu
taba ci ba don haka kema zaki rama nan ba da dadewa ba insha Allahu.
Yanzun dai tashi kin ji ki debo muna muma mu dandana muji santin da sukeyi akai
don da gani yayi dadi tunda naga Fati yau haka baje baje.
Na mike zuwa hada masu abinci daddy ya kalle matan shi da dariya ya cika yace
kar kuyi mamaki zama kauye don nan da wani lokaci ta fiku bude ido .
Dariya ya ci karfinta tace ai bamu haka da Safiya yadda take juya naman a kyamace
ne yaban dariya.
Sulaiman ya katse ta da cewa ai cin nama ra ayi ne idan bata so sai a saya mata
wani mana taci kuma kuna kallo.
Sai gani na dawo ina ce ma daddy na hada abincin dama na hada tun basu dawo ba
anty tace dani to ke kin ji uncle yace tunda mun bata maki rai zai fita dake ki
zabi naman da kike son ci a sayo maki muna kallo.
Na da yi mata murmushi nace ni fa anty kin san nama bai damay ni bane kawai ba
wai wanan ba.
Kowa wurin yai mamakin jin abinda uncle ya fada do cewa yayi idan baki son nama
sai a sayo maki wani abin don haka dana gama zamu fita.
Da sauri na dan kalle shi sai naga ba wasa ga maganan shi sai Fati ne tace Safiya
muje mu shirya dama nima ina son fita kin ga sai mu tafi tare.
Anty tace waya kasa dake a ciki babu inda zaki sarkin son yawon tsiya kawai daga
jin za ayi fita sai ki ara ki yafa har kina wani muje ki shirya kedin a shirye
kike.
Faiza ne tace don Allah anty ki bari mu fita muma mu lakaci arziki ta sake cewa
na fada maku ba mai bin su ko ina nice nace amma da twins zamu anty?
Ke kan ana kau da wasu kina jan wasu ai gara zuwa da wa yan nanbda zuwa da wa
yancan yan sa maganan.
Shine yace da ita dana ai sune gaba wa yan nan din dai da kika hana su sun hanu
babu wacce zamu fita da ita sai dai suga mun dawo.
Nai mamakin jin ashe yana magana mai tsayi irin haka don ban taba jin yayi magana
mai tsawo ba duk sani na dashi.
Amma yau tun shigowan su na fahinci akwai canji a tare dashi sosai kodan ganin
daddy tare dashi ne oho ?
Daki na shiga ba wani dogon shiga nayi ba dogon riga ne kawai sai dankwalin shi
dana yane kaina dashi.
Zama nayi ina tunane ni kadai a daki na yadda zamu fita dagani sai shi sai ga su
yan biyu sun shigo da murnan su wai in fito in ji uncle mu tafi.
Sai da na dan bata lokaci na fito anty bata falon sai su Fati ba wani magana mai
dadi sai harara da suka raka ni dashi.
Ina tambayan su anty sai Faiza ne ta bani amsa da cewa tashige ciki nace in ta
fito ki gaya mata mun tafi tace a sayo dawisu idan anje sai musan ke yar gaban
goshin tane.
Nasan magana tasa min ban kulata ba na fice kawai abin yana sosa min zuciya fati
ko tsaki naji taja tana bakar magana .
A mota na samay su shida su yan biyu zaune a baya hakan ya nuna min ke nan a gaba
nibzan zauna kenan.
Kafin ma in karaso ya bude min gaban mota haka na daure na shiga duk a takure
dani muka fice a gidan.
Tafiya muke babu mai magana sai su yan biyu dake ta hiran su a bayan motan basu
ko kula mu ba fuskan shi na kallon titi niko na mayar da fuskana gefen da nake
zaune ina kallon yadda garin a kullun yake da da girma da bunkasa duk da an dauke
headquater anan.
Naji yace Safiya kin san abin da madam ke shirin shiryawa a tsakanin mu ko ?
Na kalli yaran dake bayan motan naga hankalin su baya wurin mu nace a hankali
nadai ji tana fadi amma bamu yi magana da ita ba tukun.
Yayi ajiyan zuciya sanan ya nisa yace ya kamata in san raayin ki kiyi hakkuri
muyi magana anan don bamu da wani lokaci na sake haduwa irin haka.
