Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
ma bata samu ta ci ba, da rana yan matan amarya duk
suka yi shirin tafiya saloon, dama kafin Ummi ta lura da Jiddah balle har tace mata ta bi su, aunty ta hada
kayan wanke wanke a bakin pampo ta turata taje tayi, yawanci duk masu girki ranan sun xata ma mai aikin
gidan ce Jiddah, ko mai aikin gidan bata yi aikin da Jiddah tayi ba tunda gari ya waye, cikin ruwan sanyi
Aunty ke gallaza mata, duk tunanin Ummi kuma har da Jiddah aka tafi saloon don tun bayan da suka gaisa
da safe bata ganta ba, a gajiye Jiddah ta fito daga kitchen wajen karfe hudu ga wani yunwa da take ji, wata
tsohuwa ce ta mika mata purse tace "Yan mata ki kai min daki wajen Hajiya Hauwa ta adana min, kada a
yasheni a gidan biki, dubu daya da dari biyar ce a ciki" Jiddah ta amsa tace "Toh" lkci daya Jiddah ta gane
warce take nufi wato Ummi, bangaren Ummi ta nufa ta bude kofar parlon da sallama, Ummi da frnds dinta
Uku ne a parlon sai wasu yan uwa guda uku, Jiddah ta gaishesu gaba daya, Ummi dai sai kallonta take da
mamaki, Jiddah ta sunkuyar da kanta ta duka gefenta tana mika mata jakar tace "Ummi wai ajiya aka ce a
kawo maki" Ummi ta amshi purse din tace "In ji waye?" Jiddah tace "Ai ban santa ba" Ummi tace "Dama
baki je saloon din ba ke" Jiddah ta gyada mata kai kawai, Ummi tayi shiru tana son nuna ma yan uwan mai
gidanta da kawayenta cewar ita ce matar Aliyu amma ta kasa, can dai tana kallon jiddah tace "Toh gobe sai
a kai ki ke" a hankali Jiddah tace "Toh" daga haka ta mike, dai dai nan Abuturrab ya fito daga bedroom din
Ummi, sosai gaban Jiddah ya fadi bayan sun hada ido, amma kuma sai taji dadin ganinsa ba kadan ba, duk
yan parlon suka juya suna kallonsa, Ummi ma kallonsa tayi don tun daxu take fama da shi ya fito ya gaisa
da yan uwan Abbansa su uku sun iso daga Damaturu amma ya ki fitowa wai ya gaji, gwara frnds dinta a
parlon ya samesu da ya shigo, Hajiya Zuwaira ta rike ha6a tace "Dama Aliyu na ciki?" Ummi ta kirkiri
murmushi tace "Eh bacci yake, saukansa daga kano kenan ko awa biyu ba ayi ba" Tuni Jiddah ta fita daga
parlon, gaishesu Abuturrab yayi yana yake ya nufi kofa ya fita parlon Ummi ta bi sa da kallon mamaki har
ya kulle kofar, har Jiddah tayi nisa yace "Keee" tsayawa tayi ta juya tana kallonsa, ya karasa inda take yana
kallonta daga sama har kasa, gaba daya ta wani susuce, yace "Yaushe kika xo gidan nan" Ta sunkuyar da
kanta tace "Umma ce tace mu taho..." ya kara kallonta daga sama har kasa sannan ya sa hannu ya ciro
makulli a aljihunsa yace "Dakin dake ta can bangaren inda babu mutane, ki je can ki jirani" Tana kallon
makullin tace "Bude kofar xan yi?" Ya hade rai yace "Aa kullewa xa kiyi, bakya jin hausa ne?" Juyawa tayi ta
bar wajen don ta gane dakin da yake nufi babu wanda ke xuwa ta wajen, bata yarda ta kalli kowa ba har ta
nufi bangaren ta sa makullin ta bude dakin sannan ta shiga, babban daki ne sosai babu abinda babu a ciki,
sai dai abubuwan ciki ba masu hayaniya bane, sannan ba a wani cika kaya a dakin ba, xaunawa tayi kasa ta
jinginar da kanta kan babban katifar dakin don gaba daya ta gaji, Bayan kusan minti sha biyar taji an bude
kofar dakin ta daga kai da sauri, Shine ya shigo dakin, ya kulle kofa yana kallonta yace "Baki cin abinci ne?"
