Advertisements
Chapter 34 Reading Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   34 / 87

99K to 102K   out of 258.3K words

saya a take fati ta shiga rokon ta wai taje da
ita.
Tace karatun ki fa fati kina fa wasa da karatu gashi kun kusa rubuta jerabawan
fita ke bakiyi ma kanki fada ne wai kamarki har yanzu a secondry school ?
Nan ta turo baki gaba tana fadin na dai gane kin fi son safiya damu a gidan nan
komai sai kice safiya ita kadai.
Tace dole ne in ce safiya don tafiku hankali da tunanen abinda ya kamata ko ruwa
kuna iya ba mutum ne in ba ya kama maku dole ba.
Faiza ma ta marairaice mata saida tace duk su shirya mu tafi tare sannan aka
samu lafiya don da Fati ta hau sosai ga maganan.
Kowa ya shiga shirin tafiya don tace sako zamuyi mu tafi kala uku kawai na dauka
koshi dogayen riguna ne kawai na zaba.
Tun da safe muka kama hanyan abuja a mota mukai tafiyan don mijin ta baya nan
suna ruwa wurin aikin shi basu fitowa sai bayan watanni a ruwan shiyasa ma bai faye
zama a gidan ba.
Gidan su na abuja muka sauka wanda shi mijin tane wai yake dashi don harda funke
mukayi tafiyan bamu bar kowa a gida ba.
Gidane mai dauke da dakuna hudu da falo daya na maigidan inda ta zauna a ciki
sai dayan wanda fati da Faiza zasu zauna ni da yara tace mu shiga guda sai mu bar
ma funke na farin shigowa wanda dama saboda masu aiki akayi shi.
Ba wani hira don kowa na da gajiya tare dashi wanka kawai mukayi sai abincin da
aka kawo muna daga wani gidan abinci ina jin Faiza da fati na ta santin abincin don
dadin shi niko takura bai bari naci sosai ba don na lura dukkan su biyu kamar yanzu
sun tsane ni a gidan don yawan nuna mani kulan da maigidan namu takeyi ko a gaban
kowa.
Na riga kowa shigewa ashe sulaiman din yazo gidan bayan na shiga barci nan Fati
ta kama rawan kai saida anty ta tura ta ciki ta basu wuri.
Washe gari tun da safe da ta fita bata dawo ba sai wurare karfe hudu ta dawo
gidan nan ma bata huta ba don wasu suka zo suna tsarare dasu.
Har na kwanta sai ga anty dakin na mu hannuta rike da tasbaha tana ja shiyasa
nake son ta don wayen wata da tsabgogin gabanta bai hanata yin ibadan ta sam.
Mikewa nayi zaune daga kwanciyan da nake ta kalle ni tace wai ko kin dauko kayan
kwarai kuwa Safiya don taro ne na masu hannu da shuni za a yi.
Nace anty na dauko wanan riga ne da kika sayo muna ranan na fadi tare da kallon
ta don jin may zata fada gamay da shi.
Cike da tsukana tace min Safiya ai da kin tona min asiri a cikin taro da sai in
nuna ba tare dani kike ba a wurin kawai kisa mutane su raina min da wayo ?
Dariya nayi itama abin ya bata dariya don jin nace anty wanan riga mai balain
kyau.
Tace kin ga ni yanzu ma fita nazo kirakani muyi dama nayi tunanen hakan ki shirya
ina fitowa yanzu zamu fita da faiza ba zan je da wanan mai rawan kan tsiya ba ta
bani kunya.
Ashe harta fada ma Faiza ko koda na fito faiza na falo zaune tana kallo hijjab da
dogon riga nasa ta kalleni ta wani kwashe da dariya .
Sai kuma tace min mutumiyar na ciki tana fushi wai za a fita damu bada itaba
kafin in magana sai ga ta tafito tana saka ma kofa key tare da kiran Funke tana
cewa ta kula mata da yara da sukai barci tun da magariba.
Na muka fita tare da rufo kofan gidan mukai ma Funke sai mun dawo wata mota
baka muka samu waje a kunne yana jiran fitowan mu.
Baya muka zauna inda sai wani kamshi da ban taba ji ba ya daki hancina ga sanyi
AC mota suka hade suna bada wani irin yanayi a motar, ita ta zauna gaba tare da
driver muka kama hanya fita daga gidan kallon titi nakeyi inda naji Faiza tace ina
wuni yaya Sulaiman .
Sai lokacin na dawo daga tunanena nace dashi ina wuni ya amsa muna a tare lokaci
guda anty ke ta hira sai eh ko aa yake ce mata.