Shiru na dan yi kafin in sauke ajiyan zuciya ince dashi to uncle , uncle ina anty
ta fada maka matsalan da nake ciki, din haka ni naga kawai ayi hakkuri ba abu bane
da zai yuyu a tsakanin mu.
Saboda gaskiya sai na kasa magana karshe dai nace uncle mudai yi hakkuri kawai ya
dakatar dani da fadin saboda may zamuyi hakkuri da maganan bayan abune wanda zai
yuyu.
Ko bata fada maki cewa nima a halin da nake ciki ke nan ba sai na dan kalle shi
kadan yace yes nima victim ne amma sai wanda ya sani zai sanda hakan.
Idana na kallon kasa look safiya ba wai abune da zamu tsaya muna yi wa juna kwana
kwana ba da maganan.
Ina son ki sani wanan abinda mutanen nan suke kokarin hadawa a tsakanin mu gani
sukayi mun dace da junane.
Ina son ki sani koda wanan matsalar ko babu shi akan mu wallahi ni son ki nakeyi
tsakani da Allah ina mai tabbatar maki ba zan iya hakkura dake ba a yanzu.
Ya nisa ya sake cewa wallahi ina son ki sani ban taba haduwa da macen da
hankalina ya kwanta da dabiun ta ba irin ki.
Gashi dan haduwan na dake da madam ta fara min maganan nan maganar sai bibiyata
takeyi na rasa sukuni a tare dani.
Sai kuma naga yayi murmushi yace sorry bazan iya ci gaba da fada maki ba amma na
gaya maki gaskiyan zuciya na don ba wani lokaci nake son a dauka ba ga zancen.
Nayi shiru ina sauraren shi sai da naji abunda ya fadi a karshe nai saurin dago
fuskana sai wanan lokacin muka hada ido dashi.
Take gabana ya fadi don kwarjinin sa da na ga ya fito fili a idona nace da wuri
uncle yace dani yes I mean it, idan kina shakkun hakan gara ki daina ko kuma kina
iya bani baki ki gani.
Nayi shiru na rasa may zance dashi yadda naga ya zare min a lokaci guda to ni
may zance dashi eh ko a a .
Har ga Allah uncle ya samu karbuwa ga zuciyana don ina son shi har cikin zuciyana
saboda me ne sulaiman dai namijine wanda duk wata mace ke burin mallakan shi a
matsayin mijin aure mutunci addini kamala da natsuwa da gaskiya irin na nuna shi
din daban ne da sauran mazan dana sani akwashi.
Amma kuma nauyi da kunya ban taba ganin wanda nake jin nauyin shi da kunya ba
irin shi don haka bazan iya nuna mashi kai tsaye na amince da bukatan shi ba.
Bai kara yi min magana ba har muka isa wani shopping mall anan ya tsaya yace mu
fita kowa ya dauki abinda yake so.
Kunya bai bari na dauki komai ba sai wani turare dana dauka ganin kuya bai bari
na dauki wani abu sai naga ya shiga daukan duk abinda yaga ya dace yana kadawa
kwado sai da basket din ya cika sosai har yana zuba ya bari.
Mukaje gurin biya ya biya akai muna packeg din su a ledojin shagon muka fito.
Bai tsaya ba sai wurin wani shagon sai da nama kala kala nan ya shiga shi kadai
sai gashi ya fito da ledoji shake a hannun shi yaja mota muka tafi.
Ba magana haka muke tafiyan sai ya koma hira da yaran har muka kawo gida sun fita
na bude mota har na saka kafa na daya a waje naji yace dani ina sauraren ki nan da
two weeks.
Ban ce dashi komai ba sai da na fito daga motan ne nace mun gode bai bari mun
dauki komai ba ya kira security daya ya taya shi shiga da kayan ciki.
Lokacin yamma yayi sosai suna falo zaune muka shigo duk idanuwan su a kan mu
anty farin ciki ya kasa boyuwa a fuskanta.
Suko nasan ba komai ya zaunar dasu ba sai gulma basuyi mamaki da irin kayan da
muka shigo dashi ba don sanin waye sulaiman din da sukayi.
Bai tsaya ba baya ya aje sai yace da anty zai koma sai dai da safe idan ya shigo
karyawa mikewa tayi ta bishi baya suka fita gidan tare.
Sai lokacin Faiza tace yau kan kun sha dadi wallahi naso ace anty ta bari mun bi
ku muma mu lakato arziki don ba a barmu mu dawo haka ba.
