Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
mijin naki ke bin sawo har
kauye.
Abun da yaba inna haushi ke nan tace ke kinyi kadan ki shigo kice zaki zage ni
har dakina.
Mama lami tayi zaton dukan ta inna zatayi kafin inna ta karasa daga hannu taji an
kwashe ta da mari tajuyo a cikin mamaki taji an sake sauke mata wani marin .
Aiko danbe ya kicimay masu take gida ya rude sai ga inna a kasa mama tabita ta
haye da duka da yakusa.
Ganin inna bata diban komai a jikin mama lami yasa hausi yar inna dauko faskaren
icce ta nufi mama dashi sauran ma suka dauko tadai samu mama dashi sau daya zata
kara buga mata ne mama ta kauce iccen hau kan jikin inna.
Sai ga jini tarrrr yana zuba daga goshin inna din yaran suka kara fasa kururuwa
mutane suka fara shigowa har da su yaya sani da abokan shi.
Yaya sani har ya dauko icce zai shiga dukan su dashi sai yaji mama na fadin
yanzo kin ga abin da kika jawa kan ki in da suka shigo basu tan ka ki ba kin kyale
sune sun tafi da baa kai ga haka ba.
Amma kin bisu da zagi da gori yanzu gashi har kin jawo yar ki tai maki rotse
akai.
Sai jikin shi yayyai sanyi ya yarda iccen da ya dauka kasa yana cewa ashe inna
ke kika ja wa kan ki gashi yanzu an barki da jinyan jiki.
Baba ya shigo gidan ya samu gidan a har gitse da kyat ya samu mama ta mayar mai
da abin da ya faru yake cewa shi ba ruwan shi ta dauki mataki da kan ta in zata iya
don shi bai sata ba.
Nan inna tashiga balle ballen bagana ida take shiga banan take fita ba wai baba
an je an hada shi da boka da malam kan shi ya zare.
Baba ya shigo dakin mu don ya gaida ummi zamu fita yace mu zauna yake cewa ummi
kin dawo lafiya ya mutanen gida.
Ta amsa shi da kyat da suna lafiya.
Yace don Allah Rabi kiyi hakkuri da halin inna kin saba da halin ta kiyi hakkuri
a zauna lafiya.
Bata tankashi ba ta kawar da kai daga duban sa ma sam bata son ganin shi.
Shima yace da mu da ita sai da safen ku.
Allah yakai mu ta bashi amsa dashi.
Yana fita na sauke ajiyan zuciya nace ummi kiyi hakkiri tun da ya gane laifin sa
abin ya wuce.
Ya gane ko yana shirin ganewa ai da sauran sa duk wanda yace ya karkata wuri daya
a gidan sa ai kullun yana tare da tashin hankali.
Don dai yanzu in suyi min ba kyale su zanyi ba sai dai duk adauke mu masu fitinan
don kyaluwa bai yi.
Abin da na lura dashi da baba da mama ke aiwatar da shirin bukin su sai ko
gwagon ummi da suke dan jefawa ciki wani lakaci.
Mun kara jerabawan mu na karshe kowa na farin ciki da hakan a ban gare na bakin
ciki ne tar ga zuciya na .
Sai dai ba wanda zan fadawa naji sanyi sallama muke da junan mu na samu Amina
bakin get tana jira na mu tafi.
A kasa muke tafiya don bamu son mu rabu Amina ke cewa mun yi barka da saka
uniform yanzu muna da freedom din kan mu ba mai takurawa rayuwan mu.
Take naji wani iri a raina tace ni dai nursing school nake son zuwa idanuwana
suka ciko da hawayen bakin ciki lokaci guda don a da tare muke wanan burin kowa ya
fadi abin da rayuwan shi ke so.
Nin nayi shiru tana ta magana take cewa dani bakiji bane Safiya, cikin
raunaniyar murya nake ce mata ina jin ki ni nasan wana daman ya wuce ni ke nan a
rayuwa na.
Tace saboda may zakice hakan wanda zaki aura din ba dan birni bane zai iya barin
ki kici gaba da karatun ki bayan kuyi aure.
Na hade wasu yawun bakin ciki nace da ita kayya Amina wanan auren da za ai min
takar bauta zan tafi yi wanda yafi wanda nake yi a gidan mu.
Da sauri tace saboda may kika ce haka nan nake koro mata da yadda mukayi ranan
da suka zo da mahaifiyar shi.
Na kara dace Amina ke kin taba ganin anyi aure mijin bai ma san da zaman matar da
za a aura mashi ba.
