Advertisements
Chapter 49 Reading Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   49 / 87

144K to 147K   out of 258.3K words

iya controling ba tayi controling dina ba ko may kika ce ?
Nace Allah yasa mu dace yace amin mun ma dace din sai dai muyi adduan Allah ya
hada hankali baki daya.
Driver ya dawo bai dauki lokaci ba muka kama hanya bayan sun gama ganawa da
maigidan nashi ni kuma ya cika min jakkana da kudi wai don bukata acan .
Yace ba lalai bane mu hadu da sauri don zaiyi tafiya cikin wani sati don haka
koda zasu zo yana ganin ma bai kasan.
Da haka mukai sallama dashi muka dauki hanya sai garin mu zuciya na cike da
damuwa don ban san zan zo gida ba a wanan lokaci.
Mun shigo da dan sauran lokaci don sam bayi tsamanin cewa an gama ginan gidan mu
ba har sun tare a ciki.
Sai driver ne naga yaja ya tsaya a kofan gidan mu nan na fara raba ido ina
kallon aikin da sulaiman yayi mu agidan muna tsayawa su yaya Sani dake daban su
suka taso da saurin don ganin motan da tazo kofan gidan namu.
Ina fitowa suke fadin a safiya ashe ke ne tafe yaya sani da ke kokarin kama
marfin kofan ya ce safiya lafiya kuwa ?
Na kalleshi da murmushi nace lafiya yaya mun samay ku lafiya ?
Ya amsa da lafiya aka fitar min da kaya zuwa cikin gida ina biye dasu duk kan
gidan ya juye min kamar ba dan kangon gidan mu ba.
Dakin ummi suka nufa da kayan nawa ana cewa Safiya duk suka firfito waje din
taro na da murnan su
Sai mamakin tsarin gidan nakeyi ina mai kara bin ko ina da kallo muryan mama
naji daga baya na tana fadin kina kallin ikon Allah ko.
Kin ga yadda ubanigji ke nasa ikin haihuwar mace yayi muna rana a gidan nan don
gashi ta mayar damu yan birni a lokaci guda har wutan Nepa mun samu bana.
Nayi dariya nace mama mun samay ku lafiya tace aikece abin gayarwa keda kika sha
hanya mai nisa.
Takalmana na cire na shiga dakin ummi tana zaune saman kujeran da aka saka masu
a falon na rungumo ta sai ta ture ni tana cewa rabani da abin kunya kiji.
Nace kai ummi har yanzu kunyan ne haka takalman da na cire kanne na suka dauka
suna kallo gardama ya kaure a tsakanin su wanan yace kwalba wanan yace roba ne da
filawa cikin sa.
Dukawa nayi ina gaida ummi ga hasken wutan lantarki da ya haska dakin ya
baiyyanar da farin da lafiyan da na kara a lokaci guda.
Daidai inna ta tunkaro dakin a take taji wani irin tsana na ya shiga zuciyar ta
lokaci guda cikin yake tace Safiya ne yau gidan namu.
Da sauri nace eh inna mun samay ku lafiya ina saadatu tace ai tana tafe na barta
daki ne wai kan ta ke ciwo yau nace ayya ai gani tafe in duba ta.
Kanne na suka kwashi kayana zuwa kuryan dakin ummi sai bin ko ina nakeyi da
kallon mamaki acan ma da na shiga an gyara shi tsab ga gado har da sphare din
kujera dogo.
Na aje jakkana na fito zuwa duba saadatu a dakun su sai muka hade da ita ta taso
da kyar muka koma dakin nasu nan naga watau kowa da kalar kayan da aka saka mai a
dakin shi.
Munyi yaushe rabo da saadatun inna tana kurya tana jin mu saadatun ke ce min
komawa zanyi ne ko zan kwana biyu .
A nace cikin dariya a a saade na dawo kenan sai yadda hali yayi kuma tace kice
muna nan ke nan dake kwana biyu nace kwarai da gaske.
Nan dai muka sha hira da ita na tashi ina cewa zan tafi in gaida mama dakin ta.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGN , , , , , , , , , ,


5🧕🏿151
5️⃣
5️⃣
1️⃣ 1️⃣

NOVEL DI NA NA KUDI NE NA FADA TUN FARKO KARKI FITAR KARKI KADA KUMA KI KARANTA
IDAN BAKI BIYA BA, CIN AMANA BIBIYA TAKAI TA INDA BAKIYI TSAMANI BA, , ,


Tun farko na fada maki karki fitar min da novel don karatun ba dole bane ba kowa
nake ba amma nasan Allah ya isana dama bai tafiya ga banza.
