Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
mai wurin samun
shi ne ai murmushi yayi tare da dan buga mi baya na yace .
John zai zauna sai ki sama mai abinyi a gidan kada yayi ta karban kudin banza ko
macen kuma za a kawo maki ita goben nan in Allah ya kaimu hakan yayi maki ko.
Nace yayi uncle na gode sai dai macen ta kasance musulma uncle don Allah yace
kuma dai za a duba ba matsala da haka har na kare na kwashe na koma nayi wanka na
shirya na fito muka zauna cin abinci .
Ban yi fushi da zarah ba ina dan kula ta muna zama muyi hira sai dai bata gane
komai a gidan yadda take so.
Ranan yaya Saadu ya shigo da marance bayan na cika mai ciki da abinci nan suka
zauna da shi suna fira ganin sun dauko hiran aiki yasa na dan basu wuri na samu
zarah a dakin ta kwance.
Tana ganina ta mike zaune nace ai na dauka barci kike yi ne tace a a kwantawa dai
nayi naga yau yaya yana gida bai fita bane shiyasa ban fito ba.
Wuri na samu na zauna kusa da ita ina cewa don yana gida shine baki fita ta dan
murmusa tace ban san abinda nayi wa yaya ba baya kallona a yar uwanshi kamar kice
yar uwar tawa yanzu don kice kawai may kula ni a gidan.
Nace a a zarah kin fi ni sanin waye uncle fa dan a tare kuka taso wuri daya dashi
yakamata ace kin san ko waye uncle yanzu.
Murmushi tayi kawai mai kama da yake tace nima ina ganin dai gida zan koma nace
tun yanzu Zarah mai mukayi maki kuma ?
Tace babu komai anty gani dai nayi kamar zaman nawa yana takura maku ne nace ko
daya wallahi kece dai kika kasa sakin jikin ki damu.
Nan dai na zauna mukai ta hira da ita sai da uncle ya kirani nabar dakin nata
yaya Saadu ne zai tafi shine kiran da yake min din.
Nan yaya din ke fada min zai koma gobe dawowan da zai yi tare da iyalin shi zai
dawo garin naji dadi sosai yake ce min yaya waya gida dazun da yana hanya.
Naji dadin haka yace baba ya fada min abin arzikin da maigidan ki yayi masu da
sauri na juya na kalli uncle din .
Yace tau bai fada maki bane bana baba da ummi zasu sauke farali a kasa mai
tsarki har da Sani don ya kula dasu.
Bansan lokacin da na juya wurin uncle din ba ina murna yaya yace ai na rigaki
yin godiya ko ya fice yana yi min dariya.
Ranan ban san ma irin godiyan da zan ma uncle din ba mun dai kwana muna farantawa
juna rai kawai don banda abin bashi bayan wanan din.
Kwana biyu dayin haka na samu uncle a daki yana shirin fita nake cewa ina son
zuwa gidan Anty Aisha.
Kamar ba zai yi magana ba sai can yace nafa fada maki ban son yawo a rayuwana
nafin inganki a gida kullun.
Nace don Allah uncle kayi hakkuri ba dadewa zamuyi ba koshi don munyi waya da
itane tace yaran ta biyu ba lafiya.
Yace sai ki shirya in sauke ku in zan fita nima in duba yaran daga can naji
dadin hakan don dama tana min korafin bai taba zuwa gidan ta ba.
Mun isa gidan akai muna iso mun samu maigidan ta dakishiryata zasu fita a lokacin
nan dai muka gaisa dasu.
Mijin nata yana ta faman kamay kamay da gani baida gaskiya nan suka fice suka
barmu da ita munga yaran basu da lafiya har lokacin.
Yake tambaya ko an kaisu asibiti tace baban nasu ya sawo masu magani dai tace
baida kudin kaisu asibiti sai naga ya tabe baki kawai.
Yana bin gidan da kallo bai dade ba yace shi zai tafi zai dawo karfe hudu ya
dauke mu naji dadi sosai da zai fita ya kira Aishan suka fita tare.
Ta dawo tana murna tana fadin yau maganan hajiya ya tabbata yau yaya ne a gidana
Safiya ?
Murmushi nayi nace albarkacin yaran ki ne ya kawo shi tace a a albarkavin ki dai
gashi har da zama gidana yau safiya abinda kullun gidan nan ake min gori dashi.
Nan dai ta shiga bani labari don ta tura zarah tai muna girki haka yasa ta samun
daman sakewa tana bani labarin halin da take ciki a gidan.
