Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
min bakin nawa
yace.
A haka dai har na dan ji sauki saboda kulan da nake samu ta ko wani bangare har
naji sauki na murmure kamar bani ba.
Ranan ina zaune kwatsan sai ga Faiza gidana tazo nayi mamakin ganin ta kwari da
gaske tace wai anan abuja ta kwana ta fito lagos zata gida bauchi ne.
Nan da nan nasa a cika mata gaban ta da abinci da abin sha muna hira tana cin
abincin dake gaban ta labari take bani na anty yadda take zagina wai yanzu na guje
ta don ina ganin na samu gidan miji.
Ai tasan asiri nayiwa Uncle ya aure iyayyena makwadaita ne sun ga kudi idon su ya
rufe wai idan ummi na ta kira ta tana ganin kiran sai taki dauka.
Dariya nayi nace anty ke nan yanzu kuma nice na koma abin zagi a wurin ta tace
tun yaushe ai na fada maki halinta tun farko shiya kike ganin ina fada maki .
Yanzu haka Fati tabar wirin ta uwarta ta dauke ta ta mayar da ita can yobe garin
su don yawan matsalan da suke samu akan fati din.
Ranan dai a nan ta kwana sai dai ban yarda na fadi komai ba akan anty din don
yanzu mutum abin tsoro ne washe gari ta wuce bayan na cika ta da abin arziki .
Kwana biyu sai ga yaya saadu yazo yana ce min zai tafi lagos an bugo mai waya
jikin gwago da na Ahmed wai ya tsanan ta don haka zai tafi ya dubo ta.
Kudi na dauko nace ya kaiwa gwago ya gayar min da ita idan yaje yaso yaki karba
amma na matsa mai sai da ya karba don sako ne na bashi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/3/20, 8:54 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , ,
7️⃣0️⃣7️⃣
🧕0️⃣7️⃣0️⃣
Tu wuce wanan yaya saadu ban tuna da zancen gwago ba sai da yake da kwana biyu da
tafiya ya bugo min waya ya hada mu da gwago wai mu gaisa da ita.
Ba yadda na iya shiru ya dan biyu bayan wayan can na ce salamu alaikum ta amsa
da fadin Safiya nace naam gwago kuna lafiya yaya jikin naki.
Ta cikin wani murya mai rauni ta amsa da jiki da sauki safiya yaya wajen ku kuna
lafiya ko nace lafiya muke gwago tace naga sakon ki wurin dan uwan ki na gode
Safiya.
Nace babu komai gwago Allah dai ya baki lafiya tace amin sai ta kama kuka tana
son yin magana amma kuka ya rinjayi maganan da take son yi din.
Nikan sai na kashe waya don kada ta kashe min jijiya bayan na kashe ne yaya Saadu
ya kirani ya ce kinji gwagon ki ko ga Ahmed yana gaida ke jikin nashi ne ba dadi
sosai nace ka gaida shi Allah ya bashi lafiya.
Ya san ban amsan wayan shi ke nan yasa ya kyale ni bai hada ni dashi din ba ya
tambaye ni yaya Abbati nace yana wurin gwago ta goya shi.
Bayan mun gama wayan khadija dake zaune gefe na da mummy suka ce wai amma kina da
karfin hali wallahi.
Mummy tace ai gara da tayi masu haka na ta barsu da aniyar su ko yanzu Allah ya
gwada masu abin su ai.
Ni dai murmushi nayi kawai ban ce komai ba sai dogon tunanen da nashiga tun
lokacin kuma na watsar da zancen su a zuciya na gaba daya.
Haka rayuwa ke ci gaba ga duk mai rai da lafiya cikin hukuncin ubangiji har gashi
nayi arbain da haihuwa yaro kuma yana cikin koshin lafiyan shi.
Yayi mulmul dashi bazaka ce bai shan nono ba idan ka ganshi don iri kulawan da
yake samu na abinci da magunguna da zai bashi lafiya da kuzari.
Tun da nayi arbain nake ta shirin zuwa gida kunsan maza da jan fitina amma sai
uncle yace ba zan tafi ba sai munje bauchi mun kai ma baaba yaron ta gan shi.
Naso tayar da hankali mummy da gwago suka sani gaba sukace ko murai kada na nuna
mashi komai yadda yake so in bishi da hakana muje mukai ma mahaifiyar shi jikanta
ta gani.
Haka yasa na daure ban nuna mashi komai ba da yake tsanmanin zan ce ban yarda ba
da hakan daya tsara muna don yasan yadda nake dokin zuwa gida .
Wanda tun aure na dashi banje garin mu ba ina binshi a yadda yake sona dashi din
don kawai a zauna lafiya.
