Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
ki ibada da hakan.
Shifa yaro anbinda kake yi yake koyi dashi mai kyau ko mara kyau don shi gani
yake komai daidai kake yi.
Tace wai ni Safiya wanan mijin naki halan ustzune naga duk halaiyar ki sun kara
canzawa yanzu ba a yanda na sanki ba duk da dama can babu ruwan ki baki kaimu rawan
kai ba.
Dariya nayi kawai mun karya ban wani jin dadin zama a gidan ba don haka kamar
yadda muka bar gida sha biyu haka muka baro gidan Amina zuwa gida bayan na masu
alheri muka dawo gida.
Saboda gaba daya naga Aminan ta canza tabar halaiyan ta dana san ta dashi a baya
sai wani nuna waye taki wanda bai dace da diyan musulmai ba da matan hausawa.
Abinda nake son mata su gane shine bawai sai mun nuna wayewa a fili za a san mun
waye ba dabiun ki na diyar bahaushe musulma a ko ina ya rinjayi zuciyar ki.
Ako ina kika samu kan ki kada kiga kina zaman bariki ki watsar da tarbiyan da
kika samu ki manta da rayuwan ki a yanzu yafi muhinmanci ga Allah.
Ki dinga fita yadda kika ga dama batare da kin rufe jikin ki ba wai ke zaman
bariki kina daukan hakan a wayewa gare ki.
Kamata yayi yar musulma bahausa ta nuna a ko ina ta mai cikaken tarbiyane a duk
inda ta riski rayuwan ta wanan rayuwan duniyan ba komai bane a gare mu.
Wataran kana gani anayi ba dakai ba lokacin ka makara ga gyaran dabi,un ka don
yara sun taso sun dauki rayuwan da suka samu kanayi suna kanana.
Badon kan mu zamu daina wasu abubuwan ba sai don tunanen makomar yayan mu na
yanzu da wanan tunanen na canzawan Amina a raina har muka iso gida a lokacin.
KUYI HAKKURI DA MAGANA NA YAN UWA MUNA CIKIN WANI HALI NA SAKACI DA ADDININ MU
YANZU DON MUNA GANIN KAMAR WAYEWA NE.
MUN MANTA YAYAN MU NA TASOWA SUNA KOYI DA DABIUN MU MU CUSA ADDINI GA ZUKATAN
YAYAN MU YAN UWA.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/14/20, 10:25 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , ,
8️⃣0️⃣8️⃣
🧕0️⃣8️⃣0️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Mun dawo gida mun samu jikin inna ba dadi ranan basu kwana da ita da dadi ba don
maganin da ake mata allura a fara aiki a jikin ta sai ya jikin ta sakewa.
Dakin inna muka wuce don har baba yana gida ranan bai fita wurin sana,a shi ba
don yanayin jikin inna din mun samu ta samu barci mun dade a wurin ta muka fito
daga dakin.
Yan uwanta ma da suka zo a waje suka zauna suna tsoron shiga dakin inda take don
gudun daukan ciwon da akace masu anayi.
Sai da na fito muka gaisa da su ban tsaya ba na wuce daki bamu dade da dawowa ba
naji shigowan Saadatu gidan ashe dama tana nan ta fitane zuwa sayo masu abu.
Ina daki zaune da ummi na muna hira naji muryan ta tana cewa ashe bakin birni sun
dawo nace eh anty Saa kin shigo ashe tace dama ina nan na dan fitane dazun .
Mun gaisa na jajanta mata akan jikin na inna ta samu wuri ta zauna a dakin ummi
din tace ashe kin je wurin Amina ne birni nace eh munje ziyara wurin Amina.
Mun dade a dakin muna hira da ita tana bani labari har ta fara sana,a da fridge din
ta kayan kallo kuma tun ranan aka hada mata su yanzu bata da wani damuwa ko zaman
kadaici
Kiranta akayi waje ta fita na mike ina son in yi wanka dama sai ga mama ta shigo
gaida mu da dawo nan na tsaya muka gaisa tana fadin ai babaku bai san zaku kwana ba
ya dawo yana fada jiya.
Nace Amina tana da muhinmanci a wurina shiya naje na kwana mata daya yanzu saura
kuma in tafi kauyen su ummi inyo ziyara in dawo in fara shirin tafiya don mun kusa
cika kwanakin da aka bamu.
Tace au har can zaki tafi ashe nace ba dole inje in duba ma ummi yan tsofinta ba
kada ta hake ni daga inda ummi take zaune tace ai ba a saki zuwa dole ba.
Dariya mukayi mata mama ne ke fadin ba a sata zuwa dole ba amma idan ta koma bata
je ya isa ai mata gori ai tazo taki zuwa duba su.
