Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
sha daya, to shine ya sake fita bayan azahar,
ke a ina kika ji yana asibiti?" Aunty tace "Yanxu tsinanniyar tsohuwar can ta kirani take fada min a kai mata
bargo da pillow" Aneesah tace "Bai fa ce min asibiti xai je ba, bari xan kira Ahmad yanxu" Aunty tace "Ki
kirani idan kin tambayesa" Aneesah tace "Toh" daga haka ta katse wayar, Ahmad ta shiga kira nan kuma ya
gaya mata asibitin da suke, iyakar tashin hankali ta shiga a lokacin, abun har ya kai ga admitting, da sauri ta
kuma kiran Aunty tace "Wllh da gaske ne Aunty har an kwantar da shi wai..." Aunty tace "Wani asibitin
ne?" Aneesah ta gaya mata, Aunty tace "Toh ki biyo mu tafi tare kawai" Aneesah tace "Ai na koma baya
Aunty, mu hadu a asibitin kawai xai fi, sai mu tafi da Aunty Safara'u" Aunty tace "Aa nafi son mu je
dukanmu tare xai fi, xan jira ku a bakin hanya" Aneesah tace "Toh ai shkkn" daga haka ta katse wayar, da
sauri ta wuce sama ta sanar ma Aunty Safara'u, cikin minti goma duk suka shirya suka fito, Safara'u tace
"Wannan dai ba girmanmu bane a ganmu cikin adaidaita sahu kamar wasu en iska, katon gida haka ace
mota daya ne kacal kamar rai, duk kudinsa shi baxai siya maki karamar mota ki dinga tukawa kije duk inda
xa ki ba" Aneesah ta hade rai tace "Toh wai aunty duka duka yaushe na koyi motar, ni dai mu daga kafa
kinga kafin a fita bakin titin nan da tafiya, wllh duk hankalina ya tashi" Safara'u ta ta6e baki tana ci gaba da
bin ta. Ana kiran la'asar su Aneesah suka shiga asibitin, nurses suka masu kwatancen ward din sannan suka
wuce sama, Aneesah ce ta bude kofar ward din, Umma na dakin har lkcn da Hajja dake xaune kan kujera
daga kusa da Abuturrab dake ta bacci har lkcn, Ramlah ma na ward din a xaune kan daya daga kujeru
hudun da aka kawo, Daga sama har kasa Hajja ta dinga kallon Aneesah da ta iso gun gadon da sauri cike da
damuwa tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Hajja ta kare gadon ta bubbuda hannunta tace "Ance kada
wanda ya matso kusa da shi inji likitocin...." Tsayawa Aneesah tayi tana kallonta irin kallon rainin wayo,
Hajja ta kalli su Safara'u da suka yi cirko cirko bakin kofa tace "Oh oh Allah, likitocin fa sunce mutum uku
kadai ke iya shigowa dakin saboda yanayinsa, sunce kuma a gaskiya idan ba mu bi doka ba xa su kora mu
tunda ba Asibitin ubanmu bane, da a Masar ne ma yaushe xa su bar mutane ukun? Ai sai ni kadai ko
Ramlah uwarsa, amma kun wani kwaso jiki kun shigo daki me window biyu kacal ta ina xa a ja numfashi
saboda Allah??" Juyawa Safara'u tayi ta fice daga ward din, Aunty dai na tsaye sai kallon kasa kasa take ma
Hajja, Hajja tace "In kuma ni in fita ne to sai in fita in bar dakin, ai likitocin ne suka bani umarnin in xauna
kusa da shi" Aunty ta d'an kalli Umma tace "Sannu" Umma tace "Au ashe kece" Ko kallonta Aunty bata
sake yi ba ta juya xata fita, Hajja tace "Ina bargo da pillon da nace maki Hafsah?" Tuni Aunty ta fice daga
ward din without answering her, Hajja ta kalli Umma tace "Kinga er iska ko?? To ni nasan me ta shigo da shi
da xan bar ta ta matso kusa da jikana, Aa wllh ba ruwana kowa yayi takansa, ke Ramlah karama fita ki kira
mijinki ku koma gida ki taho min da pillow da Bargo daga gidanki" Ramlah tace "Toh" sannan ta fita daga
