Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
bata ji shigowar Jiddah ba
har yanxu, har kawayenta suka gama jiranta suka bar gidan bata dawo ba, kilan ma gidan Umma ta tafi, da
sauri tace "Kana ganin babu matsala captain, kar in kai mata kuma fa ta xageni, kaga ni bana son fitina
wllh" Yace "Ki kai mata" mikewa tayi tace "Toh" daga haka ta fita daga dakin ta nufi dakin Jiddah ta bude
kofar a hankali ta leka ciki taga babu ita babu alamarta, kulle kofar tayi ta fara knocking ta yanda xai ji...
tana cewa "Assalamualaikum, Jiddah xa ayi maki magana a waya, Jiddah, Jiddah..." Ta kira sunanta yayi sau
biyar, sai kuma ta juya tace "Ka dai ga... Tana ji wllh taki cewa komai Captain, kofar ma ta sa key" Yace
"Ohk, sai da safe" Tace "Toh Allah ya kai mu captain, goben xaka dawo ne?" Yace "No, sai friday da safe in
sha Allah, i will be piloting all throughout" Tace "Toh shkkn Captain Allah ya kai mu Friday din, Allah ya
tsare min kai, sai mun yi magana gobe" Yace "Ameen... In sha Allah" Daga haka ya katse wayar, tayi wani
murmushi tana jujjuya wayar hannunta ta koma dakinta ta karasa shirinta a hanxarce, wardrobe dinta inda
take ajiye bedsheets ta bude ta daga squeezed bedsheeta din nata ta dau wani sealed abu a leda ta cusa
cikin handbag din nata, tana ganin xanuwan gadon suka xubo kasa ko bin ta kansu bata yi ba ta dau Hijab
dogo ta saka ta boye handbag din ta cikin hijab din ta bude dakin ta fito ta kulle da makulli ta sauka
downstairs, ta daga wayarta da ya fara ring tace "Gani nan tahowa na fito yanxu" daga haka ta katse wayar
ta fito compound, sosai taji dadin ganin mai gadi yana sallah a compound din yayi backing dinta, ta lallaba
tana tafiya a hankali ta nufi gate, ta bude ta fice daga gidan. Jiddah na xaune parlon Hajiya Fatima sanye da
Hijab din Khaleesat, Hajiya Fatima ta gama waya da mai gidanta da baya kasar bayan ta nemi izininsa na
cewa xata fita, ajiye wayar tayi ta kalli er ta Rahama tace "Toh yanxu ita haka xa a fita da ita babu izinin shi
mijin nata?" Aunty Rahama tace "Atohh ai komai kamawa yake Mama, ba kuma fitar shiririta xa ayi ba, da
ma dai ana son yasan tana nan ne sai ki amshi numbersa a wajenta ki kirasa, amma ni wllh bana son ma
yasan tana gidan nan" Hajiya Fatima ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh ko dai a amshi number tasa a wajenta
sai a kirasa kar ma aje ayi ta nemanta mun ajiyeta a nan" Aunty Rahama tace "Mama don Allah mu je mu
dawo, ayi ta nemanta din, yasan baya son ya nemeta me yasa xai barta da wnn rikakkiyar matar su biyu
kadai a gida, ai shima yayi kuskure wllh, bai yi tunanin abinda xai je ya dawo ba" Mikewa tayi ya fita,
mahaifiyarta ta bi bayanta, Jiddah dai kanta na kasa, Hajiya Fatima tace "Kina da number Aliyun ai ko?"
