Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
bakuwa kukayi ne a gidan nace eh mummy anty ce tazo.
Wata anty ta tambaya cikin son sani ko wanake nufi nace anty na da nayi zama a
wurinta lagos itace tazo dazun .
Allah sarki ashe da rabin zan santa bata taba zuwa ba nake gani ai nace ko yanzu
ma ba zuwan lafiya tayi ba na zauna ina bata labarin abinda ke faruwa.
Sai dana gama fada mata tace ikon Allah haka abin Allah yake fa gashi tun ba a je
ko ina ba Allah ya fitar maki da hakkin ki baki da Alhakin ta ke nan.
Ai wanan zamanin ana abu wallahi da karfi da yaji akeson tubbuke ka a gidan auren
ka don kawai wani ta shiga ko idan shi yashiga alhaki zai barshi ya zauna ne shi ?
Mata kyashi da hassada yayi muna yawa yanzu sai kiga ko da yan uwa na jini da
nine yanzu suna kyashin junan tun dai idan an ga daya ya dara daya sai hassada yazo
ya shiga tsakani.
Ke dai fita batun yan duniya ki rungumi mijin ki tunda bai raga ki da komai ba na
bukata kuyi zaman ku lafiya ba fita kike yi balle ki ga wani abun a kan shi.
Shine amfanin zama guri daya yau idan baka kula mutane ka huta ma rayuwan ka sai
zuciyar ka ta zauna lafiya da kowa ba abinda ya damay ka.
Amma kinga yawan kwashe kwashen na babu abinda bai haifarwa shi nake guje wa
mutumiyar ki ai kullun ina kan bakina da ita samira bata san ciwo kan ta ba
wallahi.
Nace mummy may tayi kuma tace waya san iyaka yar nan gashi yanzu yar uwanta ke
fadin dawowan nan danayi tace wai sabbin abaikai tayi ko yaushe idan su basu zo ba
ta taje wirin su.
Kinga ai irin haka mutum ke gudu wa rayuwanshi don ba a gane mugu a goshi tunda
ba zuciyar mutane ake gani ba wanan abin na yarinyar nan yana damu na wallahi.
Nace ni mummy sai yanzu nake ganun fa,idar barina in fita da uncle bai yawan yi
koma wani wuri zan tafi in ba wurin Aisha ko samira zan tafi sai dai mu fita tare
sai kuma idan wani abu zan fita in sawo mai muhinmanci a gare ni.
Mun dauki lokaci muna hira da ita nafito daga dakin don magariba ya kawo jiki a
lokacin don haka na fito don zuwa sallah.
Ko da uncle ya dawo da dare tafito sun dan taba hira dashi ta koma daki ni dai
sai haba haba nakeyi da ita a gidan in samu mu rabu lafiya ina mai kara bata
hakkuri.
Washe gari ta wuce da safe tana matukar bani tausayi tace don Allah in kara yiwa
uncle magana akan zancen nace insha Allahu anty zanyi bayan tafiyan ta muka zauna
nan da mummy a falo muna hira.
Duk jikina yayi sanyi wai yau anty ne take kumsan bakin cikin da na miji a kanta
matar da suke gwanin ban sha,awa agidan su ita da mijin ta da yayan ta a gida har
damu da mu kaje cin arziki a gidan.
Yau sai gashi wai sun samu sabanin mai muni a tsakanin su dole mata mu rika taka
tsamtsam da maje komai dadewan mu a gidan miji.
Haka rayuwa ke guda yau dadi gobe madaci ga bawa watarana kuma a dara uncle yayi
kokari ya mayar da anty dakin ta tare da basu hakkuri daga ita har daddy din.
Haka yasa anty uwa da kawar ta suga shiga tashin hankali don komai sunyi na
shirin buki a lokaci da bincike da komai suka gano uncle ne yayi sanadin komawan
anty gidan daddy din.
Haka yasa suka niko gari zuwa gidan namu uncle ya shawo kan daddy ya yarda a
tsayar da zancen auren su da sahura.
Muna zaune a falo duk da safiya ne amma hakan baisa sun shigo sun samay muda
shirin mu a gidan bamu da wani makusa sai kanshi ke tashi yana kwance saman dogon
kujera don ranan babu aiki.
Abba yana saman jikin shi yana mai wasa sai ni dasu maimu dake zaune muna mashi
hiran shirmay su don yace zai saka su islamiya shine suke biya inda suke.
Sallaman su mukaji daga sama shigowa falon gidan kai tsaye da mamaki nake kallon
su don shi yana kwance a lokacin.
