Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
xa ayi da xai sa hankalinta ya karkato ta dawo gida,
idan ya so sai a maida min Bibalo can, wllh Malam ina fama da bakar talauci yanxu, jarin babu shi babu
dalilinsa kamar dai kar ta bar wajen yarinyar, ga basussukan jama'a a kaina suna min tonon asiri har na fara
tunanin in siyar da d'an gidan da muke ciki in biya bashi sai mu kama haya da sauran, in sake jan wani jari,
to amma gidan fa duk ya ru6e, wa xai siya da mutunci" Mutumin wanda da alama ya gaji da surutunta yace
"Ki fadi abinda kike so ayi a takaice" Hansai ta gyara xama tayi kasa da murya tace "Kaga Malam so nake
kayi duk abinda xai dawo min da ita duk inda take, ta dawo wajena ni ban k'i ko karuwanci ma ta xo ta min
ba mu samu na rufa ma kai asiri, nasan dai yanxu karya ne ace bata san maxa ba, dama gata da kyau ga
farin jini wllh kasuwa xa mu yi sosai" Zulai sai gyada kai take, Mutumin yace "An gama, dubu hamsin kudin
aikin ki" Zulai ta dafe kirji tace "Dubu ashirin fa Malam, ina nagansa? Bani da shi bani da dalilinsa wllh, ko
dubi daya na kaina bana magani yanxu" Yace "Toh ku tashi ku tafi duk ranan da ku ka shirya ku dawo" Xata
yi magana cikin tsawa yace "Ku fita nace sai kun shirya" Da sauri suka mike suka fita a d'an dakin, Hansai ta
fashe da kuka tace "Yanxu ya xanyi Zulai, kema kinsan bani da ko dubu biyu na kaina wllh, duk na siyar da
kayan dakina babu komai balle in dauka in siyar" Zulai tace "Daga karshe dai gidan nan kawai xaki siyar in
dai bukata xai biya, in har Jiddah ta dawo ai sai kin kera wanda ya fi wannan a cikin gari, dama ba sai an
6ata ake gyarawa ba, kawai mu je a sa gida a kasuwa..." Hansai ta share idonta tace "Toh shkkn, in sha
Allahu baxan ji kunya ba" Daren ranan Jiddah na karatu a dinning kamar yanda ta saba bayan magrib aka
bude kofar parlon, Hajja ce ta shigo sakale da jakarta tace "Assalamu alaikum" Jiddah ta amsa sallaman
tana mata sannu da xuwa, Hajja tace "Ina Ramlan take?" jiddah ta mike tace "Tana daki bari in mata
magana" Hajja tace "Toh yi maxa wancan d'an daban sai ya iya tafiya ya kyaleni, kinsan dama da kyar ya
kawoni sai da uban ya sa baki" Jiddah dai bata ce komai ba ta tafi dakin Umma, ba a dau lkci ba Umma ta
fito sanye da Hijab da murmushi tace "Sannu da xuwa Hajja" Hajja tace "Yauwa Ramlah daxu naga abun
arxiki shine nace bari dai in taso in xo da kaina inyi godiya, don mu a Masar haka ake, Allah yayi maki
albarka ya kara arxiki sai dai tafiyar ma ta lalace don wannan yaro Aliyu gobe xa a kai kudin aurensa kuma
ina nan har sai anyi komai idan Allah ya yrda" Umma tace "Allah sarki, ai da kinyi waya na xo kawai Hajja
ba sai kin fito da daddaren nan ba" Hajja tace "Aa barni na xo, banda me sonka wa xai tuna da kai har ya
baka tsaraba haka..." Tana kai wa nan ta mike tace "Toh ni dai bari in koma ni da wancan d'an kabu kabun
ne muka xo kar ya tafi ya barni in rasa tudun dafawa" Umma tace "Tare da Aliyu ku ke?" Hajja tace "Ehh
wllh, sai da ma ya xageni a hanya muna tahowa daga nace masa ba jirgi fa yake figa haka ba, ni dai bakina