Bakiji bake kaida bane don akwai wata mai fitar wa bayan ke ke ce kika fara gani
saura dayan nata sai yafi naki don ko abin ba zai zo mata da dadi ba ita.
Akan novel akan son kai tajawa kanta masifun duniya sai da na fada maku dan Allah
kada ku fitar min don kada in dauki alhakin ku a kaina.
Kullun ina nanata maku kin dauka wasa ne ba abinda zai faru dake har yau kaf
makaranta novel dina ba wanda zaice maki yasan makawa ko ya san ida take da idon
shi hmmm muje zuwa yanzu aka fara ai ya kama binki ke nan ta hanyar dabaki zata ba
yar uwa.
Ganin gidan namu nakeyi kamar bakon wuri a idona don komai ya canza min a idona
sai nake jin wani irin dadi a zuciya ta.
Ranan barci dai ne barawo da ya iya dauka na safiyan fari kiran sallah masalacin
da Sulaiman ya gina wa mutanen unguwar mu ya karade min kunni na dole mutun ya
tashi saboda karan lasifikan da yai yawa.
Duk da bani sallah amma na tashi a lokacin na kewaya na dawo na kwanta ban iya
kwaciya ba na mike zan fita don shara ummi na dake falo kwance ta dakatar dani da
fadin.
Dama kin koma kin kwanta don ko dan Albarkan nan ya rabawa kowa wurin ta don haka
yanzu ma ba komai akeyi a gidan gaba daya ba.
Na koma na kwanta kamar yadda ummi ta umurce sai dai ba barci nayi ba kwantawa
kawai nayi zuciya ta fam da tunane.
Misalin sha daya saura na safe na fito saye cikin kayan barci na da ban cire ba
a falo na samu ummi da kanne na suna karyawan safe tayi masu faten doyan da nazo
masu dashi jiya.
Na fada saman kujeran da babu kowa saman shi don kasa suke zaune dukkan su tare
da yin mika nace duk na gaji kamar nayi wani aiki mai yawa.
Ummi ne tace min ai tafiyan mota mai nisa gajiya yake sawa mutum ajiki na gyara
kwanciya ina fuskantar su dakya nace ai rabin tafiyan a jirgi nayi ummi daga nan
dai zuwa abuja ne ya saukar min da gajiyan.
Tace masu gari yau kece mai tafiya a jirgi yar nan lalai duniya abin da ya baka
tausayi wata rana shi zai baka mamaki.
Kwarai da gaske ummi wallahi ni kaina ganin abin nake kamar a mafalki don nakan
yi tunanen hakan a raina.
A jiuan zuciya naji ummi tayi tace mhmm ai tun dawowan mu gidan nan yau sati uku
ke nan inna ku sai ta baka tausayi don zaman ta a babban gida ta raina kanta sosai
a can don basu raga mata ba ko kadan.
Tace yaya wajan anty naki suna dai lafiya ko bansan adduan da zawa wanan matar
ba a rayuwana sai dai fatan gamawa da duniya lafiya.
Shiru nayi ina mai ci gaba da tunane sai da naji ummi tace yanzu yaushe zaki koma
naga kin kwaso uban kaya kamar baki da niyan komawa can.
Nisawa nayi na dawo daga tunanen da nakeyi nace ummi ba zan koma gidan anty ba
indan ba aure nayi ba in je in gaida ita.
Da sauri ummi tace akwai matsala ke nan a tsakanin ku ganin kanne na dake zaune
sun kallo ni lokaci guda yasa ni cewa babu komai haka dai na yanke a raina.
Shiru naga ummi tayi sai can tace a zubo maki faten ne kishashi da zafin sa tun
baiyi sanyi ba ki kasa sha barshi ummi ban iya cin abu mai nauyi da safen nan.
Sai kaunana tace ai kin san anty Safiya bata son cin abinci ummi kina dai wahal
da kankine sai zuwa rana zakiga tana neman abu mai ruwa ta sha shi ne karin
kumallonta ita.
Ummi na mikewa take fadin mukan na kauye ne sai da abu mai dan nauyi muke jin
dadin karin Safe don badon doyan nan da kika zo muna dashi ba da shin kafa da wake
zan masu da safen nan su karya ko wanan wanan yar sa idon ne nayi aune da ita tana
ferewa wai fate zasu sha da safen nan.
Muryan baba danaji ya nufo kofan mu yasani mikewa na isa kofa ina fadin baba har
ka fito banje mun gaisa ba.
Yace zan fita Safiya jinki shiru yasa na dauka ko barci kikeyi yaya hanya yaya
wajen su hajiyar taki nace suna lafiya sun mace agaida kai.