Baiga fuskokin su ba sai dai yana kokarin mikewa zaune a lokacin gane su da yayi
yasa ya daure fuskan shi yana cewa uwa kune tafe ?
Tace eh gamu mun shigo yau ziyara sannu ku dazuwa kawai nace dasu ban kara bita
kan su ba kuma ban bar wurin ba sai cewa dani dasu hindu su shige ciki.
Ban kuma mike zuwa dauko masu abinsha ba na zauna tare da harde hannuwana wuri
guda jikina yana gugan na shi a yanayin zaman da muka dashi.
Bayan su gaisa dashi anty uwa ta dan dube ni tace don Allah bamu wuri magana
mukazo yi dashi kallon ta nayi na cewa ni tare da nuna kai na ?
Tace eh magana ya kawo mu wirin shi mukazo kafin ince wani abu don yau nayi
niyar mata rashin mutunci sosai sai naji uncle yace da ita.
A, a bakizo ganina bakan duk abinda zaki fada min idan baki iya fada a gaban
matana ai ba alheri ya kawo ki ba ke nan.
So idan kinyi niyar gani na ba idan zata tafi don gidan ta kika shigo kinga ko
baki da right din cewa ta baki wuri ki fadi maganan ki kai tsaye kawai naji.
Don ni mata itace abokiyar rayuwa abokiyar shawarana gaba daya don ko kin fada a
bayan ta ma fada mata zanyi tsab.
Nisawa tayi tace dama bawani abu ya kawo mu ba sai zancen yayana da kawana sahura
gata har an saka lokacin aure yanzu kuma yace wai ya fasa komawar wanan macuciyar
matar tashi da ta shiga ta fi, , , ,
Dakata uwa don Allah ban son sha shanci kin sani ke har zaki iya dauko kafa kizo
min gida da wanan zancen naku na banza .
Yanzu don baku da kunya kuke kokari shiga tsakanin mijin da matan da suka shafe
sheru goma sha wani abu da aure kina kokarin cusa mashi wata bare can.
To bari kiji ban cikin wanan magana naki na hauka kuma aure yaya ba zai taba kara
aure ba muddin maimuna na gidan nan.
Tashi tayi da fushi tana fadin don munzo wurin ka neman taimakon bawai yana
nufin munzo roko ko maula ba balle kayi kokarin fada min magana haka ?
Dole yasa ka ga mun zo wurin ka don kawai ka dafa muna ba wai wani abu ba yace
oho gani mahaukacin daure kun kwaso kafan ku kunzo a hada kai ayi cuta to ban iya
ba ku bace min da ga tun raina bai baci ba na kira maki yan sanda yanzu.
Sai da ta watsa min hara nima na mayar mata daga inda nake zaune ta fita fuuuuu
sauran suna biye da ita a baya.
Yaci gaba da fada a falon yana fadin wanan matar tana da hankali kuwa ko abin
nata ya zama hauka ne wai ?
Naji dadi sosai har cikin raina yadda uncle bai raga masu ba ya kore su ya kira
wayan daddy yana fada mashi abinda ke faruwa a gidan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/21/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , ,
8️⃣3️⃣8️⃣
🧕3️⃣8️⃣3️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Haka rayuwan mu yaci gaba da tafiya a gidan muna samun kula yadda ya dace daga
wurin uncle har yasa yan kanne na wani school mai tsada a nan cikin Abuja.
Sa su makaranta yasa yanzu ina fita in kai su in kuma je hudu in dauko su in sun
shirya nakaisu islamiya ranan da ban iya fita kuma sai driver ya dauko su daga
school din.
Yau haka na kwana ba lafiya a jikina sai karfin halin da nakeyi ban son asan
halin da nake ciki a gidan sai dai jikin ya matsa min har ban iya boyewa mutane
halin da nake ciki.
Wanda ya saukar min da zazzabi zuwa rana mai karfi har yakaini da rufuwa da bargo
da kyat barci ya dauke ni cikin zafin jiki nake barcin a wahale a lokacin.
Jina shiru ban fito ba tun safe da na sauke yara makaranta yasa mummy lekowa
dakina ta duba ni ganina kwance na rufe da bargo har kaina yasa ta shigo tana fadin
.
Safiya yau lafiya kike kuwa abinda ya falko dani daga barcin dana dan samu ke nan
na bude idona dakyat nace.
Mummy ban jin dadin jikina ne yau tun dare zazzabi ya rufeni sai da nasha magani
ya lafa yanzun kuma ya kara dawowa.
