Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
tace "Allah ya kara lafiya" yace "Ameen... Me Awara" dago kai tayi da sauri ta d'an wara ido, sai
kuma ta rufe fuskarta da pillow din dake kusa da ita tana murmushi, yyi kasa da murya yace "Ko ba ita
bace?" Ta turo baki tace "Ni ai ba awara nake yi ba yanxu" Yace "Ohkk... Ko xaki fara ne?" Ta d'an yi
murmushi taki ce masa komai, yace "Har yanxu ae kina da burin fara awara a bakin titin gida na...."
Murmushi take yi sosai, a hankali tace "Toh ai ba a unguwar nake ba yanxu..." Yace "Toh idan kika dawo
anguwan fa?' ta xaro ido tace "Me xai maida ni?" Yace "Ni xan maida ki duk sanda kika shirya" Tayi wani
murmushin bata ce komai ba, yace "Ko baki son komawa?" Tace "Wai in koma inyi mene??" Yace "Ki koma
kiyi ibada" Ta xaro ido tace "Wani irin ibada?" Yace "Irin warce baki samu daman yi ba" Tayi shiru kamar
me son fahimtar abinda yake nufi, can tace "Ni ban gane ba" Yace "Irin warce Allah yace ayi" Tace "Ban san
shi ba" Yace "Xaki san shi kwanan nan" Bata kuma cewa komai ba shi ma yayi shiru, a hankali tace "Allah ya
kara lafiya" yace "Ameen, sai dai ban ta6a cin awaranki ba tun da can ma" Tayi murmushi bata ce komai
ba, yace "Yeahh" tace "Sai ayi maka" Yace "Irin na Baabarku?" Shiru tayi, ya shafa kansa yace "Sai anjima"
daga haka ya katse wayar ta kalli screen din sannan ta ajiye a hankali... Abba ne xaune parlor da Hajja sae
Aunty, Hajja na gyara daurin dankwalinta tace "Ae kaga saboda xuciyata me kyau ce bana riko duk da
rashin kunyar da yarinyar nan ta min hakan bai hanani tsayawa har sae da na tika uwar Bashir da kasa ba,
don da cewa tayi inaaa d'an ta baxae ta6a auran mara asali ba, to duk duniya banda shege waye bai da
asali, da yake kabiru na jin maganata yana min biyayya don har ma ya fi ka, ba shiri ya taka mata birki ya
dau maganata da muhimmancin gaske, to ba gashi komai na tafiya dai dai ba" Abba dai sae kallonta yake,
Aunty dake ta boiling from inside sai kallon Hajja take amma ba daman cewa komai, kasa hakura tayi daga
karshe ta dake tace "Toh shi Bashir din me yace Hajja?" Hajja tace "Aa baya ma kasar, yo shi Ina ruwansa,
galallawa ne fa yaron nan da kuke gani, duk yanda nayi yace dai dai ne yasan baxan masa xa6in da xai
cucesa ba, toh ni abinda yasa na makale ma yarinyar saboda tsaftarta ne baxan biye rashin kunyan da tayi
min ba, duk da nasan wannan narkekiyar matar Ramlah ce xata koya mata ta min haka, amma da baxa ta
min haka ba... Yanxu dai Kabiru yace kai sai ka xama madaurin aurenta wato waliyyinta, so nake kafin
Bashir ya dawo an daura sai dai kawai a wanketa a kai masa dakinsa, uban ma ya amince da hakan...."
