Advertisements
Chapter 8 Reading Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   8 / 87

21K to 24K   out of 258.3K words

, , ,
8️⃣


YAR UWA IDAN AKWAI MASU NEMAN ACCOUNT NOBA DONA TA WURIN KI GA NOBA NA NAN SHINE
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO NOBAN WAYANA DON ALLAH KU TAIMAKA
MIN.
AKWAI MASU KARBAN KUDI SUCE ZASU TURO MIN AMMA BASU BANI SAI SU RIKE A HANNUN SU
IDAN NA TURA SU TURA WA MAI SHI NOVEL DON ALLAH KUJI TSORON ALLAH YAN UWA.
MASU CEWA BAN MAGANA YAUSHE ZAN TSAYA HIRA YAUSHE ZANYI TYPING SAI DAI INDAN
ZAMU CIRE KWANA BIYU BA TYPING NE SAI HIRA SAI KUZABA MIN.
NAGODE NAGODE DA KASANCEWA KU TARE DANI KAUNA NE YA JAWO HAKAN SAI KUYI HAKKURI
DANI YAN UWA


Ina zaune bayan na gama gyan gida tare da dan dafa abin da zanci tunda shi ba
damuwa yayi da abincin dare ba sai dare sosai yake dawa kuma a buge.
Kofa naji a na murdawa sai na tashi na bude ban yi tsan manin shi bane a
lokacin.
Shine tsaye bakin kofan ya kara daure rain shi naja baya tare da mashi sannu da
zuwa tun da yau ya shigo cikin dan hankalin shi gidan.
Bai ko kalleni ba ya shige ciki da hanzarin shi nikan na koma na zauna inda nake
da farko .
Sai zuwa can ya fito yana saye da gajeren wando da yar faran singlet ajikin shi
ya samu kujera ya haye yana kokarin kuna taba.
A kawo ma abincine nagama nace dashi sai yai wani dagowa ya kalle ni a hankade
yaci gaba da abin da yakeyi.
Na ja gafe daya na kama kaina na natsu ga kallon tv da nakeyi saboda yin hakan
shine alheri a gare ni tunda naga yana jin tsiya yau din.
Haka muka zauna zugun zugun sai busar taban shi yake yi wanda warin ya cika
falon ya hana ni sukuni gaba daya a wurin.
Nake zan shige ciki naji yana cewa ke kawo min abinci in ci zan fita , koda na
kawo mai abincin ko cibi uku baiyi ba dan dama yaci dan doyan da na hada wurin
girkin dashi.
Ya tsamay hannuwan shi ya ture plate din gefe daya kasa daurewa nayi nace cikin
damuwa abincin bai maka bane in dafa ma wani.
Kamar dama jira yake tsutsayi yaja ni nai mai magana sai ko ya mike da sababi
kamar wanda naiwa bakar magana yana cewa.
Ke kada ki kuskura ki nemi takura min da tambayan banza da wofi ke zaki sani cin
abincin dole ne kokuwa da zaki damay ni da nacin tsiya.
Jikina yai sanyi na tsaya kawai ina kallon shi a cikin mamaki karo na biyu na
sake tambayan shi cikin girmamawa may kuma nai maka daga tambaya kawai .
A fusace ya jefamin wani irin harara tare da cewa ke wai baki da hankaline ki
barni mana kon zauna kina damuwa na kawai da bakin nacin ki.
Na dago idona cike da damuwa ina kallon shi daga abin arziki kawai sai hattara
irin haka sai dai a fili fadi nayi Allah baka hakkuri na ga bakaci abincin bane.
Sai ya zubo min wani irin kallo na fushi yace a hasale ke don Allah ki wuce
dakin ki, ki bani wuri kaganin ki ma kara tada min da hankali yake yi.
Zanyi magana yace waike wata irin yarinya ne mara hankali sai ya dakatar dani da
hannun shi na dama cikin wani irin murya mai cike da tsawa yace nace ki wuce ki
bani wuri in ba haka ba zan yi maganin ki yanzu nan.
Na juya zuwa ciki hawaye na zuba min na fada saman gado na ina bakin ciki da
dana sanin wanan zaman kaddaran da na samu kaina a cikin sa zama da mashayi mara
tarbiya.
Zuwa can naji ya fita yabar gidan na sauke a jiyan zuciya a hankali na mike na
fito do in yi sallah.
Bai shigo gidan ba sai wajajen karfe goma lokacin har na kwanta sai dai ban yi
barci ba ko da alama yau baya a cikin maye do banji yana haukan nashi ba.
Ban fito ba shi ma bai nemay ni ba don haka sai da gari ya waye na fito a falo
naga ledan daya shigo na kayan break fast da su sabulu da omo da maclean da sauran
su.
