Advertisements
Chapter 4 Reading Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   4 / 87

9K to 12K   out of 258.3K words

ta yadda idan ya fakaici idon matan shi yake nuna kulawan shi kan
ta har nama yakan dan ja ta da wasa ko da ba, a.
Sai dai idan matan shi sun gani ya kan dan yi kamay kamay kamar bashi ne daga
karshe dai ya koma fada kamar bashi ba.
Kadai muke zaman mu da dadi ba dadin a gidan watarana mu kwana da farin ciki
watarana akasin sa.
Sannu tashi na kamal aji uku zan shiga babba ajin aga da secondary sai ga gwago
tazo daga lagos nan mukai ta murna da zuwan ta sai awan kararon bata ita kadai tazo
muna ba.
Ita da zurian ta da maigidan tazo ganin mu nan aka shiga ina aka saka da ita da
diya ta da maigidan ta don dai ba karamin son ta yan uwa keyi ba, in zata zo takan
sayo abubuwan anfani tajo ma iyayyen mu da shi.
Nikan ina saurin naje makaranta don haka tsayawa nayi daga kofa na gaida su dan
suna dakin mama ne zaune har mijin nata da yaran ta.
Take cewa wanagani kamar yar wurin Rabi haka koyaushe za a gan ki kamar ke kadai
ke kiwo a gidan gaki tsatsab dake kamar wata wayyayiya.
Murmushi kawai nayi zantafi sai naji tace wanan ai takar ita koke kiyawu agidan.
Ta juya tana magana da mama bandaiji abin da suka fada ba nai tafiyana don ina
saurin in tafi makaranta.
A kofan gida muka tarar da wani matashi yana shan taba zaune saman mota kallo
daya nai mashi na kawar da kaina daga gareshi.
Sauri nake na wuce don da gani tare suke da gwago mu sai naji yace ke shiga ciki
ki dabo min ruwa nasha.
Na dauka badani yake ba ina kokarin wuce wa naji ya sake cewa dake nake fa na
juya baya na ko zanga wace yake magana da ita.
Sai naga babu kowa a tare dani na dan tsaya kadan yace ruwa nace ki debo min a
ciki.
Juyawa nayi nakoma na debo mashi ruwan nakawo mashi ya kurba sau daya yake cewa
wanan wani irin ruwa ne mara dadi.
Nace shi muke sha a gidan mu don haka shi ke gare mu, oho i see waya kaleni sama
da kasa yake cewa karbi ki mayar .
Haushin sa ne yakama ni lokaci guda don ya rena muna wayau da arzikin gidan a
haka dai na karba na wuce shi don warin taba duk ya isheni da hamami.
Na dawo zan wuce yake cewa dani ke yana kokarin kuna wani taban a bakin shi shigo
kice wa su mum sufito haka nan dan Allah.
Kamar nace bazan tafi ba sai dai na juya zantafi sai gasu sun fito daga cikin
uban na gaba suna biye a bayan su.
Nikan nawuce abina ban tsaya kara sauraren su ba don dama nakara zuwa islamiya
duk da nasan bawai buguna za ayi ba amma ya kamata ace na isa a cikin lokaci.
Har na isa makaranta ban dana jin warin taban da aka sha a jiki na ba gani nake
duk jikina warin taba yake kamar nice nashi taba din .
Mun dawo na debi kayan mu na wanke don ban samu wanke wa da rana ba aka raba
tsaraban gwago ko wani daki aka bamu.
Saida na shigo dakin mune na samu tsaraban da gagwo ta kawo muna a gefe, na
samu wuri na zauna gefe ina cewa da ummi.
Wanan mutumin dasu gwago suka zo dashi dazun baida tarbiya zama fa yayi kofar
gida yana shan taba a gaban ko wa.
Ummi tace dani wa kina nufin ubale aishine dan gwago kuna fari duk sain an ni
shi sunyi aure amma shi, shashanci ya na shi yi wai shi dan fari yana takama da
zama cikin kabilu ya saje dasu.
Nace Allah ya kyauta amma kan wallahi bai yi ba wallahi mutun sakace wani ibom
can.
Muna cikin magana mukaji fada ya kaule a tsakanin mama da inna kan kayan da
gwagon mu ta kawo tsaraba inna ke cewa da mama wai tarage kayan ta basu abin da
taga dama.
Mama ta bata amsa da cewa yar uwarki konawa ina yar uwa nane dai ko kaya kuma
abinda naga dama kenan na bayar inkina so ki karba inbaki so zaki iya mayar.
Mama tace idai kayane je ki ta ci saukin abindai muma muna da yan uwa bake kadai
keda su ba balla ki kawo muna bakar magana.