Tafiya mukayi mai nisa sai gamu bakin wani shago maigirma anan muka firfito inda
muka barshi a cikin motar zaune muka fara shiga mu da anty.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , ,


3️⃣5️⃣3️⃣
3️⃣
🧕🏿 5️⃣5️⃣3️⃣


YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA DON BA A YAFE
MAKI BA HAKKIN KARANTAWA BA BIYA.



Tunda nake ban taba zuwa wuri irin wannan ba a rayuwa na sai dai ban nuna ba saboda
natsuwan da Allah yai min.
Sune a gaba ina binsu baya a hankali anty tace mu diba mu gani sai ban tafiba
nabi bayan anty din wasu jakka da ta kalma take dubawa bata san ina bayanta ba.
Sai nace kai anty wanan kayan zaiwa su yan biyu kyawo sosai ta juyo da sauri tana
cemin har kin duba ne?
Jin nai shiru yasa ta juyowa tana fuskanta tana tare da cewa mai kika zaba ne
nace ban dauki komai ba kai ta girgiza kawai taci gaba da daukan abinda take so.
Tafiya takeyi tana fadin sai ki zabar ma diyan naki kayan a tare mukaje wurin
kayan yara na fara duba masu sai kuma na gaza itace tai ta zama musu kalloli masu
kyau.
Batai min magana ba sai wucewa da tayi layin riguna ina biye da ita can ma zaban
taitayi tare da atamfofi.
Ni dai har muka gama a shagon banga sulaiman din ba sai nai zaton ya ajemu ya
tafi ne to wa zai mai damu gida daren nan haka.
Acan wurin biyan kudi muka hade dashi bai sai komai ba sai turare guda biyu ya
dauka bazaka ce tare muke dashi ba yadda ya nuna a wurin.
Ni dai kafana ya gaji da tsayawa sai na fita daga shago na samu bayan wani mota
na jigina jikina dashi.
Sun gama suka kwaso kaya niki niki suka fito zuwa motar na tako inda suke na
samay su ta dago tana ceman yayi da ake sakayan a both din motan da muka zo dashi.
May yasa kika fito daga ciki nace na zata magana zasuyi ai shine na basu wuri
tsaki taja kwai tana bude kofan motan muma muka nufu motar muna budewa.
Har muka iso gida ba wanda yai magana a tsakanin ni da Faiza sai da motar ta
tsaya ne muka fito nan muka fara jidan kayan zuwa ciki dasu sai a lokacin naga ashe
ba karamin sayaya mukayi ba .
Dakin anty muka nufa dan kai kayan can amma sai tace mu zube su a falo na ta
zauna tare da jawo wani laida sai naga ashe nama ne gadade suka saya a wurin .
Tana fitar da kayan tana cin nama hankali kwance ta miko min wani laida shake da
kaya tana cewa ungo naki matsoraciya kawai ta kuma mika min wani karamin laida da
kayan sanyi da naman ciki faiza kuma ta dauki nata zuwa dakin su kowa ya shige muka
kashe wuta muka watse wurin.
Da safe kowan mu ya makara don haka bamu fito da wuri ba ni dai ina kwance bayan
nayi sallah sai na koma barci.
Banyi nisa da barcin ba sai ga anty ta shigo daki da hijjab din ta tayar dani
tayi na mike zaune tare da gaisheta da kwana takalleni tace safiya kinyi sallah
kuwa ?
A girmamay nace nayi sallah anty tun dazun sai tace madalla tashi mu fita gidan
nan tun yan bakin nan basu tashi ba mu fita daga gidan nan maza ki tayar min da wa
yan nan sarakunan barcin yanzu mu tafi.
Har muka gama muka fice daga gidan basu sani ba wurin gyaran gashi suka tafi don
har dani anyi mawa ina ban so amma sai da anty tasa akaimin gyaran na koma kamar
bani ba.
Ni kaina nasan gyaran ya fitar min da kyaun surar fuskana don ban taba gyara irin
haka ba bamu dawo gida ba sai shabiyu da rabi muka shigo gidan.
Mun samu sun cika fam sai dai ba mai iya yin magana a cikin su dole kuma suke
gyashe mu da dawowa .
Nan muka zube a falo tare da muna neman abinci ina yawan mamakin yadda sam anty
bata kyaman mu,amula dani kamar yadda gidan mu suke gwada min.
Sai da muka gama ne sai Faiza ta kula da gyaran gashin da akai mun din tace wai
dama anty wurin gyaran kai kuka tafi ba tare da muba.