Ban taba nadai kaqar na fara gyaran gidan ina tsaka da gyaran falon gidan ya
fito da jallabiya a jikin shi.
Tsaida abin da nakeyi nay na gaida shi da ina kwana yaya ?
Sai ya jefe ni da kallon nan da na tsana bai ce uffan ba ya dauke kan shi gefe
guda.
Dukawa nayi naci gaba da aiki na sai da na gama naje na duba abinci na samu ya
dahu na zuzuba a cikin plate nadawo na sama shi falon nace.
Ga abin karyawa nan na gama a saman table bani bukata ya bani amsa dashi a fusace
.
Da mamaki nake kallon shi idona ya ciko da hawaye nadake nace don Allah yaya idan
laifi nai maka laifine ka fada min abin da nayi sai in gyara don gaba.
Wai ke wata irin yarinyace idan gidan kike son na bar maki zan iya bar maki kin
isheni nida gidana kin hana ni shakat wallahi.
Wanan ai takurawa rayuwa ne an daukoki kin zo kin zauna wa mutum a gida kin
hanani shakat dani da gidana .
Da mamaki nake kallon shi nace nima bayin kaina bane zama a gidan ka umurnin
iyayyene nake bi hakana.
Ya fadi a fusace da cewa very good dama zaman umurnin naki iyayyen kike bi , ni
sai kiyi kokarin hadani da nawa yan uwan da iyayye ko ?.
Da sauri na kalle shi ina cewa ai iyayyen ka da yan uwanka duk nawa ne hannu
ya daga min yana cewa ba yan uwanki bane kan, don da basu zo gidan nan kin yi masu
wullakanci ba sun koma rai bace.
Na soma kallon shi baki bude ina fadi cikin mama ki da cewa ni har yaushe wani
dan uwa na zai shigo na wullakan tashi ina nima su nake gani a matsayin nawa yan
uwan a nan garin.
Kai ya girgiza min yana cewa ba gaskiya bane hakan don da basu gidan nan kin
masu taron wullakanci ba.
Kin raina masu wayau ko bari su zauna bakiyi ba kike cewa wai bana gida kina
kokarin rufe kofa su fita kullun suka shigo abinda kike masu ke nan.
Da sauri nake kallon shi cikin mamaki baki bude nace har yaushe suka shigo gidan
nan in ba jiya ba kuma nan suke zaune suna tanbayan ka nace baka nan ruwan ma da na
kawo masu basu sha ba nan suka tafi suka barni dashi basu ko sha ba.
Yace kenan dai sun zo din ko tabbacin cewa sun shigo kenan gidan kin masu
wullakancin ko ?
Gabana yai mugun faduwa sosai ni?
Dama sherin da sukai min kenan to wallahi wallahi ban masu wullakanci ba a gidan
nan yan uwana ne fa su dan may zanyi masu haka.
Wani harara ya watso min yace da yan uwanki ne aida baki wullakan ta su ba
harkina fadin magana a kaina , nace ba haka bane ya daga min hannu yana fadin ya
isa haka maganan ya isheni ji ki sani kuma ba zan dauki raini ga yan uwa na ba a
gidan nan.
Ya juya ya shige dakin shi can ya fito ya dauki key din motar shi ya fice a
hasale yabarni tsaye in da nike.
Kwana uku cur muka dauka bai damuwa da harkana a gidan haka muke zaune dashi ba
dadi ta ko ina saukin abin yana barmin abinci inci wanda raina yake so.
Sai dai na fahinci akwai matsala a tsakanina da yan uwan shi ke nan amma na rasa
gane ta ina wanan matsala ya ke tsakani da su.
Haka muke zama har na tsawon kwanaki ranan ko may ya gani oho sai naga ya fito
yana bude kulan abincin da nayi da safe don yanzu yakai nabar gaidashi don ko na
gaida shi baya karbawa tun ranan da na gaishe shi yace dani
Ke wata irin yariya ce wai mara zuciya gaisuwan na dole ne ko an baki ajiyana ne
wai tun wanan ranan ban kara gigin gaida shi ba a gidan kowa harkan gaban shi yake
yi.
Bayan ya gama ina saurare fita shi sai naji shiru alaman bai fita ba ke nan
agidan.
Wuraren shadayan rana na fito a zotona yana dakin shi ne ashe yana falo kwance
ban sani ba.
Gashi ba daman in koma yace dani munafuka sai na daure na wuce shi zuwa kitchen.
Dole hakana nake aiki duk na daburce na gama abin da nakeyi a kitchen nafito na
nufi hanyan daki sai naji yace dani zo nan.
