Advertisements
Chapter 10 Reading Jeedderhh by Khaleesat Haiydar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jeedderhh by Khaleesat Haiydar

Author :  Khaleesat Haiydar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   10 / 108

27K to 30K   out of 321.7K words

xuwa daya
side din ya nufi motar Abuturrab tana biye da shi a baya, Abuturrab ya bude motar ya sauko yana kallonta,
sunkuyar da kanta tayi sbda hawayen da ya kawo idonta, ya kalli mai adaidaitan ya ciro dubu biyu aljihunsa
ya mika masa yace "Nagode" Mai adaidaitan ya amsa shi ma yyi masa godiya sannan ya tsallaka ya koma
gun Napep dinsa, Ba tare da Abuturrab ya kalleta ba yace "Shiga" Ba musu ta shiga gaban motar, ya shiga
maxaunin driver ya tada motar suka bar wajen, a hankali yake driving din yace "Bayan na tafi sai me ya
faru?" A hankali ta fara basa labarin abinda ya faru bayan tafiyarsa babu abinda ta boye masa har karshe,
ganin yanda take kuka ya kalleta yace "Ya maki wani abu ne?" Ta girgixa masa kai, rasa particular tunanin
da xai yi yayi a lkcn, babban damuwarsa yanxu inda xai kai ta cikin daren nan, ya d'an kalleta yace "Yanxu
babu wanda kika sani nan cikin gari?" Ta girgixa masa kai tace "Ba kowa" ya sauke wani boyayyen ajiyar
xuciya yana ci gaba da driving dinsa almost absentminded, parking yayi bakin gate din gidan, har Mai gadin
ya mike xai bude gate ganin yayi parking a nan waje sai ya koma ya xauna, Abuturrab ya sauke glass ganin
haka mai gadin ya sake tasowa da sauri ya nufosa yana murmushi cike da girmamawa yace "Barka dai
ranka shi dade..." Abuturrab yace "Ya aikin?" Mai gadi yace "Alhmdlh, Baxa ka shiga ciki ba?" Abuturrab ya
d'an shafa kai yace "A'a, wani d'an alfarma nake nema gun ka" Cike da natsuwa yace "Toh ina saurarenka
yallabai" Abuturrab yace "Erm... Mai dakinka na nan ai?" Mai gadin yace "Ehh tana ciki wllh" Abuturrab ya
kalli Jiddah yace "So nake don Allah ta d'an kwana nan wajen ku kafin gobe, amma kamar kuma hakan da
takura tunda daki daya ne ko?" Da sauri Mai gadin yace "Inaa babu wani takura wllh ranka shi dade, ni ai
ba baccin ma nake da daddare ba yawanci nan tsakar gida nake kwanciyata wllh, kar kaji komai" Abuturrab
yace "Toh nagode, amma kada kace ma masu gidan na xo" Mai gadin yayi murmushi yace "Baxa ayi hakan
ba ranka shi dade" Abuturrab ya juya yana kallon jiddah yace "Sauka, sai da safe..." Yana fadin haka ya
bude mata motar, ta sauka a hankali, Mai gadin yace "Mu je ciki to...." tafiya ya fara yi ta bi bayansa sai da
suka kusa gate din ta waiga ta kalli Abuturrab da ya bi su da kallo, dauke kai tayi ta bi mai gadin suka shiga
cikin compound din, yayi wani sigh ya tada motarsa yayi reverse ya bar layin wani ajiyar xuciyar ya sake
saukewa feeling a bit relieved. Har aka idar da sallan asuba Jiddah bacci take, matar mai gadin na idar da
sallah ta d'an ta6ata tace "Ki tashi kiyi sallah lokaci yayi" a hankali Jiddah ta bude idonta ta mike xaune da
sauri, daki ne babba gun katifar kadai ne suka yi demarcating da labule, yaronsu daya wanda ko yayesa ma
ba ayi ba, jiddah ta mike matar ta nuna mata bandakinsu dake cikin dakin, tana fitowa matar ta bata hijab,
bayan ta idar abun ka da bata saba komawa bacci ba ta kalli matar ta gaisheta sannan tace "Babu wani
aikin da xa ayi?" Matar tayi murmushi tace "Aa babu, ki koma kiyi kwanciyar ki" Jiddah bata ce mata
komai, amma duk yanda ta so komawa bacci bata iya ta koma ba don ta riga da ta saba da wahala, gari na