Yace ina karbawa yaya wajen gwagon naki kina lekasu kuwa na dukar da kai sai yace
aiko baki kyauta ba Safiya ai ba a yanke zumunci tunda ita ta yanke da sai ke ki
raya shi lada zaki samu a wurin Allah.
Nace baba ai zan tafi amma gaskiya ba yanzu ba yanzu ba nafi son sai ina da aure
inje da mijina yafi sauki.
Yace kuma fa kinyi tunane maikyau kuma Allah yasa mu dace yaya shi Alhaji
sulaiman din suna dai lafiya ko na amsa kasa kasa da lafiya yake shima yana gaida
kai baba.
Ya juya yana magana da ummi da take kofan daki hakan yasani mikewa na shige uwar
dakin namu ban zauna ba wanka na shiga don makewayin da ke akwai a dakin kuma da
ruwa a ciki.
Na fito ina shafa mai ummi ta shigo kuryan dakin tana ce min may ke faruwa
tsakanin ki da uwar dakin naki naga ganin kannen ki yasa baki fada min ba.
Nace ummi ba wani matsala sai dai akwai matsala kadan nan dai na fara bata
labarin abinda naji da kunne na anty din tana fadi.
Ta nisa tare da fadin ikon Allah ai tayi kokari ko wanan da datayi Allah ya saka
mata da Alheri ai an gode.
Shi son kai sone ba wanda yaki nasa ya samu bata so ki ba taki dangin mijin ta
don ko sune nata don da su take zama.
Nace aini ummi banga laifin anty ba don sanin ko waye anty uwa danayi don ba
karamar macen duniya bane sosai anty uwa.
Tace Allah yai muna mafi alherin sa nace amin tace yanzu shi may yace a nasa
bangaren nace yace wani sati magabatan shi zasu zo sai a saka ranan aure dayani.
Tace to Allah ya kyauta muna magana kiran wayan shi ya shigo nan ta fice dakin ta
barni ina karba wayan nayi sallama ya karba yace.
Watau kin ga ummi kin manta da kowa ko nace ba hakana bane yanzu na tashi ina
batun kiran ka sai gashi ka kirani yanzu.
Yace yaya gajin hanya don nasan akwai gajiya nace Alhamdullahi yaya na barku
can?
Ya amsa da kalau sai nace yallabai naga ka mayar muna da gida kamar bila ubangiji
Allah ya saka da alheri ya dada daukaka da yalwatan arziki murmushi naji yayi yace
anty ki ta kiraki kuwa ?
Ya kawar da maganan nan take nima murmushin nayi mashi nace baka son godiyan
nawa ke na ko ?
Yace tambayan ki nake yi antyn ki ta kiraki da kika zo arewa?
Nace har yanzu bata kirani ba yace na san za a rina ai, kyale ta, jiya ta
kirani yau ma da safen nan munyi magana da ita.
Sai naji bakina yana tambayan shi may tace ma ?
Sai yace min ina ruwan ki da maganar mu da ita.
Haba uncle dina don Allah yaya kukayi da ita yace maganan dai ne na in rabu dake
in auri diyar hajiya uwa don tafi asali.
To kai may kace mata yace cewa nayi haka shine daidai don dama ke baki
waye ba.
Nace to Allah ya hada kowa da rabon sa yace amin ai ya hada tunda ya hadani dake
kin sace min zuciya yanzu bani jin maganan madam dina kuma.
Murmushi nayi wanda ya baiyanar mashi da jin dadi na a fili tare da sauke ajiyan
zuciya tare dacewa nagode uncle dariya yayi yace aini zan gode maki da baki yarda
sun hadani da ke ba.
Murmushi nayi nace ai ba zasu iya ba don hadin Allah ne bana mutum ba da zasu iya
da sun raba ko tunda duk wanda aka fadawa irin kazafin da sukai min dole ya dauka
gaskiya ne.
Ya katse ni da cewa ai baki san wani abu ba nace ina jinka.
Yace ai tunda ta gabatar min dake da farko hankali na ya kwanta da zancen ki don
haka ma daddy su twins shima ya yaba da hankalin ki.
Banga abinda zaisa yanzu daga baya ba kuma ta kawo min zancen wata na dai ce da
ita haka ne daidai sai idan lokaci yayi zata sani.
Mun dauki lokaci muna waya dashi kamar ba kudi yake kashewa ba sai da ya gaji don
kanshi yai min sallama na tashi na karasa shiri na dakin mama na fara shiga muka
gaisa muka dan taba hira sai na wuce dakin inna inda na samu saadatu ita kadai a
dakin wai inna tafita unguwa.