Ta girgixa kai tace "Aiki nake yi shi yasa ban ci ba" Yace "Wani aiki?" Tace "Nayi wanke wanke da safe na
share duk tsakar gidan, sannan na taya masu girki wanke naman kaza, wani wanke wanken ya taru na kara
wankewa, kuma naje siyo ledan kwasan tuwo sau uku wajen da nisa sosai almajiri ne ya rakani, da na
dawo kuma wani wanke wanken ya taru na sake yi, sannan na share tsakar gidan da aka bata...." Katseta
yayi yace "Duk wa yake sa ki?" Ta sunkuyar da kai tace "Aunty" Bai ce komai ba, bayan kusan minti biyar
yace "Tashi ki shiga bandaki ki hada ruwa kiyi wanka" Mikewa tayi ta nufi bandakin she looks so tired and
worn out, ya juya ya fita ya sa ma dakin makulli ya cire ya tafi da shi, a parlor ya tadda Aunty na welcoming
din bak'in da suka shigo da mugun fara'arta, ido hudu yayi da mahaifiyar Aneesah, Ya sauke kansa kasa
sannan ya karasa cikin parlon ya gaisheta da ladabi bata ko kalli inda yake ba balle tayi kamar ta ji, Aneesah
ce ta shigo parlon da jakar kayanta, Aunty ta rungumeta tace "Sannunku da xuwa manyan baki, ya hanya?"
Aneesah na murmushi tace "Alhmdlh Aunty don ma dai jirgi muka biyo ai da sauki wahalan" Kofa
Abuturrab ya nufa don ko hada ido bai son yi da Aunty, Babu yabo bbu fallasa yaji tace "Aliyu get them
something meaningful to eat, kasan sha'anin abincin biki, ba lallai yayi suiting taste bud dinsu ba" Toh
kawai Abuturrab yace ya fice daga parlon. Parking Abuturrab yayi bakin gate dai dai lkcn da driver ya sauke
su Seeyama bakin gate din, duk suka nufi motarsa, bai amsa gaisuwar da suke masa ba, ya dau leda biyu na
abinci yace "Ku kai ma Aunty" Seeyama ta amsa sannan suka wuce ciki, bayan few minutes ya bude motar
ya sauka ya shiga cikin gidan rike da leda daya, direct part dinsa ya nufa, ya ciro makulli ya bude kofar ya
shiga sannan ya kulle, Jiddah na kwance kan carpet idonta kulle, karasawa yayi yaga bacci take, ya buga
katifar kusa da ita, firgit ta mike xaune, ya ajiye ledan hannunsa ya hade rai yace "Baki ce ma Ummi baki ci
abinci bane duk yau?" Ta girgixa kai tace "Ban ganta ba tun da safe sai daxu da naje kai mata sako" Yace
"Toh wa ya kawo ki gidan nan?" Tace "Nace maka Umma tace in taho tare da su seeyama" ajiye ledan
hannunsa yyi ya mike ya koma can karshen katifar ya xauna ya fiddo wayarsa dake vibrate a tunaninsa
Ahmad ne don yana restaurant ma ya kirasa, amma sai ya ga akasin haka don Aneesah ce ke kiransa,
silencing wayar yyi, Jiddah ta bude abincin da ya ajiye mata ta fara ci. Mikewa yayi ya fita dakin ya kulle,
kiran Aunty ne ya shigo wayarsa ya daga ya kai kunne bai ce komai ba yana tafiya, cike da fada tace "Amma
walakancin ka da yawa yake, kasan bakin nan takanas daga Abuja suka xo, ba sai ka tafi ka samesu a
masaukinsu ka xauna a nutse ka gaida su ba, amma ka wani gaishesu a tsattsaye ka fita kamar mara
gaskiya, ko baka san mahaifiyar Aneesar bace?" A hnkli yace "Yanxu nake tahowa" Tace "Toh suna can
uwar dak'ana" Yace "Alright" daga haka ya katse wayar ya nufi bangaren Aunty a ransa yana tunanin har ta
huce kenan, or did she have anything in mind to punish him with, bude kofar parlon yayi, ya gaida frnds
dinta dake xaune parlon, sannan ya nufi bedroom dinta, sai bayan da aka amsa sallamarsa sannan ya shiga,
Mahaifiyar Aneesah na xaune tare da kanwarta sai Aneesah a dakin ga abinci iri iri a gabansu bayan wanda