Gabana ya yanke ya fadi a sanyaye na iso gabanshi nace gani sai dai ban yarda na
kalle shi ba shima din ta gefen ido yake kallona.
Yace dani ke baki iya gaisuwa bane ko may ?
Na nisa tare da cewa gaisuwan nawa ne naga baka so shiyasa tun da ba ajiyan ka
aka bani ba.
Sai naga yayi tsam ya mike yayi amfani da hanayen shi biyu ya rike min hannu da
karfin tsiya saida na sake kara.
Sai da yaga na jirkita don kan shi yadan sasauta rikon dayai min din yana kallon
fuskana dake fitar da hawayen wahala.
Jinayi gaba daya jikina ya hau rawa don kusantan juna da mukayi a lokacin.
Hakanan gabana banda bugawa ba abin da yakeyi ba bata lokaci ya shiga kokarin
manna bakin shi a nawa, nayi kokarin kwacewa shi kuma yai amfani da karfin shi ya
hanani kwacewa .
Abin da ya kama daga bakina zuwa wuyana babu inda bai mana bakin shi ba da kiss
ban yarda mun kalli juna ba sai ruwa hawaye dake zuba min nace cikin karfin hali
don Allah yaya kayi hakkuri ka kyale ni.
Kamar hadiyeni zaiyi yace ina bakin naki mai fadar bakar magana ya shiga zan
kyale ki amma ki sani duk kika kara min rashin kuya a gidan nan nasan maganin ki.
Don kawai ya kyale ni warin taba ya isheni tankar zan yi amai nake ji na amsa
mashi da uhm mhm.
Ya sake ni da karfi har ina gauruwa da kushin da sauri na shige daki na na barshi
wurin tsaye.
Jikina na rawa na fada daki ban daki na nufa naje kamar zanyi mai ina ta jakarjn
amai bai fito ba na wanke bakina nafito duk jikina ya mutu..
Ban fito ba sai da naji yabar gidan na fito ina kallon wurin da yasha taba duk
ga guntun taba a yashe a kasa.
Tsaki nayi na dauko perker na kwashe tare da gyara falon ina jan tsuki hawayen ta
kaici na zuba min ko nace zan ja Allah ya isa gawa zan ja shi.
Ga mahaifina daya sani dole ko ga gwagona ta jawo min haka gashi har yau ban saka
ta a idona ba.
Ban may su sadiya suka ce ainihin nai masu ba a gidan wanda har ya hasala ta da
diyan ta gaba ki daya sun dauke kafan su da zuwa wurina.

********* ********* *********
Tun wanan rana na koma jin tsoron shi zan tashi da wuri inyi aiyunakana na shige
ban fitowa sai ya fita zan fito falo in zauna.
Kaina ya isheni da kaikayi don haka naji ina son yin kitso na rasa yadda zanyi
dashi gashi yana damu na.
Don haka ranan zai fita da safe na samay shi yana cin abinci na dan tsuguna nace
da shi don Allah ina son in fita zuwa gyaran kai don kaina na bukatan gyara.
Baiyi magana saima nuna yayi kamar baijini ba na kara maimaita abinda na fada da
farko ya dago ya kalle ni a lalace yace umurnina kike jira komay ?
Nace bakyau mace ta fita bada imurnin mijin ta ba yagama ya mike yana ce min kin
san garin ne da zaki fita idan kin shirya na saukrle ki wani wuri a nan cikin
unguwa.
Da sauri nace na shirya na shiga daki na sauko hijjabi na saka da man kitso
nafito ya bini da kallon kamar zai yi magana sai kuma yaja tsuki kawai ya fita.
Na bishi baya ya juyo cikin tsawa yana fadim ni zan rufe maki gida ko may sai na
juya da sauri na tafi rufe gidan kafin in zo har ya tayar da mota ko ina shiga ya
fisgi motar da kar fin tsiya dan can kasan lalayin mu ya kaini ina sauka ya mika
man kudin kitson na karba yaja motar shi ya tafi.
Ni na kai kaina wuein mai kitson nai komai nan na hadu da wata mata bahausa muna
dan hira da ita harna sake jikina sai nake cewa idan zatai kitso wani karon tazo
zan mata.
Ita kuma ta fara tallanta min kitson wurin matan hausan dake kusa sukai aman,
na da zancen kitson nawa.,
Na dawo gida cikin walwala da dan sakin jiki koba komai yau na hadu da hausawa
yan uwa na mun taba hira duk da dai ba a jaha daya muka fito dasu ba amma naji
dadin hakan ayau.
Sai dare ya dawo banfito ba balle in gan shi sai da safe ko da na tashi na samu
har da abinci yaci sosai.