Ummi dai dariya tayi da jin dadin zai tafi in duba yan uwan ta kuma nace kwana
biyu zanyi a can fitan mama dakin yasa na mike na shiga bayi na watsa ruwa a
jikina.
Na fito na samu shafiu ya dawo yana cika yana batsewa a falon ummi nake tambayan
shi may ke faruwa shafiu yace bakomai cikin fushi.
Nace kuma ga yanayin ka ya nuna fushi kakeyi mana shafiu may akayi maka waya taba
min kai nazo kusa dashi na zauna.
Ya wani turo baki a shagwabe yana fadin wai da su maimu zaki tafi indan kin tashi
bayan na fada maki zan biki.
Murmushi nayi tare da dafa shi nace shafiu aikai namiji ne kuma in na tafi dakai
wazai taimakawa ummi ga sana,an ta ?
Yace namiji bai zuwa gidan yayan shine akace nace kana zuwa shafiu idan anyi
hutu sai yaya sani yakawo min kai hakan yayi maka ?
Dan shiru yayi kafin yace indai zaki sa ya kaini yayi mun don wallahi ina son
zuwa wurin ki hutu anty nace zakazo shafiu.
Yanzun dai ka shirya zamu wurin su kawu dole gobe mukai masu ziyara kafin in
koma yace ni sai kauye za a dani kun tafi birni bakuje dani ba ?
Wai shafiu yaushe ka zama haka ban sani ba bann saka da yawan hayayya ba fa ada ?
Ya mike yana fadin komai sai ace waini namijine namiji akace ba a yi dashi
wallahi nima zan bar gidan nan ne.
Barci nayi ranan ban ko fito tsakar gida ba din ina son in dan huta ina jin ummi
suna faman rikici da Abba a falon ta amma na kasa tasowa inzo inji may ya samay
shi.
Har yaron yayi shiru ban sani ba don barcin dana koma a lokacin shigowan yaya
Nura wuri na yasani tashi zaune.
Falo naa fito wurin shi mmun gaisa nace yaya Nura yaya akayi ne yace wallahi
Safiya garin ne yayi zafi yanzu sam babu aiki tunda dama ya kama mutane sun mayar
da kudin su gona.
Nace yanzu may ye shawara yaya ya shafa kan shi yana dan murmushi yace zuwa nayi
wurin ki ki dan taimaka min da wani abu in dinga juyawa.
Shiru nayi ina nazari a raina sai nace yanzu dai ba wasu kudi nake dasu anan ba
yaya gashi zan shi kauye wurin kawun ne na sai dai indan mun koma idan zaka iya
shigowa Abuja sai musan abinda za ayi a can din .
Zaiyi magana na rigashi fadin barin in baka dubu ashirin duk da nasan zasuyi ma
kadan amma kayi hakkuri dasu jibi zan koma ba dadewa zamuyi ba dama sai kazo mu san
abinda za a yi don yaya Saadu na can.
Bva zai rasa wurin da zasu saka ba yafi wanan aikin da kakeyi a nan zaifi ma
sauki nake gani idan zaka iya idan kuma kafi son zaman nan zan sama maka abin
juyawa yace sai nayi shawara da mama ummi dake kofa tace shine daidai.
Na shiga daki na fito mai da dubu ashirin din na kawo mashi ya mike yana godiya
ya fita daga dakin sai lokacin ummi tayi magana.
Kin san dai Nura ba kamar Sani yake ba karki saka shi a cikin harkan mijin ki ya
yaudare shi bake kadai abin zai shafar mu nan zai iya shafan mu.
Nace har yanzu yaya Nura bai daina halinsa bane ummi tace ina zai daina tunda
bajin maganan iyayye yake yi ba.
Shi haka rayuwan shi take a tsatsaye yake har yanzu baya ganin kowa da mutun ci a
idon shi ko gidan nan ya shigo bai iya gaida mutane yanzu ma mamakin ganin shi a
wurin ki ai.
Murmushi nayi nace amma duk abinda yake ummi ai bai kawo gare ki damu ko iya
wanda ya shiga harkan shi yake tsayawa.
Ina dai ja maki kunne kisan abinyi tun wuri nace ummi ki bari a gwada shi ko sau
daya ne kin ga ai mama bata jin dadin ganin da yaya sani kawai muke mu,amula a
gidan nan ranta baya dadi nunawa kawai ne batayi.
Ba fa gwadawa a fili amma nima nasan abin yana damun ta nace ba a dukiyar uncle
zan sakashi ba ai ummi nima nasan abinda nakeyi.
Washe gari muka isa garin kakan nina mun samu taro na mutantawa a wurin su irin
taron da mutanen kauye kiwa wanda suke mutuntawa aikai muna a gidan.
