Advertisements
Chapter 47 Reading Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   47 / 87

138K to 141K   out of 258.3K words

ke falon kallon mu yake yi a lokacin da muke shigowa gidan.
Ta bishi da dan hararan wasa tana cewa ai na dauka yau yajin shigowa gidan kake
yi don ko da rana baka shigo ba akace.
Yace yana zama wallahi ban gama abinda nakeyi bane a bakin ruwa shi ya dauke
min lokaci tace yau kuma abin yar tsayuwa kofan gida ne kawani aiko wai a kirama
safiya ?
Yace No na kirata ne taimin iso in shigo kin san yanzu kin zama antyn mu ta
harare shi tace waye antyn ?
Ni dai ban zauna shigewa nayi na barsu a nan suna wasan shammatan juna su ina
kokarin cire gyale naji anty ta kwala min kira.
Da sauri na fito daga dakin tace ba mutumin abinci mana kin shige daki kuma kafin
in juya yace No ta barshi kawai i am ok.
Yau ban jin cin komai tace yanzu naji magana amma da na dauka ko kana yajin cin
abincin gidan namu ne yanzu.
Jin haka yasa najuya zan wuce tace kaga mutanen kalaba sai yau taga daman dawowa
garin kallon ta kawai nayi na dan yi murmushi .
Yace na ganta har tana wani wai bata so ta dawo yanzu don ke ta dawo garin yau.
Tace ai da baki tafi kin barni ba kika je can kika zauna abinki hankali kwance.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , ,


4️⃣9️⃣4️⃣
4️⃣
🧕🏿 9️⃣9️⃣4️⃣
NOVEL DINA NA KUDINE IDAN KI FITAR MIN BAN YAFE BA IDAN AN FITAR KI KA KARANTA INA
BINKI HAKKINA A KAN KI.

Ina kwance saman gadona da waya a hannu na na mayar da hankalina sosai a kan wayan
ina duban sako naji an shigo dakin.
Na dago don ganin ko wacece sai Fati na ganj tsaye a kaina tana huci idanuwan ta
sun kada sunyi jawur dasu aje wayan nayi a gefe na duk da ban karasa karanta sokon
ba.
Ta harde hannayen ta saman kirjinta ta wurga min kallo mai tattare da tsana
zallah a cikin shi ta fara tafa hannu ta biyu tamai kara bina da wani irin kallo na
tsana.
Zama nayi da kyau ina fuskanta ta don inji abinda take shirin fadi lalai Safiya
kin cika rikkan yar yaudara kin kai maciyiya amana.
Ke yanzu bakiji kunya ba don Allah to ki sani in takaman ki iya asiri da kwatar
maza yau kin kai karshe don baki da wayau yanzu ina ke ina uncle ko a kafa akadaura
mashi ke ai ba zai iya ja ba.
Sai lokacin nayi murmushi nace da ita balle a daurin da akewa ko wace mace da
mijin ta za ai muna kuma na dauke shi kamar yadda ko wata mace take dauke mijin ta.
Hannu ta daga wai ta kai min mari kafin hannun ta ya iso gare ni na kwashe ta da
mari biyu masu kyau nace kin zo har dakina ki fada min abin da yai maki dadi ki
wuce kice kinci bulus.
To bari kiji uncle kamar na aure shi na gama da yardan Allah ke ce wahalala da
faman dakon son wanda bai masan dake ba a duniya.
Ashe Faiza na jin mu ita ta kira anty sukazo tare daidai Fati na fadin aure fa
kikace kodai karuwanci waye baisan abinda ake turaki yi wurin shi ba banza kawai
ana turaki gurin shi kina samo kudi don zubar da kai dama zubun ki baiyi kama da ta
mutanen kwarai ba.
Muryan anty ne ya karade dakin tana cewa wake turata karuwancin nike nan kike
nufi kowa fati ?
Da sauri muka juya kofan ta karasa shigowa ita da Faiza dakin tana cewa Fati
nace uban wa ke turata karuwanci tambayan ki nake yi ki fada min ?
Nace anty wanan maganan da take fada min kullun ya isheni don ba yau ne farko
fada min haka da takeyi ba wai kina turani wurin maza ina samo maki kudi.
Ko zuwa gida da nayi jiyar baba sai da ta fada min ha gashi kuma yau ta sake
fadin wai kin turani kalaba na samo maki kudi wurin maza dama haka kike yi.
Inna lillahi anty ke nanatawa a gigice tana kallon Fati din takeyi rai bace tace
kazafin da zakiyi min ke nan Fati sakkaiyan da zaki mayar min ke nan ?