Na hada breakfast na aje mashi komai da zai bukata na wuce daki abina zaune nake
na kunna kira, a ina bi a hankali.
Ya shigo dakin sai ganin shi nayi a kofan dakin daga shi sai gajeren wando babu
ko riga ajikin hannun shi rike da taba yana busawa.
Shi kan shiyagane dan firgita danayi a wannan lokacin da gani shi sai kawai ya
sai ya kyalkyale da dariya.
Ya lura da taban da nake kallo sai naga ya kalla ya dan girgiza kan shi saiya
kashe taban gaba daya a dakin.
Kusa dani yazo ya zauna yana bare tomtom ya jefa a baki yana tsotso a hankali.
Kusa dani yazo ya zauna ya shiga neman hannu na sai nai tsam na mike tsaye na
koma can kusa da window na tsaya na bashi baya sai tuna nake koma na barmai dakin
ne sam ban san ya baro gado ba yazo inda nake.
Sai ji nayi ya zagaye man kuguna da hannayen shi biyu yana fadin yau zan cire
wanan jin kai da kike min a gidan nan.
Take na zazzaro idanuwa na don tsoron abinda naji ya fada sai yace may kike nufi
dama yana kokarin rungumoni na shiga kokarin kwatar kaina yace dama kiwon ki nake
yi da nufin ki kina cinye min abinci ga bazane.
Ko kina nufin baki san abida aka kawo ki yi nan bane sai girki da shara ki kwanta
kawai ko nufi kike baki san matsayina a wurin ki bane yanzu.
Rokon shi na shiga yi ina fadin kayi wa Allah ya Ahmed ka kyale ni don Allah,
na samu na kwace kaina gare shi zan gudu naji ya kara fisgoni tare da zaro min ido
wanda tuni sun juye sun koma wani launi.
Yace don't be stupid baki da hankaline kike jayayya dani koke mahaukaciyane kina
nufin haka zan zauna dake ina kallon ki.
A sanyayye na sunne kaina idanuwa sai kwalla ke fita nace don Allah kayi hakkuri
har na shirya sai ya watso min wani kallo na bai amin ce ba.
Ya kara juyani a hankali muna fuskanta juna kaina yana kallon kasa na ji ya kara
dagoni tuni naji ya hada bakina da nashi irin na jiya.
Ya rinka aikawa da wasu iron dabaru na salo salon na saukan hankali masu kama da
siddabaru da gusar da hankalin matum.
Tsaye nake kikau kamar dutse na rasa sanin dadin da yake ji har yake lumshe
idanuwan shi har takai yana fitar da wani sautin nunfashi.
Jikina har lokacin rawa yake yi zuciya sai bugawa yake yi uku uku sai da ya gaji
da jagula na dan kan shi ya janye daga gare ni yana kallona ido cikin ido ina share
hawaye yace bakauyiya kawai ashe ma kodan kiss din nan baki iya ba.
Bakina yana rawa nace kaina kasa dan kuya nace ban iya iskaci ba don ni ba yar
iska bace yace ok ashe bakin naki bai mutu ba ke nan .
Zan ko gwada maki kin hadu da dan iska yau don sau kinyi regreting din fadar baka
ga abinda zai maishe ki mace.
Dago ido nayi na kalle shi tare da shiga firgicin kallaman da naji ya fito bakin
shi sai dai babu komai a idon nashi sai tsaban fitina irin wanda katattare da
lafiyyen tazurun gaye da ya dade baiji mace a tare dashi ba.
Kai tsaye ya shiga rabani da kayan jikina tare da yi min gargadin kar in kuskura
in motsa sai faman rokon shi nake yi har da hawaye da majina .
Amma bai saya fasa abinda yake yi ba saida ya barni daga ni sai under wear kadai
ya tsaya yana kallon na daga sama har kasa har yatsun kafana.
Ya tabbatar da duk abinda yake so da kwaydayi gun mace ya samu a jikina ashe
kallon da yake min na yariya don ina cikin hijjab na ko yaushe.
Azahiri ba hakan abinyake ba don na zarta tunanen sa fiyye da yadda yake
tsamani .
Take kirjin shi ya shiga bugawa da karfin gaske yayarda mahaifiyar shi tai mashi
zabin daya dace dashi yau.
Lallai zai more a gun wanan yarinyan duk wani lafiyayyen nami ya gani dole ne ya
kyasa can yace cikin tsawa me , , kukan may kikeyi haka ?
Naji muryan shi ya juye kamar batashi ba don maganan ya juye kamar wanda ya damu
da ni .
Da kyat na daure na bude bakina mace don Allah yaya kayi hakkuri kada ka taba ni.
Ya nisa yace in nai hakkuri may zaki bani da zakice nayi hakkuri

8 / 87