Na kara sa cikin kuka da fadin zan yi biyayya ga mahaifina shi dake gurin yaganni
cikin irin wannan rayuwa.
Zan zauna na rugumi kaddaran da ubangiji ya aiko min dashi amma ni nasan babu
komai cikin yin hakan da suke son yi sai hada zumunci fada.
Tace matsalan Safiya shi baba yaki gane gaskiyan magana wa yan nan matan na
zugashi in gaskiya ne ai suna da diya mata suba dasu ma ai sun fi kusa da gwago
din.
Nace da ita ai fakewa sukayi da cewa wai ni nayi karatun boko suko saura basu yi
ba don haka ni ce na dace dashi.
Tun ban da wayyo nake jin irin wayyewar su da kuma irin tarbiyan su ba daya ba
da namu amma mama cewa tayi wai zaman birni ne kawai.
Har muka kai gidan su Amina maganan muke muna tafiya ganin yadda na bata fuska
da kuka yasa ta cewa dani na shiga gidan su na wanke fuskana.
Mahaifiyar ta na tsakar gida taga shigowan mu take cewa damu yaudai kunyi barka
sai kuma a fada wani.
Ganin yanayi na yasa ta katse maganan nata ta biyomu cikin dakin ta da muka
shiga.
Ta samay ni zaune Amina a gefe na ina kuka wiwi tace may zan gani wai haka yau
duk kukan karasa makaranta ne haka ?
Amina ne ta iya bata amsa da cewa mama matsalar auren ta ne take wa kuka.
Sai mahaifiyar ta tace yanzu yaushe raban naji an tursasawa yarinya auren dole
can.
Irin wanan ma mijin ai ba zaiga darajan su ba bare kuma ke.
Cikin kuka nake sanar mata da yadda mukayi dashi din duk abin da ya fada min da
suka zo.
Taja gwaron numfashi tace shi baban naki ne bamai saukin kai ba, bai san yanzu an
bar irin wanan auren hadin ba ne.
Ai lokaci ya shude na irin haka sai dai kiyi hakkuri Allah yana sane dake yi
addua idan akwai alheri ya tabbatar muna.
Nace Mama wallahi shima mutumin bai ko san suna yi ba don kwatakwata yace ni ba
tsarin shi bane yadda na lura shima umurnin mahaifiyar shi yake bi don nagane so
yake ni na fitar da rashin amincewa ga iyayyen mu a fili san nan gashi miti biyu
yai yawa bai kuna taba ya zukaba.
Kaini ban ma taba ganin mai sha irisa ba wata kilama ba iya taba yake shaba.
Don ranan da na fara ganin sa tare fa suke da iyayyen shi amma babu kunya yanata
zukar tabanshi in na tunashi a raina duk hankalina sai ya tashi.
Nayi hakkuri na jure wai don na farantawa baba rai amma na gaza sakewa a raina.
Ba wani soyayya tsakani na dashi saima munanan halayyanshi da yake nunawa a fili.
Nakara fadi cikin wani irin kuka saboda Allah mama ta ya ya zan samu natsuwa har
nai farin ciki ga auren da na san bubu komai cikin sa sai tarin kaskanci.
Mama ta girgiza kai cikin damuwa tace kidaiyi hakkuri don bamu da wata zabbi sai
abin da Allah yayi.
Ta dan tsagai ta tana mai matukar tausaya mani tace gaki yarinua mai hankali ace
za a hada ki aure da mara tarbiya mara mutunci.
Da sun bar sulaiman ya ci gaba da neman ki aiko su da sun dara amma a kai bakin
ciki da kasancewan ku tare.
Yanzu ina mutunci ga irin hakan da ake shirin yi nace mama don ma baki shiga
gidan mu kin gani bane ummina fa bata dade da dawowa gidan ba duk akan maganan.
Maman Amina tai salati ta sanar da ubangij tace badai ta dawo gidan ba ko ?
A hankali na share hawayen dake fuskana nace tadawo amma dai har yanzu cikin
fitina suke din inna ba barin halinta zatayi ba.
Tace kin ga Safiya ki tsayar da hankalin ki debi kwanaki uku zuwa bakwai duk
abin da ya sauwaka daga biyu zuwa uku dare.
Kirinka nafila ko wani raka,a ko wani raka,a ki karanta kulhuwallahu kafa goma
sha biyu a bayan fatiha.
Idan ki idar ki zauna ki yi yabo gun mahallicin mu sai ki hada da istigfar duk
abin da ya sauwaka kar ya gaza kafa dari, sai ki kara karata kulhuwallahu kafa
goma sha biyu ko wani da bisimillah shi safiya muddin kika rike wanan zaki ga abin
mamaki idan har ba a fasa auren ba to mukkadarine daga Allah Allah ba zai barki ki
tabe haka na ba.