Na fahinci abubuwa da dama a gare ta sai da bance komai ba banda hakkuri da na
bata ta fitar da kudi masu yawa tana nuna min wai uncle ne ya bata su takai yara
asibiti.
Nace kin ga ko sai ki kai su don asan halin da suke ciki tace ai gobe in sha
Allahu zan kai su anan dai muka wuni tana cikin farin ciki damu.
Ya dawo ya kwashe muka tafi tana ta mashi godiya mun dauki hanya ne naji ya nisa
tare da fadin mai kika fahinta a zaman Aisha a gidan nan ?
Nace bari mu sauka uncle akwai magana ai sai ya dan kalli zarah dake baya zaune
yayi tsaki har muka kai gida ba wanda yayi magana a cikin mu.
Sai da mukai sallah ishai muka dawo falo nan na dauko mai maganan Aisha din yace
tun farko sai da na fada masu ba mutumin kirki bane suka ji.
Alokacin yana sakar masu kudi sun dauka mutumin kwarai ne niko tun tasowan mu
dashi nasan dan karya ne sosai.
Nace uncle yanzu tunda har akwai haihuwa har uku a tsakanin su baza a bi ta
wanan ba taimaka mata ko masu su duka ya kamata kayi.
Ta hanyar sama masu sanaa da zasu dogara dashi da yaran su don na fahinci tana
cikin wani hali a gida don baka ga part din kishiyar taba tsan wallahi amma ita ga
nata kamar na wata tsohuwa can.
Tsaki yayi yace ko an bata wanan mugun mijin ai ba zai bar mata ba nace uncle
adai tamaka mata din yafi don gorin da suke mata a kan ka.
Yace gori fa ?
Shi har yana da bakin da zai min gori akai wanda kulun yana office dina da
bukatar shi nace kagani shike morar ka itako bata kosan anyi ba.
Yace zai kira Aishan idan yaranta suji sauki ansan abinda za ayi mata din nace
uncle mun gode wallahi.
Kallo na yayi yace wai ke a ina kika koyo wanan godiyar taki ce haka tun bakiga
may zanyi ba kina zabga min godiya haka.
Nace koma may zakayi indai ka gyara mata wurin zamanta ka bata abinda kudi zai
dinga shigo mata ai ka gama mata komai.
Yace ai ido nasaka masu daga su har hajiyan don naga gidun su nace uncle kayi
kuskure wallahi idan basu dadi a wurin ka ba duniya wurin wa zasu ji.
Nan dai nayi ta kawo mashi musalai iri iri yana saurare na bai yi magana nasan
dai ya gamsu da bayani na ne da nakeyi.
Yace wai ke indan da kin yi karatu mai zurfi zan iya dake kuwa Safiya ?
Nace uncle don may ba zaka iya dani ba ai fahinta daban fannin aure daban don
haka karkaji komai a kaina .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/18/20, 10:16 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , ,
5️⃣9️⃣5️⃣
5️⃣
🧕🏿 9️⃣9️⃣5️⃣
NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN KIN FITAR UBANGIJI YABI MIN HAKKINA A KAN KI/KA DON
BAN YAFE BA, , , ,
Kamar yadda yaya Saadu ya fada haka ne ya faru don yayo kaura daga kalaba zuwa
abuja da iyalin shi inda suka zo da yar uwan Samira da mijinta ya rasu zata dan
kwana biyu a wurin su.
Sai bayan kwana biyu suka zo gidan mu don bamu da wani nisa sosai dasu dasu ban
san da zuwan su ranan ba sai ganin su nayi kawai a gidan.
Sun shigo ina daki Zarah ce tazo tana fada min zuwan su cewa tayi nayi baki suna
falo azatona ko anty uwace suka sake dawowa gidan.
Amma kuma sai nayi tunanen mai zai kawo su kuma in ba rashin zuciya ba yadda aka
kwasa dasu din nan ya nuna shi sam bai san su ba.
Wanda kuma nasan yayi hakane don ya kakabe su daga gidan namu gaba daya da zuwa
don zuwan nasu babu alheri a cikin sa.
Fitowa nayi sai mukayi arba da sister kamar yadda suke kiran safiya karama dashi.
Nace Lah bakin kalaba ne a gidan namu baku tsaya munzo taron ku ba har kun
tula min nauyi na aka ?
Samira tace a, a mun huttar dake aikin san ke amarya ce ba a matsamaki yanzu na
samu wuri na zauna ina mikawa sister hannu tazo wuri na sai yarinyar ta make hannun
ta bata zuwa.
Gaisawa mukayi ina tambayan su mutanen gida da sauran yan uwanta tare da fadin ai
na dauka zaku zo min da mummy ne wallahi.
