Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
kan su yanzu sai dai hakkuri.
Nace ni yanzu ce min da tayi wai tsintarciyar mage bata zama mage shine abin ke
damu na wallahi tana ganin nice na yaudare ta ko may gwago ?
Tace kun ga yanzu duk ba wanan ne a gaban mu ba koma may ye idan kin tare daga
baya sai ki nemi shiri da ita da sannu zata fahinci ke ba tsintaciyar mage ba sai
ta soki fiye da magen da aka haifar mata a gida.
Ummi tace shine kan mafita gwago don yanzu duk yadda za a fahintar da ita ta
riga ta hau ba ta yarda damu ko kadan.
Gwago tace may ake ciki ne don shi ya kawo ni yau din don nasan baku shirya
komai ba ga auren nan gashi kuma ba kananan mutane bane su.
Ummi tace wallahi gwago abinda muke shawara ke nan akai tun jiya da malam ya
daura wanan aure don nasan ba komai zamu samu a bangaren shi ba.
Gwago tace karki yanke hukunci da sauri don baki san ajiyan shi ba nace humm
gwago ai abar zancen baba kawai don yanzu baida yaushe ne ya fara fita kasuwa.
Nace akwai wasu kudi a hannu na barin dauko sai a kaima su mama asan shawaran da
za a yi dasu na mike sai gwago tace dawo ki zauna zasu yanzu don na fada masu mu
hadu nan ban san abin da ya tsayar dasu ba.
Sallaman su mukaji a tare suka shigo suka tsaya suna gaisawa da mama dake zaune a
kofan ta tana raba abinci.
Suna shigowa suka fara gaisawa nima gaida dsu nayi da zuwa sukace amarya ke ce
haka ba wani shiri da zai nuna farin ciki a gare ki?
Murmushi nayi nace kai haba mama tace ai gaskiya ne Safiya tun yanzu fa za a fara
shirya ki don wanan auren ba irin wancan bane.
Tace to ai kune uwayen nata kuka tsaya nawa na fada maku mu hadu nan tun da safe
amma sai yanzu kuka zo.
Yanzu dai ba wanan ba yanzu shafiu ke fada muna abin da bakar daga can tayi
jiya kuma asirin ta ya tonu.
Gwago tace don Allah ku fita batun ta kuyi abinda ya kawo yanzu don ba isasshe
lokaci ake dashi don tace yace a sati biyi yake son ta tare gidan shi.
Suna hada bakin wurin fadin sati biyu fa ?
Yo mai za a tsaya jira kuma aure ya dauro ba sai ta tare gidan ta ba yanzu duk
wani abinda za ayi ai aladane kawai don wajibi ya auku ko tunda an daura aure may
ya rage kuma ?
To yanzu gwago maye abin yi tace yanzu take fada muna akwai kudi a wirin ta sai
a san abin yi nace ta bari har ku iso ne muga kudin sai a san yadda za a kasafa su.
Mikewa nayi na shiga daki tare da kirgo kudi dubu dari uku na kawo masu na mika
ma mama Jummai don itace babba a cikin su.
Tana kallon kudin tace ai ina ga a dai tallakance wanan din zai isa ko sun kai
dari biyu ai nake gani nace dari uku ne nan tace tirkasa.
Ta juya gun su ummi tana cewa may ye abin yi yanzu ga dai kudi sun samu gwago ta
katse su da fadin akwai raguna na sai a kama biyu ku hada a laurar taku.
Nace gwago baki barin abinki tace ai don haka dama nake kiyon su yanzu ba sai ai
lalura dasu ba sai dai zanso ku soya masu shi ku jefa a gara kun dai ga gidan masu
shi zaku kai kayan.
Zan so ace kun tsaya kunyi abinda zai cika ido yadda ba za a raina maku ba.
Mama Suwaiba tace mu dai yi iya karfin mu amma ina zamu ita dasu nace mama may
zai hana ku kira mama na nan gidan kada a kebe ta zaifi ace anyi komai da ita.
Gwago tace yanzu abin da nake shirin fadi ke nan kika riga ni fada sai ummi tace
gaskiya kan kiranta aka tura Aisha da ta make dakin tana sauraren mu akayi .
Bata dauki lokaci ba sai gata nan dai akai mata bayanin ta nisa tace da son samu
ne kada muyi kayan abinci mu dai tsaya ga wanda za a rabawa yan uwa da abikan
arziki don shine abi magana.
Alabashi gaba in ta haihu sai ai mata wanan ko yaya kuka gani ta dago kai tana
kallon su ko wayace sharan ta yayi.
