Advertisements
Chapter 53 Reading Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   53 / 87

156K to 159K   out of 258.3K words

kai karshe su Amina dasu samira suna ta faman raba masu abinda aka
tana don waliman buta da dabino sai abinci a cikin take away.
Taro ya watse lafiya kowa sai sam barka akewa juna inda mafi yawan mata basu
koma gidajen su ba suka shigo yinin bukin da ake yi a gidan mu.
Sai da dare ne mahaifiyar Samira da su mama suka kaini wurin baba don muyi
sallama saboda da safe sammako zamuyi a tafi.
Ina sungun ne a gaban baba yayi gyaran murya ya fara da fadin ikon Allah Safiya
kin ga yadda rayuwa ya koma muna a dalilin ki.
Ni banda abin cewa dake sai fatan alheri da gamawa da duniya lafiya Allah ya baku
zuria masu albarka.
Ki rike hakkin aure ki rike mijin ki amana don ko shi din ba makyataci bane irin
wancan na farko da mukayi maki jeki ubangiji ya kara sa maki albarka.
Kuka ne yaci karfi na lokacin da naji baba yace don Allah ki gafarce ni Safiya
dani da duk wani wanda ke gidan nan.
Shima baba kuka ne ya kumbce mashi don haka da sauri mahaifiyar samira ta jani
mukabar dakin nashi zuwa dakin mama sai dakin inna.
Tana uwar dakan ta muka shigo Saadatu ne ta shiga kiranta tace tazo ga Safiya
nan an kawo ta wurin ta neman gafara.
Muna jin ta tana cewa ni may zan mata su tafi dai Allah ya sa mu sheda sai mama
Jummai da dake tare da mu ta bata amsa da cewa ai mun riga mun sheda sai dai muce
gwamma da akayi ba wani abu muka kawota yi ba wurin ki don zama tare a sahirce ma
junane.
Ta fito don bata dauka anji maganan ta ba sai cewa take naga dai yanzu Safiya ai
ba yarinya bace don duk abinda zamu fada mata ta sanshi Allah ya bada zaman lafiya.
Suka mike dajin abinda ta fada suna fadin amin tare da ja hannu na da uwar Samira
tayi muka bar dakin ina sa takalma na naji Saadatu na fadin kai Inna sai yaushe
zaki ja muna farin jini gun yan uwan mu ne ?
Ni dai mun tafi banji amsan da zata ba yar nata ba don jasan ba mai dadi zataji
ba ga bakin inna.
Mun koma wurin ummi na can suka tasa ta gaba wai tayi min fada nasan ba abinda
ummi zata iya fadi a gaban su dama sai cewa tati Allah ya albarkaci aure ku
yarinya.
Bayan shi bata ce komai ba sai sharan hawayen da takeyi nima kukan nakeyi a
lokacin wanda dagani har ummi bamu san ko kukan may mukeyi ba.
Sai mahifiyar Samira ce ta iya cewa haba ai bai kamata ace kuna kuka ba don abin
farin ciki ne ya samay mu bana kuka ba mama jummai tace kuka dole ne gare su ai.
Haka dai aka watse ina jin suna hiran lefen da aka kawo wanda mama tasa akai
dakin baba wai akwati har set biyu babu ne kawai babu a cikin sa.
Nan suka shiryasu tun cikin daren da za a tafi na kira mama nace a rabawa yan
uwa da abokan arziki da sukayi tsaye a wurin sha anin nan suka zaba daga cikin
wanda baaba ta turo dashi akabawa wa yanda suka dace aba.
Mutocin tafiya sun iso da dare nan suka kwana inda yaya Saadu da yaya Sani suka
zabi masu zuwa kai ni.
Don dogon luxuries aka zo da ita sai karama don daukan amarya ni dai ban san masu
zuwa ba na dai san Amina da Samira da yar uwar ta ne.
Daya daga cikin kayan da hajiya baaba ta aiko dashi nasa wanda Amina ta bayar
aka dinka min a birni.
Sai da akazo shiga mota na ke jin yadda suke ta hayaniya nadan bude fuska na ina
kallon su nace a raina wai ni Safiya yau akema gardaman rakiya gidan miji haka
abinda irun su inna basu so gani ba gare nu gashi yau Allah ya nufa anayi akaina.
Yaya saadu ne a gaban motar da na shiga sai gwagon ummi da mahaifiyar Samira
matar shi su samira karamar mota suka shiga da su Amina.
inda yaya Sani da yaya Nura suka jegoranci doguwar motar da mutanen dake cikin
ta don shiya bugo yace a cika motar azo da mutane.
Mun sha hanya don duk da sammakon da mukayi sai bakwai na yamma muka isa garin
bauchi nan naji abinda uwar Samira take cewa shi yasa ni dan bude fuskana nima in
gani.