Abba yace "Toh Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi" Hajja tace "Cewa xaka yi Allah ya baki ladan wannan
jihadi Hajja, ka ga ai da ni tsohuwar banxa ce baxan so in hada Jiddah da jinina ba don wllh gidan da Aliyu
ya kai ni a hayin rigasa yace nasu ne, duk da a rushe gidan yake amma kana ganin gidan kasan na fakirai ne,
su talaucin ma ba karamin kamu yyi masu ba, da kyar ake samun masu talauci irinsu, mu dai ba saboda
Allah kawai muke abun mu ba dama, Allah dai kawai ya bamu lada" Mikewa Aunty tayi ta nufi kofa ta fice
Hajja ta bi ta da wani kallo tace "Ae kaga da yake ta kaina nake, ni ko da wasa ban ta6a kawo d'an ta Salem
a rai ba balle wataran ta zageni ko shi ya xageni, amma yanxu haka da xaka shiga xuciyarta xaka san hadin
nan bai mata ba, na rasa abinda jiddah tayi mata da wannan tsana haka" Abba yace "Xan d'an fita Hajja,
sae na dawo anjima" Tace "Toh Allah ya tsare, cikin satin nan Kabiru yace xa a kawo komai kilan har sadaki,
wato shi ma xaman yaron a haka ya ishesa ashe, magana ce kawai baya yi, gashi sae yyi ta fita kasar waje
an rasa uban me yake xuwa yi a can" Daga haka ta mike tace "To ba ruwana, ita warcan narkekiyar sae ka
tafi har can gidanta ka yi mata bayanin komai don kar ta xo ta min rashin albarka ta cuce ku, ba karamin
aikinta bane, don duk tayi bake bake kan lamarin yarinyar" shi dae bai ce mata komai ba har ta fita, girgixa
kai kawai yake yana mamakin Hajja, ya dau wayarsa ya shiga kiran Ummi, tana shigowa ya tsara mata duk
yanda suka yi da Hajja, Ummi ta rike ha6a tace "Ikon Allah, Haka dama auren yake da sauki Yallabai, ina
laifin ma ta kare secondary din tunda ta dauko hanya? Ita fa Hajja idan ta shirya abu a ranta babu me
canxa ta, sannan tana ta nuna Bashir din ma yace ba ruwansa, tayi duk yanda tayi.. to an ta6a aure haka
babu fahimtar juna tsakanin mata da mijin? Ko magana fa basu ta6a yi ba a waya" Abba yace "Ba dai tace
shi Kabir ya amince ba ya bata goyon baya? To Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi, ita ma yarinyar Allah
ya sa hakan babban alkhairi ne a gareta" Ummi dai tayi shiru, can tace "Ba fa a tambayi yarinyar nan ko tayi
na'am da hakan ba, it's more or less like auren dole xa ayi mata, gwara a fara jin ta bakinta Yallabai, kar a
ga kamar don ba mu muka haifeta ba shi yasa ake juyata yanda ake so, hakan ba dai dai bane wllh" Abba
yace "Wannan kuma ai aikin ke da Hajiya Ramlah ne, xuwa anjima sai kije can gidan kiyi mata bayani
sannan a ji ta bakin ita yarinyar, don a yanda Hajja ta axalxali batun nan sai ta iya cewa cikin sati biyu ma
take son ayi bikin" Ummi tace "Toh Allah ya kyauta, amma ya dace ka kira shi mai martaban kaji ta bakinsa,
kilan ma shirinta ne ita kadai wa ya sani?" Abba yace "Ehh ina jiran nan da d'an anjima ne xan kirasa in sha
Allah" Ummi tace "Toh Allah yayi mana me kyau" Abba ya amsa da "Ameen" mikewa tayi ta fita daga
parlon. Umma ce xaune bedroom dinta tare da Ummi, ta jira har Ummi ta kai aya sannan tace "Kinga
yanda baxan so ayi ma Maimoon ko Safiyya ko Siyama auren dole ba, to haka ita ma Jiddah baxan yarda da
hakan ba Yaya, a ajiye batun ai ko bani na haifeta ba, wllh yanda xanyi ma 'ya yan cikina ita ma haka xan
mata, ku yaya Hajja sai tayi ta wasu abubuwa kamar dai notiran kanta sun kwance amma ku dinga biye
mata a rasa me gaya mata gaskiya? Meye amfanin hakan fisabilillah? Ni fa na xata tunda nace aa an bar
xancen ne ashe abinda ya kai ta bauchi kenan ma? To ni dai sai dai a fadi duk abinda xa a fada amma