Muna daki da ummi muna sauraren su har suka sude bamu leko ba sukayi suka kare
ba mu leka waje ba.
Washe gari kuma da safe suka aza sabon fitina a gidan baba na dakin inna ya fito
yake cewa daga yanzu indai rabo zai kawo fitina kowa ya rike abin sa a zauna
lafiya.
Da haka karshen fitinan ya mutu kowa in yaga dama ya rike kayan shi ba dole
araba wa saura inna tace yafi nono fari.
Mu dai namu dasu ido don sun fi kusa wanda yace zai shiga fadan su a ciki zai
kwana minti goma yai kadan aga sun shirya tsakanin su.
A yau asabar bamu zuwa makaranta don haka na shirya cikin kayan da mama lami ta
ba ina son zuwa gaida kawata da bata da lafiya.
Wanan ne karo na farko da na sa kayan a gidan mu don basu san ni da kayan ba nan
sukayo mani ca da idanuwan su naji mama tana fadin.
A yau kwaliya akaci haka yau sai ina da wanan adon nai murmushi kawai ba tare da
na bata ansa ba sai naji inna na fadin ke ma dai yaya da wani zance ki.
Yarinya kekaga tana wanan irn kwalliya haka ai kin san abinda take yi inba
mashin shine ai banza ya kai zomo suwa ke ma kin san aida wallakin wai goro cikin
miya.
Muka hada ido da ummi na sai taimin da alama da ido na kyaleta na kara shiryawa
nake cewa zan tafi tare da yi masu sallama.
Inna tace dama diya mace inta dadani namiji ai ba tafiba hankalinta bai taba
kwanciya yawon gantalin za, a ake sallaman mu.
Kai akwai ki da wani zance wallahi ina safiya da ga wani saurayi kyalle ta dai
da nacin son karatu a rayuwan ta inji mama ke fada mata haka na.
Ta ja tsaki tace ai ku ke kara zugata wanda baida lokacin kan shi a gida kulun
boka watafi son karatu adaiyi shaani kawai wai an cuci na kauye.
Na fito gida ina tunanen kallamin inna ba zaka taba jin kalman alheri abakin ta
ba in ba yayan ta bane sai na sheri.
Ita da bakin ta take fadi wata rana yarinya ga kyau ga wanka amma babu saurayi
yau kuma ta can za ta kuma ce maza naka bi.
Naje gidan su Amina na samu bata da lafiya sosai amma ta samu sauki na dan
zauna da ita mukai hira nawani lakaci na mike zani gida don kar na dade Inna tace
sai da ta zubar nadawo kuma.
Mun fito tare da Amina donta dan taka ta walwale jikin ta muna tafe muna hira
inda muke tafiya a hankali ina bata labarin text din da kayi muna, bata nan yadda
ya kaya.
Hon din motane ya damay mu daga bayan mu da kara daga ni har ita ba wanda ya
juya dan gani ko wa nene mai mator kuma bai daina hon din ba.
Ganin ba zamu tsaya ba yasa shi fito wa a motar ya biyo mu, sallama yai muna
duk muka juya a lokaci daya muna kallon shi.
Nikan a zato na sun san juna ne sai kawai na fara tafiya na barsu tare ban tsaya
ba kada naja wa kaina magana ban yiba ance nayi ina ga na tsaya.
Sai naji yace don Allah malama ko zaki taimaka taimaka min da yar uwar ki ta
saurare ni min ti biyu in ba damuwa.
Safiya dake ake magana inji Amina, na juyo nace wani a cikin mamaki yace nasan
badaidai ba ne na tare ku a hanya.
Amma kuma dole yasa na tsada ku a hanya yanzu don idan kun tafi ban san ina zan
kara haduwa daku ba.
Nace gaskiya bazan tsaya ba sunana ya baci ga ban za a saman hanya sai yai
murmushi yace naga alama ai amma don Allah kibani dan lokaci nasan wani abu gare
ki.
Allah daya ke hada mu dashi har da Amina din yasa na tsaya badon na so ba ya ce
sunana sulaiman ni dan garin nan ne saidai ba anan nake ba.
Ina fatan zaki bani amsa ga tambaya a wurin ki don Allah ida bazaki damu ba zan
so nasan gidan ku don na gabatar da kaina.
Gaskiya malam kayi hakkuri saboda karatu nake yi sai an jima nan nabar su tsaye
awurin na wuce.
Ya dan rintse idanuwa shi tare da sauka da ajiya zuciya yana mai sauke num
fashi , ya dan yi murmushi tare da duban Amina dake gefen shi tsaye yace.
Idan ba damuwa ki tai makeni da noba ta kokuma gidan su zai fi sauki a gare ni
nan dai yabawa Amina tausayi tabashi addresen gida yai mata godiya ta tafi.