ward din, ita dai Aneesah na tsaye Hajja taki barin ta karasa kusa da Abuturrab kuma ta ki fita, Hajja ta kalli
Aneesah tace "Toh kinga ai mun cika uku cif cif a dakin yanxu, ga kujera can ki tafi ki xauna sunce kada a xo
kusa da shi saboda halin rayuwa" Aneesah ta kalli Umma ta gefen ido kamar ana tilastata tace "Ina yini?" A
dakile Umma tace "Lafiya" Juyawa Aneesah tayi ta nufi kofa ta fita, a reception ta tarar da Aunty da
Safara'u suna xagin Hajja, Safara'u na hangota ta mike tace "Bani makullin gida inyi wucewata, ba dani xa a
ci gaba a haka ba, idan xuciya ta debeni xan iya dura ma Tsohuwar can Ashar babu ruwana, ba kuma
dangin iya balle na baba, ina dalili mata ta tijarani haka" Aneesah tace "Haba Aunty, mijina ne fa ba lafiya,
saboda me zaki ce xaki tafi kamar saboda ita kika xo" Safara'u tace "Wllh baxan xauna ba ni ba er iska bace,
toh lafiyar ni xan basa idan na tsaya kina ganin walakancin da aka mana yanxu, ke kanki gashi kin fito ward
din" Aneesah tace "Toh wai Aunty sai ki biye mayyar can? Mayya ce fa, ni dai kiyi hakuri ki tsaya, duk xan
rama maki wllh tllh" Safara'u tace "Anjima dai xan dawo amma baxan zauna yanxu ba tana nan" Aunty da
duk hankalinta ya ki kwanciya don tana tsoron kada a tada batun auren Abuturrab a asibitin su Aneesah su
ji don har sannan basu da labari, tace "Aneesah kawai ku tafi tunda tijararriyar can na nan, ga kuma
wancan munafukar Ramlan a xaune, kinga sunyi bake bake a dakin suna nuna isa da iko gwara kawai mu
tafi" Aneesah tayi wani shewa tace "Wllh wllh ba inda xanje ina nan wajen mijina, yanxu a cikinsu akwai
warce xata iya masa wanka ko wani abun banda ni da nake matarsa?? Ai duk sai dai su gama kame
kamensu a nan amma nice nan dolensa kuma babu inda xanje al-qur'an, xa su sha mamaki yau" Aunty ta
hadiye abu da kyar tace "Toh kuwa xaki sha walakanci iri iri wllh" Aneesah tace "Sai kace baki san ni ba
Aunty, wllh babu xancen respect tsakanina da su, xa su ga rashin kunya ganin idonsu" Daga haka ta bude
jakarta ta ciro makulli ta ajiye ma Safara'u a gefenta ta wuce sama. Aneesah na komawa ward din ko kallon
Hajja bata yi ba ta tafi gefen gadon ta xauna tana kallon Abuturrab dake bacci tana gyara masa kwanciya
cike da kissa, buda baki Hajja tayi tana kallonta, sai tayi tagumi tace "Yau naga jaraba, ke matar nan bance
maki ance kada warce ta je kusa da shi ba ko wata cutar kike son goga masa mu shiga uku?" Aneesah ta
kalleta tace "Cuta kuma Hajja, mutumin da muke kwana gida daya, daki daya kan gado daya, wuri daya
kice xan goga masa cuta?" Hajja ta mike tace "Toh ai nan ba gidanku bane shegiya, xo ki fita kar in tara
maki likitoci yanxu, ko kazantar ki bai isa ya kwantar min da jika ba er banxa kawai" Tun Umma na danne
dariyarta tana dakewa har ta kasa, ta mike ta fita daga ward din, Aneesah ta sake baki tana kallon Hajja ko
kiftawa babu, Hajja tace "Mata kawai duk kin cika turare a jiki xaki xo ki kawo ma mutane raini a asibiti
shashasha kawai" Aneesah tace "Shegiya fa kika ce min?" Hajja na nunata da yatsa tace "Ance maki
shegiyar ko ramawa xa ki yi?" Aneesah ta bar wajen fuuu ta koma can jikin window a fusace tace "Wllh ni