Na dauko ki cikin wahala da lalace nazo dake nan don ki zama mutum ki dogara da
kanki shine zaki saka min da wanan a gidana.
Tace da kike fada a kan sulaiman ya ko san da zaman maki a duniyan nan halin ki
na banza ya barki ki aikata alheri ne ne fati ?
Karshe kasa karasa magana tayi nasan takaici ya rufe ta sai juyawa tayi ta fice
daga dakin rai bace.
Muka dawo da kallon mu ga juna sai gata ta juyo tace ki fice daga dakin nan tun
raina bai karkare baci ba Fati.
Ta kalle ni taiyi kwafa tana cewa kin ci bashin marin da kikai min don sai na
rama abina ki sani nace daga baya ke nan na nuna maki ni yar kauyen gidi ne.
Ta fice fuuu anty ta mara mata baya suka fice aka barni da gani sai Faiza tace
don Allah Safiya ki boye ni kada ki fadawa anty anbin da nace hannu na daga mata
nace Faiza ki fice please.
Batayi musu ba ta juya ta fita daga dakin simi simi na sauke a jiyan zuciya tare
da komawa saman gado na zauna ina tunane ni may ye laifina a cikin maganan da
bazata samay shi da maganan ba shi da take so.
Na dade wurin zaune na rasa amsan da zan ba kaina dole nake kwance ina ci gaba da
tunane a raina sai da naji yunwa na iya fitowa don neman abinda zanci don ko
karyawa banyi ba ta samayni da magana.
A falo na ga Faiza zaune wuce ta nayi zuwa kitchen batare da nayi mata magana ba
na hado abinda zanci na dawo zan shige sai naji tace Safiya fushi kike yi hardani
ne wai ?
Nace fushi akan may aini Allah yayi min fada akan may zan tsaya bata lokacina
kuma aida ban gode masa ba.
A gaban anty ta nanata da kunnen ta taji ai hali shike nuna kansa wanan ya nuna
bata da alhakin ku kuke fakewa a bayan ta kuna mata sheri har na gama na wuce bata
ce dani komai ba.
Ban iya cin abincin ba don raina ya na bace har lokacin twin's na ta shigo tana
ce dani maman su na kirana abinda ya sani fitowa kenan.
A falo take zaune ga Fati da Faiza a zaune suma na samu wuri na zauna in ji
abinda zata ce muna.
Mun zauna shiru sai can ta nisa tace Faiza ta amsa naam Safiya nima na amsa mata
da naam Fati ta amsa mata ciki ciki da naam.
Tace na koraku nan ne don in yi magana da ku baki dayan ku akan abinda ya faru
dazun tsakanin Fati da Safiya a gidan nan.
Banyi mamakin jin abinda kika fada ba don nasha jin ire iren wa yan nan
maganganu daga bakunan mutane dake fitowa daga bakin ku.
Amma wanan yafi min munin saurare don da kunuwa na naji ba wani ya fada min ba
sai fatin tace ni may na fada anty maganan mu mukeyi kawai.
Kina rufe min bakin kin ki ko sai ranki ya baci yanzu in maki tsinanen duka anan
sai ta ja bakin ta tayi shiru tare da dukar da kanta kasa tace idan da banji ba sai
ince kaka tayi maki.
Ba wani ya fada min ba ni naji da kunne na abinda kika fada kenan ni ke tura ta
wirin maza tana samo min kudi kike nufi.
Ta dago za tai magana ta tare ta da tsawata yana fidin tayi shiru dole ta sake
kyalewa tai fada sosai a cikin bacin rai sai ta juya kan Faiza tana cewa.
Aure Safiya zatayi nan da dan wani lokaci zan iyacewa nan da dan lokaci mai zuwa
bazaku ce baku san da zancen ba.
Don haka zan iya hakkurewa har lokacin da tayi aure wace taga zata iya zama dani
ta zauna bazan kori kowa daga cikin ku ba don ku kuka kawo kan ku na.
Sai dai idan na sake jin wani rikici a tsakanin ku kafin wanan lokacin dukkan ku
rayukan ku zai baci dani amma ke fati tun yanzu nasan matakin da zan dauka a kanki.
Gida zaki koma don ba zan yarda ki bata min suna a banza ba da abinda banji ban
gani ba ki dora a kaina duk wanda yaji wanan zancen sai yace idan baki gani ba baki
fadi.
To komawar ki gida shi yafi zama alheri a gare ni don haka sai ki shirya next
week zan sa a kai ki gida kafin in zo muyi maganan a can.
Hakkuri ta shiga bayarwa sai ta bani tausayi ban san lokacin da nace don Allah
anty kiyi hakkuri.