Cike da gansuwa da maganan ta nace nagode mama insha Allahu zandage dayi yau din
nan zan fara basai gobe ba.
Amina ta tashi ta debo min ruwa a buta na wanke fuska na dashi bayan na wanke
maman ta tayi tayi in ci abinci naki sai da zuciyana ya samu natsuwa.
********* ********* *********
Bike ya rage saura sati biyu duk nabi na ramay kulliyomin bani da kwaciya
hankali tare dani yan gida mu sai shirin buki suke yi.
Ranan ina zaune sai ga yaya Nura da wayan shi har dakin mu wai ana magana dani a
waya na karaba ina mamakin waye zai kirani da wayan shi.
Na karba da sallama na amma sai naji muryan wanda naki jini a wayan yana cewa ke
yar kauye watau kina nan ga bakan ki ko.
Nagane shime a layin duk da gabana ya fadi amma a fili sai nace muna dai a bakan
mu ko don kaina mayen da ka dafe min kana son shiga cikin rayuwana.
Yace ke manya na san bakomi kikewa ba sai son ace kina lagos kina aure ko ?
Nace wanan ba shine matsalan ba don ba nice farko shiga lagos daga kauye ba
kafin ni wasu sun rigani.
Yace a harzuke suwa kenan kike nufi oho mahaifana kike son ki zaga ko may ?
A yadda ka dauki maganan nawa hakan nan amsa yake don bani ce farkon shiga birni
ba.
Avikin tsawa yace ke dakata kiji kiyiwa bakin ki waigi ki san wanda kike magana
dashi, ke har wata mace ce da zan tsaya ina bata lokacina a gare ki.
Yan mata wani iri ne ban gani ba ke har kinada abu yiwa maza feleke ne yaja
tsuki yace a fusace.
To ki sani ba irin Ahmed akewa irin feleken nan ba don ni baki cikin tsarina kin
sani bakuma zaki taba samu ba.
Daga kawai ana son rufa iyayyen ki asiri a taimake su da har ina macen take nan.
Nace a rifa wa iyayyena asiri taimake so ko a rufawa naka kai da ka tsufe masu
awaje kar akai ga abin kunya duk barinki ya kare babu maija.
Ya kut nasan ran shi yakai kololowar baci ne da magana yace zan gwada maki yanzu
nake a cikin bariki kuwa.
Kinga ni dama kiran ki nayi gwagon ki ta damay ni in akwai event din zakuyi na
sani.
Nace akan wanu aure zayi event badai wanan auren kaddaran ba naka zan tsaya bata
lokacina akan sa.
What ever you take it duk daya gare ni sai dai in ke baki so nasan wa yan nan
mastiyatan yan uwan ki na su.
Nace dadin abin dai ba a taba canza ma tuwo suna sai dai a kira shi da tuwon abu
kaza.
Au aikin banza bade za a iya saka mai suna ba ya kashe wayan shi yana jan tsuki.
Wasu zafafan hawaye ne suka zubo a idona nace wannan wani irin tarbiya ya samu
ko kadan muddin ba zai ragawa iyayye na bazan raga mashi ba.
Duk da kalaman da yake fada min suna da zafi kalamai ne na cin zarafin iyayye don
haka na kara tsanar shi a raina.
Haka ummi ta shigo ta samay ni a cikin damuwa yanayina kadai ummi ta duba tasan
raina a matukar bace yake cikin sallon hikima irin manya ta tuhumi abin dake
faruwa.
Tace dani kina nan kina bata ranki ga abin da kika san ba zai hannu ba sai nace
da ita ummi wannan mutumin ne baida mutunci .
Ko yaushe sai so ya zageni da iyayye na har da aibatani bai dauke shi a bakin
komai ba don shi bai san darajan iyayyen shi ba.
Ummi ta jijiga kai sannan tace, abinda nake so dake yi hakkuri yi kuma tawassali
da Allah in sha Allahu aniyar sa tabi shi baji a gare ki sai dai a gurin sa.
Abin da nake so dake shine kibi umurnin mahaifin ki koma maynene tsakanin shi da
yar uwan shi ne bai shafe ki ba ke dai ki zage ki neme aljannan ki a gurin mijin ki
zai fita masu ai in dai halin sa ne.
Kibar biye mashi ranku na baci ko banza ba saan yiki bane shi don ya girmay ki
balle kuma ga aure zai shiga tsakanin ku.
