Advertisements
Chapter 11 Reading Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   11 / 87

30K to 33K   out of 258.3K words

kallon na sama da kasa yace zanbin cika idan kice baki da
gaskiya zaki gane kuren ki.
Yana fita gidan nasu ya koma gwago najin dawowan shi ta samay ta ta cika fam har
lokacin don yar ta habiba ta zugata ta zugu akaina.
Yace mummy may ke faruwa ne tsakanin ku da yarinyar nan ina ke kika hada wanan
abin bai dace ba kuma ace akwai matsala a atsakanin ku yanzu.
Tace cikin fada kaga rufe min baki don wa nake wanan fadan duk mugun nufinta akan
mu dakai mun sani duk sherin da aka kulla azo ai muna gashinan yana fita fili muna
gani.
Mummy har wani hali ke gareta wanda baku sani ba tace kai ina zaka sani tunda a
boye akeyi don a mallake ka da yan uwanka.
Niko kowaci tuwo dani miya yasha munafuka sai ta dinga yin abu simi simi da ita
wai ita ta kwara mugun halin na nan tattare da ita na ta shiga dura mai akidar
banza daiyi min wai mun zo da nufin raba shi da kowa kuma nu cinye dan abin hannun
shi na gudu.
Tun bai dauka ba har ya fara dauka yana cewa aiko zata gamu dani dama ni ba yarda
nayi da wanan yarinyar ba sam.
Sai da ya biya wurin abokan shi ya dawo gida misalin karfe tara na dare ya tarar
dani na fito bandaki daure da tawul ya fado min dakin da masifa.
Ke mara mutunci dama na fada maki in na bincika naji baki da gaskitya zan dauki
mumunan mataki a kanki watau kun hada baki da iyayyen ki kizo ki haince mu ko.
Idanuwa na suka kada sukayi jawur mamaki da takaici suka rufe min zuciya yace an
turo ki anga kudi banza anzo aci ko har a kashe ni.
A hasale na bashi amsa da cewa kai dan Allah har ina kudin yake da za, a turoni
tun daga arewa har nan ci ku kudi ya rufe wa ido kudin da ana nema kamar ba neman
su akeyi ba.
Kafin in karasa magana na sai naji yakaiwa bakin nawa naushi saida naga wani wuta
ya gitta min na duka tare da dafe fuska na.
Nadago nace ka dukeni akan gaskiyata ban karasa ba ya shiga duka na har tawul din
dana daura yana sancewa.
Baisa ya daina ba sai da ya barni kwance a dakin ya fito yana maida numfashi
daya baya daya ya nufi dakin shi.
Kuka ma kin zuwa yayi min a idona na dade duke a wurin da kyat na daga nakai
bakin gado a haka na haye gadon na kwanta cikin dare zazzabi ne ya rufe ni mai
karfi saboda zafin bugun da na sha.
Da safe har ya fito ban fito daga dakina ba ya leka ko na gama abin karyawa sai
dai babu alaman ko fitiwa banyi ba lokacin.
Ya shigo dakin da niyar yai min fada nan ya samay ni cikin bargo ina rawan sanyi
zazzabi mai karfi ya rufe ni.
Da zumar yai min fada ya shigo dakin sai ya samay ni a haka kwance cikin bargo
ina makerketa yadan ja ya tsaya.
Ya dade tsaye yana kallona sai ya juya ya fita zuwa can sai gashi da paracitamal
da goran ruwa ya kawo min da kyat na tashi ina sha na koma na kwanta.
Wasa wasa sai da na kai kwana uku kwance ina jiyan dukan dayai min tun wanan
lakacin gaba daya zaman ya karasa jagulemuna a gidan.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , ,


πŸ§•πŸΏπŸ”ŸπŸ§•πŸΏ


NAGODE DA KUWALAWAN KU GARENI YAN UWA DA BAZAR KU MUKE RAWA

IDAN BAKI BIYA BA DON ALLAH KARKI KARANTA YAR UWA DON A KWAI NAUYI A KANKI.


