Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta
samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar
rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata
masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda
zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada
Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240
Abuturrab yace "But you didn't tell me kina xuwa Aneesah" Aneesah tayi wani murmushi tace "How will i
tell you ina xuwa Aliyu, dama dalilin da yasa kake walakanta ni kwana biyu kenan, dama wata ka samu?
Dama wannan ce dalili" Daga sama har kasa take kare ma Jiddah kallo tana murmushin takaici tace "Ki bar
murna kin samu pilot har yana kawo ki gidansa saboda tsagwaron so, nima haka ya dinga min, but...."
Abuturrab ya katse ta yace "Come off it pls Aneesah, what's all this? I thought i explain better to you her
position, she is the lady...." Aneesah ta sake kallon Jiddah da sauri, Jiddah dai banda kallonta ita ma babu
abinda take, A hankali Aneesah tace "Which lady Aliyu?" Yayi kasa da muryar yace "Ba ke kika ce in kawota
ta xauna gidanku ba" Sosai gaban Aneesah ya fadi don bata ta6a tunanin Jiddah ce wnn yarinya da
Abuturrab ke fadi mata ba, ta dinga kallon Jiddah xuciyarta na bugawa, ta ma rasa abinda xata ce masa,
Abuturrab yace "Tunda kin xo yanxu sai ku tafi tare, dama anjima nake son kai ta gidan naku, hopefully
nasan Mumy ta yarda ta xauna with ur family..." Aneesah ta hadiye abu da kyar, har sannan ta kasa daina
kallon Jiddah da tayi mata wani kwarjini, a xuciyarta ta shiga kokwanton anya ita ce me awaran da Aunty ta
ce, or is Aliyu playing her?? Abuturrab ya juya ya kalli Jiddah bbu yabo bbu fallasa yace "Dauko mayafinki"
Shiru tayi tana kallonsa, a d'an tsawace yace "Baki ji na ne?" Ta koma baya tace "Toh ina xanje idan na
dauko?" Yace "Ban sani ba, wuce ki dauko" Juyawa tayi ta koma can tsakiyar parlon ta tsaya kamar xata yi
kuka tace "Allah ni babu inda xanje, ba gidan Baabarmu nace ka maida ni ba, nasan ita wacece da xan bi
ta" Daga maganarta Aneesah ta kara tabbatarwa ita ce me awaran, Abuturrab ya saki baki yana kallon
Jiddah, Aneesah ta hade rai tace "Toh nan din gidan ubanki ne da baxa ki bari ba?" Jiddah ta kalleta, a
hankali tace "Ubana fa kika ce?" Aneesah da xuciyarta ya dau tafarfasa tace "Shi din..." Lkci daya Jiddah ta
fashe da kuka tace "Ba dai ubana dake kabari ba wllh sai dai naki" Aneesah ta saki jakar hannunta tace
"Kika xagi ubana?" Jiddah ta goge idonta tace "Ehh an xaga, me nawa uban ya maki da kika xagesa ke?"
Aneesah tayi kanta a mugun fusace, fixgota Abuturrab yyi yace "Hey are u okay, what are u trying to do?"