wayewa ganin matar ta dau tsintsiya xata fara sharan daga nan inda suke xuwa bakin gate don gidan akwai
me shara, jiddah ta amshi tsintsiyar, matar tace "Don Allah ki bari ki koma kiyi xamanki...." Murmushi
kawai Jiddah tayi tace "Aa xan taya ki" Tana fadin haka ta fara sharan hakan yasa matar ta koma ciki don yi
ma yaronta wanka tana yaba hankalin Jiddah, shi kuma mai gadin na can xaune waje, jiddah na cikin shara
aka bude gate din gidan ta dago da sauri, sosai gabanta ya fadi ganin wanda ya shigo, a hankali ta juya tana
ci gaba da sharanta, waya ne kare kunnensa ya katse wayar yace "Maman Abdallah kun tashi lafiya" Ba
tare da ta bari ta kallesa ba a hankali tace "Ba ita bace" Ko rufe baki bata yi ba Maman Abdallah ta leko da
fara'arta, cike da ladabi tace "Ba ita bace Dakta, bakuwa nayi, ina kwana" yana tafiya yace "Lafiya lau,
Abdallah bai tashi ba?" Tace "Kaya nake sa masa ya tashi tun daxu" yace "To a gaida min shi" Tace "Xai ji
Dakta" Entrance din gidan nasu ya nufa, Jiddah ta bi sa da kallo tana sharanta a hankali... Karfe takwas
Maman Abdallah ta kalli Jidda bayan ta gama shiryawa cikin kayan da ta bata tace "Tunda kinyi wanka mu
shiga daga ciki mu gaisa da 'yan gidan in amso mana kumallon mu, ko" Jiddah dai tayi shiru bata ce komai
ba, Maman Abdallah ta goya d'anta tace "Tashi mu je, Hajiyar gidan ta tashi yanxu" A hankali Jiddah ta
mike ta dau Hijabin matar ta sa sannan suka fita, Maman Abdallah ta bude kofar hade da sallama ta shiga
ciki Jiddah na biye da ita, Xaunawa tayi kasa jiddah ma ta xauna kasa, Hajiya Ramlah dake parlon da
murmushi fuskarta tace "Bakuwa kika yi Shafa" Maman Abdallah ta washe baki tace "Ehh wllh Hajiya,
bakuwa nayi da yammacin jiya" Cike da ladabi ta risina tace "Ina kwana Hajiya" Umma tace "Lafiya lau kun
tashi lafiya?" Maman Abdallah tace "Alhmdlh, su Maimuna da Siyama na ciki kenan" Umma tace "Suna
ciki..." Jiddah na kallonta a hankali tace "Ina kwana?" Umma tace "Lafiya lau yan mata, sannu da xuwa....
ya sunanki?" Jiddah ta sunkuyar da kanta tace "Jiddah" jin footstep ta dago tana kallon direction din,
Ahmad ne ke sakkowa daga sama yana kallonta babu ko kiftawa, Umma tace "Ahh me babban suna ce
ashe" Jiddah tayi murmushin karfin hali ta sunkuyar da kanta, Umma tace "Maa sha Allah, sunan yayata
gare ki, sannu da xuwa" Maman Abdallah dai sai washe baki take, Umma tace "Yar uwarki ce amma"
Maman Abdallah ta sosa kai tace "Ehh kauyenmu daya" Ahmad dai sai kallon Jiddah yake, ita kuma taki
yarda ta sake kallonsa, Maman Abdallah ta mike ta wuce kitchen don daukan kumallonsu, tana shiga ta
dauka a inda mai aiki ta ajiye masu ta fito, Umma ta kira mai aikin tace "Tunda suna da bakuwa ki kara
masu" Mai aikin ta amsa ta koma kitchen din, ba a dau lkci ba ta dawo ta mika ma maman Abdallah
coolern, Cike da ladabi Maman Abdallah tace "Mun gode hajiya Allah ya kara girma" Umma tace "Ameen"
Mikewa Jiddah tayi ta amshi warmer din a hannunta sbda Abdallah dake bayanta ita ma ta yi ma Umma
godiya sannan suka fita, Ahmad dai ya bi ta da kallo.... He looks so confused, sak tayi masa kama da mai
awaran hayi, wata xuciyar tace kawai kamanni ne me xai kawota cikin gari har cikin gidansu kuma, daga
kafada yayi a ransa ya bar sa a cewar kamannin ne, ya nufi dining don yin breakfast. Karfe goma Abuturrab