Tace mun so mu zo da ita kodan azumi dake tafe takine sai da gabaya zata biyo mu
in dan ta shirya.
Nace kai mummy ho har wanu shiri zata yi kuma makin ta biyo ku kawai kuzo tare
samira ne tace wai Safiya kin ko ga yadda kika canza gaba daya.
Nace kai samira dashi kuma zaki tare ni tace wallahi safiya kin canza gaba daya
komai naki ya canza kamar ba Safiyan yaya saadu ba.
Dariya muka ka kwashe dashi gaba dayan mu falon nace aikin Uncle tace aina gani
wallahi gaskiya aure ya karbe ki sosai wallahi.
Nayi murmushi dadi har cikin rai na nace bakomai bane Samira sai kwanciyan
hankalin da na samu yanzu.
Nura na kira sabuwar mai aikina yar kabilar yarbawa ce ita ta shigo nake cewa ta
kawo ma bakina abin sha ta kuma hada abinci dasu don da mu zasu wuni.
Samira ne ta dakatar da ita da cewa wallahi a koshe muke don bamu dade da karyawa
ba muka fito gidan.
Gaba daya Samira sai yabawa da yadda aure ya sake ni take yi nan take fada min ai
jiya yayan ki yayi waya gida ashe ita yar uwar ki ta haihu ne kuma mijin yaki aurar
ta ?
Nace wallahi ai yanzu takai wata biyu da haihuwa kyale dan iska so yake sai
anbiyu mai ta bayan gida akan zancen zaimai da hankali ayi.
Tace ai naji yayan ki na fadin karshen mako zai tafi abinda ya hana Sani zuwa
kenan cikin satin nan yace ya jirashi sai ya zo.
Nace kai mutane sai sannu baison ta yayi mata ciki dan iska kawai tace ai haka
yayan ku ya fada shima yace dole ya aure ta don bai baro garin nan sai an daura
auren su.
Nace haka yagi wallahi don idan anyi mai sakwa sakwa tsarewa zai yi ya barta da
yaron tana wallaha ita kadai.
Tace ga uwar su wata kala ita kuma naji sani ya bugo ma yayan ku waya yana fada
mashi rashin mutuncin da tayi ma mama ranan.
Nace kai inna ai sai a hankali ta tare da fadin akan makkan da su baba zasu tafi
ne wai mama na maula gashi an biya wa mahaifiyar ki anbarta nan.
Wanan matar ai halin ta sai ita Samira ni ban taba ganin mace irin ta ba wallahi
diyan ta tun suna bayan ta har sun gaji sun gane ta yanzu.
Tace wai itama ko yadda minjin nan naki ya rike Sani bata ko jin kunya ta rage
wani abin amma sam bata san wanan nace wa inna aima yanzu ta rage wani abu don baba
ya fita bayan ta yanzu.
Nan dai muke ta hira har muka shiga hiran gidan su yaya Saadu take fada min
kwanaki sun tafi gaida gwago sun samu jikin yaya Ahmed yayi mai tsanani yana kwance
yana jiya a gida.
Allah ya bashi lafiya nace da ita don dan uwana ne ko banja Allah ya isa ba Allah
zai isar min da cin amanan zumuci da suka.
Murmushi nayi ina tambayan wai su habiba fa ko sun yi aure ne yanzu tace ke dai
bari sadiya ce kadai a gida wai ita habiban ta tare gidan wani saurayin ta.
Sadiyan ce ta bugo waya kwanaki tana fada ma yayan yace zai zo har muka taho
kuma bai je ba ko ta dawo gida ban sani ba.
Sadiya din ai da tace wai zata biyo mu ta dawo nan shine yaki yarda yace ta
zauna ta kula da uwa don yanzu ba wani karfi ne gare ta ba.
Nifa Safiya ba wani shiri nake yi da mutanen nan ba tun zuwan da nayi na farko
uwar da habiba ke cewa wai ya auro masu kwatakwalin ghana.
Na lah kece wai kwatakwalin ghana tace wallahi ko ai nace masu ni uwana da ubana
yan katsina ne aiki dai ya kaimu kalaba baba kuma yayi ritaya bai koma gida damu ba
amma har yanzu muna zuwa garin mu.
Dariya nayi kawai ina tunanen rayuwan da ya wuce baya irin cin fuskan da gwago da
habiba suke min sai sadiya ce mai kula ni a garin da ban san kowa ba.
Su kuma sauran mazan biyu yanzu duk sun kama gaban su kowa ya watse dama
haihuwan bariki ke nan.