ya siyo masu, xaunawa yayi kasan carpet ya gaishesu da ladabi kansa a kasa, kanwar mahaifiyar Aneesar ce
kawai ta amsa masa a dakile, uwarta kuwa sai cin abincinta take, Aneesah dai na xaune kan kujera sai
kallonsa take ko kiftawa babu, kananun kaya ne jikinsa da suka yi matukar amsarsa, ga kamshin turarensa
da ya cika ko ina na dakin, Kanwar mahaifiyar Aneesah Hajiya Maryam tace "Allah ya sanya alkhairi a bikin"
Ya amsa da "Ameen" Ya d'an saci kallon mum din Aneesah dake fama da kaza, Mikewa Aneesah tayi ta fita
daga dakin, Bayan few seconds ya mike yayi masu sai anjima ya fita shi ma, Hajiya Maryam ta tabe baki
tace "Kaga mutum kamar shi yayi kansa, sannan ga nera, shi yasa Aneesah duk take daga ma mutane
hankali, to in sha Allah komai ya kusa karshe ynxu ai" tsaye Abuturrab yaga Aneesah corridor tana jiransa,
ya shafa kansa yace "U didn't tell me tare da su Mumy xa ku xo" Tace "Ehh ai baka tsaya ka gama saurarata
ba daxu kace ana kiranka ka katse wayar" Yace "Ohk, kinci abincin?" Tace "Bayan leda biyu ka siyo me xan
ci a ciki?" yace "Ehh ai banga Hajiya ba i only saw u and mum" Ta tabe baki tana gyara siririn gyalenta, ya
rungume hannunsa yace "Toh yanxu ya xa ayi?" Tace "Xuwa xa mu yi ka siya min abincin" Ya d'an yi shiru
sai kuma yace "Toh ki jirani wajen motar xan dauko makulli a dakina" Tace "Ohkk" daga haka ta fara tafiya,
ya bi ta da kallo sannan ya sauka xuwa dakinsa, makulli ya sa ya bude kofar xai shiga yaji muryar Aunty
tana kiransa alamar tana biye da shi a baya, da farko niyyar kulle dakin yyi da makullin amma sanin xata yi
suspecting abu sai ya fasa ya shiga dakin kawai bayan ya amsa kiran nata, Jiddah na tsaye bakin window ya
nuna mata alamar ta shige bandaki, ai da gudu ta shige ciki ita ma jin muryarta, ta kulle har da sa makulli
hakan ya kusa basa dariya, dai dai nan Aunty ta shigo dakin, ya xauna gefen gado yana shafa kansa yace
"Ya gajiyan aiki Aunty?" Maimakon ta amsa sai ta sa makulli dakin ta shigo, shi dai kallonta kawai yake, ta
kalli ledan abincin tace "Wannan fa?" Yace "Ni na siyo na ci" Kujera ta ja ta xauna tace "Abuturrab!!" Ya
daga manyan idanuwansa ya kalleta, sake kiransa tayi murya can kasa yace "Na'am...." Tace "Dama
Abuturrab ra'ayinka ne xuwa hayi kayi aure ban sani ba? Dama haka ka mayar dani gantalalliya ban sani
ba" Ya girgixa kai yace "Wllh ba ra'ayina bane Aunty" tace "To son yarinyar ka fara all of a sudden? Da ka
toxarta ni gaban ubanka?" Ya girgixa kai yace "Ko daya wllh Aunty" tace "Toh kawai xubar min da mutunci
da walakanta ni gaban iyayenka ka so yi??" ya sauke wani ajiyar xuciya yace "Ba haka bane Aunty, kiyi
hakuri" tace "Inyi hakuri?? Dama shirga ni kayi baka saketa ba Aliyu??" Da kyar yace "I'm finding it hard to
confide in u anymore aunty..." Tace "Why??" Yace "U did what i never expected, kema kin san na kowa me
sauki ne kan na Abba, how will u expect him to take it cewar na saketa da gaske? Wllh he can even disown
me, kin fa san waye Abba, kin fi kowa saninsa, amma kika yi exposing dina wajensa" Da karfi tace "Karya
kake, wllh baka saketa ba ni xaka mayarda sha sha sha yanxu? Are u stupid?" Yayi kasa da murya yace "Xa
kiyi kaffara Aunty, nace maki ba aure tsakaninmu da yarinyar nan amma kuma bai kai har ki je ki gaya ma
Abba ba, i trust u shi yasa na sanar maki" Shiru tayi tana kallonsa tana huci tace "Toh dadin xama kake ji da
