Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
xata, kawai tsorata tayi yasa ta buya, yanxu idan
na dage na kwalo mata kira xata fito wllh, kawai dai a gama da xancen yaron nan iliya tukun" Mai Anguwa
ya girgixa kai yace "Toh yanxu xa a min kiran shi mahaifin Iliyan da shi kansa iliyan" Hansai ta xaro ido a
mugun tsorace, Mai anguwan yace "Amma ke kika haifi yarinyar?" Hansai tace "Ehh 'ya ta ce" Yace "Yanxu
ki rasa wanda xaki yarda ya nemi auren yar ki sai wannan takadirin Iliya? Waye bai san halinsa ba a garin
nan, garin yaya har kika amince ya auri yar ki, duk uwa ta gari ai baxata so ma yar ta wannan yaro ba"
Hansai ta fara matsar kwalla tace "Wallahi mahaifinta ya rasu, yarinyar nema take ta gagareni, baxan boye
maka ba wllh bin maxa take, to shi nan rufa mana asiri yayi xai aureta, bayan haka kuma da tsohon bashi
tsakaninsa da mahaifinta ina jin, kuma ni bani da halin biya gaskiya shi sa kawai na sadaukar ai ba a cire
ran shiryuwar d'an mutum, ni ban cire ran shi ma xai shiryu ba sannan ai gwara shi kiriniya kawai yake yi,
ita fa bin maxa take wllh, duk iya bakin kokarina kan yarinyar nan ya ci tura, tsoro nake kada ta jajibo min
abun kunya shi sa da ya billo da xancen aurenta bani da yanda xan yi na hakura, don kowa tsoronta yake
sbda halinta, sannan yana da xuciya yaron, me yi ne shi wllh" Sake baki mai Anguwa yyi yana kallonta,
Abuturrab ma kallonta yake ko kiftawa babu with shock, ta sharce majina tace "Amma tunda abu ya xo da
haka in da wani shawara da taimakon da xaka mana kawai kayi mai anguwa mun baka wuka da nama don
a gaskiya muna cikin hatsari" Ya sauke wani ajiyar xuciya yace "Ikon Allah, to yanxu dai xan sa ayi kiran
mahaifin yaron da shi kansa yaron sai a san abun yi, idan naga sulhun baxai yiwu ba sai kawai ku tafi wajen
yan sanda su ma idan abun baxai sulhuntu a gunsu ba kotu xa su tura ku, amma abu me sauki a mayar ma
yaron nan kudadensa ita kuma yarinya a nema mata mai hankali wanda yaji xai iya ya aureta...." Hansai ta
fashe da kuka tace "Duk ba sai an kai ga haka ba wllh, Allah xai dubemu maganar ta mutu cikin ruwan
sanyi, banda ta lalata rayuwarta idonta ya bude da maxa me xai sa in yi sha'awar yi mata aure bayan
abinda xan kai ta da shi ma bani da shi, duka duka shekarta fa sha bakwai, har nawa take xan dage sai na
mata aure banda ta lalace" Kawu Jibril dai ba baki sai idanuwa, sauran dattijan dake xaune gun sai kallon
Hansai suke wasun su na tirr da ita a xuciya, don ko min lalacewar naka baxa hadasa da lalatattce ba da
yayi fice a gari, Abuturrab ya d'an yi murmushi shi dai bai ce komai ba yana kara jinjina halin Hansai a
ransa. Sai da suka yi la'asar Mahaifin iliya ya iso, sai ga iliya ma da abokansa yan daba irinsa sun iso wajen,
Mai anguwa ya dakatar da abokan dake kokarin xaunawa kan takalmansu don tabarman ya cika yace "Ku yi
hakuri yan samari kuyi jiransa ga benchi can" Suna gunguni suka bar wajen, Abuturrab ya kafe iliya da ido,
ba lebbensa ba hatta fuskarsa ya dafe saboda xuke xuke.....
07087865788✍🏻
💖💖 *Jiddatul Khair*💖💖
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
11....