Jiddah is too young for that marriage, sannan har take ikirarin uwar Bashir din bata so amma tayi ruwa da
tsaki a kan lamarin har sai da ta sa kowa ya amince, wani xaman aure take son yarinyar taje tayi a wannan
babban gidan Ummi, shikenan saboda bata da iyaye ita marainiya ce sai aka ce bata da gata? Aa wllh tana
da gata don yanda na dau su Maimoon haka na dauketa, Hajja taje can ta samar ba Bashir wata matar
amma ba Jiddah da ko secondary din ma bata kare ba" Ummi tace "Toh ina ga xai fi ki tashi kije ki samu
Hajja kiyi mata duk bayanin nan, ke wani lkcn kina magana kamar baki san Hajja ba, kin gan ni nan duk fa
abinda xai dameni ko ya bata min rai bana so yanxu, ta kaina kawai nake babu ruwana, In dai Bashir din da
bakinsa yayi admitting yana son Jiddah kuma xai xauna da ita i see nothing wrong with that, domin kuwa
shi din ba wani xama yake a kasar ba, bini bini ya fita, to ba sai ya tafi da matarsa ba, ina Jiddah xata ga
uwarsa idan ba dawowa kasar suka yi ba, kinga wllh yanda kike hakikancewa a batun nan tsaf Hajja xata ce
Hassada kike tunda ba er ki bace, don haka ina baki shawara ki bi komai saisa saisa babu ruwanki..." Umma
tace "Aa kiyi hakuri yaya a gaskiya da ruwana, Hajja kuma ba tun yau na saba da tijararta ba, kuma ni kema
kin san raga mata nake kawai sabida ke, banda haka ni baxan yi tolerating haka ba, kuma a gaskiya idan
haka abubuwa xa su ci gaba da faruwa gwara ki tafi da Jiddah can gidan don ma kada taga kamar ban tsaya
mata ba tunda ni ba uwarta bace.. ki tafi da ita kawai ku yi yanda ku ka ga ya dace da ita, dama ai Hajjar ta
sha fada min ba don Aliyu ba a ina xa a santa, don haka ki tafi da ita ku yi mata bayani a can amma ba a
nan ba" Ummi dai kallonta kawai take, Umma ta mike tace "Haka kawai ga gaskiya a dinga takesa kiri kiri,
ita Hajjar Allah ce da dole sai an bi abinda tace mata gigin tsufa duk ya rikitata kuma ayi ta bin ta a haka, ba
ga jikokinta sa'annin jiddar ba, tayi masu auren mana idan haka ne, kiyi hakuri fa kar kice rashin kunya
nake maki Yaya, aa gaskiyata nake fadi, kawai don Jiddah bata da gata a duniya sai a tauyeta?? To dauketa
ku tafi kuyi yanda ya dace da ita, babu ruwana" Mikewa Ummi tayi ta fita daga dakin tayi wucewarta...
Bayan tafiyar Ummi da kusan awa daya su Maimoon suka dawo Islamiyya, bayan sun gaida Umma dake
xaune parlor xa su wuce dakinsu Umma tace "Da wani number kike waya da Aliyu Maimuna?" Maimoon ta
dawo, Jiddah ta d'an saci kallon Umma sannan ta wuce ciki, Maimoon tace "Da numbersa ne yana shiga"
Umma tace "Toh" daga haka ta mike ta wuce dakinta ta hau kiran Abuturrab wayar bai yi connecting ba
hakan yasa ta ajiye ta fito... Sai can da daddare Umma ta sake kiransa sai ya shiga, yana dagawa bayan sun
gaisa tace "Kana ji na Aliyu?" Yace "Ina ji Umma" Tace "Ka dai ji abinda iyayenka ke shirin aikatawa ai ko?"
Ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Na me fa?" Tace "Ohh duk baka sani ba, to Hajja ta dage ita dole sai tayi
ma Jiddah aure da Bashir, na kiraka ne kuma saboda naga kamar tana jin maganarka, i want u to put a stop
to that, ko secondary bana fatan Jiddah ta gama ace xa a aurar da ita, don haka talk sense into Hajja"
Abuturrab dai yyi shiru, ta hade rai tace "Ko baka ji na ne?" Yace "Ina ji Umma, xan kirata in sha Allah,
nobody told me about it, tace to wa xai gaya maka dama tunda cutar yarinyar ake son yi" a hankali
Abuturrab yace "Shkkn, i will call her in sha Allah" Tace "Do so immediately" Daga haka ta katse wayar ta
ajiye lamarin na kara kona mata rai, wai aure kamar xa a aurar da wata mara makabuli, to su yi ta gani.