Wanan magana na ummi su suka sanyaya min zuciyana take naji komai ya kawu min a
rai na samu karfin gwiwan rake mashi abinda na kulla yi duk da manufar sa akaina
na kuntata min.
Kamar yadda su gwago sukace basu son akaini da tarkace duk da haka an yi min
kokarin wasu abubuwa wanda sam mutanen gidan mu basu zaci hakan ba.
Don ko yan uwan ummi sun hada kudi cas suka kawo mata tare da sauran tarkace na
amfani gida.
Yayan da abokan arziki na cikin gari suma suka kawo nasu gudun mawan take kaya
ya hadu ayadda baa zata ba.
Inna da ke cewa suga yaidda za ai buki uwa bata aje komai ba ta manta abin daga
Allah yake don Allah shikewa bawan sa budi yadda yawo.
Yan uwan ummi sun yake shawara a tafi da kudin asai mun abin daya kamata a can
idan an tafi kayan lafen dasu gwago suka kawo sai da inna tasa aka bude shi ita da
diyan ta duk suka wawashe abin da suke so ciki.
Ina zaune a dakin mu don cikin gidan baimin dadin fita ina ummi sai shige da
fice sukeyi na hada hada buki ni dai abin mamaki yake bani a raina.
Muryan yaya Sani naji a tsakar gidan namu yana kwala min kira na fito da sauri
ina amsa kiran nashi.
Ya na kallona ganan sa ya fadi ya tsorata ainun da irin rama da ya gani tare da
ni.
Ya ke Safiya lafiya irin wanan zabgewa da kikayi haka, keda ya kamata murna
zakiyi aure ki huta da halin gidan nan .
Take idanuwa na suka ya kawo kwalla na dan sake mashi murmushin yake nace gani
yaya.
Sai naga jikin shi yai sanyi da leda a hannun shi nasan abu yake son in dafa
mashi a lokacin.
Sai ya juya dashi yana fadin barshi dai har ya taka yace dani Safiya zo nan sai
nabi bayan shi muka fita.
Jikin bango na rabe a lokacin ne kuma kwalla ke zubo min a idanuwana babu
kakautawa.
Na sa gefen hijjabi na ina shrewa sai naji ya sauke ajiyan zuciya dan kalle ni
tausayina ya kara kama shi.
Ganin dagani sai shi a wurin kuma shi kadai ne mutum a gidan mu bayan ummi na
dazan fadawa damuwa na.
Nace yaya Sani ina cikin wani hali wanda ba mai iya fitar da ni sai Allah dakuma
baba.
Yace na sani Safiya karatu kike so amma baba yanuna karfin haihuwa a kan ki zai
maki auren hadi na katse shi da cewa auren dole dai yaya.
Don wanda zaa bani ba ao na yakeyi baba kuma darajan iyayyen mu yake gani ba.
Ya zaro idanun shi waje alaman mamaki fa abin da na fadi din yace wa ne shi don
uban shi.
Na girgiza kaina nace ko kadan baida mutunci yaya gashi kuma mashayin ne
sosaiyace dani kuma baba ya san da haka din nace ban sani ba yaya.
Ki kwantar da hankalin ki zan yi bincike akai inna gane gaskiya kika fada min
zan yi duk abin da zanyi in ga an fasa auren nan .
Maganan yaya sani shi kwantar min da zuciya har na dan ji sanyi a raina sai ya
miko min leda da imdomei a ciki yace jeki ki dafa kici kafin in dawo.
Naji dadi a raina na ahiga nayi yadda yace na dafa indomei na shiga dakin mu
muka ci da kan ne na.
Yaya sani kuma tafiya ya bincika inda yajiyo halin Ahmed babu dadi ko kadan a
wurin yan uwa dake zuwa.
Yaya sani yace wanan abin duk sherin su inna ne ba komai ba nai mamaki ga su
hausi yannen ta ne amma ce wai za ai mata aure ita.
Nan ya dawo gida ya ta yar da haukan shi ya kira yan uwan baba mu suka hadu ya
fada masu halin da ake ciki.
Suka taru da dare akan baban mu suna fadin wanan baiyuyuwa ba ai muna auren dole
ba bamuyiwa diyan mu.
Baba yai wuf yace babu mai hana wanan auren sai Allah yadda lanto ta nemi arziki
a gidana haka nima zan mata shi da cewan wai gwago.
Sabada haka yadda nayi niyya haka zan yi saidai idan na kaita ta fito matsalar ta
ne wannan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:10 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , ,