Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
anty ce da kanta tazo dauka na sai faiza.
Da murna suka tare ni bayan an dauko kaya na muka muka nufi gida yaran basu gida
sun fita da daddy sai fati ce kadai a kida.
Itama ba laifi ta tareni ba yabo ba fallasa don tun da tace in andawo bata sake
fadin komai ba kamar bata san jiyan mahaifina naje ba.
Ban shiga da kayana ba na ware wanda nazo masu dashi da wanda ya bayar a kawo
masu murna ta shigayi tana cewa .
Safiya keda kika je jiyan kika tsaya muna tsaraba haka mai yawa ta bude naman da
aka soya na zabbi wanda kaunan mama ta soya muna shi yaji hadi ta fara ci.
Tace kai Safiya mai wanan naman idan da agarin yake ai kullun ina shagon shi ke
kinji nama zau da dadi ta bude kayan miya taita murna ganin na hado masu kayan miya
na garkajiya ta shiga yabawa kamar nakawo masu wani daula.
Tasa funke ta kwashe kayan zuwa kitchen don su faiza sun far ma naman da ci tace
su bari hakana sai ta dibawa daddy na shi.
A dakina muna like da su yan biyu da suka mane min sai hira suke so in masu na
kauyen mu, suna son hiran kauye sosai sai faman tambaya na suke yi ina basu amsa
sai da daddy ya dawo ya kirasu.
Na fito cikin dogon riga sai hijjab dana saka a sama yar karama don bani zuwa
gaida daddy hakana sai dai idan ya girshe ni a gidan ba hijjab a jikina kuma idan
ya samay ni hakana bani iya sakewa dashi.
Yana gani na ya na cin naman dana zo kasu dashi anty na gefen shi zaune itama
naman take ci yace a a amarya andawo.
Kunya ya kamani na soke kaina nace daddy mun samay ku lafiya yace lafiya Safiya
yaya baban naki da jikin ?
Nace yaji sauki yace a gaishe ku ai mashi godiya a wurin ku sai yace ai ba komai
Allah dai yaba shi lafiya.
Nace amin tare da mikewa daga tsugunnin da nayi har na juya zan wuce sai naji
yace ashe sulaiman ya samu zuwa garin naku ?
Na juyo tare da dan dukar da kaina kasa saboda kunya ya sake cewa yanzu sai batun
aure don bana son a dauki wani dogon lokaci ba a yi ba .
Bandai yi magana ba na juya na wuce zuwa dakina inda ma na rufo dakin don ina son
in duba kayan da ya sawo min shake a troler.
Sai da nagama komai na jawo akwatin na buda idona ya fara tozali da wasu irin
dogoyen riguna masu kyau da daukan ido .
Guda guda nake fitar wa saida na fitar da kala bakwai sai kuma wasu lace da aka
dinka su kamar an gwadani guda ukku suma.
Ya tashi kala goma ko wani da gyalen shi da takalman shi ido na runtse tare da
sauke ajiyan zuciya nace a fili Allaj miskara ziratin .
Yau ni safiya keda wanan kayan da sai a film ko a jikin wata data kai, nake ganin
su yau ni safiya gani dasu a matsayin nawa ga wa yanda ya saya min kafin in tafi
gida.
Na hada suka tashi sha biyar kenan nace wanan wani irin mutum ne da baya jin
kyashin kashe kudin shi haka sai naji ina son kiran shi a wanan lokacin in dada
mashi godiya.
Waya na mike na dauko bayan na mayar da kayan na kirashi ringing uku ya dauka
yanayin shi kamar na mai barci.
Yaya jikin na yimashi yace yaji sauki yace kin sauka lafiya kin samay su lafiya
ko ?
Nace suna lafiya sai dan shiru sai naji yayi murmushi nace dama dai na bugo inji
yaya jikin naka yace ashe andamu dani ke nan da har za a kirani.
Murmushi nayi kamar yana gabana sai nace yallabai kuma wani hidima akaimin haka
yace yes kin san yanzu matar sulaiman kike dole ne nayi maki ko kina son a ganni
cikin sutura ne ke kuma azo a ganki haka ?
Nace to na gode kwarai sai naji ya kashe wayan murmushi nayi nace har kullun idan
kai min alheri baki bazai gaji dama godiya ba don kacancanci hakan.
Gidan Ahmed dana zauna har nabar gidan ko kyale bai hada ni dashi ba banda
tsaraban kanjamau dana samu koma wani hali yake yanzu oho ?
Muna gama wayan dashi ya tuna da cctv din da ke gidan ya jawo ya hada ya fara
kallon barin mu gidan da yayi da yaya sani.
Don yaga fuskana na sai ko ya fara ganin badakal da muka yi da yaya din tun fitar
shi har shigowan shi da shiga dakin shi da yayi ya bar mu.
Lumshe ido yayi yana jin wani iri a ranshi yanayin da yaji a lokacin da haka ya
samay shi har yakwanta ciwo don bakin ciki gani yake a lokacin kamar zai mutu ne a
take.
Kamar ba zai yi wanan rayuwan da yake yi ba yanzu har da fadawa vikin soyayyan
yarinya karama da yake jin shaukin ta akoda yaushe.
Lumshe idon shi yayi yana jin wani irin yanayi a zuciyar shi a haka barci ya
dauke shi da tunane barkatai a zuciyar shi.
Washe gari da ya tashi sallah yayi bai kara kwantawa ba yayi abinda zai yi ya
fito yaya Sani ma ya fito yana falo zaune shi kadai.
Yana ganin ya fito yake ce mai ina kwana yaya ce yaya sani ashe ka tashi ya gaida
yaya sani din nan suka zauna suna dan hira a kaina a wurin yaya sanin ne yaji
labarina tsab ba ragi ko kari.
Yace in sha Allahu karku ji komai a kaina zaku samay ni da yiwa yar wanka a dalci
sai dai idan wani abu ya fito daga gare ta.
Yaya Sani yaji dadi sosai har ya kasa boye farin cikin shi sun karya yace zai
fita sai ya dawo akwai maganan da zasu yi da yaya sani din.
Ya kara da cewa idan yana son fita ya zaga gari yayi magana sai a fita dashi
driver yana nan waje
Kwarai yaya sani yake jin dadin zama garin ko ba komai yaci mai kyau yasha mai
kyau idan zai fita ga mota nan a fita dashi yana kallon gari
Gashi har yau sulaiman bai samu zama ba balle suyi maganan da yace zasuyi dashi
shi kuma yana cikin fargaba don bai san maganan da zai mashi ba.
Ko yaushe muna waya da yaya sani din yana fada min daular da yake ciki a gidan na
sulaiman din
Nakan yi mashi dari idan yace Safiya kin ko ga yadda na koma wani dan birni dani
sati gudan man danayi a gidan ku.
Nakan ce kai yaya wai gidan gidan mu yana can kauye gidan sulaiman din dai sai
yace gidan ku mana aini inna nake son tazo taga irin gidan da Allah ya nufa zaki
zauna aciki.
Muga yadda zata yi ranan nasan bata da bakin magana nasha gayawa inna tun kina
yarinya akan ta daina irin abinda take gwada maki don bata san abin da Allah zai
mayar dake ba wata rana.
Amma sai inna tace min wai ni yaro ne bani sani komai ai yadda uwar ki take yar
kauye basu da komai kuma diyan ta haka zaku taso baku da komai.
Yanzu gashi Allah ya gada masu shike da komai yayi ikon shi a kan ki wanda nasan
har duniya ya nade gidan mu babu mai cin maki a ratuwan duniya.
Nace kai yaya banda sheri dai don kaga inna bata nan kai mata kaza fi yace
safiya ke baki ganewa ne inna fa sam bata son kowa a gidan mu in ba mi diyan ta ba
ni kuma wanan halin nata yana damu na sosai a raina.
Nakan yi mashi nasiha akan ya tuna fa inna uwa ce a gare shi sai yace ya sani shi
dai halinta ne baya so sai nace sai hakkuri da iyayye yaya.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGO, , , , , ,
4️⃣4️⃣4️⃣
4️⃣
🧕🏿 4️⃣4️⃣
DA FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH YA MAIMAITA MUNA NA BADIN BADADADA YA BAMU CIKAWA
DA IMANI A ZUCIYAR MU, , , ,
Sai bayan kwana takwas ya samu zama da yaya sani din bayan sun gaisa dashi ne yake
cewa yaya sani dama maganan da zamuyi akan yadda za a gyara gidan nan naku ne kafin
daurin auren mu.
Yaya Sani ya dago ya kalleshi da sauri yace kana nufin gidan baban mu ko ina yace
cikin gyada kai eh nan nake nufi a gyara .
Ya ce dashi dakuna nawa ne a gidan ya fada mashi yadda tsarin ginan gidan mu yake
sai yace ba a samun fili daga waje sai a kara yawan fadin filin gidan.
Yaya Sani yace daga gaban mu har bayan mu filin babane wanda yake shuka masara da
damana a cikin su don haka akwai fili sosai daga bayan.