Tace fuska gimtse eh idan kun shirya driver yana waje sai ya kai ku kuma bata da
daman da zatai mata wani korafi ba.
Sai harare harare suke aikamin a fakaice bandai kula suba anty ta shige dakin ta
sai lokacin Faiza ta samu yi min magana akan fitan mu nace nine nace zan bita da
zata fita tace idan kun tashi zaku tafi.
Fitowan anty ne ya hana maganan yayi nisa sosai ta fito tana cewa da au baku
tashi kun shirya bane ke kuma Safiya tashi zakiyi ki sallah sai mu fara hada kayan
gift din nan tun ba ai yawa ba ki kira funke ta taimaka maki hadawa.
Su idan sun dawo sai su karasa a inda kuka tsaya din don takwas za a fara program
din ban son a samu matsala a wurin mu ko kadan.
Mikewa nayi din zuwa sallah nake cewa da su idan sun wuce sai sun dawo ni zan
shiga in sallah faiza ne kawai ta amsa min ciki ciki na shige abina.
Sallah nayi na fito anty bata falo don haka na bita dakin ta a inda na samay ta
zaune a kasa inda ta idar da sallah tace yauwa Safiya kin ga dauko wancan buhun ki
miko min.
Koma da yake ai shi uban gayyan yace ba zai gayyaci mutane dayawa ba a gurin sai
nine ma na gayyato mai abokaina da mazan su sai abokan mai gidan da suke garin nan.
Nace haka nake ganin sa kamar baida rigima ai tace haka yake sai kuma wanan
kaddara da samay shi ya kara sawa yana gudun mutane yanzu.
Kamar ince wani kaddarane anty sai naga ni may ya shafe ni kuma da zan je wani
tambayan abinda bai shafe ni ba can.
Na miko mata inda na aje a gabanta sai tace ai ma mu tafi falo kwaso su duka ki
fito min dasu tamike tana cewa ko dai in tai maka maki ne da kwasa.
Ida da sauri nace haba anty barshi kawai zan iya ai basu da wani yawa ta fice
inda na fara kin kimo wa zuwa falon inda har ta zauna ko kasa saman center carpet.
Na dauko sauran na samu sufi na farkon nauyi haka dai na ta kwasowa zuwa falon
har na gama.
Ba bata lokaci muka fara hadawa dani da funke tana directing din mu ina mamaki a
raina wai bukin bude gida da company akewa wanan gift din kamar na wani buki can da
ya shahara nace kai masu kudi na shagalin su.
Anty ne ke fadin ko basu yi ba a kara ne safiya naga abin bai wani cika ido ba
sosai nace wai anty duk wanan za a ace bai cika ido ba tace kin ko san wa yanda
muka gaiyata a wurin ne.
Jakka ne dan na tafiya sai towel da sabule da turare da man shafi da su drinks da
snack muke zubawa ako wani bag.
Tsab muka shirya komai yadda ya dace sai tace funke tai ta kwasa zuwa mota inda
driver da ya kai su faiza yadawo yana waje sai da aka gama kwasa ta ce in fito mu
tafi inda za a kai.
Na gaji amma babu halin in nuna mata gajiya na don ban so ta fahinci hakan daga
gare ni a tare muka fito inda yaran har sun fice waje ko.
Nan mu ka kama hanya sai wani unguwa mai nisa tsarin unguwar yafi na su anty
haduwa sosai don ginane sai kace a kasan turai mutum yake ga ba yawan hayani ya a
wurin ko wani gida a rufe yake.
Wani tsararen gida muka shiga da motan mu tace bude ido da kyau kiga gidan da
sulaiman ya kera dan dawowan nan nasu kai kudi suna aiki wallahi.
Nai mamakin jin kalaman anty tace wallahi sulaiman mutum ne dake tsaya ga neman
na kasa yaro ne wanda tun farko bai tsaya jiran sai ambashi ba haka ya taso da
neman na kansa.
Gashi maraya ne bai tashi da mahaifin shi ba don tun yana matakin karatun shi na
farko mahaifin shi ya rasu sanadiyan hatsarin mota.
Dan dukiyan da aka raba masu ne a wanan lokacin ya fara juyawa shine Allah yasa
masa albarka har yakai haka yanzu sai dai ya taba aure duka duka watan su shida
suka rabu da matar.
Motan mu ne ya tsaya a ciki gidan koma suna tsaye a waje da wasu abokan shi shi
ya dakatar da labarin shi da take bani a motan .