Hajja ta gama sauraron Abuturrab tsaff sannan tace "Toh ko ubanka Usman wanda shine lallai dole ne bai
isa yace xai dakatar da ni kan abinda nayi niyya ba, kai kuma a wa Allah na tuba? Kai da ka walakanta
yarinya ka cuceta ka mayar da ita baxawarar karfi da yaji sannan ka saketa? Kai fa ba wani abu ke damunka
ba banda kishi, kuma sai dai ka hadiyesa don tayi maka nisa wllh, idan ma sa ka aka yi ka kirana ka koma ka
fada ma wanda ya sa ka ai ba Hajjar da bace yanxu, bana nufin er yarinyar nan da sharri banda alkhairi,
yanda ta taso cikin bakar talauci da rashin ga ta so nake ita ma ta ci arxiki ta bar sa a inda ta gansa, so nake
ita ma ta shiga babban gida a dama da ita, to na meye kowa sai bakin ciki abinda ni Allah bai daura min ba
kenan, to kowa dai ya ci kansa ya kurkure da bakin ruwa, kai kuma ina baka shawaran ka kauda idonka a
kan duk wani abu da ya shafi yarinyar kayi mana me wuyar tunda ka kawota cikinmu" Tana kai wa nan ta
katse wayar, Abuturrab murmushi kawai yake yi... Kawai bayan sati daya sai ga shi Aunty ta kira Umma wai
an kawo kudin Jiddah daga masarautan bauchi... Ummi ta fi minti talatin rike da wayarta bayan aunty ta
katse, Allah kadai yasan yanda take ji a xuciyarta a lkcn.... Sai yamma ta shirya ta tafi gidan don bata son
xuwa ta tadda mutane, ai ko duk yan kawo kudin sun watse, parlon Abba ta shiga direct, yana xaune shi da
duk brothers dinsa, Umma ta xauna bayan sun gaisa gaba daya tace "Alhaji Usman dama wajenka na xo"
Abba na kallonta ya dau wayarsa yace "Toh Allah ya sa lafiya, in taso ne?" Tace "Ehh" tana fadin haka ta
tashi ta fita, Abba ya mike ya bi bayanta, can kofar gida suka fita tana kallonsa tace "Yanxu Alhaji an xaunar
da ita yarinyar an tambayeta ko tana son auren nan da ake shirin kulla mata? Domin bata da kowa ba yana
nufin bata da gata Alhaji, this is wrong wllh" Abba yace "Domin bata da kowa mu ma ba yana nufin xa mu
cutar da ita bane, did you know this is a great privilege to her also? Ki duba fa wanda ake son hadata aure
da? Wa kike tunanin Hajja xata yi ma hakan banda ita din??" Umma tayi wani murmushi tace "Wato
privilege? But she never begged for that privilege Alhaji, idan kuma xa ayi adalci kamata yyi a ji ta bakinta
don a fita hakkinta, an ta6a yi ma mutum dole a aure? Shkkn sai aka ce ita bata da choice da dream
dinta?" Abba ya duba wayarsa jin shigowar message yana dubawa yaga message din Abuturrab, and the
content goes as thus "Kada ya kasance ana neman Aure ne a kan Aure Abba, that is highly prohibited in
islam.... We plan but Allah plans best in sha Allah" Abba ya karanta text din ya fi sau uku, can ya mika ma
Umma dake kallonsa, Umma ta amsa tana dubawa ita ma dai sau ukun ta karanta tana sake duba sender
din, a ranta tace Aliyu?? A fili kuwa tana kallon Abba tace "Shashasha, to me yake nufi da text din? Wa ake
nema ma aure a kan aure?" Abba yace "I am still trying to understand that too" Umma tace "Ka kirasa" Ba
shiri Abba ya hau kiransa amma ya ji layin a kashe, ya kira sau uku duk a kashe, Umma tace "Wai wa yake