Mai Anguwa na kallon Iliya dake maxurai yace "Kai yanxu Iliyasu baka da masaniyar inda wannan yarinyar
take?" cikin murya irin ta 'yan da6a yana nuna Hansai yace "Wllh wancan munafukar matar tasan inda
take, kuma ni dama daga ita har wancan mutumin banxan na basu kwana daya su fito min da ita, matata
ce fa, abinda har na bada sadaki me ya rage? Akuyar baabata fa na dauka na kai kasuwa na siyar na kai ma
wancan mutumi da wasu kattin banxa a wajen kudin sadakina...." Mahaifin Iliya dai ba baki sai idanuwa,
don kamar ma tsoronsa yake, Mai Anguwa yace "Toh yanxu idan ba a ga yarinyar nan har bayan kwana
dayan da ka bada ba ya kake son ayi iliyasu?" Yace "Hansatu ta biyani duk hatsin da na dinga kawo mata a
maimakon na kai ma baabata, ba hatsi kadai ba, lissafi xa mu yi tiryan tiryan ta biyani duk abinda na kashe
sannan ta bani kudin sadakina dubu sha uku da kudin gaisuwa da sa rana da na kai, idan ba haka ba to wllh
xan yi ta'asa, ai ba yau muka saba xaman kurkuku ba, banda yanxu da na fara gwangwan daga garin nan
xuwa legas ai mu bama wata uku bamu leka gidan yan sanda ba daga nan mu garzaya kotu sannan gidan
kaso, ko da mune da gaskiya ko mu ne bamu da gaskiya wannan ba sabon abu bane" Mai Anguwa ya kalli
Hansai dake xare ido duk hankalinta a tashe sai xufa take yace "To ke kin ji Hansatu, lissafi yace xa ayi" kasa
cewa komai tayi xufa sai karyo mata yake ta ko ina, yo ba gwara ya kasheta ba da ta ta6a kudin da
Abuturrab ya bata, tabbb.... Mai Anguwa yace "Kai xuwa yaushe xa a baka kudin naka Iliyasu?" Ya gyara
xama yace "Ae kafata kafar kudina, baxan bar wajen nan babu su ba, idan ko ba haka ba wllh wllh xan yi
aika aika" Mai Anguwa ya kalli Hansai da jikinta ya dau rawa ta kasa cewa komai, Abuturrab ya sauke
boyayyen ajiyar xuciya yana kallon iliyan yace "Nawa ne gaba daya kudin naka?" Yace "Al-qur'an kudi na ya
kusa dubu dari da wani abu, abinda duk xuwana legas sai na kawo mata garin alabo da gawayi ga hatsi da
nake siya mata kwana biyu kwana uku... Sannan ga sadakina dubu sha uku na tinkiyar babaata, ga dubu
biyar kudin gaisuwa da sa rana" Calmly Abuturrab yace "Kana da account?" Iliya yace "Aa amma abokina
Kallamu na da shi, gaya can a xaune" Abuturrab yace "To ka kirasa ya bada account din" Iliya ya kwalo ma
abokin nasa kallamu kira, Kallamu na karasowa Abuturrab yace "Account number dinka xaka bada" sai da
ya dubo a waya sannan ya nuna ma Abuturrab, cikin few minutes Abuturrab yayi masa transfer din dubu
dari da ashirin, sannan ya kalli Kallamu yace "Xa a maka alert na dubu dari da ashirin yanxu" Wani kara
wayar yayi alamar shigowar alert din, Abuturrab ya amshi wayar ya duba sannan ya mika ma mai anguwa
da sauran mutanen wajen duk suka ga dubu dari da ashirin, Hansai ta fashe da kuka sosai, Kawu Jibril kuwa
Hamdala ya dinga yi a ransa yana sauke ajiyar xuciya, Hansai na kallon Abuturrab cikin kuka tace "Allah ya
saka da alkhairi Alhaji, ka min taimakon da babu wanda ya ta6a min wllh a duniyar nan, nagode nagode,
Allah ya kara maka budi da dukiya me yawa, wayyoo wani irin godiya kuma xan maka Alhaji" Abuturrab ya
ki bata amsa dai a fili, Iliya ya mike yace "Toh amma fa duk ranan da jiddah ta bayyana wllh sai na aureta
don na kwallafa rai, an kuma sa min ran ne, wllh wllh sai na aureta ko kuma in dauketa kawai in wuce legas
in je a daura mana auren a can, so nawa aka yi hakan" Sake baki duk mutanen wajen suka yi suna kallonsa,
