Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
zai buge yaya saadu ya rufe da duka.
Ranan iyakan bacin ranshi na gani a gidan ni kuma naki fadin inda na samu maganin
na tsaya kai da fata maganin ya dade min a cikin jakkana kuma ba wanda ya bani
maganin saye kawai nayi don na san shi.
Naki fadi ne don kada naja wa matar mutane jiddali daga taimako nasan kuma idan
na fadi gaskiya abin zai iya shafan samira duk da bata da laifi aciki amma muna
tare aka bani.
Har magariba ya gwauta muna wurin zaune yaya Saadu da mommy sai bashi hakuri suke
yi suna fadin nayi kuskure sosai na bashi hakkuri.
Nace ni ban sha ba koda yake fadin nasha ban sha maganin ba aida cikin ya fita
inda nasha din yace cikin dai yafi karfin ki ne yaki fita.
Nace ban dai so zubar dashi ba da babu abinda zai hana na zubar din yace yaya
Saadu kana dai jin abinda take fadi.
Tayi laifi ban isa ta bani hakkuri akan abinda tayi min din nace ni ban san nayi
laifi ba tunda ban sha komai ba.
Yaya Saadu ya tursasa akan in bashi hakkuri a gaban nace nayi kuskure ka yafe
min daki ya wuce zuciyar shi nayi mai kuna sai tuna maganan hajiya baaba yake yi da
tace mai ya rage matsamin don zan iya bijere mai daga baya.
Yanzu ko gashi ya ga na fara din wai safiya ce yake fadi take fadi har tana
ikirarin na rushe gidan da nayiwa mahaifanta na mayar masu da kangon su.
Kwafa yayi yace dani kike wasa yarinya zan nuna maki kuren ki a gidan nan zaki
san kin taba ni don sai kin gane kuren ki.
Yana alwala yana maganan zuci a falo kuma yaya saadune yayi min fada sosai akan
yadda nayi ban kyauta ba nayi laifi kawai in bashi hakkuri.
Nace yaya kanaji fa yana fadin ban kwana mashi gida yau akan maganan ga zai ta
fadin haka in ba dama ya gaji dani bane yana son mafita akaina.
A daidai lokaxin ya fito daga dakin shi ya kallemu kamar harara yana fadin Saadu
muje muyi sallah rabu da ita mommy jekiyi sallah lokaci ya kure ko.
Yaya Saadu ya kalleni yana mikewa yace safiya yaushe kika kuma haka ne wai duk
kin bi kin tada hankalin mutane a lokaci daya haka.
Don Allah ki kara bashi hakkuri idan na wuce don ba lalai ne in dawo tanan ba
yayiwa mommy saida safe ya fice daga gidan, itama mommy tashi tayi zuwa sallah
inda na dan dade zaune ina tuna irin karfin halin dana rufe idona nayi masu.
Mikewa nayi zuwa sallah nima ban fito don ishai yayi nan na zauna abina sai su
hindatu ne suka shigo dakin suna min hira wanda ba fahintar su ma nakeyi ba.
Fitar maimu sai gata ta dawo tana fada min anty baban Abba ya dawo yana falo
zaune nace ku tafi ku gaida shi yau banjin dadin jikinane.
Yaran suka fita zuwa wurin su suna gaida shi da dawowa ya amsa masu fuska a sake
kamar yadda ya saba yi dasu kullun.
Nan suka dan zauna suna mashi hira suke fada mai antyn mu tace yau jikin ta yana
damun ta bata iya fitowa Allah ya sauwaka yace ai na bata magani dazun.
Mommy ce ta kirasu suka shige ciki wurin ta ya gama abinda yake yi ya shige
dakin shi batare da ko waigowa kofana ba.
Nima nasan da hakan shiyasa nayi zama na a daki ban fita don yasan nima ina jan
zancen na gama har na kwanta a lokacin naja bargo na rufe kaina a ciki.
Da safe Samira ne tazo gidan dubani da kuma tambayana yadda akayi haka ya faru
har na bari uncle yaga inda na aje maganin.
Nace kedai bari Samira baban Abba yakai dan halas wai mutumin da bai taba, taba
min jakka ba shine wai da yake Allah yayi asirina zai tono sai gashi yaje daukan
maganin da muka karbo asibiti a cikin jakka ta.
Na manta shaf wallahi da wanan maganin ai da na yunkura na tashi komai ciwon da
nake ji na rufawa kaina asiri.
Tace ke dai bari aini da yayan ki ya fara min maganan baki ga yadda na tsure ba
ina gudun suna na yafito a maganan tawa ta samay ni, in shiga uku gashi muna
alkunya da mutum da ina zan saka kaina.