Fixge hannunta tayi kamar wata zakanya ta nufeta, cikin tsawa Abuturrab yace "Don't try that Aneesah, u
will definitely see the other side if me by touching her" Tuni Jiddah ta tsorata ta bar wajen da gudu ta yi
hanyar kitchen hakan bai hana Aneesah bin ta ba, shakota Aneesah tayi tace "Uban wa kika xaga?" Tuni
Abuturrab ya nufesu, Jiddah ta kwala kara ta gatsa mata cixo a hannu, Aneesah bata yi wata wata ba wajen
sauke mata lafiyayyen mari a fuska sannan ta wuntsular da ita a kasa tana cewa "Don kaza kaxanki ubana
sa'an kaf danginki ne aka ce maki?" wani ihu Jiddah ta fasa tana cewa wayyo bayanta, wayyo kafarta,
Kamar daga sama Aneesah taji saukan tagwayen mari wanda sai da yasa taga duhu na few seconds, ya
fixgota fiercely yace "How dare you? You bitch" with shock Aneesah ke kallonsa, ya nufi kofa ya wuntsular
da ita waje kamar yanda ta ma Jiddah yyi banging kofar, Banda rusa kuka babu abinda Jiddah dake yashe a
kasa take tana kiran Baabarmu, Bude kofar Aneesah tayi tana daga tsaye bakin kofa hawaye kaca kaca a
fuskarta tace "You called me a bitch Aliyu?? Ni ka walakanta ka sauke yatsunka fuskata a kan wannan yar
talakawan bagidajiya jaka? Ni ka ci ma mutunci haka in her present? U threw me out of ur house a kan yar
talakawa me tallan awara?" Jiddah ta goge idonta ta mike cike da tsiwa tace "Idan ana tafiya lahira da
arxiki sae ki daura naku a kai ki tafi da shi in ga, kuma Allah ya isana, ban yafe maki ba, axxaluma...." Fixgo
hannunta Abuturrab yyi ya nufi daki, cikin kuka tana son kwace hannunta take cewa "Ni ka kyaleni, me na
mata xata mareni...." Turata yyi cikin dakin ya sa makulli, sai a snn ya daga kai ya kalli Aneesah, ji yyi gaba
da gwiwansa ya sace, ya nufeta, tana ganin haka tayi wani murmushi tace "Watch out for it Aliyu, xaka san
ba a ta6a mu a xauna lafiya, daga yau ka kafa daka sanin abinda ka min a rayuwarka..." Daga haka ta dau
jakarta xata fita parlon hawaye na sauka idonta, ya rikota yyi kasa da murya yace "But Aneesah...." Ko rufe
baki bai yi ba ta sauke masa mari sau biyu, hakan bai sa ya saketa ba ta dinga dukansa a kirjinsa, ya
rungumeta gamm yace "I'm sorry Aneesah" kuka kawai take, shi kam duk jikinsa yyi sanyi, cikin rawar
murya tace "A kan wannan bagidajiyar xaka mareni and throw me out of ur house Aliyu??" Ya kwantar da
ita kirjinsa yace "U are misperceiving me Aneesah..." Turasa tayi da karfi ta nufi kofa tana kuka ta fita, dafe
kansa yyi ya xauna saman kujera yana furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, daukar wayarsa yyi ya shiga
dialing number Ahmad, har ya katse bai dauka ba, yana ta xaune parlon har kusan magrib sannan ya mike
da kyar, bedroom din da Jiddah ke ciki ya nufa ya bude kofar, kwance ya ganta a kasa, ya karasa ciki yana
kallonta ya duka, bacci take, ya kai hannu goshinta, bude ido tayi, ya daure fuska ya mike, ta tashi xaune
tana mitsika ido, yace "Kin san warce kika xaga daxu?" Ta kallesa tace "Toh ai nima bata san wacece ni ba"
ya duka yana kallonta da kyau yace "Gaya min ke wacece?" Ta turo baki ta taki cewa komai, kallon fuskarta
da shatin mari ya kwanta kawai yake, can ya mike jin xa a tada sllh ya fita dakin.