Jiddah ta girgixa kai tace "Aa bani da shi" Tace "Toh tashi mu je" Mikewa tayi ta nufi kofa suka bi bayanta,
Aliyu dake xaune parlor yana jiran fitowarsu tun daxu ya mike ya fita yana rike da makullin motarsa, Jiddah
da Hajiya Fatima suka xauna back seat, Aunty Rahama kuma ta xauna a gaba, cikin minti ashirin suka isa
hayin rigasa, Jiddah ta nuna masu hanyar gidan nasu, bayan Aliyu yayi parking ya juya yana kallon Mum
dinsa, Hajiya Fatima na kallon Jiddah tace "Xa mu shiga ciki ke ki xauna a mota kin ji" a hankali Jiddah tace
"Toh" Duk suka sauka motar har Aliyu suka bar ta ita kadai, Aunty Rahama ce tayi sallama kofar xauren
gidan, wani d'an tsoho ya fito yana kallonsu yace "Wa ku ke nema?" Hajiya Fatima ta gaishesa tace "Sannu
baba, matar gidan fa?" Ya d'an buda ido yace "Wai matata?" Sake lekowa waje yayi yana xaro ido ganin
katuwar motar dake parke a firgice yace "Bayin Allah lafiya kuwa?" Hajiya Fatima tayi murmushi tace
"lafiya lau baba, kar ka wani samu damuwa" Tsohon da ya ji hankalinsa ya kwanta yace "Toh bari ayi
kiranta..." Juyawa yayi ya koma ciki sai gasu sun dawo tare da matar tasa, ita ma a tsorace take kallonsu
tace "Lafiya??" cikin kwantar da murya Hajiya Fatima tace "Ba ke ce Malama Hafsatu ba" Da sauri matar
tace "Aa bani bace ba wllh...." Tsohon yace "Hajiya siyan gidan muka yi, ko wata uku bamu yi da dawowa
nan ba..." Matar tace "Kuma tunda muka dawo nan yan bashi ke xuwa neman matar nan da kika ambata,
kusan kullum sai an xo mana nan... idan ku ma bashin ya kawo ku to kuwa ance bata ma garin ta gudu, ta
cinye ma jama'a kudi ta tsere" Hajiya Fatima tace "Hasbunallah, yanxu bata garin nan kuma?" Matar ta tafe
hannu tace "Wllh kuwa, wannan gidan ma da ta siyar ance ko dubu hamsin bata tsira da shi ba sbda duk
bashin lapo ta biya, kuma har yanxu da nake maki wannan magana mutane sun fi ashirin da take bi bashi a
hayin nan, ta tsallake kawai ta bar garin, an dai ce hakkin er marigayin mijinta ke bibiyarta, mu ma haka
muka ji, wllh babu wanda yasan inda take" Hajiya Fatima tace "Toh Allah ya kiyaye Allah ya kyauta" Suka
amsa da "Ameen" Hajiya Fatima da su Aunty Rahama suka juya suka koma gun motarsu, Jiddah dake cikin
motar sai kallon wasu mutane da suka fito daga gidansu a maimakon babarta da Bibalo take, nan da nan
taji gabanta ya fadi, Hajiya Fatima ta bude bayan motar tana kallonta, sai kuma tayi kasa da murya tace
"Babu wani naku a unguwar nan bayan stepmum din taki Jiddah?" A sanyaye Jiddah tace "Basa gidan kuma
ko Mama?" Hajiya Fatima tayi shiru tana kallonta, sai kuma a hankali tace "Ta siyar da gidan, ta bar garin"
Jiddah bata san lkcn da ta fashe da kuka ba, Hajiya Fatima ta hade rai tace "Meye haka kuma? Meye na
kuka? Kukan naki ne xai dawo da ita" Jiddah ta girgixa mata kai tana share idonta wasu hawayen na xubo
mata tana tausayin rayuwarta kuma, Hajiya Fatima da duk jikinta yayi sanyi tace "Wa kike tunanin a
unguwar nan gaba daya xai iya sanin inda ta tafi ko inda ta koma?" Jiddah na share idonta da kyar tace
"Kila Iyah, ga gidanta can" Hajiya Fatima ta sa ta sauko daga motar suka nufi gidan Iyah gaba dayansu,
banda Aliyu dake jingine jikin motarsa, sosai shi ma yake tausayin Jiddah... her story is heartbreaking, no
relatives, no siblings, no parent, nothing nothing, what a life, Jiddah ta rungume Iyah bayan sun shiga
gidan, Iyah ta kasa boye farin cikinta ta rasa inda xata sa Jiddah tsabar murnan ganinta sai ta fara hawaye,
Hajiya Fatima dai kallonsu kawai take tana tsaye daga gefe da Aunty Rahama, Iyah ta farga da su ta dauko
tabarma da sauri bakinta har kunne ta shimfida masu tace "Sannunku da xuwa, kun xo bamu da wutan
nepa, fitina kuma batur yayi sanyi, ku xauna don Allah" Hajiya Fatima ta xauna, Aunty Rahama ma ta xauna
sannan suka kara gaisawa, Iyah na kallon Jiddah dake xaune ita ma tayi nisa tunanin da take tace "Jiddah
Hansai dai ta siyar da gida ta bar garin..." Jiddah ta sauke idonta kasa wasu hawayen na taruwa idonta, A