Mun dade muna hira sai da muka mike zuwa sallah muka dawo muka zauna cin abinci
tare muka gyara gidan dasu kafin su wuce sai yamma yaya Saadu yazo ya kwashe su.
Kafin su tafi mun dan tsaya da yaya saadu munyi magana akan matsalar saadatu
dashi in da nace kafin ya wuce gida ya biyo ta wurin tukun.
Mukai sallama suka tafi lokacin shima mai gidan ya dawo wurin aiki ya samay su a
gidan mintsila naji yakai min gefe na na dafe wurin da sauri ina kallon shi.
Yace yau don kin ga yan uwanki shine ko hugging ban dan samu ba nace afuwan
yallabai kasan dan uwa aikwai dadi wallahi.
Ya riko min hannu muka shiga ciki yana fadin tafiyan mu fa yana matsowa don haka
nake son muje ai maki pasphot din ki.
Naji dadi nace uncle ashe da gaske kakeyi batun tafiyan dani zaka tafi kai ya
gyada min tare da fadin kin dauka wasa nake yi baza mu dawo ba sai mun tsaya umura
daga don watan azumi da zai kama.
Don ni ban azumi a kasan nan a can saudiya nake azumina don haka nake son mu samu
lokaci muyi list din mutanen da za a taimakawa.
Nisawa nayi alokacin da muka iso wurin kujerun falon tare da zaunawa sama har
lokacin bai sake min hannu ba.
Nace uncle, , in uncle dama akan maganan su Aisha ne har yanzu naji shiru akan
zancen shine nake maka tuni na fada tare da dukar da kaina kasa.
Tallabo habana yayi yana fadin ban manta ba ai akwai abinda nake shiryawa a kan
su su ukun duka har ma da sauran yan nasu.
Sai dai da farko tunda kin matsa sai ku shiga da ita Niima house decoretion ku
zabi abinda ya dace da ita sai a gyara mata part din nata ni inda mijin zai yarda
sai in bata gidan da zata zauna da ga ita sai yaranta kawai.
Dadin maganan shi naji kamar yan uwa na za aiwa hakan sai nakai mashi runguma
tare da bashi kiss gefen fuskan shi.
Murmushi ya sauke yace ashe kin iya nokewa kawai kikeyi yanzu da nayi maganan
masoyiyar ki aikin bani ba tare da na nema ba.
Nan dai muka zauna har lokacin sallah yayi muka mike zuwa sallah ina maijin dadi
sosai a raina bayan na idar da sallah ne na jawo wayana dake jone a caji ina kiran
Aisha din.
Ta dauka tana fadin matar yaya dazun fa nake maganan ki a raina nace na zama yar
halas ke na kin ki ambato tayi dariya kawai.
Nace kin samay tace a a matar yaya sai kin fada nan dai na kora mata albishir din
dayayi mata akan gyaran wurin ta da kuma zancen mijin ta ko zai yarda a bata wurin
zama ta zauna daga ita sai yaran ta kawai.
Tace cikin sauke ajiyan zuciya wallahi da yaya yaimin haka da ya kyauta min
wallahi ni ko bai yarda ba komawa zan yi idan ya bani wurin zama.
Nace ki dai lalabashi ko zai yarda da hakan tace wallahi ba wanda yasan halin da
nake ciki a gidan nan ne da yaya ba zai fadi haka.
Daga maigidan har abokiyar zaman nawa hakkuri kawai nakeyi a zaman mu don dai
kada in koma gida ne aimun dariya da kuma yara da suke samun karatu a nan.
Nan dai mukayi ta hira tana fada min irin kuntatawan da suke fuskanta ita da
yaran ta a gidan wurin kishiyar ta da mijin ta.
Shigowan shi dakin nawa ne ya katse muna hiran mu sai da ya zauna bayan mun gama
wayan naji yana tambayana ke da wakuke wayane haka tun dazun.
Nace anty Aishan kace yace ok nan dai nake fada mai halin da take fuskanta a
gidan har na gama baiyi magana ba dama kuma ni ban tsanmaci yayi din ba yana dai
iya bani lokaci wurin saurare na.
Da safe Aisha tayi sakkon samun shi gida kafin ya fita nan dai na basu wuri suka
kebe da dan uwan nata karshe dai da ya fita na shigo na samu tana share hawaye.
Ruwa na koma na dauko mata na kawo mata ina fadin tasha ko zataji sanyi take ce
ai bata ko karya ba ta fito Nura na kira nace ta hada masu breakfast a daning.
Sai da taci ta koshi har yaran nace Anty Aisha kiyi hakkuri don Allah komai na
duniya mai wucewa