ya fito gida, driving yake yi with different thought in mind, wayarsa ne ya fara ring ya kalli wayar ganin
Ahmad ke kiransa ya daga, Bayan sun gaisa Ahmad yace "Muna chatting kuma ka sauka" Abuturrab yace
"Ehh i am driving now" Ahmad yace "To where?" Abuturrab yace "Aunty ta aikeni" Ahmad ya d'an ta6e
baki yace "Ohk, wai ka dauki hutu ne naga baka koma gun aiki yau ba?" Abuturrab yace "Kai me ya dawo
da kai during week day?" Ahmad yace "Wani taro xa mu yi nan kaduna, amma gobe xan koma ai, in sha
Allah" Abuturrab yace "Ohk anjima xan shigo idan na dawo" Ahmad yace "Alright" daga haka ya katse
wayar ya ajiye, parking yyi inda ya saba parking din, ya sauka motar yana kallon layin dake cike da mutane,
wani d'an saurayi dake fitowa daga layin ya kalla yace "Abokina me ke faruwa a nan?" Saurayin yace "Wata
amarya ce saura sati bikinta aka nemeta aka rasa, wasu sunce angon ne ya dauketa, wasu kuma su ce uwar
rikonta ta san inda take, ynxu dai ga shi angon na neman cinna ma gidan wuta wai sai an fito masa da
matarsa, uwar rikon na can tana kuka da rantse rantse bata san inda take ba, jama'a kuma na ta dannan
shi angon, da yake babu wanda bai san halinsa ba a unguwar nan, sai ya iya kona gidan, yanxu dai wajen
yan sanda ko mai anguwa suke shirin xuwa" Abuturrab yace "Toh Allah ya kiyaye" Barin anguwar
Abuturrab yayi, yana isa gidansu Ahmad yayi parking a waje, ya sauka motar gaisawa yayi da mai gadi dake
xaune a waje sannan ya xauna kusa da shi murya can kasa yace "Kayi hakuri babu wani bayani na kawo
maku yarinya..." Mai gadin ya katse sa da sauri yace "Babu komai ranka shi dade, kar ki ji komai wllh, xata
iya xamanta har iya sanda xaman nata xai kare a nan, ni bani da matsala haka ma mai dakina.." Abuturrab
ya sa hannu aljihu ya fiddo dubu biyar ya mika masa yace "Gashi ka rike wannan" Mai gadin ya girgixa kai
yace "Aa kar mu yi haka da kai don Allah" Abuturrab ya ajiye masa kudin ya mike ya shiga gate din gidan,
Babu kowa tsakar gidan ya kalli building din mai gadin sannan ya nufi main entrance din gidan. Kiran
azahar ne ya sa shi fitowa tare da Ahmad xa su tafi masallaci, Jiddah na xaune compound din kan karamin
kujera kusa da dakin mai gadin da ruwa cikin buta a gabanta tayi nisa tunanin da take, Har suka kusa isowa
wajen Abuturrab kallonta yake haka ma Ahmad, kamar ance ta daga kai tayi ido hudu da su, sosai gabanta
ya fadi ta sunkuyar da kanta da sauri ta fara alwala da ruwan butan gabanta har suka fita compound din,
sai a sannan Ahmad ya kalli Abuturrab yace "Don Allah wa yarinyar nan tayi maka kama da???" Abuturrab
yace "Wacce yarinya?" Ahmad yace "Yarinyar da ke xaune a compound" Da mamaki Abuturrab yace "Ohh
dama akwai yarinya xaune a compound din?" Wani kallo Ahmad ya jefa masa, Abuturrab ya daga
shoulders dinsa yace "Banyi noticing ba" Ahmad yace Karya kake "Wllh" Abuturrab bai kuma ce masa
komai ba, Ahmad yace "Joke apart captain, bata yi maka kama da wannan yarinyar da muke siyan awara a
wajenta a hayi ba" Abuturrab ya ta6e baki yace "Kai da kake kallonta kenan idan kaje siyan awaran, ni kam
banda murhu babu abinda nake gani a wajen" yana fadin haka ya shige Masallaci kafin Ahmad ya sake ce
masa komai, Ahmad ya bi bayansa kawai. Ko da suka fito masallacin Ahmad ya tsaya gaisawa da abokansa
na layin, Abuturrab ya shiga compound din kawai, Jiddah na ta sauri tana kwashe kayan shanyan da
Maman Abdallah ta shanya don garin akwai hadari, tun da ta kallesa sau daya ta dauke kai sai da ya iso dai