Ban da lafiya da fatan zakuyi hakuri da mistake din kuka gani anan kwana uku ina
typing ban iya hadawa ba.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:10 PM - Ummi Tandama: BAHAGON, , , , ,


4️⃣🧕🏿


SEENABU MAKAWA
DON ALLAH NAMIJI KAYA SHIGA DON MATAN MUTANE MUKA KA TARA ANAN INKA KA SHIGA ALLAH
YA SAKA MU NA
DON ALLAH YAR UWA ABIN DUNIYA KAR YA JAKI GA HALAKA IN KI BIYA KADA KI TURAWA
WANDA BAI BIYABA DON BAZAN YAFE MAKI HAKKI NABA, , , ,


Dare ne kowa na zaune a tsakar gida saboda zafi da duhu da akwai yaro ya shigo yana
kwala sallama a kofa.
Baba na gida ya amsa yaron yace wai ana sallama a waje sai baba yace yaya Nura
ya duba yagani.
Zuwa can ya dawo yace wai wani wai wurin Safiya yazo amma ya ba son ganin ka.
Inna tai caraf tace Safiya kodai Ainau, Safiya ina taga saurayin da zai mata
sallama, ga wayannen ta tanan wake maganan ta.
Yace nidai abinda ya fada min kenan na fada yasamu wuri ya zauna yaci gaba dacin
abincin sa.
Inna tace tashi maza Ainau jeki ki gani wake sallama dacewan Ainau yar wurin
Mama taje ta ga ba wurin ta bane tadawo kafin Ainau ta dawo ta shige da yar ta
mairo daki.
Sukayi ku ku ku da ita saiga Aina tadawo tana fadin Inna ba wurina bane wannan fa
dangaye ne ke sallama a waje.
Saiga Mairo ta fito zata har takai kofa taji ance ke dakata wurin ki aka zo ko
kuwa tace zan duba na gani ne.
Maza koma ki zauna yaya sani ne ke wannan maganan da mairo daga dakin Inna ta
daka mashi tsawa tace kabari tafita ta duba mana ko ita akewa sallama.
Ya ce yaushe mairo ta koma Safiya a gidan nan ne ke bana son rainin woyo maza
kidawo wurin nan tun ranki bai baci ba.
Sanin hali yasa ta juwoyo simi simi ta da dawo cikin gida ta zauna ya mike ya
fita zuwa kofan gida wurin bakon da kansa.
Duk wanan kace nacen magana da suke faman yi kunnen mu nida ummi sukeyin sa,
kallo daya zai kayi min kagane a rikice nake.
Ummi dai batai min magana ba don tsaban tsoro duk jikina ya dauki rawa a lokaci
daya can najiyo muryan yaya sani yana kwala min kira.
A rikice na fito daga dakin na rabe gefe guda a tsugunne lokaci guda yake cewa
dani, akwai wanda kukai magana dashi zai zo gida ne ?
Gaba daya hankalin yan gidan mu ya dawo gare mu suna sauraren mu a hankali na
bude bakina zanyi magana .
Naji Inna tace dani ke yan zuwa har da masu mota kike tsayawa don tsaban
miskilan da munafunci irin naki na gado.
Nasoma rantsuwa baki na rawa ina fadi wallahi tallahi na rantse da Allah inna
bantaba magana dakowa waye ba
Ji nayi yaya sani yace Safiya na amsa da sauri da naam ya ce tashi kije inda ake
maki sallama waje.
Ai gara dake daza ki jawa mai mata kika jawo muna su diyan su da kara da doki duk
zuwa yake wurin su fa.
Maza tashi tafi kada yaga an tsaida shi kin dade baki fito ba ya dauka bakya nan
ne.
Na mike gwaiwa da sanyi da ce tau yaya nufi kofar gidan wurin wanda aka ce din
yana min sallama wanda yaja min zagi da zargi agida uwurin mutanen gidan mu.
A kofan gida nahango shi tsaye ya jingina jiki da mota hannu daya kuma ya dafa
motar shi dashi ya tsura wa kofar gidan mu ido.
Yana gani na ya dan muskuta tsayin shi yagyara da kyau har na iso kusa dashi.
Fuskana kamar zanyi kuka a lokacin nazo na tsaya sai yace dani ba gaisuwa yan
mata kamar baki na na ciwo nace dashi Ina wuni ?
Shima cike da yanga yace min lafiya lau yan mata,
Wai halan ba ke kadai bane Safiya a gidan naku sai naga wasu yan mata nata
fitowa da sunan safiya mana.
Saida na dan bata lokaci kafin nace ni kadai ne mana kawai da sun fito ne sun
dauka wiri su aka zo yaron yai matuwa yace safiya don sun ga ba wanda ke aikowa