Nazama sha tikan duk dare yaje yawon shi ya dawo, acikin maye zai nemay ni idan
nakiya kuma zai min mugun bugu ya biya bukatan shi.
Gari kuma ya waye in tashi in girka mashi abinda zai ci don ciki ya kwakware mai
da ruwan giya.
Daya tashi babu abin da yake nema sai abinci mai dan nauyi da zai cika ciki dashi
idan ya gama wani bi ya kara nema na koda karfin tsiya ya biya bukatan shi.
Acikin irin haka na ranan yana tsaka da buguna, sai ga yaya saadu ya shigo gidan
namu yayi sallama har ya gaji amma yana jiwo ihuna daga ciki.
Kai tsaye ya fado cikin gidan ya samu ya danne ni ya ta bugu a kasa da karfi ya
tire shi samana daga ni sai underwear a jikina.
Ya na ganin na haka nan ya juya baya da saurin shi shiko gogan sai mazurai yake da
idon yana mai mai da numfashi .
Sai ya hau zage zage yana fadin sai ya halakani a gidan nan wani tsawa saadun ya
daka ma wan nashi daidai na samu na daura zani a jikina ta dawo ciki yana cewa .
Amma bros baka kyauta ba wallahi ina yarinyar ga taga karfin ka da zaka dinga
dukanta haka yace dakata mallam kada kazo min gida kace zakai min nasiha kan wanan
bazan yarinyar mara mutunci.
Yace haba bros matar kace fa ta sunna kake zagi haka ya kamata ace yanzu ka daina
abubuwa da daba ka kama kanka.
Ya juya wurin ina ta faman kuka yace kin ga Safiya ya isa haka shiga ciki ki
kitsa kan ki kizo haka bakyau wallahi.
Nasamu naja kafana zuwa daki wanda da kyat nake dagata don wallah ina shiga naji
yana cewa dan uwan nashi wanan abin baiyi ba wallahi.
Na dawo sadiya ke fada min irin sherin da habiba ta kulla mata wurin mummy a
gaskiya abinda kuke yi baku rike amana ba.
Yace wani amana can dama waya ce yana son ta ko waya nemota sai dan uwan yace
mummy kuma hakan da akai maka bakaji dadi ba yanzu ji yadda ka koma kaima kasan
akwai banbanci da yadda ke da a watse.
Ashe ko aure dadi gare shi ko ba a fada ba yarinyan nan tana fa da hakkuri har
yakai ka kure hakkurin nata ta soma mayar maka da martani kana babban kanka.
Nan dai yake cewa yarinyar baza ne kana ganin ta wurin nan munafukane ta kware
bata da kunya sai na gwada mata ba irin mu akewa haka ba a tashi lafiya.
Yaya saadun yace baka ko kyauta ba wata mace zaka samu ta zauna tana hakkurin da
irin halin ka nan dai sukai ta kwasan dashi.
Daga karshe ya shige dakin shi ya barshi a zaune a wurin ya kwala min kira na
fito ina kuka ina share hawaye da habar zani na.
Nazp na durkusa kasa gefen kujera ina cewa gani yaya ya dago yana cewa a haba
dai hau kujera ki zauna mana na girgiza kaina nace nan ma yayi min.
Yace Safiya msi yasa bakiyi wa mijin ki biyayya har kika bari yana dukan ki haka
kamar wata mara gata eyeh.
Kuka yaki tsaya min nace yaya bana mashi komai haka dai ya daukan wa ran shi yai
ta dukana do ban da daraja a idon shi.
Don kawai yana ikirarin da cewa bashi ni akayi ya tare ni da cewa a haba kibar
fadin haka mana ke fa kaunar shine ko banza.
Yadai bani hakkuri ya lalashe ni da kuma nasiha har zuciya na tayi sanyi da zai
tafi ya kawo duba goma ya ce na rike a hannuna zan samu na kashi.
Nai mai godiya ya taka har kofan dakin shi yana fadin bros ni zan tafi sai na
saike lekowa kenan sai ya amsa mashi daga ciki da yaushe zaka koma.
Yace ina nan har kwana biyu sai yace sai mun hadu ke nan ya saadin yace don
Allah aita hakuri yace is ok ai.
Ina shiga daki na raba kudin da yaya Saadu ya bani biyu na boye rabi kamar nasan
zai karba sai ko gashi ya shigo yana ce min .
Ke bani kudin da saadu ya baki nan ashe wurin rabawa ban raba daidai ba bakwai
din na boye na bashi ukun sai ya kalla yai tsaki yace munafuka kawai.
Ya fice gidan na harare shi ina cewa a fili mugu kawai ashe baiyi nisa ba ya
juyo yana fadin may kika ce nace ni badakai nakeyi ba.
Yafice yana kutawa tare da gaura kofar gidan da karfi na sauke ajiyan zuciya ina
mai kallon jikina inda na ji ciwo tare da dan tabawa.