alaikum naki biye masa ya kunyata ni a kasar mutane" Umma tace "Amma yace wani abu, shine baxai
shigo ya gaisheni ba??" Hajja tace "Ahaf ai wannan mutumi dai daga d'an iska sai shi, baya ganin kowa da
gashi" Umma ta kira Huraira a daki tace "Tafi kice ma Abuturrab ina kiransa a waje" Tace "Toh" sannan ta
fita, Hajja ta koma ta xauna tace "Gwara dai kiyi masa soso da sabulu sannan ki hadani da d'an arxiki ya
maidani gida kar kasheni a hanya" Umma dai bata ce komai ba, Maimoon ta fito tare da Safiyya suka
gaidata, Hajja tace "Allah maku albarka, ya baku ilimi me amfani" Jiddah dai tuni ta koma ta ci gaba da
karatunta a dining, Ba a dau lkci ba Abuturrab ya shigo parlon kansa a kasa, Ya karaso ciki ya gaida Umma
da ladabi tace "Saboda ka isa yasa ka xo gidan nan ka xauna mota baka shigo gaisheni ba?" Ya ki kallonta a
ido, yana kame kame yace "Aa waya nake yi a motar dama xan shigo Umma" Hajja tace "Karya yake
algungumi har cewa yayi minti biyar ya bani wllh, ni dai ki hadani da me hankali ya maidani gidan d'a na
don Aliyu abun tsoro ne, babu uwar da na hada dashi balle ya cuceni, gashi uwar tayi ta xuba masa ido
kamar tana tsoronsa bata fada masa gaskiya, ita kuma yar Benuen can tayi kane kane a kan lamarinsa, ai ni
ina ganin iftila'i tunda ja sauka gidan Usman, abubuwa suke babu tsari kamar dai gantalallu" Abuturrab dai
sai kallonta yake ta gefen ido, Umma tace "Toh ka kyauta, from henceforth i don't want to see ur legs in my
house again, get out" Bai ce mata komai ba ya juya ya nufi kofa ya fita, Jiddah ta bi sa da kallo, Hajja ta
ajiye jakanta ta cire mayafinta ta linke ta ajiye, ta gyara xama tace "Dama idan babu me mayar dani gida sai
dai in kwana a nan kawai, baxan bi mutumin can ba abu ya lalace min" Maimoon ta fashe da dariya Hajja
ta marairaice tace "Allah kuwa ke baki ga yanda ya wani fita kamar Zaki ba daga fadan gaskiya" Umma tace
"Kiyi xamanki kawai a nan Hajja" Hajja tace "Toh a kai min kayana daki" Karfe tara da rabi Umma na
dakinta tare da Jiddah dake gyara mata press din kayanta, Umma tayi dialing number yayarta, nan kuma ta
sanar mata duk abinda Aliyu yayi mata daxu, Ummi tace "Kiyi hakuri Ramlah, Ni yayi ma ba ke ba, kinsan
wannan xancen auren da ya kirkiro ma kansa da Hafsah kawai suke sabgarsu, ban san komai a kai ba, uban
ne ma yace min gobe xa su kai kudi, wllh bai ce min komai ba shi har yanxu" Umma tace "Innalillahi wa
inna ilaihi raji'un, Yaya ina ta ce maki a tashi tsaye kince Aa ba komai, wllh wannan abu ba lafiya a ciki, ga
dai abu kiri kiri fa" Ummi tace "Aa ki kyalesu kawai, shi ba yaro bane kuma sarai da hankalinsa, abinda kike
tunani ba shi bane, shi dai ne ya xabar ma kansa haka, ai ba shi daya na haifa ba dai? Dama shi da namiji ai
wasu kake haifa ma" Umma tace "Ki kyaleni da shi xan saita masa xama wllh" Sun jima sosai suna waya,
Jiddah dai duk sai bata ji dadi a ranta ba, taji kuma a xuciyarta tana son yi ma Abuturrab magana, to amma
a ina xata gansa??