ita ne da kaki rabuwa da ita har yanxu???" Yace "Ko daya, idan na rabu da ita bata da wajen xuwa Aunty,
Aunty da xa ki kwantar da hankalinki ki xuba min ido xaki ga me xai faru in sha Allah, i have plans wallahi,
ba haka nan kawai na ajiyeta gidana ba, the house isn't meant for her..." tace "Which nonsense plan Aliyu,
dubi fa yanda yarinya tayi wani kyau ta kara uban haske fatarta lui lui kamar a latsa jini ya fito, a haka ne
xan amince da kai baxan sa shakku a raina ba? Dubi fa yanda tayi fresh alamar bata da wani damuwa ta
samu gida kawai, sbda ita ko weekend ka daina dawowa gidan nan sai dai ka sauka can kayi yanda kaga
dama da ita, don wllh ban yarda baka harkanka da ita ba" Kallon Aunty ya dinga yi ba ko kiftawa, sannan
yace "Inyi harka da ita fa fa kika ce Aunty" Tace "Toh eh mana, kana xaune da budurwa irin wannan a gida
baxa kayi yanda kaga dama ba?" ya girgixa kai yace "Ba yanda kike tunani bane aunty, amma dai yanxu ya
kike son ayi?" Aunty tace "Kawai ka dawo da ita gidan nan gaba daya da xama, she will be very useful wllh"
Kallonta kawai yake yi, tace "Ko baka ji abinda nace ba?" Yayi murmushi yace "Na ji" tace "Wato baxa ka yi
ba kenan??? Wato wllh ban ma yrda cewar babu abinda ke shiga tsakaninka da yarinyar nan ba da ya sa
kaki rabuwa da ita har ynxu duk da ba auren" Ya girgixa kai yace "No plss, Wllh babu wani abu Aunty ai
kinsan ba haka nake ba" Tace "Toh ka maidota gidan nan nace idan na isa da kai, tunda already tana nan
kawai kayanta xaka debo gaba daya ka maido su nan" Ya shafa kansa yace "Toh Aunty amma sai mun yi
magana da Ummi ko...." Wani kallo ta jefa masa tace "Sai kun yi magana da Ummi? Ni ban isa da kai ba
kenan da xaka yi involving Ummi??" Yace "Kin isa" tace "Toh ba sai ka sanar mata komai ba, kawai taga ta
dawo nan din, idan tace don me, sai kace ita kadai ce a gida kuma aiki ya maka yawa" Yace "Ohkk" mikewa
tayi tace "Xan koma wajen bak'ina, bayan bikin xa muyi magana a tsanake" Daga haka ta bude kofa ta fita
ya bi ta da kallo, mikewa yayi ya karasa ya kulle kofar dakin sannnan ya dawo ya bubbuga kofar bandaki,
bude kofar Jiddah tayi ta fito tana kumbure kumbure tace "Don Allah kar ka dawo dani gidan nan kayi
hakuri" sai kuma ta sakar masa da kuka, dariya abun ya basa, ya dake yace "Gidan namu kike kuka kar in
dawo da ke??" Tace "Don Allah kayi hakuri" yace "Dole ma ki xauna nan din ki samu saiti sosai"
Durkushewa tayi gabansa ta hade hannayenta tana kara rushewa da kuka tace "Aa don girman Allah kayi
hakuri" Xaunawa yayi gefen gado yace "Kin fi son xama tare da ni kenan, duk da kince ni ba muharraminki
bane?" Ta gyada masa kai a hankali tana share idonta, ya kauda kai yana murmushi, tuna Aneesah dake
jiransa bakin mota yyi, da sauri ya tashi ya dau makullin motarsa ya fita ya kulle dakin ta bi sa da kallo. Har
Aneesah xata shigo parlor suka hadu bakin kofa, sai da ya fara surveying wajen yaga ba mutane ya riko
hannunta yace "C'mon dear, am sorry Aunty ce ta bata min lkci wllh" hararansa kawai take, yayi murmushi
ya ja hancinta sannan yace "Mu je" duk abinda tace xata ci ya siya mata a eatry din da suka je sannan suka
dawo gida, ta tafi bangaren Aunty shi kuma ya tafi dakinsa, bude kofar yayi ya tadda jiddah yanda ya barta,
ya kulle kofar ya shiga bandaki yayi wanka ya fito ya sauya kayan jikinsa xuwa pajamas sannan ya kwanta....