Acan lagos kuma sai faman zage zage anty ke durawa da taji ance mahaifiyar shi ta
tura akai kaya ta wurin ta don har kiranshi tayi din ta fada mai bakar magana sai
bai daga kiran nata ba.
Da daren nan maigidan ta ya dawo garin nan ya samay ta tana cika tana batsewa sai
da ya huta yake tambayan ta abinda da ke faruwa.
Nan ta shiga labarta mashi karya da gaskiya yana sauraren ta sai da ta gama yace
amma ban taba sanin baki da wayo haka ba maimuna.
Jin ya kira sunan ta kai tsaye yasata natsuwa yaci gaba da fadin yan zu ke uwa ce
zaki bari har ta saki a gaba ki yarda da bukatan ta bayan kin fi kowa sanin halin
ta dana yaranta.
Waima tsaya don Allah idan uwa ta juyaki zata iya juya Sulaiman ne kai tsaye ke
kin fi kowa sanin ko waye sulaiman don shi dan kaifi guda na kuma ya nuna maki
koshi waye.
Ya nuna maki in dake ayi in ma babu ke zai iya gashi sunyi bukin su hankali
kwance yace amma ko da labari za a bani cewa zaki iya yin haka bazan taba yarda ba.
Sai gashi keda bakin ki ba kunya ba tsoron Allah kike labarta min shirin ku na
shirmay kin dauka kowa baida hankali ne irin ki.
Jikin ta yai sanyi don ganin daddy bai goyi bayan ta ba dama dashi ta dogara ya
dawo suyi ma sulaiman din sheri sai gashi ya dawo bakin su daya da sulaiman din.
Bata san cewa da daddy ake kulla komai ba akan bukin nan yayi mata tas yace yanzu
dabara ya rage gareta ta gyara tsakanin ta da sulaiman din da ni.
Nan ya shige ya barta tana tunane tare da yin na daman abinda ta aikata gashi
anty uwa taja mata hasara da tasan ita zai ba hadin lefen da yaje da yar uwan shi
suka yi.
Don ba karya ba ne anty tana da son abin duniya dama maishi akace abu bai isan
shi su ko yan uwan Sulaiman sai murna sukeyi yana yi dasu yanzu.
Don dama hurda da ita ya hana shi ya kula da yan uwanshi amma yanzu gashi su yaba
su aiwatar mai da komai yadda ya kamata su yi.
Gida ne mai kyau na zamani wadda ya tsaru iya tsaruwa wurin haduwa wata da gani
tobashiyan shi ne ita tazo tana muna jagora zuwa ciki sai zolaya take yi.
Maman Samira ta sani karanta wasu ayoyi daga cikin kurani tare da wasu adduoi na
neman tsarin ubangiji.
Part din din mu aka fara kaini ko zama banyi su gwago suka ce akaimu wurin uwar
mijina.
Mutane suna biye damu inda har zuwa dakin sai dai yan uwana sun tsaya a part
dina basu biyo mu ba sai gwago da mahaifiyar Samira da mama da su samira da amina
su bakwai dai suka rufa min baya.
Ta idar da sallah ke nan aka ce mata ga amarya an kawo mata tace sun koyi sallah
mahaifiyar Samira ne tace yanzu dai muke so a bamu wurin muyi mun kawo amarya
masauki ta ne.
Dariya tadan yi tana mikewa daga inda take tare dafadin aiko na gode da wanan
zumuntan da kuka nuna min iso inda nake rufe da fuskana ta rugumay ni tana kokarin
zaunar dani saman kujera.
Sai na zamay na zube kasa tace a a taso ki hau kujera mana kai na girgiza mata
tace Allah yai maki albarka tasa hannu tana bude rufin fuskana.
Naji tace tubarkallah masha Allahu tare da zubamin idanunta akaina ina duke da
fuskana kasa ban yarda na dago kaina ba munyi ido biyu da ita.
Gaba sai faduwa yakeyi ta juya wurin sauran yan uwanta dake shake a dakin tace
tubar kallah kunga baba na ya iya zaben mata Allah yasa yadda fuskan ki yake dakyau
har da halin ki mai kyau ne inji wata daga cikin matan dake dakin tace.
Mahaifiyar Samira ta amshe dace insha Allah yadda take dakyau haka ma zuciyar ta
yake farar belbelace wanan mai farin nama.
Sai suka sa guda dakin ya amsa da shewan su nan dai su gwago suka mike suna
fadin a basu wuri suyi sallah.
Nima daga inda nake zaune a kasa rufe da fiska nace sallah sai wata daga cikin
kan nen shi tazo tace may kike fada amaryan mu kasa kasa nace sallah zanyi.