Fitowa nayi na kara gyara wurin da ya bata nagama nai wanka na gyara jikina ina
shirin dan kwatawa na mike naji nocking din kofan gida.
Na fito don ina ga kowa nene akofan sai ganin yarinyar aikin gwago da tai
alkawarin zuwa kitso wurina a kofan nai mata sanu da zuwa tare da sake mata fuska
tashigo ciki.
Baya mun gaisa da itane take cewa dani kitso tazo in mata na ji dadin koba komai
zandan sake yau a gidan a wurin ta nike jin wasu halaiyan shi da ban sani ba da
farko take cewa amma ke ba yar uwar su hajiya bane.
Nace may kika gani tace gani nayi dai bata kaunar ki koda yake hajiya ai da kowa
zata kwasa indan ya taba mata dan lelenta.
Murmushi nayi mata kawai tace tana masifan son shi cikin yaran ta gashi dai yana
aiki kuma yana samu amma bata jin kyashin kashe mai kudi.
Nace aidon su take nema ko tace wallahi yana da hanyan samu sosai amma yan matan
shi basu bari ko wanan gidan da mota da ya saya sai da dabara ya saye su.
Na dauka da yai aure zai daina amma da yake dan duniya sai abin da yai gaba ga
abinda yake yi.
Nan nake ji wai ai da dawata yake zaune a gidan sai da hajiyan tayi da kyat ta
raba su da kamar sun rabu yanzu kuma sun dawo sun dinke wuri guda da ita.
Nan tashiga bani hiran abokiyar shashan shi din da irin rayuwan da sukayi a baya
dama wanda suke yi yanzu din har nagama mata kitsa tana min hiran shi ne.
Mun gama ta ciro kudi ta bani ban karba nace ta barshi sai idan ta sake dawowa
tace a, a karba wallahi idan kika soma da haka zakita aikin banzane wa mutane nan
garin neman kudine ba a wasa da neman kudi.
Naimata godiya taimin alkwarin zata sake dawo idan an kwana biyu na rakata ta
tafi sai da ta wuce na duba kudin nayi mamaki don har dubu daya tabani.
Ina ta murna na shiga daki naje hadawa da wanda na boye sai naga ashe dubu uku
na bashi na boye bakwai.
Yanzu ga shi taban daya sun tashi takwas taban shawara na sayo kayan yin kitso
don akwai wa yanda zata turo min.
Tun ranan da tazo kamar ta buda min hanyane na yin kitson na dinga samun
customers mssu zuwa ganin haka ina yi a boye sai na sheda mashi don karya zo ya
sani ya hauni da jidali.
Baice komai ba sai ke kika sani kardai ki bata min gidana kan wani kitso naki na
banza can.
Don haka idan sun zo muke fita ta waje muyi kitson basai mace ta shigo gidana ba
mun bata mai gida.
Wata rana wata mace tazo da diyan ta sai suna neman ruwa sai da aka tafi wani gu
aka sayo mata sai take ban shawara na dinga saida abin sanyi mana.
Wanan shawaran yai min dadi sosai tun wanan ranan na fara sayar da ruwa sai nai
shawaran ko na dinga zobo sai inayi dashi da wasu yan kakanan drinks ina sayar wa.
Aiko sai abin ya karbe ni matan hausawa harda kumshi nake masu mai zane take
sunana ya fara dagawa.
Hankalina ya dan fara kwantawa koba komai dai ina samun abokan hira har ina
dariya sai dai in sun tafi na koma dip.
Wata rana na gama kitso na gyara gida na dora girki gap da zan gama na shiga
wanka koda nafito abinci yayi na kwashe.
Ina zaune a falo ina cin abinci sai gashi ya shigo ina gaida shi da dawowa ya
amsa ciki ciki ya wuce dakin shi.
Ya fito ya zauna kenan wayan shi yai kara ya dauka zaune nake a takure a falon
ina gudun in daga yace min munafuka.
Sai na dake na zauna a takure a yadda na fahinci wayan da yake da mace yake
magana amma ko yaji darr dan ina zaune a wurin.
Daji lalashinta yake yi don a yadda suke magana hakkuri yake bata ita kuma sai
masifa take mai a wayan.
Zuwa can ya mike zai fita sai na sasauta murya na nake cewa kayan miya sun kare a
gidan na gobe ya rage kawai da zanyi.
Ya juyo a wullakance ya dube ni yana cewa ina kudin da kike samu a wurin kitson
naki ki fitar ki saya mana.
Ya fice ya barni ina mai binshi da kallon mamaki don tunda kayan da nazo gidan na
sama ya kare idan nai mashi magana sai ya hauni da fada.