Abuturrab na dawowa masallaci ya ga kiran Ahmad a wayarsa, ya xauna sannan ya kuma dialing number sa
ya kai kunne, daga daya bangaren Ahmad ya daga yace "Ya kwana biyu?" Abuturrab ya shafa kansa ya mike
ya koma dakinsa, a hankali yace "Alhmdlh, how is work?" Ahmad yace "Alhmdlh, baka yi piloting xuwa
Abuja bane yau" Abuturrab yace "Ina Abuja" Ahmad yace "Alright, ya na ji ka so calm dude?" Abuturrab
bai ce masa komai ba, Ahmad yace "Xan shigo after isha" Abuturrab yayi kasa da murya yace "Ka taho da
paracetamol or any pain reliever" Ahmad yace "Ko har Aneesar ta je ne?" Abuturrab ya katse wayar, ya
ajiye yana tunanin where he is going to start from, sure yasan yana son Aneesah sosai baya son komai da
xai bata mata rai, But why did all this happen, why did things turn out this way.... Shafa kansa kawai yayi
knowing the only way out now shine ya tura gidansu in few days time, wayarsa ya sake dauka har xai yi
dialing numberta ya fasa. Abuturrab na xaune parlor bayan ya dawo isha yana jiran xuwan Ahmad, karfe
takwas da few minutes Ahmad ya danna bell, ya mike ya bude masa kofa, Ahmad ya shigo parlon, xaunawa
yayi saman kujera yace "After leaving me all my self with my wedding preparation, still u have d gut not to
ask how everything is going.... right?" Abuturrab yace "Ohk ka fara shirye shirye ne?? Sure juma'ahn sama
ne koh? I'm sorry na manta wllh, what are u up to now? Kasan ba haduwa muke yanxu a kadunan ba
kamar da" Ahmad yyi dariya yace "Ya xa mu hadu kuwa, tunda ga ka ga amaryar ka Jiddah" Abuturrab ya
tsura masa ido, can yace "Is there anything i will gain idan na maka karya Ahmad?? But don Allah ka gaya
min me yasa kake ganin har ynxu matata ce ita?" Ahmad yace "Toh gashi nan ba sai na fada ba, da fa duk
na shigo kd sai mun hadu, infact kai ma kake xuwa gidanmu ynxu kuwa kana gidanka, idan ba wanda yyi
sabon aure ba, giyan auren na dibarsa waye ke yin haka??" Abuturrab yace "Ka dai jira xanyi auren kwanan
nan sae kaji dadin fadin duk abinda ke ranka, amma yanxu kam i am a bachelor just as u, sae sabon title da
na samar ma kaina na xama Uba, i am more like a father or guardian now" Ahmad yyi murmushi yace "Toh
ka bani ita inyi ta biyu da ita Captain" Abuturrab ya kallesa, kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Are
you for real?" Ahmad yace "I'm serious wllh in dai Umma xata yrda i will" Abuturrab yace "Ohk, but.... How
are we going to open up all this to our parent? Kasan dai ynxu banda Aunty da kai, sai ita yarinyar babu
wanda yasan babu auren nan" Ahmad yace "We will cross the bridge when we reach there, yanxu dai ka
amince min kai?" Calmly Abuturrab yace "In da gaske kake na amince, nima burden xai sauka kaina, if not
for her da banyi making mistake da nayi daxu ba" Ahmad yace "Wani mistake?" Abuturrab ya dau remote
din TV yana canxa channel yace "Ba ruwan ka" Ahmad yyi murmushi yace "Everything is settled now tunda
ka amince"
Kafin karfe tara Jiddah tayi bacci bayan tayi wanka, Hijab din Aneesah dake gidan ya bata tayi sllh tun
magrib. Abuturrab na xaune har sannan a parlor tare da Ahmad sae dai hankalin sa baya tare da Ahmad,
bai yi tunanin Ahmad xai kai har 10 a gidan ba, Can dai Abuturrab yace "Wai kana kallon agogo kuwa?"
Ahmad yace "Ohh
ta kusa xuwa kenan, anyway ko baka fada ba dama yanxu xan wuce sai da safe" Daga haka ya mike ya nufi
kofa Abuturrab ya bi sa da kallo, mikewa yyi ya bi bayansa yace "Ka ajiye ni eatry let me get something to
eat" A tare suka fita gidan, sai kusan karfe goma da rabi Abuturrab ya dawo, yana shigowa parlor ya kulle
gidan sannan ya wuce dakin da Jiddah take, tayi nisa baccinta, Ya ajiye ledan abincin ya nufi gadon, buga