Baaba wai amaryan mu zatayi sallah tace kaita daki don Allah suyi sai sukace
wani abu sai amaryan Abbati baaba dako jikoki bata yarda su shiga mata bayi yau
gashi tace amarya ta shiga nan na fahinci yawan tsabtan da tijuwar ashe a gunta ya
gado tsabtan shi.
Ni da samira Amina da yaya Samira muka shiga dakin sai lokacin na bude rufin
kaina ina jin Samira na fadin ikon Allah wai dakin tsohowa ke nan garin dadi na
nisa.
Bayan munyi sallah an wadda tamu da abinci da sha zuwa takwasa akace in fito a
kaini part dina mun fito tare da rakiyan matan da hajiya baaba tace su rakani
wurina.
Nan muka shiga suka bude dakin dake rufe wanda nasan shike zamana a gidan muka
shiga .
Nan suka fice suka barmu sai nida yan uwana a dakin wanda sai lokacin na bude
rufin fuskana don in sha iska tare da bin dakin da kallo.
Nan kowa ya sake yana diban abin da yake so da aka wadata mu dashi a part din
nawa sai hira ake kwasa sai jefi nake saka baki don zulmin da ya ke damuna a raina.
Yaya Saadune suka shigo wurin mu dasu yaya Sani nan akai ta bakwanci dasu suna
biyewa gwago da take jan su.
Wurina ya nufa yana fadin amarya yaya dai na duk kinyi wani laushi dake ajiyan
zuciya na sauke tare da kakaro murmushi a fuskana.
Nan muka zauna dashi yana kara yimun nasiha a kan sabon wurin da na shigo yake
fafin in kwantar da hankali na in fahinci yanayin su.
In zauna lafiya da kowa a yadda ya fahinci family kamar Sulaiman bai shaku da
su ba sosai don duk wanda yazi sai yaji suna mai korafin bai zuwa gida.
Yace kin ga yanzu sai kiyi amfani da wanan daman ki sakashi a hanya ta yadda zai
mami yan uwanshi kan sashi kuna zuwa gida lokaci lokaci.
Ki kuma sa ya danga masu alheri yadda ya kamata ke ma dai kin san sauran ba sai
na gaya maki ba.
Dagowa nayi idona yana zubar da hawaye nace na gode yaya insha Allahu zanyi
kokari inyi yadda ka koya min din.
Nan su yaya Sani suka shigo suma mun dauki lokaci dasu muna hira a wurin sanan
sukai muna sallama suka fice.
Amina ta dawo wuri na tana kara haska min rayuwa abinda ya dace in daga yi da
yadda zanyi in sa sabo a tsakanimu daidai sauran su.
Naji dadin shawaran ta duk da dama nasan wasu a dan zamana da anty danayi sai dai
karin da tayi min na wasu da nake ganin kamar ba masu amfani bane a lokaci.
Sai dare sosai muka samu muka kwanta inda suka ce da safe zasu fita zuwa cikin
gari don su bada labarin garin bauchi idan sun koma gida.
Washe gari akai haddaden walima a gidan aka watse lafiya nan mutanen mu suka
shiga zaga gari ya rage saura ni da gwago da mama a dakin.
Sulaiman ne ya shigo don ganin fitan su da yayi yana saye da babban riga da yar
ciki na farin voile sai dan dinkin da akaimai ba mai yawa ba can.
Ganin su gwago yasa shi jin kunya zai koma gwago tace mukan bari mu fice wurin
hajiya mu barku ku gaisa yana fadin su zauna amma sai suka fice.
Acan suka samu su hajiya na al,ajabin kayan garan da muks kawo masu sukace kuko
wanan dawai niya haka babu iyaka don roban guguru har bakwai da ruban nama biyu na
ragon da aka soya sai zabin da ya sha gyara da hadi biyu alkaki roba biyu kwan
zabbi an cika roba biyu sai jarkan man shanu da na nono da sauran tarkace masu
muhinmanci.
Bai iya tsayawa ba a dakin don kunya yace barin in fita na dauka ai ke kadai ne a
dakin na shigo yana magana yana min wani irin shuumin kallo har sai da gabana ya
fadi.
Bai iya tsaya ba juya zuwa wurin baaba nan ya samu suna kallon kayan da aka baza a
kofan dakin hajiya baaba ana kallo.
Lumshe ido yayi dayaji baaba da yan uwanshi na ta yabon karanmacin da muka nuna
masu da kawo wanan kayan haka a matsayin gara.
Nima kuma a nawa bangare sai yabo sulaiman din da yan uwanshi ke sha wurin yan
kawo ni don irin karamcin da aka gwada masu a gidan.
Washe gari suka kama hanya sai dai an bar gwago da mahaifiyar Samira su zasuyi
min rakiya Abuja sauran aka tafi dasu mun dade da Amina muna tataunawa.