ya kakkabe wandonsa ya kara gaba yana cewa "Sai in bani ne Iliya d'an me karfi ba" abokansa duk suka
taso suka maya masa baya suna hailing dinsa, Mahaifinsa Malam Kabiru ya sauke ajiyar xuciya cikin sanyin
murya yace "Abu me sauki da xa a samu wani ya auri yarinyar nan kawai, idan kuwa ba haka ba wllh xai
aika abinda ya fada, kwakwalwarsa ya ta6u da dadewa mu kuma bamu da halin kai sa ko ina a dubasa, har
cewa aka yi mu kai sa dawanau a kano to ina kudin?" Wani mutumi a wajen yace "Alhmdlh abinda xan
fada kenan ka riga ni Malam kabiru, gwara kawai a aura mata wani tunda uwar ma tace ba ji take ba
yarinyar, kun ga tana dawowa sai a kai ta dakinta kawai..." Abuturrab yace "Akwai wani yaro na, ina son
nema masa aurenta yanxu" Kallonsa duk suka yi, Mai Anguwa yace "Toh in dai kasan halinsa ina ga wannan
ba matsala bace amma kafin nan ya kamata ka gabatar mana da kanka..." Abuturrab ya shafa kansa a
hankali yace "Ni sunana Aliyu Usman Umar... An haifeni nan cikin garin kaduna, ni matukin jirgin sama ne"
Sake baki duk suka yi suna kallonsa kamar ranan suka ta6a ganin me tukin jirgin sama, yace "Gidan iyayena
na nan Malali..." Mai Anguwa yace "Maa sha Allah Aliyu, to amma a ina kasan ita wannan yarinya da ake
magana a kai?" Hansai ta amshe tace "Wllh daga siyan awara muka sa6a da shi, customer na ne shi da
dadewa, da motarsa yake xuwa yyi parking ya siya har na dubu biyar dubu goma yana siya, toh shine jin
rasuwar mai gidana sai ya kawo mana kudi dubi hamsin dubu dari, ta haka muka saba muna mutunci sosai
da shi" Mai Anguwa yace "Ikon Allah" Abuturrab dai bai ce komai ba, Mai Anguwa yace "Toh amma shi
wannan yaron da kake son hada yarinyar da shi wanene, sannan a ina yake?" Abuturrab yace "A kano yake,
yana aikace aikace ne a airport din kano..." Hansai tace "Shi ma jirgin yake tukawa?" Ya girgixa kai yace
"Aa..." Wani datijo dake xaune wajen da baxai wuce shekara sittin da takwas ba yayi gyaran murya yana
taunan goransa yace "Amma fa wata kusan ya fi wata kusan nake ji ai... Tunda haka ne ni yanxu xan bada
sadaki sai a daura min aure da ita wannan yarinyar...." Da mamaki Abuturrab ke kallonsa, can ya girgixa kai
yace "Haba Baba ai addininmu ma bai ce haka ba, da taxara sosai tsakaninku da yarinyar nan...." Dattijon
ya hade rai ya katse sa yace "Toh kai idan taimako kake son yi ka aureta mana kai da babu taxara me yawa
tsakanin ku, shi fa wannan yaron da kake son hadata da shi nasan ba kowa bane d'an goge gogen iyapot
ne, ni kuwa kowa yasan babu rashin ci babu rashin sha a gidana, matana uku ko wacce kuma tana da yara
shidda shidda, shi me anguwan ai yasan wanene ni, auren yarinyar nan da xan yi tamkar jihadi xanyi don
ance bin maza take" Kallonsa kawai Abuturrab ke yi with disgust, Dattijon ya ja tsaki yana ci gaba da
taunan goronsa da jajayen hakoransa yace "Idan tsakani da Allah ne kai ka aureta mana yaro xaka wani
kawo ma mutane fi'ili a nan, kaga mai anguwa a yanke min sadaki yanxu in bada a wuce wajen dama ina
da niyyar auren kwanan nan" Yana fadin haka ya fiddo yan dari biyar biyar a aljihunsa, lokaci daya tunanin
Abuturrab ya kwance, Hansai ganin 'yan dari biyar biyar tana d'an kame kame tace "Ai wllh tamkar
taimako xaka yi Alhaji, wannan babban taimako ne, ni kaina da na haifeta bana shaidarta, kawai dai Allah