Ina gyara kwanci nace karfe nawa yanzu mummy tace uku da rabi ya wuce dan
yunkurawa nayi ina son in dauko waya amma na kasa.
Sai mummy ta gane abinda nake son yi tazo da sauri ta dauko min wayan ta mika min
neman layin uncle nayi don in fada mai a dauko min su maimu daga school .
Jin murya na yasa shi fadin may ya samay ki safiya ?
Banda lafiya na iya fadi kawai sai naji ya kashe wayan da sauri na gyara
kwanciya nayi don ko sallah ban iya yiba a lokacin.
Ba afi wasu mintina ba sai gashi gidan yacewa malam musa yaje ya dauko yaran daga
school ya dawo yanzu ya juya ya fita daga gidan kamar yadda ya umurce shi dayi
din.
Ciki ya shigo bayan ya sallami malam musa din dakina ya nufo don yafi tsamanin
ina can din a lokaci ya turo kofan da sauri.
A kwance ya hangoni kwance na dunkule a wuri daya ina makarkyatan dari duk jikina
rawa yake a lokacin .
Bargon dana rufe jikina ya kwarai tare da dan taba jikina a hankali zafi yaji
radau a jikin nawa jin hannun shi a jikin nawa yasa na bude ido na hanshi zaune a
kusa dani yace .
Safiya baki da lafiya ne har haka baki fada min ba kuma baki kirani ba take ya
daga waya ya kira likitan shi yace yana wani wuri amma gashi nan zuwa yanzu.
Yana dakin har likitan ya shigo gida fita yayi sai gasu sun shigo tare da likita
dakina ya ce madam sannu yaya jikin ?
Nace da sauki ina takurewa a wuri daya yace yaya nake ji ne ?
Nan na fada mai yau kwana hudu da amai amai ya fara min sai kuma daren jiya ya
saukar min da zazzabi .
Yayi min yan tambayo na bashi amsa uncle na zaune ya kafeni da idanuwan shi sai
yace bari ya fara saukar min da zazzabin gobe zai dawo akwai awon da zai min.
Wani irin ras ras naji gabana ya bada don ambatan awon da yace na dauka akan
maysalan ciwon mu zai mun awo din na yaba allura har biyu tare da magani.
Suka fita da uncle daidai lokacin yan makaranta suka dawo dakina suka shigo don
tun a hanya malam musa ya fada masu banda lafiya shiyasa banzo daukan su ba.
Don su fison in tafi dauko su don duk abinda suka gani na marmari a hanya sukan
ce min insaya masu ko kuma in tambaye su asai maku abu kaza ne ?
Gaishe ni sukeyi kowa tana kokarin ganin fuskana kamar an fada masu a fuska na
ciwo dake damu na yake min.
Dan samun saukin da nayi na rarafa naje ban daki na dauro alwala nazo na tayar da
sallah don har da azahar banyi ba ina kwance.
Ina sallah naji shigowan uncle dakin bai fita ba don ina sallah zama yayi har
lokacin da na idar da sallah din ya miko min maganin da likita ya rubuta mai ashe
shine ya fita sawowa.
Nan ya tsaya sai da na shaye maganin na koma na kwanta fita yayi ya samu Nura mai
aiki yace ta hado min tea takai min dakina.
Ina kwance sai ga Nura ta shigo dakin dauke da dan karamin tire a hannun ta da
kayan tea ta kawo min tana min sannu.
Ban tashi ba sai ga uncle ya shigo dakin na lura sallah yayi yana fadin kinsha
tea din kuwa yana kai idon shi inda kayan suke aje kai kawai na girgiza mai alaman
ban sha ba.
Zama yayi ya hada min tea din yana tashi kisha cikin commad yayi maganan shi
bawai alaman lalashi ba dole na tashi na sha tea din rabin kofi na koma na kwanta
ya mike yana fadin zai dan fita ba dadewa zaiyi ba zai dawo.
Har yakai kofa wani irin amai ya taso min da sauri na yunkura zuwa ban daki
kafin in isa na sake amai mai karfi a tsakiyan daki na.
Wani irin kallo ya bini dashi tare da yi min sannu cikin tausayawa a gare ni na
karasa zuwa ban daki amai nayi sosai duk da ba komai a cikina.
Fita yayi ya fadawa mummy nayi amai na bata dakina dashi da sauri ta taso da
Abba goye a bayan ta ta nufi dakin nawa.