Dariya nayi mata nace ni zan fara ne in fadi gaskiya da fa har gidan matan nan
yana iya zuwa yai mata cin mutum ci shiyasa na kafe dacewa dama nasan maganin na
dade da sayan shi.
Zai kuma iya hani zuwa gyaran jiki shiyasa nayi mai borin kunya na labe ga zancen
gida don yabar maganan.
Kuma nasan abinda yasa yayi sanyi ke nan a yadda ya dauki niyar ci mun mutunci
ido rufe tace kai safiya sai kika lauye bawan Allah da jijiyoyin shi.
Nace ke kuwa kin san yadda uncle ya hau har fa maru biyu ya bani masu kyau rabona
da duka tun gidan yaya Ahmed fa samira.
Tace ni banga dalilin ki sin zubar da cikin nan ba safiya baki rasa ci ba baki
rasa shaba a gidan nan wanda zai gina maki jiki.
Don may zaki nace sai kin halaka dan cikin ki kika sani ko gwauna ko shugaban kasa
kika samo muna zakiyi muna sawalwalin tsiya haka.
Nace samira ai yanzu na yi nadama sosai yadda naga uncle ya kwalafa rai ga
haihuwan nan haka yasa jikina yayi sanyi wallahi.
Tace yanzu dubara ya saura gare ki ai sai ki san yadda zaki bashi hakkuri ya
sauko maki don nasan yanzu ya hau sosai dake a gidan nan.
Nace ya hau kan zan jira sai ya sauka don yanzu yi mashi magana wani jidalin zan
kara jawowa kaina barshi mu tafi haka har ya sauko da kan shi dai.
Tace kina ganin haka zaifi safiya nace ni na san halin uncle Samira barshi dai
muje a hakan tace to shike nan ai mai daki shiyasan inda ruwa ke yoyo.
Tace sai da na fada maki tun farko safiya kada ki yunkurin zubar da cikin nan don
dan halas sai an haife shi tunda an samu.
Wasa wasa mun share wurin sati biyu yanzun ba mai kula wani sai dai zan mai ina
kwana ya amsa min a dake ba sakin fuska ko kadan.
Tun ina dari dari har abin yazo ya daina damuna tunda ban rasa ci da sha ba ba
kuma korana yayi a gidan shi ba.
Sai dai wani lokaci abin yakan damay ni amma yaya zanyi tunda yaki tsayawa mu
fahinci juna har in bashi hakuri ga kuskure na.
Allah ya gani tsoro nake ji don abin da ya samu kawata shine ya tsaya min a raina
sosai saboda irin haka tayi tasha da kyat.
YAR UWA BA SAI KIN RUBUTA BATSA BA NOVEL DIN KI ZAI SAMU KARBUWA, KE MAI GYARA
TARBIYAR AL, UMMA CE BA MAI BATA WA BA.
KIN SAN YARA NAWA NOVEL DIN KI YA HALAKA DA WA YAN DA KIKA SAKA ZINA TA SANADIN
NOVEL DIN KI NA BATSA.
KI WA KANKI FADA TUN LOKACI BAI DAINA YI DAKE BA ABIN KWARAI AKE YAYI BA NA BANZA
BA, , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/21/20, 10:00 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RARYUWA, , , , , , , , , ,
8️⃣6️⃣8️⃣
🧕6️⃣8️⃣6️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Yau ya kama jumma, a tunda safe ina shirya yan kanne da zasu makaranta don dole duk
safe koni ko mummy daya ya tsaya wurin su don su shirya.
Idan ba haka sai su tsaya shiririta da gardaman banza har su makara don yanzu
sun rage zagwadi son makarantar da sukeyi .
Tunda sukaji baba ya yarda da zaman su a guri don da farko kin yarda yayi lokacin
da hutun su ya kare yaji shiru sai gashi ya bugo min waya wai baiga yaran shi ba.
Nace baba yaran ka suna nan lafiya makaranta ne ya boye su yace wani irin
makaranta kuma nace ai mun saka su school a nan din dana boko dana muhamdiya.
Yace bam yarda da wanan tsari ba don ba haka mukayi dake ba nace baba na sani
amma kayi hakkuri da hakan da nayi.
Fada yayi sosai a wayan ina sauraren shi saida ya gama nace baba nasan munyi
kuskuren yin haka da mukayi.
Amma ba nayi bane don mu raina maka nayi ne don taimaka wa rayuwan mu baki daya
saboda indan suna nan zasu samu karatu mai inganci da ci gaban rayuwa.
Kayi hakkuri baba don Allah kabar min su anan don zama su a nan din yana da
matukar muhinman sosai yace.
Safiya ai wanan rashin hankalin ne ki dauki yara har biyu ki kai wa mutum gida
wanan ya zama rashin hankali ai.