Su yaya sani basu kwana ba suka dawo bayan sunci abi mukai sallama dasu suka tafi
naji dadin kasan cewa a cikin yan uwan ummi danayi saboda yadda suke nuna muna don
dukkan mu yaran ummi mukaje garin.
Mun so zuwa da ummi amma baba yahana ta zuwa don haka muka zo bada ita ba sai
yamma mazan suka dawo daga gona wurin aiyukan su don da aiki noma da kiwo suke
dogara su.
Sai da suka huta muka bisu daya baya daya muna gaida su a part din su najin dadin
ganin mu a yadda sukaga munzo mu duka.
Mun fi dadewa a wurin kakan mu wanda tsofa ya kama yanzu har dan rankafa abu ga
dogon mutum wanda ya manyanta don ko diyan shi ba yara bane balle shi tsawo rai
daine daya samu yakai hakan.
Washe gari da muka tashi jumma a ne don haka kowa na gida basu zuwa gona duk
ranan jumma, a ranan suke samu su dan huta a gida don yin sallah jumma a din.
Tsaraban da muka kawo masu ake ta rabawa a kofan kakan mu mace duk da ita ta
haifi ummi mu ba wanda ta haife ta ta rasu tun ummi bata girma ba.
Amma ta rike su kamar ita ta haifesu yadda ta rike su a gidan nan suka fara
shigowa godiya a gare mu duk mazan shaddan da ya bani na kawo masu dama na aje masu
nasu.
Mun je wurin kakan mu gaida shi sai jan mu da hira yake yi yana bamu labarin
rayuwa shi na baya yana kuma fada muna dan tarihin ummin da tasowan wata har auren
ta a kauyen da tayi ta koma wurin gwago a garin mu.
Abba ke rikici a gaban shi yayi murmushi yace miko min shi nan khadija ta mika
mashi yaron ya dauke shi tare da kara shi saman kafadan shi daidai saitin kunnen
yaron ya dora bakin shi a hankali yana karato adduan daba mu san may yake fadi ba a
lokacin.
Kara juya shi yayi bangaren hago ya kara maimaita abinda yayi mashi a bangaren
dama ya gaba sai ya dan hura mai fuska take yaron ya zauke numfashi a hankali yake
rage sautin kukan da yake yana ajiyan zuciya shikuma yana dan jijigashi a hankali
saman kafadan shi har yai shiru ya lafe sai ajiyan zuciya yake sakewa a hankali.
Mudai mana kallon abinda yakewa yaron yace idan kunga yana kuka haka daukan yaro
akeyi aimai kallaman shada sau uku a ko wani kunne da bissimilah zaku fara kowani
sai kuga yaro ya yi shuru koda kuwa shedanune suka shafi yaro yana yawan kuka akai
akai.
Nace aiko mun karu tsoho ya nisa tare da tambayana jiki na nace da sauki sosai
yanzu gaskiya don ina shan magani kuma ina cin abinda zai gina min jikina ko
yaushe.
Yace kin dai daina amfani da fitsarin rakumin ko don banga kin kara aikowa in
sama maki ba nace gaskiya malam tunda na shanye wanda ka bani da farko ban kara
amfani da shi ba kuma naji dadin shi sosai wallahi.
Yace tsiyan ku ke nan yaran yanzu baku tsaya ma magani har kuga aikin shi da kyau
sai ku camza wani .
Nace tsoho ba inda zan samu ne a can kaga muna da nisa sosai yace kinzo a saa ai
yau jumma a za a soke rakumi ayi tom tom din shi zan sama maki wasu abubuwan amfani
da dama a ciki sai kije kiyi amfani dasu can idan kinji dasin su keda kan ki zaki
aiko a kara maki wani.
Godiya nayi mashi tare da dan bashi kudin da na riko mashi duk da ina ganin basu
da yawa amma shi sai washe baki yake yana saka min albarka.
Tashi mukayi daga wurin shi wanka mukayi muka shirya muka zagaya gaida dangin da
suke a cikin gari
Bamu dawo ba sai yamma lis agajiye kowan mu yake abincin da suka aje muna na rana
muka samu ba wani ci mukayi ba dama na bada sakon a saya min ganye da kwai da man
shanu mai yawa da zan koma dashi Abuja.
Ganye nace khadija ta dan gyara min naci har dare dashi na kwanta a cikina don
banji wani yunwa ba kuma.
Washe gari sai shirya muna tsaraba suke yi kin san kauye da kara wanan ya kawo
wanan ya kawo sai gashi mun tashi da tsaraba mai yawa a gidan.
Sha buyu rana driver dasu yaya sani sun iso daukan mu bamu jima ba mukayi sallama
dasu muka kama hanyan gida biyu da wani abu muna a cikin gidan iyayyena.