Nan na sake jikina muka dauki lokaci muna hira da ita nake tabayan ta fanin Isah
dayai mata ciki take fada min bata da labarin shi.
Nace baya kawo maki komai ne tace tun wanan lokacin bai kara kulata ba kuma ba
wanda yai masa magana akai ana batun ginan gidan mu.
Da yaya sani ya shigo na tuntube shi da zancen sai cewa yayi min ai shi ba
abinda ke gaban shi ke nan ba nace haba yaya sani idan baku tsaya muna tsaye ga
alamarin mu ba wa zai tsaya muna akai yace zai duba yagani yadda za a yi.
Anan muka bar zancen ban jima da fita dakin nasu ba inna ta dawo gidan tana
shigowa sai ta fara budan hancin ta tana shakan kamshina dana bari dakin tace.
Safiya ta shigo dakin nan halan sai Saade tace eh tace karuwan banza ina shigowa
naji kamshin turaren ta.
Haba inna Safiyar ce kuma karuwa Saa ta fada mata haka na tace idan ba karuwa bane
may nena ita uban wa take nema a birni.
Abinda kikeyi gaskiya inna baida kyau shiyasa kullun bamu ganin karuwa ga
alamarin mu don bakin hassada irin naki.
Aiko tayi cikin Saade din da fitina ita kuma kamar mai jiran uwa nan suka shiga
yaba ma juna bakar magana har ya jawo hankalin mutanen gida aka tsaya sauraren ta
yaya Nura da yaya Sani ne suka shigo gida suke tambayan ba asin maganan.
Inna ta kama inda inda sai Saaden ne ta fada masu abinda ya hada fadan da sukeyi
daidai ina fitowa daga daki kenan maganan ya daki kunne na.
Cak na tsaya raina ya baci sai yaya nura ne yace in ma karuwanci Safiya ke yi a
birni ai anci albarkacin karuwancin ta a gidan nan.
Yaya Sani ya karbe da fadin wallahi fa ke yar taki mai take zaman suna takeyi
maki a daki da tsohon ciki komay ba gara safiya ba kowa ya san alherin ta ne ya
kaita ga haka.
Wallahi inna idan kice bazaki bar halin nan ba watarana sai kinji kunya ba kadan
ba zuwan Safiya dakin ki alheri ya kawo ta ba tsiya ba.
Don zuwa tayi ai magana da Isah asan halin da Saadatu ke ciki don bai waiwaye ta
ba har yau mama tace kai kedai Rakiya halin ki baiyi ba wallahi.
Safiya tayi maki kama da wacce take karuwan ci koda ba a ganin zuciyar mutum ai
abin duniya baya boyuwa da muji tun tuni.
Daki na koma van iya tsayawa na saurari sauran maganan ba sai dai na sa a raina
cewa ba zan sake shiga dakin inna ba komai ya faru kuwa.
Har yamma naji anty bata kirani ba don haka na dauki waya na kirata amma har
wayan ya katse bata dauka ba.
Ban kara kiranta ba da dare muna zaune a dakin mu sai ga baba ya aiko a kira
masa ummi ta dan dade wurin sa ta dawo muna hira da kanne na sai tambayan ta kauna
tayi tace halan baba yaji zancen maganan dazu ne ummi ?
Tace ina ruwan ki sai kin san abinda naje yi gunsa nace kai kedai baki da kunya
Aisha may zai kara ki idan kin ji ni ban ma son baba yaji zancen tace sai dai kada
a kara don Nura ya tare shi da zancen a waje.
Ina ga ki je gun su kawun ki kafin bakin ki su iso kin dawo zaifi nace to ummi
zan tafi amma ba don naso a raina ba don dai ta ce in je ne kawai ba yarda zanyi.
Kwana biyu da zuwa na na shirya dani da kani na sai kyauyen su ummi na ida
mahaifanta suke da zama.
Tafiyan safe mukayi don haka muka isa da wuri mun samu karbuwa na mutunci a wurin
su aka kai muna kayan mu dakin kakan mu mace .
Bayan muci mun sha daga abincin su da suka fi karfi suka gabatar muna dashi muka
zauna a na gaigaisawa da yan uwa.
Sai yamma mazajen suka dawo daga gonakin su wanda dashi suka dogora suna ci suna
sha daga gare shi sai kiwo da suke hadawa dashi.
Kakan mu ne na karshen shigowa gida sai da ya huta mukaje gaida shi bayan mun
gaisa ya tambaye mu mutanen gida.
Yake tambayana zancen aure nace insha Allahu malam ba za a dauki lokaci

49 / 87