ya shirya mana xuri'a" Alhajin ya murmusa yace "Babu komai ai tamkar jihadi xan yi, Ni mai anguwa ne
waliyi na, ita kuma sai a samu wani...." Abuturrab ya rufe ido ya bude, yaji kansa ya fara juya masa ya dinga
kallon tsohon nan da ya fara kirga kudin da ya ciro, rasa tunanin da xai yi yayi, he was totally lost, Hansai
dake ta kallon kudin hannun tsohon tace "Kawai a daura tunda ga sadakin a kusa" Jibril yace "Wannan
taimako ne me girma xaka yi Alhaji, Allah ya saka da alkhairi, tana dawowa daga gantalin da ta tafi sai a
wanketa a kai maka gida kawai" Abuturrab ya kalli mai unguwa after gathering much courage yace "Ni xan
aureta, sai ka xama waliyi na" Ba Hansai ba kowa na wajen sai da yayi mamaki, mai Anguwa wanda da
alama dama bai yi na'am da daurin auren da wannan tsoho me suna Alhaji Saleh ba yace "Toh Madallah
Aliyu" Tsohon ya d'an ja tsaki ya mayar da kudinsa aljihu, A nan take kuma aka daura auren Abuturrab da
Jiddah a kan sadaki dubu arba'in, su kenan kudin jikinsa da ya ciro daxu bayan ya siya ma Umma drugs,
Xaune kawai Abuturrab yake a wajen amma gaba daya he is absentminded and lost ga wani sanyi da yaji
yana shigarsa kamar xai yi xaxxabi, har aka gama komai aka raba dabino da alawan da aka siya a nan cikin
layi, Hansai dai ta kasa gane ko murna xata yi ko akasin haka, Ya xa ayi babban mutum kamar wannan gashi
har yace jirgin da bata ta6a gani ba duk tsawon rayuwarta yake tukawa ace wai ya auri Jiddah maimakon
Bibalo, tunanin hakan yasa taji wani bakin ciki ya tokareta a kirji, lkci daya hankalinta ya tashi sosai ba
kadan ba ta dinga xufa daga inda take xaune, yanda take xufa haka Abuturrab ke xufan shi ma, tunda yake
bai ta6a shiga rudani da confusion lkci guda irin wannan ba, wait!!! what did he just do now??? What have
he done to his life?? A cikin lkci ba me tsawo ba aka gama komai, sama sama ya dinga jin albarkan da
dattijan wajen ke sa masa na cewar ya rufa ma jiddah asiri duk da ga abinda aka ce tana yi amma hakan bai
sa ya kyamaceta ba gashi ya taimaketa ya aureta domin nisantata daga cutarwan iliya, Abuturrab ya mika
ma mutumin karshe hannu sannan ya mike a hankali ya nufi motarsa walking slowly kamar mara lafiya,
yana shiga motarsa ya tada motar ya kashe Ac don sanyi yake ji sosai ya fara driving ya bar layin, ikon Allah
ne kawai ya kai sa gida lafiya cause blurry ya dinga gani ga kansa dake juya masa ya dinga ganin komai
double, ko parking din kirki bai iya yayi ma motar ba ya sauka ba tare da ya rufe ba ya shiga ciki mai gadi ya
bi sa da kallo, direct dakinsa ya nufa ba tare da ya kalli kowa na parlon ba, duk suka bi sa da kallo, Aunty ta
kalli Ummi, Ummi dai bata ce komai ba, Aunty ta mike ta bi bayansa da sauri, cikin bargo ta gansa ya
lullube har kansa, da mamaki tace "Are you okay Aliyu???" Bai iya ya bata amsa ba, ta sauke bargon a
hankali ganin he is shivering so much, da mamaki tace "Baka jin dadi ne?" Ya gyada mata kai kawai, tace
"Subhanallah, let me switch off the Ac"
Nan na kawo karshen free pages na *Jiddatul Khair* in sha Allah, and the paid book is 500 Via
👇🏻
3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah.....
And u show ur evidence of payment via my WhatsApp Number 👉🏻 07087865788.....
Plss just WhatsApp ban fiye son phone call ba, and i am begging you don't come to my DM without any
concrete reason, it's tiring wllh....😓😰 just come, patronize, i save ur number, and i add u to my groups...