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last
bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd
getting rid of any skin problems
Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta
samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar
rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata
masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda
zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada
Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240
Ranan asabar kamar yanda Ummi ta sanar ma Umma aka kai kudin auren Aneesah, on that same day
kuma aka saka ranan bikin wata biyu, Umma na xaune parlor da yamma Hajja ta shigo parlon ta rike ha6a
tace "Ramlah kinji wai an sa bikin Aliyu nan da wata biyu, yanxu Usman ya kirani yake sanar min, sun kai
komai saura sadaki" Umma tace "Toh Allah ya sanya alkhairi" Hajja tace "Atoh dai, mu iyakar abinda xa mu
ce kenan, yaron da baya mutunta iyayensa...." Daga haka ta juya ta koma ciki, ita dai Umma bata ce komai
ba. Abuturrab na xaune shi kadai a parlorn gidansa dake Abuja idonsa na kan screen din wayarsa da yake
dannawa.... knocking din kofar parlon aka yi ya kalli hanyar kofar, amma bai yi wani yunkurin tashi ya bude
ba, aka sake knocking duk a tunaninsa Aneesah ce, wayar hannunsa ya fara vibrate ya ga Ahmad, yyi ta
kallon wayar kafin ya daga ya kai kunne, Ahmad yace "Are visitors not welcome any longer?" Abuturrab
yace "Nace maka ina nan ne?" Ahmad yace "Su kuma takalman da ka bari bakin kofa fa?" Abuturrab bai ce
komai ba ya katse wayar, bayan few seconds ya mike ya nufi kofar ya bude ya dawo cikin parlon, kallonsa
kawai Ahmad yake don rabon da ya gansa an yi sati uku yanxu, ya kirasa severally baya responding, har ma
ya daina kiransa, Ahmad ya karasa ya dau drugs da ya gani kan center table yana jujjuya su, lkci daya ya
ajiyesu yace "Bai kamata ka dinga shan irin wa ennan magungunan saboda yanayin aikin ka, and why are u
having sleepless night?" Abuturrab ya kallesa yace "Haka nace maka?" Ahmad yace "Aa haka dai drugs din
yace min..." Abuturrab yace "Then you are mistaken, ka kara gaba can da karyar likitancin ka..." Murmushi
Ahmad yyi yace "Toh Shikenan, amma da an canxa maka prescription din drugs din" Abuturrab yace
"Wannan kuma likitan da ya fi ka yayi prescription din" Ahmad yace "Ohk then, kwana da yawa, i called
severally baka responding ko nayi wani laifi ne" Abuturrab ya ki kallonsa, Ahmad yace "Shine dai yau sanin
schedules dinka nace bari in karaso gidanka na nan inji laifin da nayi" Abuturrab yace "I just decided to live
my life without hypocrite" Ahmad ya buda ido sosai yace "Hypocrite? Su waye hypocrite din?" Abuturrab
yace "Decision dina kenan" Ahmad yace "Kai ne babban hypocrite ai tunda har kana tunanin anyi wronging
dinka amma ka kasa bude baki kayi magana ka dau gaba da mutane, balle ni dai nasan i did nothing to
you" Abuturrab ya jefa masa wani kallo yace "You did nothing to me?" Ahmad yace "Of course, ba abinda
na maka" Abuturrab yace "That's ur cup of tea... To yanxu bayan munafurcin da ku ka je ku ka hada har aka
sa na saki wancan yarinyar ko da akwai wani abu da ya ragu a rayuwata tun bayan wannan lkcn, akwai
