Advertisements
Chapter 66 Reading Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   66 / 87

195K to 198K   out of 258.3K words

saurin fadin tazo gulma bata da ko lafiya.
Shirin fita dakin sukayi su sai ya dakatar dasu da fadi No ku zauna abinku ni
fita zanyi nazo duba madam dina ne.
Samira tace gako madam nan ta sauke gajiya yaron ya tambaya khadija tayi saurin
fadi yana gurin gwago ai kun samu maigadi yau gwago bata bari kowa ya dauke shi ba
yau ita da mummy.
Yace amma sun kyauta min ina can ina tunanen wanan taron dana gani za ai ta
jagulamin yaro da kuma na tuna mummy na nan sai ban damu sosai ba.
Khadija tace oho ita anty nawa fa dariya kawai yayi ya fita dakin har ya kai kofa
ya juyo yace khadija ba fa dake za a koma ba kinji na fada maki.
Samira ce tace bayan ya fita daga dakin ashe uncle yana magana haka mai tsawo
nace yan maganan dai ke kusa yau.
Washegari baki basu shigo da wuri ba don gajiyan da suka tara sun fita zuwa
kasuwa masu shiga gari ma sun shiga ziyaran yan uwa sai iyayyena da suka ce gidan
yaya Saadu zasu tafi suga gida.
Dare anan sukaci abincin dare aka kwashe su zuwa masauki sai washe gari zasuyi
asubancin komawa gida.
Zaune muke daki suna ta faman saka kaya a leda wanda yaya Saadu ya shigo dashi
gidan da za a bawa baki sallama matsayin kyautar bukin su.
Na kalli Rukaiya nace yanzu haka kike zaune a gidan baki sanaan komai Rukaiya ga
yaro ta dago kai tace to yaya zanyi Safiya.
Ni dai zaman yafi min zama gida wurin inna don yanzu sai ta ganin zatai fitinan
ta ranan da ya samu ya kawa muci randa bai samu ba muyi hakkuri hakana.
Nace yanzun dai zan baki wasu dan kudi sai ki dinga juyawa shima zan baki kikai
mai amma don Allah ki bashi don zaman magidanci ba sana,a ba dadi wallahi.
Don ina tuna lokacin da muke kanana baba baida wani sana,a irin wahalan da
iyayyen mu mata suka dinga yi a gida.
Tace bari kedai lokacin ai ba a magana amma yanzu ga baba nan kamar ba ayi ba ya
gyagije ya zama kamar yaro dashi.
Nace wanan leda ta saka mai turmi uku takai wa kishiyoyin ta komai ta saka ma nan
na shiga lissafa masu duk muka cire ma wa yanda suka zo sai mahaifiyar Amina don
Amina nada tsohon ciki bata samu zuwa ba.
Kudi na mike na dauko na bata nace ta cire dubu hamsim taba mijin nata dubu
hamsim Khadija ne ta katse ni da fadin itafa ba a cire mata leda ba.
Nace ba kinji uncle yace ba tare dake zasu koma ba nasan kuma da gaske yake yi
tunda kikaji ya fada.
Tace ita dai a cire mata nace zabi wanda kike so ba shike nan ba Rukaiya na ta
min godiya nace tadai samu sana,a da zatayi dasu nasan zasu isheki ai.
Washe gari ko wani mota ya basu na shan ruwa hanya kusanna lokaci daya suka tashi
sai gidan ya koma saura mu kadai a ciki.
Sai yan wirin aikin su Nura dake ta faman gyaran gida don tsabatace wuri uncle
badai tsabta ba kan don bai son kazanta ko kada shi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/2/20, 11:42 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , ,

6️⃣9️⃣6️⃣
6️⃣
🧕🏿 9️⃣9️⃣6️⃣


Ban fasa ja maki Allah ya isa ke ko kai mai fitar min da novel waje ubangiji yayi
min bakar isa akan ko waye don gangancin yayi yawa baki da tsoron Allah ko baka da
tsoron Allah na roki Allah yabi min hakkina akan wanda ya fitar da wanda ya karanta
bai biya ba cikin gagawa.
Allah nasan kana amsa min rokona don akan hakkina na nake magana bana wani ba
ubangiji na kara kai kuka na gare ka kahana ma mai shi farin cikin da yake nema don
shiga hakkina da yake yi.
Ranan da bakin mu suka tafi munyi barcin gajiya sosai a gidan sai yamma kowan
mu ya ya tashi naji dadin barin khadija da akayi min don zata debe min kewa sosai a
gidan.