Gidan ya rage daga ni sai su mummy kamar yadda naji samira na kiran mahaifiyar
nata.
Babu kowa a dakin nawa ya shigo ina tsaye gaban mirrow dakin ina kokarin tubke
kaina da ya sha kitso ya zubo min a fuska.
Kamshi turaren shi ne ya fara sanar min da shigowan shi dakin nawa sai kuma na
gashi ta cikin mirrow tsaye ya soka hannayen shi a cikin aljihun wandon shi tare da
kare min kallo don bai taba ganina haka ba hijjabi ajikina ko gyale duk sai na
daburce na rasa natsuwana a lokaci guda.
Daidai baya na yazo ya tsaya daidai inda nake a hankali ya ciro hannun shi daga
aljihun da suke ya sauke su saman kun kuruna ban san lokacin da na lumshe idanuwa
na ba.
A hankali ya dora kanshi saman bayana ban daina abinda nakeyi ba amma na kasa yi
masa magana a lokacin saboda kunyan shi da nake ji.
Wai nice yau gani ga uncle a karkashin inuwa daya a matsayin ma aurata nauyi da
kunya sun hanani juyowa gare shi in fuskance shi.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , ,

5️⃣5️⃣5️⃣
5️⃣
🧕🏿 5️⃣5️⃣


NOVEL DIN NAN ONLINE NOVEL NE NA KUDI IDAN KIN SAN DARAJAN ALLAH DA MAZON SA KADA
KI FITAR MIN DA NOVEL DINA YAR UWA.
Fuska biyu ga mulsumi abune mai muni ga alumma a hada dashi da Allah bai san
darajan shi don zuciyar ta tayi tsauri shedan ya rinjaye shi amma kuma yana musulmi
babu Allah a zuciyar shi.
Kafiri ma yana tsoron Allah balle ke mai sallah biyar a rana ina zaki da hakkin
wani a kan ki naki ma ya ishe ki kaya gobe kiyama.
Bai damuwa don nasan da kayana zaki dauka ranan dauka akai babu mai taya ka sai
halin ka muje zuwa yar makawa yanzu ta fara novel yar matashiya ce a cikin ku.
Ana cewa novel ba dadi ba ma ana kuma gashi ya zama kamar dole a karanta harda
sato maku akeyi don kawai son duniya.
A hankali ya sa hannuwanshi ya juyo ni ta yadda zamu iua fuskantan juna dashi
irin tsabar soyayyan da nagani a cikin kwayan idon sulaiman din ban taba ganin shi
a cikin kwayan idon wani na miji ba.
Haka yasa ni sunkuyar da kaina kasa da sauri gabana ya na bugawa uku uku don
firgice sai ji nayi idanuwa sun ciko min da hawaye ban san sun zobo ba.
Sai gani nayi yasa hannun shi yana sharewa a hankali jikin shi babu idan inda bai
rawa a lokacin don wani irin sha,awa dake fisgan shi a lokacin.
Sannu a hankali yake goge min hawayen sai naji sun zubu gaba daya kuka ne yaci
karfe na ji nayi ya rugumoni zuwa jikin shi.
Cikin sautin kuka nayi karfin halin bude baki na ina cewa dashi Uncle, , , Uncle
sulaiman don Allah , , , don Allah ka rike ni amana karka ci amanata don Allah ka
soni tsakani da Allah ka so ni saboda Allah badon wani abu ba.
Sassauta rikon dayai min yayi don yaji maganan ya doki kwakwalwan shi a lokaci
guda.
Sai kuma naji ya riko ni fiye da na farko kamar zai hadiye ni, shima magana ya
soma cikin sanyin murya kamar haka.
Safiya ki kwantar da hankalin ki mu fahinci juna mu zauna lafiya wallahi Safiya
bazan taba hada son ki da wani ko wata ba.
Ina son kine tsakani da Allah, ina son ki sani ni ban soki dan wani abu ba ko
wata manufa nawa, ina mai tabbatar maki ba zan ci amanar ki ba a rayuwana don
banga ribar da zan samu ba ga yin haka.
So dan Allah ki saki jikin ki dani mu zauna lafiya cikin amincin Allah, ina tare
da ke komai wuya komai dadi.
Don ba zan taba hada darajan girman ki ba da wata mace a fadin duniysn nan
mahaifiya ta ce kadai zan iya hada son ta da naki don ita kadai ne mafi daraja a
gare ni a duniyan nan yanzu bayan ke.
Don haka ku biyu ne kada yanzu zaku iya juya ni yadda kuke so a rayuwan ku.
Ni nace ina son ki duk yadda kike ba zan taba kowa dake ba mudin na samay ki
yadda

53 / 87