Yace abu yazo ka da sauki nan ya fitar da plan din yadda yake so a yi ginan gidan
namu nan yace gobe in Allah ya kaimu nake son ka tafi amma kuma idan akwai fili a
kusa daku kadan ina so don akwai abinda zanyi dashi.
Yaya sani ya rasa abinda zai ce mai sai ya kama kuka kawai don bama zai iya bude
baki shi ya yi mashi godiya ba.
Ranan haka ya wuni suku suku yana tunanen wai gidan su ne za a mayar kamar na
yan birni a garin mu gidan bulo da bulo wanda sai wani da wani suke ginan bulo da
bulo zalla.
Gaskiya Safiya ta kasance alheri a cikin mu dan ta zama muna hasken rayuwa shi
ko ma a haka aka tsaya ai ta wadatar dashi don ya samu karuwa.
Washe gari tunda safe ya gama shirya mai komai na tafiya yaya sani ya fara hanya
shi wanda zai mayar dashi gida.
Sai yamma suka isa don sun tsaya hanya sun sai doya da su majan da sauran
tsaraban Abuja suka kama hanya.
Mutane na zaune sunyi daba kamar yadda yanzu maza suka koyi yi a ko wani gari
gungu gungu ya shigo garin sai budawa yake yi shi a dole ga dan birni ya dawo.
An bi motar da kallo har ya tsaya a kofan gidan mu abokan shi na ganin ya fito
suka dauki ihu shiko sai faman washe baki yana mika masu hannu .
Da kyat ya samu ya shiga gida bayan an gama kwashe mashi kaya daga cikin mota
zuwa cikin gida.
Yara na shiga gidan da kayan sai suka nufi kofan ummina da shi kamar yadda ya
fada masu sai inna tace maza su kawo kayan a kofan dakin ta.
Yana shigowa ana mashi sannu da zuwa bai ko amsa ba ya hango an tara tulin doya
kofan inna yace kai amma yaran jan nan suka zube kayan nan kuma bayan na fada masu
inna zasu kaiwa.
Inna tafito da sauri daga dakin ta tace kamar yaya akai kofan Rabi kuma ba kai
kazo da kayan ba ?
Yace kayan ummi ne don ita surikin ta yace a kawo wa don haka ku kwasa ku mayar
don Allah yace ma yaran dake shirin fita daga gidan.
Bayan an gama kawarwa sai da ya tabbatar sun kwashe komai ya kara yana cewa mama,
mama ga mutan Abuja sun dawo fa.
Mama tace ai naga kashigo kana ta sababi da yaran ta fada a fakaice yace wallahi
fa ga inda akace sukai abu sun kwasa sun kai wurin da bashi ba.
Inna tace muma Allah ya bamu ba sai anbamu ba ta diya har ana daga muna kai a
cikin gida yaya sani ya kada kai yace inna ke nan.
Kin ko san gidan da Allah yakai Safiya kuwa inna da kike fadin wanan magana haka
gida ne fa gidan bene sai inna din ta katse shi tace rufa mana baki sakarai kadawo
kenan da katobaran ka kamar , , ,
Tau tau baba ya fada may akai wa cirko cirko haka kuma ya fada daidai yana
shigowa gidan da leda baka a hannun shi.
Mama tace umm umm mutan Abuja ne suka iso muke shan labari yace to kai haka akeyi
kazo da mutum sai ka barshi a waje kuma ?
Sai lokacin ya tuna da yabar driver a waje baiko kai mashi ruwan sha ba sai inna
tace ya kai kai ruwa yaya nan yana fadi ba a tambayeka ba.
Mama tace ai abinda ya gani yake fadi magana ne yakawo magana har yake fada muna
yaya Sani ya fita daga gidan yana aiken yaro ya sawo mai ruwan pure water.
Bai shigo ba yana can yana nema wa bakon shi wurin kwana don haka bai samu zama
su gaisa da mutanen gida ba ranan.
Sai washe gari tun da safe inna ta samu baba a dakin shi wai yaya sani yazo da
tsaraba inna takama tasa shiyan ta.
Bata raba ba yace anya Rabi zatai haka kuwa a gidan nan amma barin kira ta inji
dalilin ta nayin haka din ?
Da bi ar bane in magana ya kama ya kirasu dukan su don haka har da mama aka kira
suka zo bayan sun zauna yace da ummi na.
Rabi yaya akayi kuma sani ya dawo da tsaraba kin kwashe kin tura dakin ki ko dan
tsaraban ya fito daga gefen diyar ki ne kikai haka don yanzu Rakiya ta samay ni da
maganan .