Hankali Hajiya Fatima tace "Haka muka samu labari kaka, domin can muka fara xuwa kafin nan, yanxu kaka
baki da masaniyar inda ta koma" Iyah tace "Ai babu wanda yasan inda wannan mata dai ta koma, duniya
tayi mata xafi, kowa ya juya mata baya, er ta kuma Bibalo ta dauko mata abun kunya, ko kafin su bar
anguwan nan bibalo Haihuwa yau ko gobe, abun dai babu dadin fadi, Hansai na cikin gararin rayuwa
yanxu..." Hajiya Fatima tace "Ya salam, Allah ubangiji ya bamu dacewa..." Iyah tace "Ameen, alhakin Jiddah
kadai ya isa hanata xaman lafiya a duniya duk inda xata je kuwa, haba ai Allah ba axxalumin bawansa bane,
ta xalunci yar nan da kike gani, ta xalunci uwarta... Duniya kam ta juya ma Hansai baya, ita kanta kawarta
me xuxxugata tana can ciwon kafa ya sa ta gaba ana tunanin yanke kafar ma xa ayi, bata iya xuwa ko ina,
Zulai ba" Jiddah dai sai kallon Iyah take hawaye na sauka idonta, Hajiya Fatima tace "Toh ita zulan yanxu
bata san inda Hansatun take ba?" Iyah tace "To sai dai ko gobe in shirya inje in jiyo maku, amma babu
tabbas ta sani, in sha Allah ni dai xan je" Hajiya Fatima tace "Mun ko gode kaka Allah ya kara girma" Dubu
uku Hajiya Fatima ta ajiye ma Iyah daga haka suka yi mata sallama da xummar gobe xa su dawo su ji yanda
suka yi da Zulai a kan whereabout din Hansai, har suka koma gida Jiddah jikinta a sanyaye yake sai goge
hawaye take a idonta, Hajiya fatima ta sa yayar Khaleesat ta kawo mata dinner don bata ci ba kafin su fita.
Karfe tara da yan mintuna that same day Abuturrab yayi horn bakin gate din gidansa, Mai gadi ya taso da
sauri ya bude masa gate din ya shiga yayi parking sannan ya sauka, gaba daya a gajiye yake, kwanan nan
stressing kansa yake sosai na kai wa da komowa da yake xuwa kaduna, ya shiga ciki yana jin shoulders
dinsa na ciwo saboda driving da yayi, sama ya tafi ya bude kofar dakin Jiddah ya shiga ciki, ya dinga bin
dakin da kallo kafin ya juya ya fita, dakin Aneesah ya nufa ya murda kofar ya ji sa a kulle, mamaki ne ya
cikasa, ya tafi bangarensa ya xauna, bayan minti sha biyar ya mike ya sake komawa dakin Jiddah don a
tunaninsa daxu tana bathroom ne, ganin har sannan bata cikin dakin ya karasa ya tura kofar bayin yaga
wayam babu kowa ciki, juyawa yayi ya sauka kasa da mamaki, ya shiga kitchen yaga babu kowa ciki nan
ma, ya fito yana bin parlon da kallo cike da surprise, Ya kalli agogo dake nuna goma saura ya nufi kofa ya
fita, gun mai gadi ya tafi mai gadin ya taso da sauri ya sake gaishesa, bai damu ya amsa ba yace "Babu
kowa gidan... Da yaushe suka fita?" Mai gadin yace "Toh ita dai Hajiya daxun nan bayan magriba ina sallah
naga fitarta, ita Hajiya karama kuma gaskiya tun da safe naga fitowarta kamar da matsala don hankalinta
ma baya jikinta ta fito, ina tambayarta lafiya ma bata saurareni ba ta fita gate, sai na tafi da sauri in ga
meke faruwa, to ni dai ban ga kowa a parlon ba ma" Abuturrab ya rasa ma exactly tunanin da xai yi ya
dinga kallon mai gadin xuciyarsa na bugawa, juyawa yayi da sauri ya koma ciki ya dau wayarsa ya shiga
kiran Maimoon tana dagawa yace "Jiddah tana gidanku ne?" Maimoon tace "Jiddah kuma? Aa yaya bata
nan, lafiya?" Strictly yace "I am not joking" Tace "Wllh Allah bata nan yaya" he was shock at that, yace
"Look, bance kice da Umma komai ba" Daga haka ya katse wayarsa ya kira Nafisah ita ma tambayar da yayi
mata kenan tace bata xo ba, lkci daya ya ji hankalinsa yayi mugun tashi, ya juya da sauri ya fita ya koma gun
mai gadi yace "Ita warce ta fita da safen ina kaga ta nufa?" Mai gadin yace "Yallabai ai ina ganin yanda ta
fito kamar da matsala cikin gidan sai na yi cikin gidan da sauri, wllh ban san inda tayi ba, kuma ko da na fito
babu alamarta" Abuturrab ya ji wani xufa na keto masa duk da yanda garin yayi sanyi don da akwai hadari,
he was shock, a xuciyarsa ya dinga nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ya nufi gate ya fice daga gidan
direct ya tafi gidan Hajiya Fatima....