Baba shi ya yarda da zaman su don shi da kan sa ya kaisu makaranta mai tsada ta
kudo anan din munyi kuskure ba zamu kara ba in Allah ya yarda.
Bayan ya gama saurare na ya kasha wayan ya nufi wurin su ummi da fada mama ya
fara kira sai ummi suka fito yake fadin.
Ashe kun hada kai da yarinyar nan safiya ne ta yaudareni ta kwashe yaran nan, ta
tafi dasu su zauna a wurin ta ne ?
Haba malam ai wanan abin kamar taimokan ne tayi inji mama ta katse shi ga
maganan shi yace ke dakata min.
Taimakon may nace na gaza da "ya"ya ne ita a ina ta taso in ba nan din ba ummi
tace amma ni wanan abin sai naga kamar taimakon kane yarinyar nan tayi banga abin
fada ba don safiya ta dauki kannen ta ta kaisu gare ta.
Mijin ta baiyi fadan haka na sai kaine zakiyi haka dakan shi ya bata baki kan
hakan yace ke nan da sanin ku aka yaudare ni ?
Yaudara kuma malam babu yau dara acikin hakan wata rana hakan zai maka dadi yaya
Nura ne yashigo gida a lokacin yake tambayan may ke faruwa.
Ummi ke fada mai yace baba koni safiya zata dauka yanzu ai zuwa zanyi da gudu
balle maimu da hindatu yara nacen cikin daulan duniya za ai masu bakin ciki kuma.
Kaifa mahaukacine sakaran banza kawai waye zai masu bakin ciki din niko uwar ka
ya wuce yana a bakin ciki za ai masu mana mai kaya ya daure sai mai cira ke wassh
Allah.
Uwarka nace ya nufe shi gadan gadan shiko ya fice gidan yana dariya wanan abin
yasa su ummi saurin watse wa gaban shi yaci fadan shi yana fadin ai zai gamu dani
ne.
Murmushi nayi da tuna wanan magana da ummi ta fada min ya faru a gidan mu sauri
muke mu tafi sai Abba ya kama kuka ina jin mommy tana lalashin shi yaki shiru.
Uncle ne ya leko daga dakin shi yana fadin wai may yaron nan yake ma kuka haka ne
ke kuma baki dubashi ba ?
Bai mai magana ba sai wucewa da nayi dakin kawai na samu mommy tana lalashin shi
yaki shiru daukan shi nayi ina lalashi bai yi shiru ba.
Mummy ta tara hannun yaki zuwa wurin ta dole sai na goya shi don yayi shiru
saboda mommy ta saba mai da goyo yau kuma bata jin dadin jikin ta ne.
Ya fito daukan ruwa ya samu su maimu zaune falo suna jirana yake fadin baku tafi
bane har bakwai da minti goma yanzu suka ce anty muke jira ta fito Abba ne ke kuka
yaki yin shiru.
Sai gani na fito dakin mommy da goyon shi da goran ruwa a hannun shi ya dago yana
kallona goye da yaron a bayana.
May ya samay shine yau ya fadi yana kallo na cikin dakewa nace fitane kawai yake
ji mommy bata jin dadi tun jiya miko min shi nan yace dani ina kokarin sance yaron
a baya ma in mika mashi sai yaton yaki ya kara lafewa.
Ke mi ko min shi yace goyon nan zai iya maki illar koda dama ba son cikin kikeyi
ba nace yake zaune a jikina idan ban so ka barshi kawai mutafi in kaisu in dawo.
Barshi in kaisu naji yace tare da fadin ku tashi kada ku makara sosai yaran suka
mike sai maimu ke fadin anty kudin exam din fa uncle zai bada ?
Nace ku bari monday zanje in biya maku idan na kaiku yake cewa nawane kudin suka
ce five hundred kowan mu fita yayi baiyi magana ba ya wuce suna biye dashi a baya.
Nan suka fice na sauke ajiyan zuciya yaushe rabon da yayi min magana haka sai yau
sanadin Abba dake kuka a gidan ya jawo yayi min magana.
Da motana ya fita dasu bai jima ba ya dawo ina zaune goye da Abba a bayana ya
shigo wurin mu yayo direct yana fadin .
Babana may ya hadaka da mommy yau kake fushi haka ban san ka da fushi na fa ya
dan duka yana yiwa yaron wasa sai kuma yace.
Kin bashi abinci yaci ko yunwa yake ji kai na girgiza mai yace ki bashi a gani ko
yunwa yake ji don yanzu dai madara ba isan shi zaiyi ba.
Mikewa nayi zuwa inda Nura tafara jera abincin na dibo mashi dankali kadan na
dawo ina sance yaron sai ya karbe shi a bayana shi da kan shi yake bashi abincin
yaron yana karba.