Na suka fara kitasta abinda zasu inda za a kai yin cicin din a birni can wajen
kaunan miji mama jummai dake zaune a birni su kuma zasu yi sauran abubuwan a nan .
Kowa ya dauki part din abinda zai yi a cikin su inda aka bar wa mama da ummi yin
suyan kaji da ake so cika roba guda dashi.
Tun wanan ranan basu zauna ba kowa da abin da yakeyi don kar a girshe shi muna
waya dashi ko wani rana yana kara kwantar min da hankali.
Faiza ne ke fada min cewa su anty uwa sun koma abuja a fusace wai Nafisa tana ta
kuka tana fadin ba zata yarda ba.
Ita sai ta auri uncle ko ta halin kaka wai da kyat ta yarda ta bisu ta kare da
cewa wai yanzu ashe an daura auren ku da uncle baki fada mu na ba sai a bakin
mutane mukaji.
Nace wallahi Faiza nima ban san za a daura min aure ba a wanan lokacin kawai daga
zuwa tambaya sai gashi ance daurin aure za ayi.
Tace ai dake da madam din mu ne yanzu don naji tana ta zage zage tana ta fada daga
ke har uncle din wai kun munafunce ta.
Nayi murmushi kawai nace ba haka bane wallahi kowa baba bai fada wa zancen daurin
auren nan ba sai da akazo yi aka sani wallahi ki yarda dani Faiza tace wallahi na
yarda.
Tace yanzu yaushe ne tarewa kuma ?
Nace da ita babu rana Faiza don bamu tsaraba sai ya dawo zai saka rana tace aini
abin yayi min dadi wallahi sai dai nasan yadda madam ta hau ba zata barmu mu zo
wurin bukin ba.
Kin san may nace a a Faiza tace naji suna magana wai ai gidan ku ba abinda zasu
kai tin anan zaiji kunya ita ko mutumiyar kullun tana daki tana kuka wai bata da
lafiya.
Allah ya kyauta nace da ita ban yarda na furta wani kalma da zata kaini gaba ba
don sanin halinta da nayi.
Mun gama wayan ta barni cike da tunane halin da muke ciki da anty don da ka gan
ni na ramay babu walwala a tare da ni kamar wacce za ayiwa auren dole na koma.
Nasan dawowan shi Nigeria sai da ya kwana biyu ya wuce bauchi wurin mahaifiyar
shi don kiran gagawa da tayi mashi akan maganan mu.
Ya iso sai dai mutane basu bari ya samu kebewa da ita ba sai da dare suka samu
ganawa da mahaifiyar tashi.
Yana zaune kasa tana saman kujera ta kafa mudubin ido a fuskan ta da ke taimaka
mata vurin gani.
Shiru dakin yayi kafin tace babana wata irin mace ka dauko muna don ban ji dadin
labarin da ya kawo min ba.
Ko da yake mutanen duk da bamasu karfi bane amma sun san mutuncin kan su a yadda
mahaifin yarinyar bai karbi sadaki mai yawa ba kuma da irin taron da sukai ma
wayanda na tura daga nan.
Sun yaba kwarai da mutuncin da aka nuna masu a gidan sai da abin damuwa wanan
labarin da Nafiu yazo min dashi shine banji dadin shi ba.
Nafi son kayi bincike mai karfi kafin yarinyar nan ta tare don ni ban kita ba don
kaine mai zama da ita amma tunda kananan magana ya fara fitowa daga gare su sai a
tsaya a bincika a hankali kada azo ai abu a cikin duhu.
Ban son ka kara auren dana sani kamar yadda kayi a baya auren da baida amfani a
gare mu sai barnan suna.
Shiru yayi kafin ya dago kai yace hajiya akwai abin da nake boye maki da dadewa
wanda baki sani ba har yau.
Gyara zaman tabarau ta tati dakyau ta dago kai tana sauraren shi tare da fadin
baba na maye kake boye min wanda ban sani akan ka.
Ashe akwai abinda zaka iya boye min wanda ya shafi rayuwanka yace hajiya kiyi
hakkuri don Allah fada maki wanan zancen tashin hankali ne a gare ki.
Nan dai ya fara bata labari tun auren shi da Samira matar shi ta farkko sai
innalillahi kawai take furtawa har yakai yadda anty ta hada ni dashi dakuma yanzu
da take shirin ruguza auren namu.
Innalillahi take ambata tace yanzu shi Nuhu da matar shi sun san maganan ga suka
iya boye maka sirin ka ta yadda ko ni da na haife ka ban sani ba.