Mummy ta gashe ni ta sauke yaron ta fara gyaran wurin dana bata din da amai sai
sannu nake mata ina fadin ai da ta barshi zan gyara wurin ko ta turo su maimu su
gyara don suna gida yau ba islamiya.
Tace haba wanan ai ba komai bane aikina ne barin yi ta gama gyara wurin ta dawo
tadan zauna sai ga maimu tashi tana saye da wandon tie baki iya gwiwa da yellow din
dan riga sannu take min cikin tausayawa.
Nace jeki kitchen ki dauko min lemo guda biyu ki wade min su ki kawo min da sauri
ta fita ta dan dauki lokaci ta kawo min na yunkura na tashi dakyat na iya shaye
guda na koma na kwanta don sam banjin dadin jiki na.
Ban dade da kwanciya sai barci yau ni dake hana wasu barcin bayan laasar sai
gashi ni ina yi fita mummy tayi da yara don kada su ta dani tare da jawo min kofan
dakin.
Uncle ya dawo gida kafin magariba ya wuce dakina kai tsaye ya tura kofan ya samu
ina barci ga lemon da aka wade min a gefe na aje yadan dade tsaye kaina ban san ya
shigo ba.
Ya dan taba ni kadan sai na bude idona yace tashi magariba ya gabato da kyat na
samu na tashi zaune yayi min sannu da kara tambaya ko na sake yin aman bayan fitar
shi nace banyi Allah ya sauwa yayi min.
Bayan fitan shi daga dakin na daure na tashi na shiga bayi wanka nayi da ruwa
masu dumi sosai na dan gasa jikina tare da dauro alwala na fito.
Sai da na zauna na dan huta na mike na gabatar da sallah a inda na idar na sake
dunkulewa a cikin hijabi na banyi barci ba ina jiran inyi ishai a wurin mummy ne
tashigo duba na.
Ta samu nayi sallah ta yi min yaya jikin nace da sauki mummy murya can kasa kasa
na amsa mata tace har yanzu bai fada maki ba ?
Nace na rage jin sanyi yanzu kaina ke ciwo kamar ya tsage nake jin shi sannu tayi
min ta dan jima zaune a wuri duk da ba hira muke yi ba a lokacin sallah ya tayar da
ita tana idar wa suka dawo tare dasu hindatu suka zauna a dakin.
Uncle ya dawo dauke da ledoji a hannun shi dakin ya nufa dasu su Mommy na ganin
shi suka shiga gayar dashi hindatu da maimu suna rige rigen amsan ledojin dake
hannun shi din.
Mika masu yayi tare da fadin su aje karamin su tafi da babban suci ya juya wurin
mommy data mike tsaye ko tana shirin fita dakin .
Yana tambayan ta bata kara amai ba ko mummy tace bata sakeyi ba sai dai kanta
tace yana mata ciwo sosai kamar zai tsage.
Yace kuma again ban san may yasa zata boye min bata da lafiya haka ba har saida
abin yayi nisa sosai yanzu ai ba a wasa da ciwo.
Tace kila bata dauka sosai bane haka ko irin dan zazzabin da kan zo ya wuce ma
mutum ne shaaa .
Fitan mummy ya dan kwanto yana tambayana yadda nake ji nace da sauki yace kan fa
ya lafa yanzu nace eh kawai badon ya lafa min ba din.
Ya ce in tashi inci wani abu ga nama na da fresh milk in sha kai na girgiza
alaman a a yace to a hado maki tea ki sake sha nacs uncle ko nasha ba zai zauna min
ba ne .
Ya mike yana bakuma zaki kwanta da yunwa ba kin sani dole ne kici wani abu sai
cewa nayi koko zan sha ka fada wa mommy.
Koko kuma a ina za a samay shu yanzu da daren nan nace muna da abindama shi a
fridge mommy ta san inda yake na bashi amsa.
Uhmmm yace kawai ya mike tsaye ya nufi wurin mommy din ya fada mata abinda nace
ta tashi da sauri ta shiga kitchen din don Nura ta tafi gida ko dare yayi.
Ta damo min kunun ta kawo min shi na dan samu na sha ya zauna min a cikina har na
samu barci ya dauke ni sosai ban farko ba sai cikin dare fitsari ya tayar dani.
Nan dakina naga uncle kwace a kusa dani yana barci jin motsina bayan na fito
banda yasa shi falkawa yace yaya ne kuma ?
Nace ban daki na fito da sauri yace haras wan ne kuma nacs fitsari nayi yaya
jikin yanzu nace da sauki cikin gundura da magana