kirana sai yau.
Ya nisa tare da cewa "kai, kice ni din nazo a sa, a ke nan nine zan bude fage in
bar tarihi.
To amma naso naga baba ne da kaina koda yake ai naga yayan mu ya bani go ahead
naci gaba da zuwa .
Kallon sa nakeyi ta gefen ido ya yagyara tsayuwar shi da kya yace na samu goyon
baya kai tsaye ke na kinga duk lokacin da nake son ganin ki ina iya zuwa.
Na turo baki ina cewa indai na amince da hakan ko nifa na fada maka karatu nake
son yi ban da lokacin tsayawa soyayya.
Ba zabin ki nake son ba illa yaka ki bani hadin kai shikaratu nufi ne na Allah.
Don haka ki bar Allah yai maki zabi kar ki raja, a a bangare daya don kinfi son
karatu kice gareshi zaki tsaya.
Kunya bakin ciki da takaici suka sauka min a lokaci daya na rasa amsa da zanbashi
kawai sai hawaye suka dinga zubo min .
Ganim ina kuka yasa shi cewa subbahanallahi ko ban fadi daidai bane ga magana na
kike kuka.
Ganin bazan yi shiru yace Allah ya naki hankuri idan kin huce na dawo mu gaisa
watarana dama yan yanzu zuwa nayi wurin baba don neman izini ban samay shi ba naga
yayan ki.
Ya bude motar shi ya dauko leda cike dakaya ya miko min nace yabarsu na gade yake
cewa Safiya nadai gane bakiyi naam dani ba ne.
Nace ba hakana bane in son samu ne nafison saina gama karatuna tukun yace wanan
baida matsala mudai samu fahintar juna tukun shi yafi.
Nan nabarshi da kayan naki karba ashe ya samu dan makwabtan mu yace ya biyo ni da
kayan ciki.
A Cikin gida kuwa tun fitana mutan gidan suka kasa suka tsare suga yadda za a yi
yayin da inna take ta masifa da yaya sani akan wai nata mata shiga hanci da
kudundune kan ala, amarin ta inda take shiga ba nan take fita ba.
Shigowa na kenan yaron da ya biyo ni da kaya ya shigo gidan shima inda na nufa
can yaron ya nufa da kaya niki niki.
Yaya Nura ne yake tambayan yaron maynene yadauko a hannu shi haka sai yaron kewa
Safiya ace nadauko mawa .
Gaba daya suka sako ido suga kamay nene a cikin ledan saidai bazasu iya ganin ko
may a ciki ba saboda duhun dakeyi.
Inda da hali dazasuce akawo ledan suka abinda ke cikin sa sai dai hakan bazai
yuyu ba don yaya sani na gida alokacin.
Dole da ido suka koma yin magana ba halin su maganta yai cikin su da rashin
kunya.
Har washe gari kayan na nan a jiye ba a taba ba ba a kuma bude ba a cewar umma in
yazo na mayar mai da kayan sa kada na nadauko mata wahala tana zaune kalau.
Daga ni jar ummi tsoron taba kayan muke ja agidan bamu yarda nun taba komai ba
daga ciki Ummi tai mashi dogon ajiya.
Abim duniya ya isheni a raina ga kayan mutumi a je a gidan mu ina tsoron tabawa
a tsakar gidan mu sai habaici ake min cewa a samu a hanawa dangi.
Amina na samu a school nake fada mata halin da nake ciki don dai gaskiya ni
sulaiman yafi karfina da soyyaya.
Dariya Amina ta soma yi min tana cewa safiya kenan ina kika taba jin haka kedai
kawai kice matsayin ku ba guda ba.
Amma zancen yafi karfinki bai taso ba don dai sulaiman mijin da mata da yawa zasu
so ne.
Balle mutumin daya nemi izzini ta gidan ku ai zance ya kare iyaka muyi fatan
alherin ga hakan, nisawa nayi nace da ita Amina nifa in son samu ne nafi son sai
na gama karatu kafin na fara zance da wani namiji .
Safiya kin kwantar da hankalin ki bafacewa akayi zaki aure shi ba dole, abune
nufin Allah .
Nace haka ne amma ni sherin mutanen gidan mu nake jiwa don masheran tane na
karshe sun sa yadda zasu kulla wa mutam sheri ya zama gaskiya .
Da dai zai jaye ya je gaba yane mi wata zai fi sauki don ina gudun jefa shi a
cikin zargin mutamen gidan mu.
Ba tadai yarda sai

4 / 87