ba shegiya bace, da uwata da ubana kam" Hajja ta ja kujera ta xauna kusa da gadon tace "Oho dai, ni dai
ba kin matsa daga kusa da shi ba" Aneesah kallonta kawai take xuciyarta na tafarfasa, Bude ward din aka yi
Ummi ta shigo tare da Umma da Nafisah, kallo daya Hajja ta ma Ummi ta dauke kai, Ummi ta karaso ciki ta
ajiye basket din abincin hannunta, with respect ta kalli Hajja tace "Ina wuni Hajja?" Hajja tace "In dai kika
kashe Aliyu nima ki kasheni kawai Hauwa" sai kuma ta fashe da kuka tace "Mata ki haifi yaro ki fi kowa k'in
sa?" Umma tace "Ya xa ayi ta k'i sa Hajja, ranan da ku ka yi masa caaa a kai so kike ta bude baki ta ce wani
abun kice tana goyon bayansa, ko kice ta maki rashin da'a?" Hajja ta mike tace "Aa wllh baxan ce ba ai
nasan xafin Haihuwa, idan nice ita ai sai inda karfina ya kare, kaca kaca xan ma duk wanda yace xai sa d'a
na a bakin duniya, amma sai tayi shiru kamar jira take a walakanta Aliyun, to wllh Allah xai maku hisabi da
shi ba ruwana" Ummi dai bata ce komai ba, Hajja ta fyace majina ta koma ta xauna, Aneesah ta kalli Ummi
bbu yabo bbu fallasa tace "Sannu da xuwa" Ummi tace "Sannu" Umma ta kawo ma Ummi kujera ta xauna
tana kallon Hajja tace "Toh ayi hakuri Hajja, xa a gyara in sha Allah" Hajja tace "Aa gwara ki gyara kam,
yanxu ni da nake dolensa ba gani xaune a gefensa ba tun daxu, kema banda kina uwarsa baxan bari ki xo
kusa da shi ba ma wllh, likitocin sun ce yana bukatar hutu sosai" Ba a dade ba Ramlah ta shigo da bargon
da pillow hade da tabarma, Hajja tace "Yauwa er albarka, ajiye min can gefe da daddare a shimfida min
inyi kwanciyata" Ramlah ta tafi ta ajiye inda Hajja tace.... Tun lokacin da Hajja ke ma Aneesah ihu
Abuturrab ya farka don har tsakiyar kansa dake masa ciwo sosai yake jin surutun Hajja, amma ya ki bude
ido ko nuna ya tashi, jin muryan Umminsa yanxu yasa shi bude idonsa ya mike xaune... Hajja tace
"Alhamdulillah sannu Aliyu, ya jikin yanxu, amma inji dai ba surutunsu ya tashe ka ba duk su fita kawai,
don ance a bari ka huta" Ya girgixa mata kai kawai, ya kalli Ummi a hankali yace "Ina wuni" Ummi tace
"Lafiya lau, how are u feeling now?" Yace "Alhmdlh" Aneesah dai na tsaye sai kallonsa take tana tsoron
xuwa kusa da shi Hajja ta koreta kuma, Kallonta yayi ai suna hada ido bata san lkcn da ta nufesa da sauri ba
tace "How are u feeling now?" Hajja ta dinga mata wani kallo daga sama har kasa tana yamutse fuska,
Umma ta tafi gun abincin da Ummi ta kawo ta dau plate ta shiga xuba masa har ta gama Hajja ta amshe ta
kai masa tace "Ka daure ka ci ko kadan ne ka ji Aliyu?" Ya dinga kallon white rice din kafin yace "Ba shi nake
so ba" Hajja tace "Me kake so Aliyu, fada min ko meye shi kaji" Ya d'an yi shiru, Hajja ta shiga lallabasa tace
"Daure ka fada ko meye shi kaji Aliyu" Yace "Awara xan ci" Daga sama har kasa Umma take kallonsa,
Aneesah tace "Toh Baby bari in koma gida yanxu inyi, i know it wont take long" Da sauri Hajja ta kalleta
tace "Ba fa indomie yace xai ci ba Nanisa, Awara yace..." Umma tace "Xan kira can gida xa a soya yanxu a
kawo, muna da shi ajiye a freezer dama" Hajja tace "Yauwa to maza kirasu, ko Jiddah ce sai a sa tayi tunda
naga ta iya duk abun gargajiyan nan, dubi dambun da tayi ranan nan me shegen dadi wllh, sannan uwa uba