Dole akalan tafiyan yacan za ta zuwa bauchi din mummy da gwago zamu barsu gida
sai mun dawo da khadija kawai zamu tafi.
Mun shirya tsaba inda ranan jumma, a zamu bi jirgin safe mu tafi kamar yadda ya
tsara don har da buki zamuyi na diyan wani kawon shi haka yasa na dauki kaya na
alfarma don tafiya dasu.
Inda motacin shi na shiga biyu sun kama hanya da tsaraban mu da kayan mu zasu
samay mu acan kamar yadda ya tsara din.
Mun sauka lafiya inda su Nafiu suka zo daukan mu zuwa gida da motaci biyu mun isa
mun samu yan uwan shi mata suna gidan kaf din su sun zo tariyan mu har da Aisha da
ta tafi sati daya daya wuce bukin kannen mijin ta.
Mun sauka inda suka fito waje taron mu yaron yana hannun khadija har muka isa
gidan nan suka karbe shi kowa na nuna kulawan shi akan yaron sai fadi suke Abban mu
Abban mu.
Suka nufi cikin gida da yaron su kuma suka tsaya muna gaisawa tun a waje part din
hajiya baaba muka nufa gaba dayan mu don mika gaisuwa a gare ta.
Koda muka shiga mun samu ta karbin yaron tana fadin Allahu akbar yau jinin babana
a hannu na haka ina kallo da raina da lafiya na.
Muka shigo da sallaman mu muna gaida ita ta juyo gare mu cikin farin ciki tana
muna sannu da zuwa tare da fadin ai yanzu kin zama uwar mijina kuma wanan irin
mijin da kika haifo min haka?
Murmushi nayi ina kai gwiwana kasa dukka guda biyu tare da fara gaida ita cikin
girmamawa .
Amsawa take yi yayin da hankalin ta ke yaron tana fadin wanan duk gida ya kwaso
wallahi ana fada ban yarda ba sai yanzu dana gani da ido na.
Uncle ya ce hajiya mun samay ku lafiya tace sannu kai dai dan Albarka ai duk na
rude da ganin wanan mijin nawa da Allah ya nuna min zuwan shi da raina da lafiya
na.
Sai da ta jagula yaron anty Suwaiba ta karbe shi sannan ta dawo da hankalinta
gare mu sai lokacin taga khadija da muke tare tace a a da bakuwa kuke ashe ?
Da ganin wanan yar uwar Safiya ce don kama ya nuna kanshi basai antambaya ba
wanan kamar uncle ne ce kaunar ta dake wurin ta ne ai tunda ta haihu suka zo suna
take nan tare da mu.
Gaisawa sukayi da khadijan tare da tambayanta yaya hanya ta amsa cikin ladabi da
lafiya lau hajiya.
Juyawa tayi tana fadin ku kawo masu abinci mana kun tsaya kuna shiriri ta haka
suka ce hajiya baki ce a dauko masu bane ai.
Yau ga tsiya tace dasu abincin ma sai nace ku kawo masu zaku dauko masu uncle ne
yace hajiya bar abincin nan yanzu a dai kai muna can part din mu zamu fi jin dadin
ci acan.
Nan aka shiga kwasan abincin zuwa part din mu dashi shi kuma suka ci gaba da
gaisawa da mahaifiyar tashi.
Nan na juya wurin Aisha nace mutanen bauchi ke nan ina yaran suke tace suna can
gida na barsu banzo dasu ba yau.
Hiran mu muke yayin da hajiya da dan ta suna can zaune a inda muka barsu suna
magana a tsakanin su.
Karshe ma sai su Aishan suka jamu zuwa cikin uwar daka nan muka shige daki guda
daga cikin dakunan part din nan dai muka fara hira tana cewa ai ta godewa Allah da
muka iso yau gobe ne bukin gidan su sai muje mata karan buki da sauran yan uwa.
Kiran da hajiya tayi ma suwaiba sai gata ta dawo tana fadin wai mu fito zuwa
part din mu uncle yana son ya huta haka muka fito muka nufi can har lokacin yaron
na wurin hajiya tana bashi madaran da khadija ta hada mashi.
Mun shiga part din komai neat kamar muna cikin shi ko yaushe yasha gyara sai
kyali yake yi nan na aje handa ban dina Aisha ta biyo mu da dan troley din da muka
riko.
Abincin da aka aje muna muka fara zama ci inda masa ne wanda yasha mai sai kyali
yake fari tas a cikin kula sai miyar kassan rago da akayi da ganye alaihu sai
kamshi ke tashi ga ferfesun kaji dayaji kayan kamshi yana tashi shima a kulan shi.