To amma ita maimuna may zai sa tayi haka bayan ta hada alheri kuma ta bata
rawanta da tsalle a karshe.
Yanzu na gamsu da kai sannan ita wanan yarinyar itane rufin asirin ka ga kowa ta
yadda ba kowa zai san abinda kake ciki ba.
Allah ya albarkaci aure ya baku zuria mai albarka ya amsa da amin tare da mata
godiya ta kara kwantar mashi da hankaki tayi tare da cewa tasan yadda zata kashe
maganan daga bakin kowa.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , ,
5️⃣4️⃣5️⃣
5️⃣
🧕🏿 4️⃣4️⃣5️⃣
NOVEL DINA NA KUDI NE WANDA YA SAN BAI IYA RIKON AMANA TA FADA MIN IN BATA KUDIN TA
, , ,
Shirye shiryen buki aketayi amma ni hankalina baya gare su cike yake da damuwa don
ban san yadda zai kwashe da mahaifiyar shi ba.
Na kwanta zuwa dare naji kiran wayan shi ya shigo min a sanyayye na daga wayan
gami da sallama a bakina.
Yace kin fara barci ne nace ina naga barci ban san hukuncin da baaba zata yanke
a kaina ba kuma ma ai yanzu barci bai ga idona ba tunda nace aure nake so.
Dariya yayi sosai har yana lyalkyatawa yace fada min may zai hana ki barci don
Allah ?
Na abubuwa da yawa mana Uncle yace kamar su mai nace wayan san iyaka sai dai
ranan da na tare a gidan ka.
Don kullun cikin kawo kudi ayi kaza nake yace look nafa fada maki bana son
tarkace daga ke sai boxes din ki za a kawo min na fada maki .
Nace naji uncle amma dai ai za ayi abinda zan ba yan yinin buki ko ?
Yace kai mata ho wanan kuma kina son ki sawa kan ki nauyi ne nace ki bari inzo
in dauke ki daga ni sai ke sai gida na amma kin ki.
Nace wani gidan uncle yace gidana na Abuja mana ba anan zaki zauna ba ?
Nace haba uncle kai ka ga haka ya dace ga hajiya baaba da ranta da lafiyan ta a
dauke akaini gidan ka na Abuja ?
Ai ka bata damarta na mahaifiya ta sa muna albarkan aure dariya yayi yace Safiya
wanan halin ya kara sa ina son ki wallahi yanzun dai sai an kaiki bauchi ke nan
wurin hajiya baaba ko ?
Nace a wani irin murya mai sanyi shiya yafi mutunci uncle yace to shike nan hakan
yayi kyau zan fada mata su shirya nan za a kawo ki direct idan an dauko ki.
Muka dan taba hira yana fada min yadda suka kwashe da mahaifiyar tashi nace uncle
dama bata san halin da kake ciki ba duk wanan dadewan yace bata sani ba.
Kuma ko yanzu na fada mata ne don kada daga baya tazo ta zargeki ga abinda ba
laifin ki ba ya kawar da zancen da fadin zan turo maki da sako gobe sai ki kara
kiyi hidimar bukin dashi yan uwa na zasu zo ranan alhamis da kayan lefen ki wanda
naso ace madam ne zata zo dashi.
Amma wanan matsalar yasa baaba tace daga wurin ta za a kawo komai yadda ya kamata
nace Allah ya kaimu lafiya amma ni da an bar lefen don baaba ta riga ta aiko min da
akwati biyu yace ta fada min wanan ai mun gani muna so ta hada maki wanan kuma ni
na hado maki shiya kaini Dubai dama.
Mukayi sallama ina mai kara yi mashi godiya ya kashe wayan na sauke ajiyan
zuciya.
Ina mai ci gaba da tinanen wanan baiwa da ubangiji yai min amma ma kuma baiwan
sai yazo min a bahaggon rayuwa.
Washe gari ya shiga gaida mahaifiyar tashi nan yake fada mata yadda mukayi akan
nafi son in tare anan bauchi don ta sa muna albarka.
Murmushin nuna jin dadi tayi tace mashi shiya har kullun bani dana sani da zaben
ka don nasan bakayin abinda za a yi da an sani cikin sa.
Ko wanan auren kaddaran na Samira da kayi don yan uwanka ne da sukai hadin ba
bincike yanzu gashi an bar mu ciki.
Daren jiya banyi barci mai dadi ba a rayuwa na amma da nai tunane sai naga bawa
bai wuce kaddaran sa mutuwa kuma tana iya riskuwan bawa a ko wani lokaci.