Kwana biyu yarage muna a garin sai shirya muna ummi da mama keyi nan ma dai
tsaraban ake ta kawo min don duk wanda na ba tsaraba dana zo sai da ya dan samu
abin da ya bani da zan koma sai dana ragewa su ummi wani abin.
Ana gobe zan koma ne da safe sai ga maimu da kuka ta samay ni wai baba yace ba
zan tafi da kowa cikin su ba.
Hakkuri na bata nace zanyiwa baba magana da yamma da yadawa gida naje gaida shi
yana zaune yana cin abinci mama na gefe shi na shiga wurin shi.
Gaisawa mukayi nayi mai yaya kasuwa ya amsa min cikin fara a na samu wuri na
tsugun na yace kuna ta shirin komawa gobe ko nace eh baba.
Shine ma nazo fadama zan tafi da maimu da hindatu suyi min hutu idan hutu ya kare
sai a dawo dasu.
Dan jimm yayi sai yace Safiya maigidan ki bazai ga rashin hankali mu ba kuwa nace
ko daya baba babu ruwan shi ai shi bamai zama gida bane ko yaushe.
Sai yayi kwana nawa ma bai gansu a gidan ba idan ba ya kama ba yace nasan halin
yaran nan basu jin magana kada kina zaman ki da mijin ki lafiya su je su tayar maki
da hankali can.
Nace baba babu komai wallahi ai khadija ma baiso ta dawo ba itace ma ta matsa
zata dawo din yace dayake tasawa kanta shiriritan son wanan yaron ba.
Niko da raina da lafiya na wanan abin ba zai yuyu ba muddin ina raye shirmay ta
dai takeyi kawai.
Mun dan taba hira dashi yana ta min nasiha akan zaman aure da zaman takewa a
cikin mutanen da ban saba dasu ba har magariba ya gabato muna wurin.
Haka ya mike yaje yayi alwala ni kuma na koma cikin gida ina shiga mama ta biyo
ni dakin tana fadin kai Safiya ke kika iya da halin mahaifin ku.
Nace mama nasan halin baba don haka ban fito mai kai tsaye da daukan su zanyi ba
sai na laba ga hutu ba sai ya gansu ba kuma ko yayi magana nasan abinda zan fada
mashi gaba.
Yaran da sukaji za a tafi dasu suka fara murna mace kada su dauki wani kaya mai
yawa kada baba ya gane tafiya zasu yi kayan sallah ku kawai zaku dauka.
Tun da safe ana ta fita muna da kaya waje duk sai naji raina ba dadi a lokacin
ina kuryan dakin ummi ina shiri ta shigo dakin nace ummi amna dai ya kamata kizo
kiga gida na idan na koma gaskiya.
Tace ba iyayyen ki sunje sun gani ba zuwan may zanyi kuma ni nace haba ummi kamar
wace bata da gata ai dai dake da baba ku dan leka watarana ko ?
Tace ba dai yanzu ba sai maigidana zaiyi aure ko nace haba ummi khadija dake
zaune gefe na tace kyale ta ninan zan rakota har Abuja idan kin koma.
Gwago dasu mama jimmai sun shigo sallama na dasu Saadatu har da mijin ta da
kishiryar tan nan na fito tsab dani na shiga wurin baba na rusun na tare dasu maimu
nace baba zamu tafi asa muna albarka.
Yace kullun cikin sa maku muke safiya nan yayi wa su maimu fada sosai na su natsu
har su dawo lafiya na shiga wirin inna mukayi sallama nayi mata Allah ya sauwaka.
Na fito kofan gidan namu ya cika da jamma a ina tayiwa mutane ban kwana na shiga
mota Adamu ya zo mukayi magana dashi ba wanda yaji may nake fada mashi.
Sai dariyan da yayi yana daga muna hannu nan muka barsu tsatsaye suna bin motar
da kallo idona na lumshi ina jin wani iri a zuciya na gida a kwai dadi wallahi
indai kazo da zuwan bakunta nace a raina.
Suka yaran sai farin ciki sukeyi yau zasu birni duk sun sallami abokai da yan uwa
sai washe baki sukeyi cikin murna.
Sai karfe biyu da rabi muka shigo garin Abuja inda muka wuce gidan mu direct daga
shigowan mu kanne na da suke ta surutu sai suka koma kallon gari.
Mun iso gidan duk zuciya ba dadi har lokacin a hankali na furta Alhamdullahi a
fili tare da yunkurawa ina shirin fita daga motan ji nayi sunce anty mun iso ne eh
kawai na iya ce masu.
Security din ne ya fito ya bude muna mota tare da fadin sannu madam sannu ismail
na iya fada mai nace nagode.
Fita nayi daga motan tare da amsan Abba dake