Wai safiya kodai wani abu na shirin faruwa ne keda uncle nace may ko ke shirin
faruwa rabona ne kawai ya koka a wurin shi dariyan ku akaina yazama min sanadin
samun alheri yau a gurin sa.
Tace indai yai wari maji amma ai banza baya haka da sauri fati tace balle ma may
zai yi wari a nan wanda ke gogayya da mata hamshakai ne zai tsaya a nan.
Nace ako hakan in Allah ya nufa sai ki ga ya faru anan din inda ba komai tai
saurin cewa ki iya lafazin bakin ki ramin kura ba wurin wasan yaro bane koda kuwa
an rika masa.
Dariya na wuce dakina ina yi ga leda a gaban su babu halin budawa su gani kada
anty taci masu mutunci akai dole suka zauna zaman jiran ta ta dawo.
A can waje kuma sun tsaya wuri motan shi ne yayin da ya dafa mota da hannun shi
daya suna magana da anty din tace to yaya ina fatan dai kun dan fahinci juna wanan
fitan da kukayi tare.
Yai murmushi cikin jin kuya yace mata wanan kaunar taki kunya yai mata yawa taki
sakin jiki mu fahinci juna kamar mai tsoron kar na sayar da ita.
Tayi saurin fadin may Safiyan tayi maka kuma yace yace kiyi hakkuri zakiyi mamaki
amma wallahi nidai yarinyar tayi min so sai ta tsaya min a rai.
Amma naga kamar ba za iya shawo kanta ba don tana da kunya sosai ga kurciya a
tare da ita kuma.
Anty zatayi magana ya hanata yace don Allah madam ki taimaka min ki shawo kanta
wallahi son safiya nake yi da zuciya daya ina son ga na taimaka wa rayuwanta .
Auren ta nake soyi na bada dadewa ba sai dai ban san yaya zaku dauki maganan ba
yanzu.
Ga baki daya maganan shi ya gama kashe mata jiki da mamaki don bata taba tunanen
zai afaka haka da sauri a sona ba shiru kawai tayi ma rasa may zatace dashi.
Ganin tayi shiru yace madam kina mamakina ne ko tace ina jin ka dadi ne ya kashe
ni wallahi wai yau kaine kake maganan aure haka a gabana babu kunya sanan wace kake
so din gata yar gida ce.
Sulaiman gaskiya ka gama kasheni da jin dadi don haka ka kwatar da hankali ka da
yardan Allah kamar ka auri safiya ka gama.
Bari ma ka gani yanzu da na shiga zan tun kare ta da maganan har sai ta bani baki
ayi don yarinyar na jin magana na sosai.
Don haka ka barni da ita kawai zan san yadda nayi da ita kar abin ya dauki lokaci
mai tsawo iyayyen ta kuma zan san yadda na lurar dasu akan zancen.
Yaji dadi har ya kasa boyewa ya rika fadin na gode madam thanks alot Allah ya
bar min ke kin zama babban yayada gaske.
Tace au dama ke nan ta karyace yace ai da madam kike yanzu ko zamu zama sarakai
dake tace aban tukwaici na yace ai tukwaicin ki shine daga ke ba wata a gidan
nan .
Na biyun bazan fada maki ba sai abin ya yuyu zaki sani sai suka sa dariya a tare
a haka ya tafi tana shamatar shi yana cewa yaji.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , ,


4️⃣0️⃣4️⃣
4️⃣
🧕🏿 0️⃣0️⃣4️⃣


YA ALLAH MUNA ROKON KA KABA MU IKON BAUTA MAKA BAUTA TSARKAKKEKE KA KUMA KARBA MU
NA IBADUN MU, , , , ,


Lumshe idona nayi tun da muka fara tafiya ashe da haka nayi barci sai da mukai nisa
sosai ni kadai a baya zaune sannan na falkafirgigi daga barcin ina kallon gaban
mota inda driver keta faman sharara gudu.
Sai yamma lis muka iso makwabtan karkaranmu nan na dan fahinci ida muke don da
gaba yana tafaduwa don ban fahinci komai ba.
Garin muke shiga lokacin marance yayi sosai don haka mazaje da yawa suna kofan
gidan su suna dakon kiran sallah.