dai inda take tace "Ina yini?" Bai amsa ba yace "Kina da wani matsala?" Ta girgixa masa kai, ganin haka ya
ci gaba da tafiyarsa, dai dai nan Ahmad ya shigo compound din bata yadda ta kallesa ba har xai wuceta sai
ya tsaya yace "Bakuwa muka yi yau a gidan ashe?" Taki yarda ta kallesa still, tayi kasa da murya tace "Ina
yini" yayi murmushi yace "Lafiya lau, sannu da xuwa" Maman Abdallah ta leko tace "Dakta Abdallah fa
boyewa yake idan yaji muryar ka" Ahmad yayi murmushi yace "Ae kice masa alluran ya kare" Ta kwashe da
dariya tace "Lallai kam, shi dai ya tsorata da kai kawai Dakta" Ahmad yace "Ashe bakuwa muka yi gidan"
Tace "Ehh wllh yar uwata ce daga kauyenmu ta xo jiya da yamma" Yace "Allah sarki, toh barkan ta da
xuwa" Maman Abdallah tace "Ae ko dai Dakta, mun gode" Murmushi yayi ya ci gaba da tafiya a xuciyarsa
ya kara gaskata cewa lallai kamanni ne kawai suka yi da me Awara a hayi, but the resemblance is so
obvious even the dimples and large eyes, can balcony Abuturrab ya tsaya duk yana jin abinda suke fada,
sai da ya iso Abuturrab yace "Kai dai baka abu da class Ahmad, meye na tsayawa hira da matar mai gadi
pls?" Bai jira me xai ce ba yayi wucewarsa ciki, Ahmad ya girgixa kai kawai ya bi bayansa. Da yamma
Mamam Abdallah ta ba jiddah kwanukansu ta kai can cikin gida sbda a ciki xa a sa masu abincin dare,
Jiddah tace "Ta cikin parlon ake bi xuwa wajen girkin?" Maman Abdallah tace "Ehh inda muka je daxu ba,
ynxu ma babu kowa gidan yaran duk sun tafi islamiyya, Hajiya nasan tana bangarenta yanxu haka, ai kinga
dakin girkin da mai girki ta fito ta miko mana kumallo daxu da safe, nan xaki shiga, dakin ma ya kusa biyun
wannan da muke ciki ae wllh" Jiddah ta mike ta dau babban samiran ta fita ta bar Maman Abdallah na
linkin kaya, Babu kowa babban parlon kamar yanda Maman Abdallah tace, ko ina tsaf sae kamshin turaren
wuta da ya kama parlon, Kasa karasawa can cikin parlon Jiddah tayi, tun da ta xo duniya bata ta6a ganin
irin wannan parlon ba da ma komai na cikinsa, duk sai tsoro ya kamata, hanyar da taga Maman Abdallah ta
bi daxu da safe ta bi ta d'an leka kofar da ta gani a bude ganin wasu mata biyu kuma har sun hada ido ta
risina a hankali tace "Sannun ku da aiki" Duk suka amsa mata dayar tace "Shigo ki ajiye kwanon" Jiddah ta
karasa kitchen din, ta kara masu sannu da aiki sannan ta ajiye kwanon, kanta a kasa tace "Me xa a kama
maku?" Dayar matar tace "Aa babu komai 'yan mata, mun gode" Doguwar tace "Sae dai kawai wanke
wanken dake cikin bahon wanke wanke, ba shi da yawa" Jiddah ta juya tana kallon sink da matar ke nuna
mata, karasawa tayi wajen ta tsaya tana tunanin ta ya xata yi wanke wanke a takurarren waje haka sannan
ta ina xa ta dinga xubar da ruwan wanke wanken, a hankali ta juya tana kallonsu tace "Ruwa da omo fa"
Matar tace "Ga pampo a gabanki ki kunna, wannan roban kuma sabulun wanke wanke ne a ciki xaki matso
ya fito"

Bayan magrib Abuturrab yyi parking inda ya sa6a parking ya sauka motarsa ya kulle da kafa ya karasa kofar
gidansu Jiddah. Yaro ya aika ciki yayi masa sallama da mutanen cikin gidan, Hansai ce xaune tsakar gida da
kawayenta biyu, Hansai ta sharbe majina tana matse hawayen kumburarren idonta tace "Wllh xai aika,
waye bai san cewar shaye shaye Iliya yake ba, ni dai baxan kwana gidan nan ba yau gaskiya gwara in tafi
wani wajen in kwana" Zulai tace "Aa nima dama ban bada shawaran ki kwana ba tunda ya furta sai ya