Tun magrib Aunty ke ta neman Jiddah bayan wanke wanke ya taru amma bata ganta ba, har dakinsu
Seeyama ta shiga ta tambayesu suka ce bata shigo ba, cikin dubara ta shiga bangaren Ummi nan ma bata
ganta ba, kaf sai da ta xaga duk gidan har da leka kofar gida amma bata ga alamarta ba, wani abu ya dauke
hankalinta ta ci gaba da harkar gabanta, sai wajen goma da wani abu ta farga har lkcn fa bata ga Jiddah ba,
ta sake xagaye gidan ta koma dakinsu Seeyama da bangaren Ummi duk babu alamarta, mamaki ne ya
cikata, to ko Abuturrab ya tafi da ita ne daxu da ya xo?? Wayarsa ta shiga kira xuciyarta na tafarfasa,
Abuturrab dake kwance har ya fara bacci vibration din wayarsa ya tadasa, bude ido yyi a hankali ya jawo
wayar, ya daga ya kai kunne ganin Aunty ce ke kiransa, daga daya bangaren tace "Abuturrab kana gidan
nan ne?" Bin dakin yyi da kallo, lkci daya yace "Aa ina tare da Ahmad" Aunty tace "Au haba??" Yace "Ehh a
nan xan kwana, da wani abu ne?" Ta girgixa kai tace "Aa tunda baka nan sai da safe kawai" Daga haka ta
katse wayar tayi wani murmushi, dama so take ta ta66atar da cewar ba shi ya dauketa ba, addu'a ta shiga
yi a ranta na cewar Allah yasa karawa gaba jiddah tayi kawai... Abuturrab ya kalli kasan carpet din dakin ya
ga jiddah kwance ta gaji da kukan bacci ya dauketa, har ya koma ya kwanta ya mike ya bude press dinsa ya
fiddo da xanin gado ya rufa mata sannan ya kwanta saman gado ya kashe wutan dakin. Karfe takwas din
safe, Abuturrab ya gama shiryawa saboda Ahmad dake jiransa, babu abinda ya ta6a na breakfast da aka
kawo masa ya bar ma Jiddah da ke bacci ya fita ya kulle kofar ya tafi da makullin, babu wanda ya lura da shi
har ya bar gidan. Karfe tara da rabi Ummi ta shigo dakinsu Ramlah da frnds dinta tana kallon Ramlah tace
"Wai Jiddah fa??" Ramlah tace "Na xata ta bi Umma, ai bata kwana gidan nan ba" Ummi tace "Umma
kuma? Umma ta xo gidan nan ne jiya?" Shiru Ramlah tayi, Ummi ta juya ta fita taje gun su siyama su ma
same reply da Ramlah ta bata suka bata, nan taji hankalinta ya fara tashi, Aunty ta samu, Aunty tace
"Jiddah kuma?? Ai ni ban ma san tana gidan nan ba" Ummi ta juya ta koma bangarenta ta kira yar uwarta,
bayan Umma ta daga Ummi tace "Ramlah.... Jidderh ta koma gidanki ne??" daga daya bangaren Umma
tace "Jiddah?? Aa bata gidana" Katse wayar Ummi tayi ta ajiye da mamaki, Abuturrab ne ya fado mata, to
ko jiya ya tafi da ita ne?? Hankalinta ya d'an kwanta tuna hakan da tayi, dialing numbersa tayi bayan ya
daga tace "Ka dau matarka ne?" Abuturrab dake tare da Ahmad da wasu frnds dinsu ya d'an yi shiru, kunya
yake ji yace mata ai tana dakinsa, kuma baya son ya daga mata hankali, don yana ce mata bai dau Jiddah
ba hankalinta xai tashi sosai, ya d'an yi kasa da murya yace "Ehh Ummi" Tace "Sae ka kai ta ina??" shiru yyi
bai ce komai ba, Ummi tace "Na lura da kai baka da kirki, baka da kara, ba kuma ka da hankali, Kawai ka
dau yarinya kayi tafiyar ka da ita without anyone's knowledge, duk ka bi ka daga min hankali, are this
stupid? yarinyar da kake ikirarin ka aura ba da son ranka ba kamar yanda