Nan dai muka taru muka fara cin abincin sai santi kowan mu keyi kan dadin masan
dake gaban mu uncle ne kawai bai magana sai murmushi yake muna kawai.
Mun ci munyi kat ko dinban ferfesuf din bamuyi ba ni da uncle sai khadija ne ta
dan sha kadan ta ture don ta koshi da masan da taci .
Yaron ne aka shigo dashi yana kyallara ihu kamar wanda wani abu ya sama karban
shi nayi ina fadin yanzu haka fitsari yayi yake damun shi haka yake yi idan ya bata
pemppers din jikin shi.
Tube shi nayi gaba daya na cire mai tufafin dake jikin shi don in sauya mashi
wani na shan iska nagama shirya shi na kara mai madaran tare da bashi grive water
yasha sai gyatsa na bawa khadija shi ta goya.
Kwantawa nayi don in huta don tafiyan safe da mukayi barci ne taf a idona lokacin
shima uncle ya kwanta bai fita hanin kowa ba a lokacin don yace yana son dan hutawa
ne .
Koda na farka khadija na kwance sunyi barci da Abba a jikin ta haka yasa na dan
mike a hankali kada na tayar dasu daga barcin dakin .
Na samay shi yana barci ga sanyin AC ya karade dakin zuwa nayi wurin shi na dan
taba mai huska a hankali sai ya bude ido nace lokacin zuwa masallaci yayi kada ka
makara.
Salati yadan yi tare da juyawa yana fadin badon kin shigo ba da na makara don
naji dadin barcin nan sosai wuce wa nayi bathroom na hada mai ruwan wanka na dawo
ina fada mashi ruwa ya hadu.
Ok kawai yace na juya zan fita daga dakin yace ai na dauka za a bani goron jumma
a ne kuma sai zaki fita .
Na juyo da dariya na nace kai uncle har a garin mutane ba a bakun ta na fice ina
dariya don nasan in nayi sake bai da wasa wirin wanan harkan.
Wanka nayi nima na sauya kaya a lokacin sai gashi ya shigo cikin wani farin yadi
mai laushi da taushi yana daukan ido da hular shi a hannu yana gyara karata da
kyau.
Wayan shi ne tayi kara ya dauka su musa driver ne suka iso suke sanar dashi zuwan
su tare da tambayan ina za a nufa da kayan.
Yace su shigo dashi part din shi nan ya juya zuwa wurin su yana fadin daga can
zai wuce masallaci ne nayi mai a dawo lafiya.
Lokacin khadija ta falka bayan fitan shi ne tace sai yanzu masu motar suka iso
garin kai amma akwai nisa ashe haka ?
Kodon da jirgin mukazo mu sai naga kamar ba nisa wallahi nace kema kin san ai da
nisa mana zaki hada tafiyan mota da jirgine.
Shigo da kayan yasa na fito falon ina gwadaasu inda zasu zube muna kayan don ba
karamin tsara muka lafto masu ba wanda zamu raba har uncle na fada wai kayan sunyi
yawa haka.
Sallah na dawo na tayar don lokaci ya gabato ina son inyi nafila kafin jumma a
din sai da na idar na juya wurin khadija dake kwance har lokacin nace hajiya sallah
fa.
Ta nuna min yaron dake saman hannun ta kwance wai kada ta tashi yaron ya motsa
na watsa mata harara nace yanzu don kada ya tashi ne bazaki je kiyi sallah ba.
Tana mikewa yaton na wani irin zabura ya fara dan shure shuren kafa yana dan
kuka sama sama nace ashe aiki ya ganku kuda kuka koya mashi hakan ?
Nikan ba wanda zai hanani barci yanzu kuka yake sosai dole nabar adduan da nakeyi
na kamashi ina lalashin shi.
Dan shiru yayi dole na goya shi a karo na farko tunda na haife kasan cewa su mummy
da gwago ke faman dawainiya dashi a gida.
Ni iyaka na dashi in dan dauke shi inyayi koka kuma in mikawa mummy shi su karata
can amma kasancewa yau basu kusa dole reno ya dawo kaina.
Khadija na fitowa bayi wanda nake ganin wanka ta tsaya yi ta kalle mu ta
tuntsure da dariya tace ai na fada maki bai yarda wallahi ya saba da dumin mutum a
jikin shi.
Idan bayaji mutum a tare dashi ba bai yarda yayi barci nace ai duk ku kuka
shagwabashi dake dasu mummy yanzu gashi yazo nan yana wahalda mutane.
Sallah ta tayar muryan Aisha naji tana fadin ina matar gidan nan take ni zan
tafi nawa masauki yanzi yaya gobe din in sa rain zuwan ku ne cika muna taron buki.