gadon yayi ko motsawa bata yi ba, yayi hakan ya kai sau uku ganin bata tashi ba ya dau bottle water ya
bude, sai kuma ya fasa xuba mata ruwan ya ajiye sannan ya kai hannu kafarta yana tashinta, bude ido tayi
a hankali, yace "Tashi ki ci abinci" Ta girgixa masa kai tace "Na koshi" Yace "C'mon tashi nace" Mikewa
xaune tayi da kyar tana kallonsa da idanuwan bacci tace "Na koshi" Ya hade rai yace "Sakko nace" Xamowa
tayi ta sauka kasa tana lullumshe ido, ya bude mata tuwo da veg soup din, ta tashi tana rurrufe ido yace
"Ina xa ki?" Tace "Xan wanke hannu" Bai ce komai ba ta tafi ta wanke hannun ta dawo, tun da ta fito yake
kallonta, Kana ganin yanda Hijab din yayi a jikinta xaka kasan bata saka komai ba a ciki, dama kuma hijab
din har kasa yake ja mata, xaunawa tayi ta jiginar da kanta jikin gadon ta lumshe ido, buga gadon yayi ta
bude ido da sauri ta kalli abincin gabanta sannan ta kai hannu ta fara ci a hankali, juyawa yayi ya fita
dakin.... Washegari da safe Abuturrab ya fita yayi mata shopping din few clothes, karfe goma kuma ya nufi
airport tare da ita, babu abinda ya sanyaya masa jiki sai yanda kiran Aunty ya dinga shigowa wayarsa babu
kakkautawa, shi kuma yaki dagawa, Jiddah na ganin inda suka xo hankalinta ya tashi, marairaice masa tayi
tace "Ni fa bana son hawan jirgin wllh" Yana kallonta yace "Sai me xa ki hau?" Tace "Motar" Wani kallo yayi
mata yace "Sai ki hau motar inda kika gansa ai" Lkci daya hawaye ya kawo idonta bata kuma ce masa
komai ba, tun bata kai ga shiga jirgin ba taji kanta ya fara juya mata, Tana rike da wayansa da ya bata ta
nemi kujera ta xauna a business class, sai waige waigen inda xata gansa ta mika masa wayar take, to ina shi
yake xama ne a cikin jirgin, tunawa tayi a inda ta gansa jiya bayan jirgi ya sauka, and she assumed a wajen
yake xama shi, jin taku a gefenta Jiddah ta juya, buda ido tayi sosai ganin wanda suka shiga jirgi tare da shi
a rana na farko, seat dinsa ya nufa ya ajiye karamin jakar hannunsa a sama sannan ya xauna, da sauri ta
dauke kanta gabanta na faduwa, wata mata ce ta xauna kusa da ita tayi mata sannu, murmushi kawai
Jiddah ta mata tana juya wayar Abuturrab dake hannunta, bayan wani lkci jirgin ya tashi, suna keta hazo ta
cire seat belt dinta da sauri ta mike bayan ta ajiye wayar Abuturrab, hanyar lavatory ta nufa sai a sannan
Yousuf ya ganta ya bi ta da kallon mamaki, ba a dau lkci ba ta fito, matar dake kusa da ita tace "Did u feel
nauseous?" Jidderh tayi mata murmushin karfin hali ta xauna, Ta d'an saci kallon Side din da Yousuf yake
suka hada ido, sunkuyar da kanta tayi, throughout the short journey to kano bacci tayi a jirgin, snacks da
aka kawo mata ma bata ci ba, Matar dake gefenta tayi tapping dinta tace "Ki saka seat belt dinki" Bude ido
Jiddah tayi ta fara saka seat belt din, runtse ido tayi da jirgin ya fara sauka bayan ya samu izinin yin hakan,
matar da ta lura she is very uncomfortable ta riketa, tace "It's just for a few seconds, sorry dear" Jiddah
bata ce mata komai ba har jirgin ya sauka, rufe bakinta tayi kar ma tayi ihu, matar na Kallonta tana
murmushi tace "it's all over" A hankali Jiddah ta cire seat belt din, bayan da jirgin ya tsaya ta mike ta dau
hand bag dinta ta fara fita kamar yanda ta ga sauran nayi, da kallon mamaki matar ta bi ta, tana mamakin
to ko kurma ce dai, Yousuf ya mike ya dau jakarsa ya bi bayanta da sauri, a hankali take sauka daga
matakalan jirgin iska me sanyi na kadawa a filin airport din, tana sauka kasa kamar ance ta juya taga Yousuf
yana saukowa shi ma, murmushi ya sakar mata har ya iso inda take yace "Jiddahh" Ta sunkuyar da kanta