Don haka yanzu kafin ka tafi sai a fara shiye shirye tunda buki ya dawo wurin mu
don da ina dauka acan za a yi komai.
Bai baro bauchi ba sai da suka gama shirin komai da za ayi a nan ya san nan ya
baro garin ina kwance naji waya alaman sako ya shigo min ina dubawa kudine wanda
sai da ya sani kaduwa.
Na duba na kara dubawa naga milayan guda chur ya turo min tare da sakon da ya
biyo baya na .
Nasan wanan zasu ishe ki komai da kuke son yi har da gyaran dakin ummi yadda ya
dace asha buki lafiya.
Ummi na kira kurayan daki nake fada mata abinda ya turo min tsaye take sai da
takai zaune tana fadin.
Yarinya wanan mutumin kuwa yasan ciwon kudi ashe nifa abin nasa yana ban tsoro
wallahi.
Nace ummi samu kudin yake a lokacin su kuma nema akeyi ko yaushe wanan ai ba
koma a wurin shi sai kin ga company da ya bude nasa na kan shi.
Tayi shiru tace duk dai da haka abi abin sannu dai yaya Sani na kira da ummi ta
fita yazo nake neman shawara a wurin shi yace yanzu abinda za a yi shiryawa zakiyi
mu samu Amina aminiyar ki can birni ita zata taimaka maki da sharan da ya dace
tunda sune yan birni su suka san abinda ya dace ayi.
Banki ta nashi ba don shawara ne mai kyau ya bani ko banza ya kamata tun farko in
neme ta amma na manta da ita.
Don haka shiryawa na yi muka nufi gidan su ni dashi da Rukaiya da tace zata bimu
mun isa mun samu taro na arziki a wurin mummy din .
Bayan ta gabatar muna da abinsha cikin wanda takeyi na sana an ta sai na fito
mata da maganan abinda ya kawo mu.
Taji dadi sosai tace bari ta kira Amin nan taji yaya za ayi nan ta buga mata
waya ta dauka sun gaisa sai take fada mata gani a gidan ta ga kuma bukatan da ya
kawo mu zamu zo wurin ta.
Ina jin yadda take murna tace ai ba sai na zo ba gobe ita zata shigo sai a san
abin yi mun ji dadi sosai don haka muka koma gida.
Daga yaya sani har yaya Nura basu zauna ba don duk abinda ake so suke zuwa birni
su sawo su dawo shafiu kani na ma ba abarshi baya ba.
Amina ta iso da kaunan mijin ta dake zawarci a wurin ta nan suka shiga shiri do
ba lokaci issashe gare mu.
Komai an kamala don haka aka kai gidan gwago ana tarawa a can nima na bar gidan
mu can gidan gwago din na koma.
Ranan da yan uwanshi zasu iso ana gobe zamuyi walima sai abin ya taru yai masu
yawa nidai nawa ido sai dai ina kewan anty na don da yanzu itace zata shirya min
komai.
Maimakon bakin da muke jira su iso yaya Saadu ne da iyalin shi suka iso da
mahaifiyar Samira da yayanta mace da na miji sai Sadiyan shi da tace zata biyo su.
Nan aka shiga murnan ganin su sai dare bakin shi suka iso garin don haka aka
kaisu gidan su Amina a can aka sauke su.
Su yaya Saadu kuma suka sauka wurin mama amma ita Samira da yarta dakin ummi na
suka sauka don tace can ne dakin su.
Sai da safe suka gabatar da kayan lefen da suka zo dashi bisa jagorancin
mahaifiyar Amina da ta zamay masu uwar daki anan don har sun saba da itako sabon
mata baida wuya.
Ga ganin lefe ga shirin walima da za ayi wanda duk kusan matan karkaran mu mama
ta aika masu da mintin gayyata wurin.
Inda Amina ta gyato malama khadija daga birni tazo ta wayyar ma mata da kai akan
hakkin aure da na yayan su.
Tako zo din don ta wayar dakan mata a wurin da sanyaya masu zuciya da nasihohin
ta daga niimar da Allah yaba mace ta gari da jin tsoron Allah a cikin rayuwan airen
ta bawa yaya hakkin da ya dace na fanin kula da hakkin su daya rataya akan uwaye
mata.
Alamarin ya kayatar sosai don bazaka fahinci haka ba sai kaga yadda mata suka
natsu a wurin har da mazaje a can baya da suka zo don saurare.
Ko wace mace a wurin ta natsu ta kama kan ta alokacin kalaman malama na shiga
jikin ta nan aka