Abuturrab na shiga compound din gidan ya tafi entrance din parlon yayi knocking, he is just trying his very
best to be calm, mai aikin gidan ta bude kofar, ta gaishesa bai amsa ba yace "Mama na ciki?" Tace "Eh
Bismillah" shiga parlon yayi ya xauna saman kujera, sosai ya ji kansa ya masa nauyi dama ga gajiyar da yake
tare da shi, Mai aikin ta tafi dakin Hajiya Fatima, bayan kusan minti biyar Hajiya Fatima ta fito parlon
ganinsa tace "Aa, ashe kai ne, welcome son" Ya daga kai ya kalleta ya kasa cewa komai, ta xauna saman
kujera cikin sanyin murya yace "Ina yini Mama?" Tace "Lafiya lau, ya su Jiddah da abokiyar xamanta" Bai
san lkcn da ya kara gyara xama ba xuciyarsa na bugawa yace "Mama Jiddah bata shigo nan ba?" Hajiya
Fatima tace "Jiddah kuma? Tace maka xata shigo nan ne?" Rike kansa yayi ya kasa bata amsa, ita dai sai
kallonsa take, can tace "Aliyu" ya dago da kyar ya kalleta tace "Ina Jiddar tace maka xata je?" Cike da
confusion yace "Mama daga wajen aiki nake yanxu haka... I have to drive all the way from Abuja after
piloting d whole day..." Rasa ma takamaiman abinda xai ce mata yayi, sai kuma ya dafe kansa yace "Ban
san inda ta je ba, ban san me ya faru ba, i called home duk ance bata je can ba, bata da wajen xuwa kuma
da ya wuce can..." Mikewa yayi ganin he is just sounding foolish, ba abinda ya ke fada da yake making
sense, bata lkci kawai yake karawa gashi dare yayi, to shi a ina xai ga Jiddah? Ina Jiddah ta je? He felt like
he is going to collapse, lamarin yayi ma xuciyarsa nauyi, ya rasa exactly tunanin inda Jiddah xata je da xai
yi, is this really happening, gaba daya ya ma mance batun Aneesah ma bai ganta a gida ba, gathering much
courage yace "Sai da safe Mama, dama na xata nan ta shigo" Juyawa yayi yana jin kafafuwansa sun masa
nauyi ya nufi kofa, tace "Aliyu" ya juyo ya kalleta, tace "Me yasa xaka bar Jiddah da matarka kadai a gida
bayan kasan halin wannan ita matar taka?" Dawowa yayi da sauri xuciyarsa na bugawa, tace "Why Aliyu?"