Yaya Saadu na samu ya tsaya min akan ta tsaya din don su mama sun kafe sai da ita
zasu koma don baba zaiyi fada idan ya dawo.
Sai yaya yace ace shiya ce ta tsaya din haka yasa sukai shiru suka kyale ta badon
sun so ba tun dai inna da tasan zaman na ta na iya zama wani alheri a gare mu.
Samira bata shigo ba sai bayan kwana biyu da suna tazo gidan nan muka baje muna
duba kyaututukan da muka samu ga bukin.
Itace da dago tana fadin yanzu ai zaki fara shiga mutane musanman matan yan
wurin aikin mijin ki da sukazo maki kara kin san dole suma idan ya samay su kije
masu.
Nace nasan zamu kwasa da uncle ta wanan fanin don ba ko wani zai bari naje ba
tace ana dai son mutum da zumunci ba ko yaushe ki zauna sai dai azo maki ba.
Muna cikin hiran ta jefo min tambaya tace anty ki dai bata zo ba bata turo maki
sako ba ko nace antyn nan nawa fushi take yi dani har yanzu samira.
Ai dole tayi fushi dake tunda baki bar masu miji sun aura ba nace ba haka na bane
akwai dai kila abinda nayi mata wanda ni ban sani ba.
Samira tayi saurin cewa ga abinda kikai mata nan kuwa Allah ya kyauta nace da
ita tare da fadin ni ban son komai ya fito daga wuri na don irin halarcin da tayi
min a rayuwa na ba zan iya matawa da ita ba.
Ikon Allah yanzu kayan da khadija na take sakawa sai naga sun zama min na yan
kyau wanda a da ni bani ko saka irin su don ban ma samay su ba.
Haka yasa na bude wardrove dina na fitar mata da duk kayan da nasan ban amfani
dasu yanzu don samun ci gaban rayuwa da na samu a tare dani .
Wanda Allah yayi min gatan da ban taba zaton zan samay shi a rayuwa na sai gashi
cikin hukucin Allah ya wadatani da abinda ko a mafalki ban taba mafalkin haka ba
agare ni.
Yau da nayi wanka na tunkari dakin Uncle dauke da Abbati a hannu na wanda yasha
kayan sanyin da mummy ta saka mai cikin kayan da muka da uncle a kasan Spain.
Kayan sun matukar karban jikin yaron don ko wa yaga kayan zai yaba da kyawon su
a jikin yaron ya hade da kyau halittan da Allah yayiwa yaron.
Sallama nayi tun daga kofan dakin uana ciki kwance ya amsa min na shigo tare da
kura mai ido ina mamakin ganin shi kwance har wanan lokacin.
Sai da na samu wuri na zauna na fara gaida shi da kwana ya karba min cikin dan
dagowa yana kokarin mikewa zaune nace Uncle yau ba aiki ne , ?
Murmushi yayi yana kai hannun shi ga yaron haka yasa na mika mai yaron dake
hannu din gaba daya ya karbe shi ya rungumay a jikin shi tare da fadin.
Bawan Allah ka yafe muna Abbana ba laifin mu bane hana maka abincin ka da mukayi
son lafiyan ka ne ya kawo haka gare ka.
Wani irin abu ne naji ya ziyarci zuciyana lokaci guda tausayi da damuwa nace
tamu kaddaran ratuwan ke ne ubangiji ya bamu ikon ciye jerabawan mu.
Amin ya fada cikin lumshe idanuwan shi yana sauke ziciya yace duk abinda nake yi
tunanen yaron nan yana cikin raina wallahi.
Uncle sai hakkuri ai tunda ma yana shan madara da sauki sosai wallahi yace yana
sha sosai ko nace yana sha cikin sanyin murya.
Yace ai mu godewa Allah da ya nufe mu da rike zurian mu da hannun mu sai muyi
fatan Allah ya raya munashi nace amin Uncle.
Dakata yace dani nayi saurin dago kai ina kallon shi yace ni wanan Uncle da ake
kiramin ya isheni fa yanzu Allah ya bani da kamar kowa don haka akirani da sunan
baban dana.
Dariya ya bani nace ai su yan biyu suka sakani kiran ka uncle da sauri yace dama
ina son in tambaye ki wai ko madam ta kiraki tunda kika haihu ?
Nace eh ranan da na haihu ta kirani da yamma tana fada dani wai ban fada mata
cewa ina da ciki ba sai haihuwa kawai taji a wurin daddy.
Bata ji ba fatace maki nace abinda ta fada min ke nam yace tun muna Spain na
kira su na she da mata zancen cikin ki.