nufi ne?? Wa ake nema ma aure kan aure?" Abba yace "Tare mu ka karanta text din nan yanxu Hajiya
Ramlah" Umma tace "Toh ina jin shaye shaye ya fara a can din ko" Abba dai bai ce komai ba, Umma tace
"Ni dai na gama magana, idan xa ayi mata adalci ayi mata, a tunaninku gata xa ayi mata tunda xa a aura
mata d'an sarki, to amma kwanciyar hankalin xaman gidan auren fa, tunda naji ance uwar tasa ma ba so
take ba, kuyi ma Allah a duba lamarin nan idan kuma shakkar yi ma Hajja magana ake ni sai inyi mata wllh"
daga haka tayi ma Abba sai anjima ko gidan bata sake shiga ba ta bude motarta ta shiga, driving take
amma tunanin solution da xata samar ma Jiddah take don in dai kuwa aka yi auren nan kilan bata doron
kasa ne, samm baxata ta amince da auren ba, baxata ta6a bari a shiga hakkin yarinya ba. Abba na komawa
cikin compound ya sa a kira masa Ummi, tana fitowa ya mika mata wayarsa yace "Ko xaki iya fahimtar wani
abu a message din nan kiyi min bayani??" Ummi sai karanta message din take da surprise barin da ta ga
cewar Aliyu ne sender din, can ta kalli mai gidan nata tace "What's the meaning of this?" Yace "Shine nake
son ki min bayani" tace "Jiddar matar aure ce da xai ce kar a nemi aure kan aure?" Abba yace "Shine nake
son fahimta Hauwa" Ummi tace "Ikon Allah, to ka kirasa" Abba na kokarin sake kiransa yace "A kashe
wayar" sai gashi ance wayar a kashe, Ummi tace "Ji d'an rainin wayo, aurar da ita yayi ne ba a sani ba, ko
ko?" Abba dai bai ce komai ba yayi shigewar sa ciki, Ummi ta bi sa da kallo, gaba daya ta ma rasa wani
tunanin xata yi, anya kuwa Abuturrab na da kai? Menene manufar wnn text din wai kar a nemi aure kan
aure, to ko aure yake nemar ma Jiddar basu sani ba ne. Abba na komawa gun brothers dinsa su ma ya basu
wayar su duba message din, bayan sun duba da daddaya da daddaya, suka dinga kallon Abba, Alhaji
Salmanu yace "Neman aure kan aure kuma? To ko dai bai saketa ba ne dama Alhaji Usman?" Abba yayi
dariya yace "Ya fara hauka kenan, ai har yanxu takardan na nan bai je ko ina ba" Abba na fadin haka ya
mike ya wuce daki sai gashi ya fito da takardan ya mika ma Alhaji Salmanu ya amsa ya karanta sannan ya
ba duk sauran ma suka duba, Alhaji Salmanu yace "Ikon Allah, to me yake nufi da hakan? Is he even in his
right senses?" Abba ya daga kafada yace "I thought as much" naxari duk suka yi shiru suna yi, Alhaji Umar
yace "Try his line ko xai yi connecting" Abba ya sake kira yaji a kashe, Alhaji Lawal yace "Toh ko dai komawa
yayi aka sake daura masa aure da yarinyar?" Kallonsa Abba yayi da sauri almost with shock, sai kuma yayi
wani dariya yace "Aa he must be joking ashe, har ya isa ya sake yin hakan? Da kuwa nayi disowning dinsa
wllh... Allah kuwa da ya ga the other side of me, wato ga yan iska ya ajiye, wllh in har hakan ne ya kasance
Aliyu xai yi mamakina ainun" Alhaji Umar yace "Ikon Allah, that just dawn on me bayan Lawal ya fadi haka,
in dai kuwa ba shi ya koma ya aureta ba to wani ya kai ya aureta, don babu yanda xai turo wannan
message din idan ba dayan biyun abinda na fada ya kasance ba, but that's bad... Who does that,