Ya marairaice mata yace "Mama ta shigo nan ne? Wllh ban san abinda ya faru ba, daga Abuja nake few
minutes ago ban tadda kowa a gidan ba" Hajiya Fatima tace "Tashin hankali Abokiyar xamanta ta nemeta
da shi shine ya shigo nan, don ko takalmi balle mayafi babu a jikinta ta shigo gidan nan" Abuturrab ya buda
ido sosai yana kallonta so speechless, Ta girgixa kai tace "Sakacin yayi yawa Aliyu, ganganci ne barinsu su
biyu kadai a gidan nan, a da ni banyi niyyar nuna maka Jiddah tana nan ba sbda naga kamar u are not
ready to take any action, it's not as if i am trying to intrude into ur privacy amma naga bai kamata in xuba
ido ba a matsayina na babba, ba wai ina maku shisshigi bane amma lamarin abun dubawa ne kada
wataran ayi kisan kai" Ya duka gabanta without knowing he did so yace "Don Allah yanxu tana cikin gidan
nan Mama?" Hajiya Fatima tace "Tana nan" Mikewa tayi ya bi ta da kallo har ta wuce ciki, ya sauke wani
irin ajiyar xuciya ya rufe idonsa sai dai har yanxu xuciyarsa bai dawo dai dai ba, bayan kusan minti hudu
Hajiya Fatima ta shigo parlon tare da Jiddah dake biye da ita a baya, Jiddah na hada ido da Abuturrab dake
kallonta ko kiftawa babu ta sunkuyar da kai fuskarta babu walwala, Sounding so grateful yace "Nagode
Mama Allah ya kara girma..." Tace "Aa ba ka gode ba, so kake matarka ta kasheta ne ko kuwa kana da wata
manufarka daban na barinsu a gida daya?" Ya marairaice mata yace "Not at all Mama..." Tace "Toh tashi ka
dau matarka ku tafi, xa mu yi magana gobe" Godiya ya dinga yi mata kamar warce tayi masa albishir da
aljanna, infact shi tunda yake bai ta6a yi ma mutum irin godiyan nan da yake mata ba, sai taji ya bata
tausayi kana ganinsa kasan matan nan nasa suna basa tension, Hajiya Fatima tace "Ku tafi Jiddah sai da
safe, xan shigo in sha Allah da safen" Mikewa Abuturrab yayi yana kallon Jiddah da taki yarda ta hada ido
da shi, babu yanda ta iya haka ta bi bayansa tana jin kamar ta fashe da kuka har ranta taji bata son xaman
gidan, duk da yayyafin da aka fara, haka suka fito compound din ya kama hannunta kamar xa a kwace
masa ita suka fita gidan sannan suka shiga nasu, suna shiga parlor ya kulle kofar ya rungumota jikinsa gam,
ya runtse ido da damuwa yace "Me yasa kike bani wahala haka Jiddah, me yasa kike sa min ciwon xuciya?
Kince ban maki komai ba duk xaman mu na farko balle ko ince ramawa kike yanxu, why are u giving me
heart attack jiddah, tell me pls wife, kin ki barin in nutsu in yi aikina, so kike a bani query Jiddah? Do u
want me to lose my job?" Tayi shiru tana jin yanda xuciyarsa ke bugawa, ga kamshinsa da ya cikata, lumshe
ido tayi ita ma xuciyarta na bugawa, ya dago kanta a hankali yace "Me ya faru kika fita gida just like that?
tell me plss" Hawaye ya kawo idonta a hankali tace "Nemana take da fada a ko da yaushe" yace "Me ta
maki? Tell me" Cikin sanyin murya tace "Daxu da safe na sakko xan shiga kitchen shine ta xageni ta xagi
iyayena, kuma har da marina" Ta fashe masa da kuka, lkci daya mood dinsa ya koma na bacin rai karara,
yace "Ta mareki?" Cikin kuka tace "Ehh shine ni kuma ta kwala mata wancan vase din na fita parlon" Ya
rungumeta bai ce komai ba yana tunani iri iri a ransa, hannunta ya kama suka wuce sama, ya tafi
bangarensa ya dau wayarsa ya shiga bedroom dinsa ya dau spare key sannan ya fita, Jiddah dai na tsaye
parlonsa ta bi sa da kallo har ya fita, ta xauna a hankali gefen kujera, bude kofar dakin Aneesah yayi yana
kokarin dialing numberta, har ya katse mata daga ba, ya sake kira yana bin dakin nata da kallo, dagawa aka
yi daga daya bangaren, murya kasa kasa tace "Hello my Captain" Yace "How are you?" Tace "Lafiya lau My
captain, are u missing me this much?" Yace "Ya jikin yanxu?" Tace "Yanxu na sha magunguna na na kwanta
har na fara bacci kiranka ya tasheni" Yace "Ohk kina daki ne?" Tace "Ehh wllh, ina daki a kwance" yace
"Ohk can u go give Jiddah the phone plss?" Tace "Why not my captain, Allah ya sa ta karba din, bari in kai
mata" Shiru yayi bayan wani lkci yaji tana cewa "Assalamualaikum, Jiddah, Jiddah..." Sai kuma tace "Ohh
kofar ma a bude take