Wai may matar nan take nufi ne haka shiru nayi mashi ya sake cewa ko bayan
maganan mu akwai abinda ya farune a tsakanin ku na kada kai tare da fadin wallahi
ni matsalan komai bai taba shiga tsakani na da ita ba.
Doka tasa min in dinga tura mata kudi zata san abinda zatayi min dashi nan gaba
kuma ina tura mata da kudin duk karshen wata idan kaba salary dina.
May ne ?
Ya tambaya cikin dan zaburowa daga inda yake kishingide da yaron saman kirjin shi
yana dan shafan bayan yaron a hankali.
Nace a hankali ina tura mata kudin kamar yadda ta bukata yace Safiya ashe baki da
wayo haka ban sani ba ?
Yanzu ko shafiu ku ko khadija suna iya yin wanan wautan da kikayi to bari kiji ni
ina baki kudin nan ne don ki tare lalurar ki wanda ba sai kin fada min ba.
Na dauka gida kike tura masu suna amfani dashi ashe ke baki san ciwon kan ki ba
ban sani ba to bari kiji.
Inda maimuna ko ba da ita tunda Allah ya kadara aure a tsakanin mu har da rabo
ita bata isa ta hana ba ko ta sa ayi wanan abu ne nufin Allah.
Allah dai ya nufa ta dalilin ta zamu hadu idan kuma yaso zai iya hada mu ta wani
dalilin bata gurin ta ba.
Daga yau na yanke duk wani hurdan dake tsakanin ki da ita har ma da kowa nata
idan kina yi don ban son rainin hankali.
May ta mayar dani ne wai taga ta biyo ta hanyana bataci galaba na ba shine yanzu
ta dawo gare ki .
Zan kira mijin ta yayi mata iyaka dake tun wuri ta shiga hankalin ta dani kafin
rayuka su baci kada tace ko ban san abinda takeyi bane a baya na sani sarai
albarkacin mijin ta da yaranta take ci gare ni.
Mun kwasa da ita akanki sosai amma ke baki sani ba don ba dole bane sai kin san
yadda mukayi a kanki da ita shine ta biyo ta baya wurin ki tana min yankan baya
ko ?
Ta nuna min cewa ke ba komai bane na nuna mata cewa ke wani abune mai muhinmanci
a gare ni yadda take daukan ki kin wuce nan a gare ne.
Don so tayi shawaran komai dole sai da ita zanyi ban isa in ma dan uwana wani
abuba ko ke ba ta hanyan ta ba.
Ranan ta jini sosai don rufe ido nayi naci mata mutunci ta yadda bata zata zan
iya masu ba.
Na nuna mata kina da mahinmanci a gare ni fiye da kowa nawa a yanzu da taga hakan
ta bai cin ma ruwa ba sai ta juyo tanan din dake.
To zanyi maganin ta tasan nafi karfin ta da mijin ta taci albarkacin shi wallahi
da yau nasa ta dawo maki da kudin da duk ta karba daga gare ki.
Zan kara maki kashedi a kanta kada naji kada na gani na yanke duk wani alaka da
ke tsakanin ki da ita daga yau din nan kinji na fada maki ko ?
A sanyaye na amsa mashi da eh ya koma ya kwanta tare da lumshe idanuwan shi ya
fita batuna ranshi na bace da maganan da mukayi akan anty din.
Na dade zaune na kasa ko motsawa daga inda nake shi kuma ya fita batuna sai can
na yunkura na mike na fita dakin na barshi da yaron .
Daki na koma na samu khadija kwance tana kallon tv dake aiki tana kallon wani
series na yan Chaina kin dawo tace min na amsa mata rai babu dadi da eh kawai na
bata amsa dashi.
Samun wuri nayi na kwanta ba tare da nakara magana ba nasan itama ta fahinci
akwai matsala ne sai ta kyale ni taci gaba da kallon ta.
A idan nake har barci ya dauke ni ban sani ba ina cikin barci ne naji yana
kokarin ta dani daga barcin yana dan jijigan yaron dake dan kuka a hannun shi.
Mikewa nayi zaune ina kokarin amsan yaron a hannun shi yace abashi abinci ina
ganin yunwa yake ji ya fada.
Madara khadija ce ta mike da sauri ta hada ma yaron madara ta karbe shi a hannu
na ta fara bashi ya karba da sauri yake jan feeder.
Uban ya dan dade tsaye yana kallin yadda yaron ke jan feeder da sauri murmushi
yayi ya nufi kofan dakin yana cewa Khadija ashe kin iya reno ne haka ?
Dariya tayi kawai bata samu bashi amsa ba hankalinta na ga yaron da take ba
abinci saida ya fita dakin na samun bakin magana.