Gashi kuma ance kudi yake samu sosai a wurin aikin shi amma baya nuna yana dashi
sai yaga dama yayi.
Nidai na fahinci anyi sallah na mike zuwa yin sallah nabar falon ban fito ba ina
shirin kwaciya ne naji dawo wan shi gidan.
Na dan tsaya inga da may ya dawo min a cikin mayen ne ko a birkice naji shigowan
shi na mike na fito falon inda yake sai naga yana shigowa yana dariya.
A zatona waya yake yi sai naga ashe ba waya bane yana magana ne da wata da suka
shigo gidan tare.
Yana dago kai ya ganin ya hade fuska tare da cewa a fusace ke kuma may kikeyi
anan baki kwanta ba ?
Yarinyar da suka shigo da ita gidan tana wani taunan chewgun kas kas tana harare
hararen ko ina na gidan.
Naji tace wanan ne dama matar taka ashe karamar yarinyace haka no warder kake
gudun mutane yanzu
Ta kalle ni sama da kasa sai tace dashi muje don Allah karma ta kwanta mana ita
ta sani tai gaba ya juya ya bita a baya.
Suka barni tsaye a wurin imani ya kashe ni may yake nufi kenan karuwa ya dauko
min a gidan ko may ?
Jin sun rufo kofan daki ne nadan zabura na dawo cikin hankalina dakyat naja
kafana na koma daki.
Tunane nakeyi wanan wani irin bariki ne haka karuwa har cikin gidan tazo ta wuce
ni ta shige daki ita da mijina ina tsaye.
Da kyat naga safe don banyi barcin kirkiba a gidan da safe ban fitoba don haka
ban dora girki ba a gida ko gyaran gida ban fito nayi ba.
Sai zuwa can ya kwala min kira daga falo saida ya kirani sau uku na amsa mai na
fito falon ina saye da hijjab dina har kasa.
Ya kalle ni a wullakance yace dani ina abin karyawan mu banga kin aje min ba nace
a sanyaye banyi ba.
What ya fadi da karfi nace banyi na sake fada mai saboda may zaki ce baki dafa
min abinda zanci ba.
Cikin dakewa nace ita wanda ta kwana gidan bata dafa maka bane koba mace bace da
baza ta dafa ma ba.
Ban san ya iso inda nake tsaye ba sai ji nayi ya buge min baki kub da nashi basan
lokacin da na dafe wurin ba.
Ya daga hannu zai kara kai min wani marin sai ga ta ta fito daure da tawul a
jikin ta iya cinya tace a, a marta koma ta dafa ba iya ci zanyi ba wanan kazaman
yarinyar ba zan iya cin girkin ta ba.
Ta jashi zuwa cikin daki tana wani kariraya tana kwanta mai ajiki suka rufe
kofa dakin garam ina wurin a tsaye.
Na sauke ajiyan zuciya a raina nace lalle yau na ga iyakar barikin da nake ji ana
fada anayi a lagos na ganshi a wurin wanan bawa shine giya shine taba gashi kuma ya
buga ga dauko karuwa kwana a gidan mu na sunna.
Ina jin sun gama watse war su suka fice a gidan da ihuce ihucen su da tafawa a
tsakanin su.
Nace shashu banza kawai a haka zaka kare ba aga farar ka a gida ba sai gun matan
bazan za suna fita sai ga yaya saadu ya shigo gida.
Natare shi da mutunci muka gaisa dashi yake tambaya na yaya gidan na amsa mai da
lafiya kalau.
Sai yake tambaya na yanzu abubuwa sun yi sauki a tsakanin mu ko sai nai murmushi
kawai nake cewa dashi babu komai yaya.
Ya ce a, a Safiya kada ki biye min komai ni dan uwanki ne nasan kuma halin mijin
ki sarai da rashin mutunci do haka in baki fada min ba wa zaki fadawa.
Sai idanuwa na suka ciko da hawaye a lokaci guda nace yaya komai na nan a yadda
ka san shi saima abinda ya karu.
Yau ma da wata mace suka kwana gidan a gaban ta yai min rashin mutunci don naki
dafa masu abin karyawa.
Hakkuri ya bani ya dade yana mun na siha ina ta fada mai irin matsalolin da muke
samu dashi a gidan.
Yana bani hakkuri tare da fadin sai na hada dayi mashi addua don addua baibar
komai ba in kuma yi kokari in kawar da idona ga abin da yake yin don ko na ce zan
fada wa iyayyen mu ba yarda zasuyi da ni ba.
Da zai tafi yakawo kudi ya bani yana cewa na rika in dinga sayen abinda zanci
basai na tambaye shiba kar yaita duka na a banza.
Nace mai akwai kudi wanda na tara do yanzu kitso nake ina samun kudi yace tona
kara kawai dasu.
Yai min alkawarin zai saya min fridge

11 / 87