Ta dago kai ta kalle sai na saukar da kaina a kasa na kara fadin don Allah anty
kiyi hakkuri sherin shedan ne .
Kina ji da bakin ki abinda ta fada akaina kuma kince ba yau ta fara fada maki
haka ba sai fati tau sarin cewa wallahi bani na fada ba Faiza ce ta far fadi nima
naji na fada.
A take Faiza tace kada kimin sheri yaushe na fada ta juya gare tana cewa wai
Safiya ranan wa kiji ya fada har muka baki hakkuri akan karki bari anty taji
zancen.
Murmushi nayi nace anty don Allah kiyi hakkuri da zancen in ma har suna hasashen
haka ne a ransu ai Allah shiyasan gaskiya.
Haba haba kuyi min adalci mana maye laifina na ajeku a gida na danayi tare
dani ?
Idan bani ba wacece zata ajeku haka a gidanta amma tunda ku kuka kawo kanku
gareni na karbe ku hannu bibiyu na zauna daku may na rage ku dashi a gidan nan na
jin dadin rayuwa.
Duk mukai shiru muna sauraren ta tace ke Faiza ai akwai gidan anty Ai a abuja
may yasa baki je can kin zauna ke kuma akwai gidan anty mami a kaduna ai uwarku
daya may yasa baki tafi wurin ta ba.
Sai nan bayan haka da halina ne hakan da ku da kuka riga Safiya zuwa nan aida
daku zan fara ba Safiya da tazo daga baya ba.
Ko don ita din ta fiku kyau kuke tsamanin haka zanyi da ita toni aure na hada don
raya sunnan ma,iaki SAW ba yin zina ba yadda kuke tsanmani.
Allah ne ya yanke mata wahala da zuwanta ta samu miji ku da kuka dade da zuwa
aida aikinane hakan akwai maza da yawa may zai sa ban hada ku dasu ba ku samo min
kudin ko ku ba mata bane yan uwanta.
Faiza tace munyi kuskure amma kiyi hakkuri ba a karawa in Allah ya yarda ta ja
tsaki tare da kawar da kanta gefe.
Nan muka zauna zugun zugun damu ita dai bata sake magana ba sai duban tv da
takeyi tana sauke ajiyan zuciya kawai.
Nice na fara mikewa na bar falon zuwa daki ban san lokacin da sauran suka watse
ba tun wanan ranan aka rage yawan gulma a gidan.
Sai dai ban yarda na sake wa Faiza dake yawan shige min ba wai ita ala dole tana
tsara yadda zamuyi buki in ya taso.
Na fito daki da safe na samu anty a falo don yau ba ranan fitanta aiki bane don
haka mukan wuni da ita a gida bata fita ko ina a wanan ranan ne takanyi gyaran
jikin ta.
Sai yanzi na gane hakan da nake zaune a gidan ta ina fitowa tare da gaida ita
tace yauwa Safiya kin fito don Allah ki taimaka min da kan nan nawa.
Yau kitso nake so da gyaran jiki tace yan biyu ta dauko mata kayan kitson su nan
na zauna muka fara banyan kai muna hira sai ga Faiza ta fito zauna nan take fada
mata ai kan yayi dauda nan dai mukai ta mahara karshe dai tace zataje wankin kan.
Wayana dage gefena ne yayi kara alaman sako ya shigo min a lokacin ban dauka ba
sai anty ta lura dani take cewa in diba mana ko soko ne mai muhinmanci.
Ga abinda na gani rubuce ga sakon.
Safiya badon na isa ba sai don girman Allah Safiya ki taimaka ki kashe min
wutan kaunan ki dake famar kunar zuciyata har kullun, Safiya ina sonki ina kaunar
ki wallahi wallahi ina son ki tsakani da Allah, Auren ki nake so don auren ki
alheri ne a gareni.
Ki taimaka ki kirani a wayan ki inji muryan ki don in samu natsuwar gudanar da
ayyukan dake gaba anan idan kina raayina ki kirani inji muryan ki Sulaman Habbi
Bauchi.
A hankali na runtse idona bayan karanta sakon ina sauke ajiyan zuciya sai kuma
gabana ya fara bugawa a hankali kamar zai tsage min.
Ganin sakon na rinkayi kamar a mafarki na shiga tambayan kaina may ya kawo wanan
sakon haka har uncle ya tsaya ya rubuto min shi.
Na sake tambayan kaina may ke faruwa ne wai muryan anty naji tana cewa dani kin
gama karanta sakon ki sance ma su yan biyu nasu muje a wanke muna.