Allah ya kaimu nace da ita har zaki tafi ke nan gashi ko da ina son zaki tayani
fitar da tsaraba wa mutane.
Sai naga ta kalle ni ta tuntsire da dariya tace yau Allah ya kamaki mummy bata
kusa ai dole baban mu ya samu baya ya hau.
Dan tsaki naja nace ai uwar shi ta idar da sallah ta karbe shi su da suka saba
mashi da jiki nace muje falo ki ga kayan da muka zo dashi din don yanzu su musa
suka iso dasu suna can sun tafi masallaci da uncle.
Falon muka fito ta kalli kayan tare da fadin dan kari duk wanan uban tsaraba haka
safiya nace to kin san mun dade bamu zo ba ai.
Nan muka fara aikin in duka yaron yace baison dukawa sai ga khadija ta fito daga
daki tana zuwa ta karbe shi saman cheast din ta ta dora shi tana lalashin shi.
Nan naji dadin aikin da muke inda muka kwashe sauran zuwa wani daki tace ko da
daga baya zaki tuna wani ba a bashi ba kin ga sai a diba anan.
Sai bayan mun gama ne ta wuce har waje muka fito rakiyan ta da motar ta tazo don
haka a ciki muka saka mata nata tsaraban nan muka tsaya take fada min kishiyar ta
lami tazo tana nan sun hada kai da uwar gidan ta suna kulla mata muna funchi.
Nace rabu dasu Allah ya fiso duk abinda zasuyi basuyi kamar Allah ba ai tace
wallahi da da yaya baya kulamu an samu abin fada yanzu kuma da yake muna ance ina
muka fito
Mun dauki lokaci muna magana tsaye a waje nace taje ta kama yaranta dake gida
tace wallahi nasan suna can yamzu wuri wuri suna nema na mukayi sallama badon mun
gama gulman mu ba ta wuce tana jaddamin batun zuwa na gidan su gobe.
Ciki muka koma muka kwaso ma hajiya tsaraban ta zuwa part din ta su kuma su anty
suwaiba duk wanda zai tafi na bashi nashi tsaraban.
Sai dare su uncle suka dawo gidan lokacin muna falon hajiya baaba muna hira don
gidan an watse sai mu da tsirarun mutane wa yanda ke gidan wurin ta muka rage a
gidan.
Yashi alokacin ya cire babban rigar dake jikin shi ya rage daga shi sai yar ciki
a jikin shi tafiyan shi kawai ya isa ka gane a gajiye yake a lokacin.
Sannu da zuwa mukayi mashi ya isa gaban mahaifiyar shi yana gaida ita inda ya
juyo gare ni yana fadin .
Madam yaya bakunta nayi dan murmushi nace ai mun sauke shi yanzu mun zama yan
gari ko dariya yayi yace yana zama na gaji wallahi.
Hajiya ta tambaye shi ina ya shiga haka shiru shiru yace yarima ya jani muka
dinga zuwa ziyara tsufin abokan mu har yamma yayi muna haka.
Tace ai hakan na dakyau ba karamin lada kuka samu ba wallahi ai ziyara nada kyau
mutane ne basu gane ba.
Ban iya magana ba don hajiya na wurin ina jin kunyanta don haka ma sai na kawar
da kaina gare su muna hira da su khadija mikewa nayi.
Abinci na mike na dauko mai tare da aje mai komi da zai bukata a wurin shegewa
mukayi can wurin yaran hajiya don mu basu wuri su tatauna da mahaifiyar shi.
Muna shiga tace mashi babana harda wani uban tsaraba haka mai yawa kuka zo wa
mutane dashi bayan kullun dawainiyar ka bai karewa gare mu.
Yace hajiya ban ko san ta hada tsaraban nan ba sai gani nayi ana sakawa a mota
tace yanzu duk itace da wanan dawainiyar haka , ?
Shiyasa ake son samun mace tagari wacce zata dinga kare wa mutum mutuncin shi
dana yan uwan shi wanan yarinyar gata dai karama amma kuma tana da wayau wallahi
tasan darajan mutane sosai.
Sai bayan goma na dare muka fito zuwa shiyan mu bayan mun yi shirin kwanciya ne
nake fada mai zancen zuwa gidan su Aisha buki da muke son yi gobe.
Yace mantawa nayi Aisha na garin nan dana dage tafiyan mu sai wani lokaci don
nasan yawo zata jaki ku dinga yi a nan niko kin san ban bukatan hakan ko.
Shiru nayi don idan na tanka zai samu hanyan da zai hana fitan gobe wanda ba
zaimin dadi ba har Aishan bayan nayi mata alkawari.
Jin nayi shiru ne ya kyale baici gaba da maganan ba sai ji nayi ya jawo ni