bata ce komai ba, mika mata hannunsa yayi yace "Bani wayar taki in sa maki number na tunda Allah ya sa
kin taho da shi yau" Ta buda ido sosai tace "Ba wayata bane, na yayana ne" Da mamaki yake kallonta yace
"Yayanki? Yana ina?" Ta kalli cikin jirgin tace "Kaman yana ciki, ni dai ban gansa ba" Yace "Ina ku ke xuwa
tare da shi ko da yaushe a jirgi?" Tace "Nima dai ban sani ba" Yace "Baki sani ba kamar ya?" Tace "Allah
ban sani ba ne" Yayi shiru yana kallonta walking slowly together with her, can yace "Me ku ka je yi a
Lagos?" Ta kallesa da sauri tace "Lagos?" Yace "Ehh" Tace "Nan ne Lagos din don Allah?" He couldn't help it
but left his mouth agape yana kallonta with surprise, ta dauke kanta tana ci gaba da tafiya yace "Wait
Jiddah, are you kidding me, or you just don't want to give me an answer" Bata ce komai ba, calmly yace "I
am talking Jiddah..." Tsayawa tayi tana kallonsa tace "Ni fa ba wani turanci nake ji ba" Sake baki ya kuma yi
yana kallonta, bai san lkcn da yace karya kike.... Tace "Wllh ba karya nake maka ba" Sincerely ta fadi hakan,
ya shafa kansa yana sake kallonta daga sama har kasa yana naxarin abinda tace wai bata jin turanci, but
how?? tsadadden abaya ce jikinta blue da ya mugun haskata, ko kwalli babu a idonta, wanda kuma bai kalli
lips dinta da kyau ba, sai yayi assuming pink lip gloss ta saka coz after being pinkish har sheki lips din nata
yake, ga manyan idanuwanta farare tasss kamar madara, hancinta kuwa have the perfect shape a nose
should have snn ga tsayi, ya d'an mata murmushi yace "Na yarda Jiddah, yanxu ina xa ki?" Tace "Nima ban
sani ba yayana nake jira, kilan yana saman jirgin har yanxu" Yace "Yayanki... iyayenku daya da shi?" Shiru
tayi can kasan ranta kuma tana tunanin abinda xata fada masa, yace "Ki gaya min gaskiya Jiddah" Ta kallesa
still bata ce komai ba, yace "Ina sauraranki" ta kwantar da kai tace "Me yasa kake son sani?" Yace "I just..."
Shiru yayi kamar wanda ya tuna abu, sai kuma yace "Kawai ina son sani ne" Tace "Ba iyayenmu daya ba
amma yayana ne" A hankali yace "Ko dai saurayin ki Jiddah" Ta wani xaro ido, sai kuma ta kyalkyale da
dariya tace "Saurayi na? Saurayina fa kace? Aa ni ba saurayina bane shi wllh, saurayina sunansa Umar
amma mun rabu yanxu" Yace "Umar?" Tace "Ehh, shi wannan kawai yayana ne" Wayar hannunta ya amsa
da sauri tace "Nace maka nasa ne wayar" Bude screen din yayi don wayar a bude yake, ya dinga kallon
hulan pilot dake jikin screen din wayar, karban wayar tayi hannunsa, xuwa lkcn bbu kowa haraban parking
din jirgin sai ma'aikatan airport, Yousuf ya daga kai yana kallon Abuturrab dake saukowa daga jirgin yana
kallonsu babu ko kiftawa, har sannan pilot uniform ne a jikinsa, Jiddah ta daga kai ganinsa ta kalli Yousuf
tace "Shine yayan nawa" Yousuf ya d'an yi murmushi yace "Shine matukin jirgin... i guess right" Juyawa
Jiddah tayi da sauri tana kallon Abuturrab, Yousuf ya karasa gunsa ya basa hannu suka gaisa yana
murmushi yace "I guess you did the landing..." Abuturrab na kallonsa ya d'an yi murmushin gefen baki
kamar wanda aka tilasta ma yace "Yea, i did" Yousuf yace "Nice landing...." Abuturrab yace "It's a pleasure
flying you" Yousuf ya masa murmushi sannan ya juya ya bar wajen, yana isa inda Jiddah take yace "Ina jiran
kiranki kamar yanda kika yi alkawari ranan" Yana fadin haka ya wuce, Jiddah ta kalli Abuturrab da ya hade
girar sama da ta kasa yana kallonta.... A motarsa suke tafiya xuwa hotel din da suka sauka a kano, har
sannan babu abinda yace mata, sai dai fuskarsa bbu ko digon annuri, har suka isa hotel din, kulle dakin
hotel din yyi after going in together with her, yana kallonta fuskarsa a tamke yace "Waye