Nace dama bai sha ba da akai mai wanka yayi barci shine na kai shi wurin baban
shi su gaisa nasan ya tashi ya damay shi da kuka ne ya kawo shi.
Hira muka dan fara yi da ita kadan kadan har na dan sake na fitar da damuwa da
nake ciki tana mi labarin yadda zaman gidan mu yake yanzu.
Nace yanzu da baki koma ba wazai dubi su wasila dake gida tace ai gwago ta fada
ma su mama Jummai su koma wuri su da zama kafin ummi ta dawo.
Amma kuma nasan ko basu koma can din ba ai mama zata kula dasu a gidan don mama
na kokari sosai wallahi duk da gorin da inna take mata akan abinda take yi din.
Yunwan da na fara ji yasa muka fito falo in ci abinci khadija na goye da yaron a
bayan ta lokacin su gwago suka fito daga dakin da suke suka samay mu a falon.
Mummy ne ke fadin ai na dauka kuna barci ne danaji shiru nace barcin baiyi nisa
ba muka tashi sallaman akayi kofan shigowa muka amsa.
Aisha ne tare da wata makwabciyar ta suka shigo gidan nan aka shiga gaisuwa ta
kalle ni tace wai madam wanan irin kiba da kike narkawa fa ?
Dariya ne nace ina kiba anan duk na zube yanzu ma haka wallahi banjin dadin jiki
na karfin halin kawai nake yi wallahi.
Mummy ne tace akasarin mata idan sun haihu dama sai sunyi zazzabi wanda ake kira
dahuwan kassa don wahalan haihuwa da sukayi .
Kin san mace a wurin haihuwa duk sassanta jiki ta sai ya motsa to wanan motsawan
shike haifarwa mata da irin wanan zazzabi daga baya.
Kayan da na ware zan bata cikin wanda muka samu daga yan uwa da abikan arxiki
nabawa samira nata na Aishan ne dama ya rage shi nace khadija ta dauko mata a daki.
Basu dade suka tafi tun tafiyan su na kwanta zazzabi wasa wasa sai da ya kwantar
dani dole washegari sai da muka tafi asibiti wuri likitan shi.
Magani ya rubuta min da allura akai min yayi muna bayani cewa dole dama sai nayi
ciwo saboda jinin da na zubar a wurin haihuwa saukin abin ma don ina samun kulawa
yadda ya dace ne.
Sai dai in matsa da cin abubuwan da zasu kara min jini a jiki don kada na
jirkita da yawa kamar yadda masu irin lalurar ke shan wahala yayin da suka haihu
don jinin da ya rage a jikin su.
Duk da allurai da maganin da aka bamu sai da na wahala sosai don ba karamin jin
jiki nayi ba har na ramay sosai.
Wanan raman da nayi shiya daga hankalin Uncle sosai har ya koma wurin likita yace
mai babu komai zan samu lafiya haka abin yake wani lokaci.
Ai nawa matsalan yana da dama don kafin ciwon ya bugeni sosai an daukar mai
matakin daya dace gashi kuma ina kula da shan magani.
Na dan fara jin saukin jikina wanda ya koma nake jin shi kamar ba jikina ba ya
shigo dakin yana min sannu cikin nuna kulawan shi a gare .
Zaune nake lokacin da ya shigo dakin yake tambaya na ko ina jin wani abu yanzu a
jikin nawa ?
Nadan lumshe idona a hankali na nace mashi banjin komai uncle sai dai jikin nawa
ne ban jin karfin shi ko kadan.
Kina ko shan maganin kin akai akai nace ina sha na yaune ban sha ba don ban
karya ba tukun yace may kike jira baki ci abinci ba har tara da rabi na safe yanzu.
Nace bakomai a hankali bakin nawa ne dai banjin dadin shi dan sunkuyowa yayi gare
ni yana fadin may kike son kici sai a dafa maki.
Kunu da kosai nace mai sai naga ya daga yana murmushi yace khadija taje ta fada
ma mummy asa Nura tayi min .
Tana fita yace bari ya dauko min fruits in sha kafin a gama kada yunwa yai min
yawa a ciki nace uncle banjin cin komai wallahi bakin nawa ba dadi nake jin shi.
Ido ya dan tsura min sai yake kai zaune bakin gadon cikin kwantar da murya yace
dani ki daure ki ci diyan icce zasu taimaka maki wurin gyaran dandanon bakin ki kai
na gyada mai alaman to.
Ya mike ya fita yasa aka wanke fruits shida kanshi ya shigo min dasu dakin ina
zaune a yadda ya barni lemo mai bawa ya fara bani don zai wanke

66 / 87