Shikenan
Thanks and i love you all as u patronize.💖
💖💖 *Jiddatul Khair**💖💖
Kashe Ac din dakin Aunty tayi ta sauke curtains ta dawo ta xauna kusa da shi tace "Sannu, ko dai a kira Dr?
amma daga ina kake haka?" Girgixa mata kai kawai yayi don bai jin ma xai iya magana, ta mike ta fita don
daukan wayarta ta kira Dr din, Tana cikin dialing number likitan ta kalli Ummi tace "Baya jin dadi ne wllh"
Ummi tace "Ikon Allah, to Allah ya sauwake" Aunty na gama kiran likitan ta koma daki..... Abu kamar wasa
Abuturrab har da karin ruwa, he was so weak and sick, sae bayan isha family Dr din nasu ya bar gidan.
Karfe goma da yan mintuna wayar Abuturrab dake gaban mirror din dakin Aunty ya fara ring Aunty ta dau
wayar ganin Ahmad ne ta kyabe baki ta dauka don tun daxu yake kira, bayan ya gaisheta yace "Ya tashi
Aunty?" A takaice tace "Aa..... ko minti sha biyar ban yi da fitowa daga dakin ba" Ahmad ya d'an yi shiru
sannan yace "Amma jikin da sauki?" Tace "Eh toh amma har yanxu his temperature is high" Yace "Toh Allah
ya sauwake, likitan ya tafi?" Aunty tace "Ehh" Yace "Toh Allah ya bashi lafiya" Aunty tace "Ameen" daga
yayi mata sallama ya katse wayar, Aunty ta ajiye wayar ta koma bangaren Abuturrab ta bude kofar dakinsa,
tsaye taga Ummi a dakin kusa da shi tana kallonsa, Aunty tace "Ya tashi ne?" Ummi ta juyo tace "Aa" Aunty
ta karasa kusa da shi ta xauna ta sauke duvet din tana kallonsa ta kai hannu goshinsa, taji har sannan da
xafi, juyawa Ummi tayi ta fita daga dakin... a hankali Abuturrab ya bude idonsa da yayi masa nauyi sbda
ciwon kai, ji yake kamar ana sara masa goshinsa, Aunty tace "Sannu son, ya jikin?" Bai iya ya bata amsa ba
ya sake lumshe ido, tace "Baka ci komai ba, in hado maka shayi?" Girgixa mata kai yayi, bai sake bude
idonsa ba har ta ga alamar ya koma bacci, ta mike ta fita daga dakin ta kulle masa kofar. Can cikin dare
Abuturrab ya farka, da kyar ya mike xaune coz he was pressed, ko hasken fitilan dakin bai so don kara masa
ciwon kai yake yi, ya kalli drip din hannunsa da ya kusa rabi, ya mike tsaye da kyar yana jin jiri ya kashe
ruwan ya bar cannula din kadai a hannunsa bayan yyi disconnecting dinsa daga jikin ruwan, kamar me
counting steps dinsa ya nufi bandaki ya shiga duk da jirin da yake ji, da alwalansa ya fito ya xauna gefen
gado ya dafe kansa, ko kadan bai son tuna komai da ya faru yau, it's making him down and weak, Bude
kofar dakin aka yi Aunty ta shigo ya daga kai da sauri, tace "Ka tashi Abuturrab, sannu ya jikin" A hankali
yace "Alhmdlh" Ta karasa kusa da shi tana dialing number Ahmad don kiransa ne ma ya tasheta yana fara
ring tace "Duk abokinka ya takurani gashi nan ni dai" Tana fadin haka ta mika ma Abuturrab wayar, ya amsa
ya kai kunne yyi shiru, daga daya bangaren Ahmad yace "How are you feeling captain?" Cikin sanyin murya
yace "Alhmdlh" Ahmad yace "Ka samu ka ci wani abun kuwa?" Abuturrab yace "I will take tea now" Ahmad
yace "Do so plss, Dr Shariff din ya baka drugs ne?" Abuturrab yace "I just woke up ban sani ba" Ahmad
yace "Ohk, ruwan yayi rabi yanxu?" Abuturrab ya kalli drip din sannan yace "Almost" Ahmad yace "Toh
Allah ya sauwake" Abuturrab yace "Ameen" sallama Ahmad yyi masa ya katse wayar, ba a dau lkci ba
Aunty ta dawo dakin rike da cup din tea ta mika ma Abuturrab tace "Gashi ka samu ka sha" Ba musu ya
amsa, tana nan tsaye sai da ta tabbatar ya sha shayin sannan ta amshi cup din ta fita, Mikewa