kona gidan da kyar baxai aika ba" Ladi tace "Toh yanxu ina yarinyar nan ku ke tunanin xata tafi haka, wa
gareta a duniyar ma gaba daya?" Hansai tace "Ai wannan magana ma bai taso ba, dolenta ta dawo duk
inda ta tafi ta xo ta rabani da wannan mahaukacin mutumi, idan ya kona min gida gidan ubanwa xan koma
kowa na ta kansa a rayuwar nan, dama gidan iyah nake ta tunanin ta shige amma duk dubawan da yan
sanda suka yi a gidan babu ita babu alamarta" Kallon yaron da ya shigo suka yi gaba daya, yaron yace "Wai
ana sallama a waje" Abuturrab ya daga kai bayan Hansai ta fito cikin gidan, ganinsa ta makale kofar xaure
ta kasa karasowa, Ya karasa shi, yana dubanta yace "Ina yini?" Da kyar cikin rawar murya tace "Lafiya lau
Alhaji, sannu da xuwa" kafin yace mata komai ta fashe da kuka tace "Muna cikin tashin hankali da alhini
Alhaji" yana kallonta yace "Me ya faru?" Tana matsar kwalla tace "Tun jiya ake neman yarinyata har xuwa
yanxu babu labarinta, ban san inda xan sa kaina ba xuciyata kamar ta fashe" Yayi shiru yana kallonta, ta
sharbe majina tace "Shi kansa wanda ke da niyyar auren nata nan ya xo daxu da yamma ba irin tijaran da
bai min ba har da ikirarin xai kona mana d'an gidan nan idan ba a fito masa da matarsa ba, wllh wllh bamu
da masaniyar inda take, babban tashin hankalina ban san halin da take ciki ba yanxu" Yace "Yanxu ya ake
ciki da shi wanda xai aureta din, baki basa kudin nasa bane?" Tace "Wllh yace baxai amsa ba, yanxu haka
ma da kudin na tafi gun yan sanda na kai rahotu kasan sai an basu wani abu me d'an tsoka kafin su kula ka,
sannan gidan radio da gidan talabijin duk na bi na rarraba masu kudin don su yi ta sanarwa har Allah ya
bayyanata, yanxu maganar da nake maka ko dubu talatin ina jin kudin bai kai ba a ajiye a daki, 'ya ta bata
fiye min komai ba a duniya?" Kallonta kawai Abuturrab yake bai ce komai ba, ta sake sharbe majina cikin
rawar murya tace "In dai da wani taimakon da xaka mana yarinyar nan ta bayyana da wuri ka taimaka
domin girman Allah Alhaji" Abuturrab yace "Ina shi madaurin auren nata?" Tace "Kawuna ne, tare da shi
ma muke ta sintirin gidan radio da police station tun safe" Abuturrab yace "Ina son ki hadani da shi" Sosai
gabanta ya fadi, yace "Yana da waya?" Da sauri tace "Aa bashi da shi, sai dai gobe in je in sanar masa, idan
ka xo sai Bibalo ta kai ka" Abuturrab yace "Toh shkkn, nagode, sai goben" Daga haka ya juya ya bar wajen,
ta bi sa da kallo gabanta na faduwa, da sauri ta koma ciki, Zulai tace "Waye hala?" Hansai ta share wani
xufa da ya keto mata tace "Aa yan xuwa jaje ne, yanxu dai gidan Kawu Jibril xan tafi tare da Bibalo idan ya
so sai mu kwana can kawai kada Iliya ya far mana cikin dare mu mutu" Ladi tace "Gaskiya kam, ku tafi can
din kawai ku kwana, don kwana gidan nan ba karamin hatsari bane" Sai kusan karfe tara Hansai ta isa
gidan kawun nata da Bibalo, Suna shiga d'an tsakar gidan yace "Me kuma kika xo yi nan kina neman ki ja
min fitina Hansatu, ni nasan Iliya d'an daba ne amma bansan dabancin nasa ya kai haka ba, babu irin
tijaran da iliya bai xo nan da tawagarsa sun min ba, in don dai shegiyar dubu ukun da kika bani ne cikin
kudin sadakin yarinyar Allah ya kai mu gobe da safe in tafi in siyar da kaji na in baki kudinki, wannan tashin
hankali har ina a kan dubu uku, wllh ban san tantirancin iliya ya kai har haka ba, to gaskiya

10 / 108