Salati ummina ta saka tace ni malam da dare fa Sani yazo da kayan kuma tun fitan
shi bai dawo gidan ga ba balle inji yaya kayan suke ya dai ce ma yaya akai kayan
kofana .
Sai mama ta tara tace kai ba haka zancen yake ba da yara suka shigo da kayan ita
Rakiya tace su kawo kofan ta.
Sani na shigowa yace su kwashe sukai kofan Rabi surukinta ne yace a kawo shine ma
ka shigo ka samay mu muna maganan dashi jiya.
Ko da dare Rabin ta samay ni da zancen kayan nace tabari har Sanin ya shigo muji
yaya kayan suke sai kuma nace ta kwashe tasa daga cikin dakin ta don sata kuma da
dabbobi.
Ya juya ga inna yana ce mata kinji dama na fada maki tun farko Rabi bata yin haka
ke gajin hakkuri gareki Rakiya.
Ta mike zabban kuya tana cewa in ba a bayarwa ne a barshi mana doya ne mutum bai
taba ci ko manja tana kokarin fita yaya Sani yana shigowa gida neman kulan da zai
ba bokon shi abin karyawa a ciki.
Ummi ya nufa yana kiranta yace ummi don Allah bani kula zan sai ma boko na abin
karyawa ta mike a kasalance tana cewa dashi ai nasa an mashi abin karyawa ko.
Yace da kyau ummi ashe barince mai abincin ta wuce din har na tsayar da ita baba
da yaji muryan shi yace kai sani kai ka dawo baka zauna da mutane ba.
Yace baba ina zuwa akwai labari mai dadi yau a gidan nan barin ba bako abin
karyawa jin haka da inna yayi sai ta shiga daki ta aika yaro ya kira yaya sani.
An samay bai ko tsaya sauraren yaron ba ya korashi ran inna yakara baci sosai
dashi ta cika fam tana jiran shigowan shi gidan.
Don taso ta jamai kunne akan in alheri ya samo da kada ya fada kowa yaji a gidan
subar zancen a yi su dakin su ba sai kowa yaji ba sai ga yaya sani din yaki
shigowa.
Sai da ya gama da bakon ya samu shigo dakin baba ya nufa direct nan ya samu baba
yana shirin fita kasuwa don yakan dan leka saboda sabo kasuwan.
Yace baba mun samay ku lafiya yaya jikin naka baba ya amsa mai da Alhamdulillahi
baba yace yaya kabar su can ya gyara zama yace lafiya .
Ai ita Safiya tun ranan da muka rabu nan ta hau jirgi ta wuce lagos daka can bata
kwana abujan ba don ba mace a gidan.
Baba yaji dadi yace dakyau dama tunanen da ya tsaya min acikin raina ke nan yaya
yace ai baba sai kaga gidan da aka gina ma Safiya.
Wai ita zata zauna a ciki da mijin ta baba mutumin nan ba karamin mai kudi bane
ko a abujan don gidan kawai zai nuna wa mutum haka a zahiri.
Baba albishirin ka yace goro sani don naga a rude kake yace ai dole ne baba kaga
zuwan nan da nayi baba ya amsa mai da eh sani.
Yace baba nazo ne da shirin rushe gidan nan gaba daya a gina ma wani.
Baba yace kai sani a cikin hankalin ka kake kuwa koko dai ?
Yace wallahi baba abinda ya kawo ni ke nan yanzu yau din nan zamu je birni muzo
da masu aikin da zasuyi ginan don yace bai so ya wuce wata daya ba a gama komai ba.
Ido baba ya zaro yace Allahu Akbar wai sani da gaske kake yi ko kowa wasa yace
wallahi baba da gaske nake yi abin da ya kawo ni ke nan yanzu haka.
Su mama ya kwala ma kira yana fadin kuzo kuji ikon Allah da sani yazo muna dashi
gidan nan.
Da yara da manya suka nufo dakin baba nan yace yaya sani ya kara maimaita abin da
ya fada mashi ya mayar masu.
Gida ya dauki ihu mama tace haihuwa tai ranan ta safiya kin kai diya Rabi kin iya
haihuwa tankar da dubu.
Mama na guda ummi ko ko bakin magana bata samu ba inna tace a dai yi sannu kar
aje a debo muna wahala muna zaune zaman mu.
Don yan birni babu abinda basu iyawa sai ta tashi ta fita daga dakin tana
maganganu tana fadin ba inda zan daga ni.
Tana fita ummi na ta nisa tare da