Cikin dauriya na amsa mata da eh sai dai saukina kitson kan su ba wani mai yawa
bane ina gamawa na shige daki don ban da kwanciyar hankali a tare dani a lokacin.

Acan kuma uncle one two ya duba wayan shi yana tsamani ko sakona zai shigo kai
sai yaji shiru hakan yasa ya fara zargin ko maganan da yaji ya zama gaskiya a
kaina.
Zama nayi ina kara karanta sakon sai zuciyana ta bani cewa da Allah fa ya hadani
mai zai hana na kirashi inji komay ke gudana.
Yana zaune a office din shi na abuja tunane na kawai ya keyi akan don may zanyi
mashi haka bayan tafiya ya nisa in nemi canza raayi a kan sa kuma.
Sai yaji kira ya shigo mai a waya da sauri ya dauko wayan don ya matsu ya dauki
wayan ya tabbatar da zargin shi.
Yana dauko sunana ya baiyya na fuskan wayan sai da yaji gaban shi ya fadi don bai
san may zan fada mai ba.
Ya amsa wayan da hello,
Murya kasa kasa nace mai salamu alaikum.
Ya amsa min da wa, alaikumu salam Safiya, tare da karfin halin cewa yaya naji
muryan ki a sanyayye ?
Murmushi yaji nayi wanda ya fara kwantar mai da hankali nace haba uncle wanan
irin sako ai sai ka tayar min da hankalina.
Bancin kasan ka riga ka gama daure zuciyana da sarkan kaunan ka kasan yadda na
dauke ka da muhinmanci .
Uncle kafi kowa sanin kunya ke hanani kiran ka kan ina matukar jin nauyin ka da
kunyar ka fiye da kowa yanzu.
Shine kuma zaka rubuto min sakon da ya tayar min da hankali kasa zuciyata cikin
kwankwanto tun dazu.
Ajiyan zuciya naji ya sauke ya gyada kai tankar ina ganin shi yace safiya ina son
ki sani yau da baki bugo min wayan nan ba sai ince abinda ake fada a kanki
gaskiyane.
Da sauri nace Uncle may ake fada a kaina kuma yace forget it, bar zancen kiyi
hakkuri amma ina son ki sani akwai ta inda aka fara ma zancen mu zagon kasa .
Amma ni kaina na yi tsamanin haka tun farko yanzun dai ina son ki sani ni kaina
ba karamin kokari nayi ba da na iya turo maki sokon nan don in tabbatar da zargin
da nakeyi maki.
Luckyly sai gashi kin kirani din kamar yadda na bukace ki kiya kin ga hakan ya
tabbatar min da cewa akwai matsala kenan.
Shiru mukayi dukkan mu na dan wani lokaci kowa na tunane a ranshi kawai sai yaji
na fara yi mashi kuka a wayan ina fadin ni may nayi wa wani da yake son rabani
dakai ?
Safiya come on ki tsaya ki saurare ni kada wani yazo ya samu kina wanan kuka haka
kuma a san abinda ake ciki.
Ki saurare ni kiji idan da ana iya rabamu da tun farko na dauki maganan da
muhinmaci a zuciya na kwata kwata ni maganan bai tsaya min azuciya ta har da zan
daukaba.
Haka kuma idan baki daina kukan nan ba mai sakon zai fahinci mun samu matsala
dake .
Sanin mun rabu lafiya dake last week yasa kawai nayi tunanen in gwadaki in gani
da kwata kwata ba zan taba barin ki san abinda ke zuciya ta ba to amma ba zan iya
bane wallahi na kasa daurewa sai da na jerabaki yanzu share hawayen ki muyi magana
na fahinta a tsakanin mu.
Share fuska nayi kamar yadda ya bukata ina fadin don Allah uncle may aka fada ma
a gamay dani ne wai ?
Naga tun farko ba a boye maka komai nawa ba, nisawa yayi yace baki jin magana
ko ta bari in kashe wayan tunda baki tsayawa ki saurare ni.
Na nisa nace uncle kayi hakkuri amma gaskiya maganar ne koda banji ba akwai cin
rai don sheri baida kyau sam wallahi.
Kalmomin da nakeyi tuni suka jefa zuciyar shi a cikin tunane fiye da musali
saboda bai taba tunanen haka ba da tun farko in yasan za a samu wanan matsalan ba
zai tsaya har muyi nisa haka ba
Amma a fili cewa yayi dani come on ba nace ki manta da komai ba kiyi kamar bakiji
komai dake gudana ba, idan na zo zan maki bayani yadda zaki fahinci abin
Ko kinfi son ki tadda min

47 / 87