Shi da kansa ne yazo ya bude mata motar muka firfito nan abokan shi suka shiga
gaida ita wanda da gani sun san ta dama.
Ciki muka shiga nikan ba boyo dama bakauya nake nan ko nai ta zuba kauyan ci
wurin kalle kallen gidan.
Nayi mamaki wai wanan dai sulaiman din ne mai wanan gidan haka dana gani mun
shiga mun fita ko ina sai faman yaba mai anty keyi.
Niko duk na takura a wurin don ban saba hurda da maza irin hakaba don yawan kalon
da suke min din yayi wa a gani na.
Nuna mata nayi na gaji sai tace inje in zauna a mamakeken falon in jira su a nan
tare da twins din ta muka zauna a falon nan na ci gaba da ba ido abinci don in samu
na karaswa.
Wayana ne yai tsuwa na dako da sauri inda naga ummi na ce ke kirana a lokacin
nace Allah sarki ummi taji shiru yau shine ta kira ni don kaida ne a rana sai na
kirasu kusan sau biyu ko uku inji lafiyan su.
Nan nake fada mata bamu lagos mun zo Abuja ne da anty wurin bukin bude company
kanin mijin ta da za a yi yau tace shi gidan harda wani buki ake mai kuma ?
Dariya ummi ta bani ban san lokacin da na bude baki ina kwasan dariya ba a daidai
nan suka fito daga daki shine agaba sauran na bin shi a baya.
Nan nai saurin gimtsewa kamar bani bace mai yin dariyan a farko muna ta magana da
ummi inda suka zauna sai na kasa sakewa a wurin.
Karshe dai don in fitar da zargi sai nace wa anty ga ummina su gaisa da ita ta
karbi wayan tana murmushi nan suka gaisa ina jin anty nace mata gata nan ina ta
bata wahala bamu zauna ba yau tun safe ai Safiya tana da kokari wallahi naji dadin
zama da ita sosai ummi.
Sun gama gaisawa ta bani wayan nai mata sallama tare da kashe wayan nawa nan na
zauna a takure a cikin su inda anty ta umurce ni da in bude jaka guda suga yadda
muka hada kayan ciki.
Mikewa nayi ina gyara gulyalena dake zamewa akaina na dauko jakka guda tare da
bude masu sai naji sulaiman din yace kai basuyi kadan ba.
Ban san lokacin da na dago na dan kalle shi ba sai naji anty din tace gata nan ai
nace a kara don nasan halinka tace wai ya isa hakana.
Yace No if possible don Allah a kara mana why not na mata a saka zanuwa a cikin
sa na maza ku saka masu shadda a ciki kai hamza kaje ka dauko su a cikin dakin nan
a zuba.
Daga haka suka fice aka barmu nan muka ci gaba da aikin kara kayan bamu dawo ba
sai shida na yamma don mu shirya.
Mun dawo mun samu su Fati na gida itakan anty dakin ta shige tana cewa mu shirya
bakwai zamu bar gidan.
A kusan tare suke tambaya na ina muka tafi haka nace mun je inda za ai event din
ne don hada wurin sai ita Fati tai tsaki tace to mu wai may ya kawo mune tunda ba a
yi damu.
Faiza ne tace a a zaki iya wanan jigilan da Safiya keyi haka ba gajiya tace wane
ni kuwa sai fatin tace wai mun ga sulaiman a wurin nace a a bamu ganshi ba ai.
Tace ai gara ma da ban tafi ba don ni shi kadai nake son gani dama ban damu da
wasu can ba.
Sai faizan ta harare ta tace hum,umm ashe kina da aiki indai wanan miskilin ne
mai yi kamar yana jin warin mata tace wasu matan ba.
Ni dai ban zauna ba shiga nayi sai na samu kaina da dan kwantawa don a gajiye
nake so sai yaran ne da suka shigo na tashi dole na fara shirya su.
Ina cikin shirya sune anty ta leko tace da ni aa kunanan da mutanen naki kuna
ta fama yauwa safiya sannu da kokari kiyi ki gama sai kema ki shirya.
Tace karbi nan nasan ki da sin dogon riga shiyasa na sayo maki ban baki bane don
wa yan nan yan sa idon kada su damay ni da korafin banza.
Na amsa hannu bibiyu ina godiya tace kin ga don Allah ni kuyi sauri bamu da
lokaci ban so ma in kai yanzu ba a nan bamu tafi ba.
Nan tafita ta barni ina duba kyawon rigan data bani rigan yakai riga wurin haduwa
sosai na ce a raina

34 / 87