Kwantace hanyan gidan mu nake mai har Allah ya kawo mu lafiya na nuna mashi gidan
mu ya nufi kofa yai packing a kofar gidan .
Duk hankalin mutane ya dawo kan motar suna son su ga wanda zai fito a wanan mota
mai kyau haka ganin ta tsaya a kofan gidan mu ya su yaya sani tasowa da abokan shi.
Da sauri driver ya fito ya bude min mota na sagalo kafa daya dayan na a ciki na
tsaya dauko hand bag dina zan fito.
Yaya sani yace ah Safiya ne fa da sauri yazo yana kokarin rike marfin motan da
nake fitowa ciki daga ciki suma sauran sannu da zuwa suke man na gaishe su cikin
mutunci sai na nufi cikin gida.
Nan suka fara biyo ni da kayan yar wurin mamace zata fito sai gani ta tsaya tana
kallo na don bata sanni ba sai da nace da ita maimuna ina zaki sai ta dauki muryana
tace Safiya ke ce nace nice maimuna.
Nan ta fara ihu lah ga Safiya ga safiya daidai lokacin da nake kutso kaina cikin
gidan kenan duk hankalin su ya koma wurina suna mun kallon kurrullah.
Duk suka rufe ni suna min sannu da zuwa yayin da abokan yaya sani suke ta shigo
min da kaya daga ciki ni kaina abin ya bani mamaki ko shiga daki ban yi ba bayan
mun gaisa dasu mama sai na wuce dakin baba kai tsaye don in ga halin da yake ciki.
An zaunar dashi wai yai sallah amma saida ummina ta tsaya daga bayan shi na shigo
dakin ina cewa sannu baba yaya jikin ?
Yadago kai zabban tausayi yace safiya kece tafe nace eh sannu baba yana fadin wai
may yasa su ka fada min baida lafiya banji may yake fadi ba sai da na tambayi mama
dake gefen shi take fada min.
Na juya wurin mama ina tambaya anko tafi asibitin birnin yau sai tace man wai
kudin da aka samu arro baya isa don tun a daukan mota da za a tafi rabin kudin ya
kara nace haba haba mama nace a kaishi ko nawa ne , gani nan tafe ai zan biya.
Na dan tsaya tsaye shiru ina kallon yadda baba yake wahala da bautar Allah sai
na fita dafa daki na samu kanne na sun shiga min da kayana dakin mu .
Sai dai suna waje suna gardaman wai kwali goma ne inji yar wurin inna sai dan
wurin ummi kanina yace hummumm sha biyu ne na gardama ya kaura a tsakanin su.
Inna ta kwala ma yar ta kira wai ina ruwanta ko kwali dari ne na shigo dashi
tasan sanan da nake yi na samu kwalayen da na shigo dasu iyayyayena suna murna.
Kai kawai na girgiza na ce a ban buta nayi alwala daga dakin ummina ban tsaya
sauraren ta ba bayan munyi sallah ne na fito na samu yaya sani nake cemai yaka mata
mu tafi asibiti da baba sai yace ai maganan kudi ne da mota nace motar da na zo da
ita zamu tafi.
Yace sai a bari sai da safe ina shiga dakin nace dashi yau dai zamu tafi yanzu
ma zamu kama hanya dawa zamuyi tafiyan ?
Nake tambaya yaya Sani din ina dafa baba ina kai sannu yaya jiki ya gyada min
kai alaman da sauki jikina ya kara yin sanyi don dai ni a yi sani na dashi ban taba
ganin yayi ciwo irin haka ba.
Mama tace bari taje ta shirya don da ita za a tafi inna da ummi su zauna gida
amma da inna ta samu labari sai ta tada fitina wai ita zata .
Yaya sani yace ai ba kasuwa zamu ba da kowa zaice zai tafi da mama kawai zamu sai
ni da Nura yace mata.
Na fita naiwa driver magana kamar yadda Sulaiman yace in sanar dashi duk abinda
nake so nasa ankai mai ruwa da maltina da abinci yana ci ne sai gani na fitinan
nake fada mai tafiyan mu birni.
Sha daya na dare muka isa asibitin basu so su karbe mu ba a lokacin sai da na nuna
masu kudi sannan suka fara nan nan da mu, har likita suka tayar cikin daren nan
yazo ya duba baba maganin da ya rubuta.
A cikin daren nan su yaya Sani da driven nan

38 / 87