tsafta, a tsaftace xata yi masa ta kawo tunda shi sarkin son tsafta ne" Aneesah da lokaci da mood dinta ya
canxa ta hade rai tace "Nima ina da shi a freezer din, kuma cikin minti kadan xanyi in kawo..." Hajja ta kalli
Umma tace "Yi min kiran Jiddah" Umma ta shiga dialing number Maimoon tana dagawa tace "Ba Jiddah
wayar" Maimoon na ba Jiddah Umma tace "Kina ji na Jiddah" Jiddah tace "Ina ji Umma" Umma tace "Ku
soya awara yanxu kuyi sauce xa ku kawo asibiti, xan kira driver ya je ya dauko ku" Jiddah tace "Toh Umma"
Umma ta katse wayar, Hajja tace "Allah ya maki albarka Ramlah, yanda kika tsaya kan Aliyu kamar d'an da
kika haifa Allah ya tsaya maki haka ke ma, uwarsa kuma Allah ya shiryeta..." Ummi ta mike tace "Toh Allah
ya kara lafiya, Xan dawo anjima Hajja" Hajja tace "Je ki, tunda dai ga mu, idan da kara ma bai kamata ki
biyo mu rigirigi asibiti ba sai kace ba d'an ki na fari ba, ai kara ma wani abu ne, duk sai naji kunya da na
ganki wllh" Ummi dai bata ce komai ba ta nufi kofa ta fita Ramlah ta bi bayanta don Ahmad na jiranta tun
daxu a waje, Umma dai ta tabe baki tana girgixa kai tana jinjina lamarin Hajja. Aneesah kam abun duniya
ya isheta gashi har ga Allah bata iya awaran ba, to ko dai ta koma gida tayi order kawai yanxu yanxu, kallon
agogo dake nuna shidda saura tayi, sai kuma ta nufi kofa ta fice daga ward din, bayan ta sauka downstairs
ta shiga kiran Chef Salma, tana dagawa tace "Salma don Allah ina xan samu Awara yanxun nan na order...."
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk
wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun
mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda
kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm
yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga
glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulu mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd
guess what😍munyi upgrading kayanmu gbdy domin jindadinku🥰bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku
domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida
💯 Natural/organic
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki komai da komai
Akwai soap 3k
Student package 7k
Beauty kit 11k
Bridal kit 18k
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏
Ko gida Aneesah bata koma ba bayan ta amshi awarar a bakin hanya ta hau adaidaita ta koma asibitin,
tana isa bayan ta sauka tana kokarin ba mai adaidaitan kudi sai ga Jiddah tare da Maimoon driver ya
ajiyesu sun sauka motar, Hijab har kasa ne jikin Jiddah, Aneesah na ganinta bata jira amsan canjinta ba ta
shige gate din asibitin kamar ana tunkudata ciki, Maimoon ta kalli Jiddah da sauri, ta rike ha6a tace "Saurin
me wancan matar kuma take daga ganinmu? Ko dai sleepless night din ne tun yanxu" Jiddah dai bata ce
komai ba, suka shiga gate din asibitin tare. Suna kallon Aneesah na ta xabga uban sauri, Maimoon bata san
lkcn da ta kyalkyale da dariya ba tana tafe hannu tace "Ke wllh kamar tsoron mu take, saurin da take fa
hade yake da guduwa" Aneesah na shiga ward din bata bi ta kan kowa ba tana kallon Aliyu dake kwance ta
nufesa da sauri tace "Baby gashi nan har na yi" Tana fadin haka ta tafi gun basket din da Ummi ta kawo ta