Yace don Allah ku bar barin shi da yunwa haka yaya madara kawai zai ishi yaro
dan wata tara yanzu nace ya dai so cin abincin ne yanzu amma in an bashi sai yaga
dama yake ci.
To na dai ce a dinga bashi in baici a barshi daga yau naji nace dashi ya gama sai
kuma yace sai in kara goya shi yasa muna fitina a wurin yana jawo zanin da na sance
goyon shi a bayana.
Wuf uncle ya dauki yaron yayi ciki dashi murmushi nayi bayan sun shige daki da
yaron wanda nasan ya fara saukowa ne da kanshi da ina binshi ina bashi hakkuri da
yanzu bai isa saukowa ba haka.
Ya fito cikin shirin fita yake cewa Abba na nace daki yana barci ki lakashi don
kada ya tashi yana kuka ya fado ya fada ba wani sakin fuska gare shi.
Fita yayi daga gidan mukai mai a dawo lafiya bayan awa daya ne naje dakin leka
yadon yana kwance yana barci abinshi hankali kwance har lokacin nan nabi dakin da
kallo yayi kaca kaca sai na fara gyara bathroom na fito na gyara ko ina na goge na
sa mai room fresh yaron ya tashi kafin in gama.
Na sauke shi na canza mai zanin gadon na jawo mai kofa sha biyu daidai na fito
zuwa dauko su maimu ni da Abba ne muka fita na dauko su tare motan mu ya kunno kai
kwanan gidan.
Bayan mun shiga ciki na rufe mota bai fito ba har na shiga gida sai can gashi ya
shigo muna falo zaune muna cin marasa gasas da muka sayo a hanya hajiya tana hanya
zata shigo yace dani.
Ras naji gabana ya fadi ban san lokacin da nace mai hajiya baaba ba yace ita yana
wuce wa dakin shi bai tsaya falon ba nasan shirin jumma,a yadawo yayi lokacin.
Yana shiga idon shine ya sauka a dakin dana gyara mai shi tson ya sauke ajiyan
zuciya ya aje waya ya nufi ban daki nan ma a gyare yake komai sai walkiya yakeyi a
wurin yasha gyara.
Murmushi ya sauke a fuskan shi shi kadai a dakin yace mata halin su sai su watau
tunda yau nayi mata magana shiyasa ta shigo tayi min gyara itama ta iya ke nan
yanzu.
Daren jiya kamar ummi ta sani tasa ni gaba a waya tayi min tas sai da nayi kuka
sosai tace lalai lalai in bashi hakuri don nice ban da gaskiya ko ina akaje kuwa da
maganan mu.
Kuma akan may zance wai ya rushe gida ya mayar muna da namu yaushe na koyi
rashin kuya haka ko nice nasa ya gina muna gidan.
Idan banyi hankali ba zata hadani da mahaifin mu kuma zata kira uncle ta bashi
hakkuri da sauri nace ni ummi ba sai kin kirashi ba ni zan bashi hakkuri da kaina.
Sai washe gari kuma na tashi naga ya rigani ma saukowa ko shima mahaifiyar shine
tayi mai magana oho ?
Yanzun kuma da yace zata shigo sai tunane na ya kai ga ko tasan da matsalan ne
zata zo inko har uncle ya fada ma hajiya yabar ni cikin tsunbul.
Fitowa yayi cikin farin voil na maza wanda har zaka iya hango farar singlet din
shi na shiki yana haskawa a inda ya bar mu ya samay zaune har lokacin muna wurin.
Ke maimu ku shiya kafin in gama mu je masallaci ku shirya Abba yace dasu ya nufi
hanya waje dama yakan je da yaran idan ya bushi iska amma ya dade bai tafi dasu ba
sai yau.
Namike na nufi dakin mommy nace ta ban kayan shi zasu je masallaci ne da baban
shi nan na zauna dakin ta na shirya yaro tsab anan kuma nake fada mata yau
sarakuwa na zata zo.
Tayi murna da jin haka sai dai tace dani zato za ta samay ki cikin wanan zaman
doya da manja da kukeyi a tsakanin ku haka ?
Ni mommy yaya zanyi tunda in ya hau bai sauka sai yaga dama don kan shi tace ke
ko keda yadda zakiyi don ke ce mace safiya nasha fada maki kada ki fushi haka dashi
tunda ke ce baki da gaskiya.
Babu namijin da zai kama mace da wanan laifin ya iya kyale ta ni naga hakkurin
shi kwarai da gaske wallahi.
Mommy har yanzu fa fushi yake yi dani kan maganan kuma sai kice kinga hakurin
shi mommy ?