duka ta dau plate da sauri tayi backing dinsu don kar su ga tambarin inda tayi order din awaran ta juyesa a
plate har da katon part na naman kaza ta sa spoon snn ta mike tana murmushi xata nufi gadon da
Abuturrab yake Hajja tayi saurin mikewa ta dakatar da ita tace "Aa Nanisa... Ba xancen baby gashi har nayi
bane, bani in ga irin awaran, wa xai ci abinda xae cucesa?" Aunty da shigowarta kenan kafin Aneesah ita
ma da d'an coolern farfesunta ta dinga hararan Hajja kamar ta shaketa, Dai dai nan Jiddah suka shigo ward
din da Maimoon, kallonta Abuturrab ya dinga yi without blinking, ita ko tun da suka hada ido sau daya ta
sunkuyar da kanta, ta karasa gun Hajja ta durkusa ta gaisheta, Hajja tace "Tashi tashi, maza xuba masa ya ci
tun daxu yake jira" Jiddah ta gaida Umma, sannan Aunty da ta ki amsawa, bayan nan ta mike, daga sama
har kasa Aneesah dake rike da plate din awaranta take kallon Jiddah haka nan kawai taji gabanta na
bugawa, Jiddah ta dau plate din da suka xo da shi ta bude warmer din awaran, Aneesah na ganin haka ta
karasa gadon da Abuturrab yake tana mika masa awaran fuskar nan nata a tamke tace "Gashi nan na maka
awaran Baby, eat it now" Ya amshi plate din ya ajiye gefensa yace "Thank you" Hajja ta bude hannu tace
"Atoh dai" Mikewa Jiddah tayi tana mika ma Hajja awaran da ta xuba Hajja tace "Ya kike abu sanyi sanyi
kamar kina shakkan wani, ki tafi kanki tsaye ki mika masa awaran tun daxu yake ta jira wllh, ko ke baki ga
ya gantalar da wanda ta mika masa a gefe ba tunda ya san me xai ci ma kansa, atoh wa xai ci gaibu, maxa
karasa ki basa, ae shi sa ake son duk runtsi ka xamo mai tsafta, Maimoon fita ki amso masa ruwan gora me
sanyi, naga wa ennan duk ba sanyi...." Maimoon bata so ba, amma haka ta dau kudi da sauri ta fita taje ta
siyo ruwan, Umma dai sai kallon ikon Allah take a cikin ward din nan yau, Aunty kuwa lkci daya ta ji xufa na
keto mata daga inda take tsaye, a hankali Jiddah ta daga kai ta kalli Abuturrab suka hada ido cause bin ta
kawai yake da kallo as if his life depends on that, kawai ta sauke idonta ta nufesa ta tsaya opposite side din
da Aneesah ke tsaye ta kafeta da ido xuciyarta na ci gaba da bugawa babu sassauci, Jiddah tayi kasa da
murya tana mika masa awaran tace "Ya jikin?" And he felt he was melting, kallon cikin idonta kawai yake,
wanda hakan ya sa ta dawo uncomfortable ta sauke idonta da sauri tace "Is this enough??" basu ankara ba
sai gani suka yi Aneesah ta kai hannu ta kwa6ar da plate din hannun Jiddah da karfi, har sae da awaran ya
kife gaba dayansa a kasa, Jiddah ta ja baya da sauri tana kallon Aneesah gabanta na faduwa, tsalle Hajja
tayi ta mike tana rafka uban salati ta kankance ido, Abuturrab yayi mata wani tsawa bayan ya fixge drip din
hannunsa yace "Are you stupid Aneesah?? Are u mad???" Cikin daga murya Aneesah tace "Yes i am Aliyu,
a gabana wata banxa yar talakawa xata wani kawo maka abincin ka ci bayan ni ma na kawo maka, ita a su
wa? ko uban me ka hada da ita da xata wani xubo maka abinci ta taho simi simi kamar munafuka tana
kallonka kallon cikin ido tana mika maka awara bata ji tsoron matarka na kusa da kai ba???" Ae tuni Aunty
ta nufi Aneesah tana kokarin jan ta su fice daga ward din tana tutturjewa lkci daya kuma tana kunduma