wani abu da nayi loosing?" Ahmad yace "Eh mana gashi har bacci kayi loosing, sbda duk wanda ke isasshen
bacci babu abinda xai hadasa da wa en nan kwayoyin dake gabanka...." Kallonsa kawai Abuturrab ke yi
babu ko kiftawa, Ahmad ya daga shoulder yace "And da bai dameka ba ko baka yi loosing komai ba babu
abinda xai sa ka dinga isolating kanka daga cikin al'umma, but that's not my problem now, my major
problem is that daga yanda na ganka nasan you are down for now may be they took u unexpected, don
haka take a break from work, kada wataran muje mu ji labarin da ba shi kenan ba, shi Pilot banda nutsuwa
da kwanciyar hankali ba a bukatar komai daga garesa, amma yanxu yanda kake a birkicen nan bai kamata
ka dinga daga al'umma xuwa sararin samaniya ba, toh bayan wannan kuma ina son ka cire duk xargi a
ranka, ka bar ganin ko da hadin bakina aka saka ka saki Jiddah, i know nothing about it... Kawai dai
coincidentally nayi maka magana da kwana biyu sae kuma abinda ya faru ya faru, da ina da niyyar sanar
ma kowa tun farkon auren xan sanar ae ba sai da aka dau lkci ba" Abuturrab yace "To ko kai ka fada ko ba
kai ka fada ba ance maka abun damuna yyi ne? Banda ma wani burden da aka sauke min meye nayi
loosing a lamarin nan, sae ma peace of mind da freedom da na samu, plss close this chapter, ba shi da
wani amfani a gareni" Ahmad yace "Ok then, i heard su Abba sun xo gidansu Aneesah yau" Abuturrab yace
"You heard right!!" Ahmad yace "Toh Allah ya sanya alkhairi" Abuturrab bai tankasa ba ya mike ya shiga
kitchen, Ahmad ya bi sa da kallo yana murmushi, Hmm is Abuturrab really sure he looses nothing living
without Jiddah?" Har karfe sha biyu Ahmad na gidan kasancewar bashi da night duty, ya tashi ya shiga
bedroom yyi kwanciyarsa ya bar Abuturrab yana operating laptop. Karfe uku da yan mintuna Ahmad ya fito
parlor ganin Abuturrab bai shigo ba, bai gansa a parlon ba har sannan kuma wutan parlon na kunne ga
laptop dinsa ka a kunne, kitchen ya karasa nan ma bai gansa ba, ya fito ya duba sauran dakunan duk baya
ciki, ganin kofar parlon da ba ayi jamming ba ya karasa ya bude kofar, xaune ya gansa balcony with his
phone, da mamaki Ahmad yace "What are you doing here by this time?" Abuturrab yace "Zafi nake ji" Da
mamaki Ahmad yace "Xafi kuma ga Ac ga fanka? Are you okay?" Abuturrab yace "To iskan waje nake so ba
na Ac ba" Ahmad ya fi minti biyu tsaye yana kallonsa, Abuturrab bai kuma kallon inda yake ba, Ahmad yace
"Ka sha drugs din naka?" Abuturrab yace "Ae ba kai ka min prescribing ba balle ka tambayeni" Ahmad bai
kuma ce masa komai ba don sae a sannan ya tuna cewar ya sha wajen karfe sha daya, juyawa yyi ya koma
parlon ya xauna yana mamakin is Abuturrab okay?? Har kiran sallan farko Abuturrab na xaune balcony,
Ahmad ya gaji da xama ya koma daki ya kwanta. Da asuba Ahmad ya fito da alwala parlon, dai dai sanda
Abuturrab ma ya fito daga bathroom din parlon, shi dai Ahmad kallonsa kawai yake har ya fita don bai ga
alamar ya kwanta ba, Abuturrab ya bi bayansa xuwa masallaci... Bayan an idar sun fito mosque din Ahmad
na kallonsa yace "Karfe nawa xaka yi piloting yau?" Abuturrab yace "Karfe daya..." Ahmad yace "Okay..."
Gidan ya shiga ya dau makullin motarsa ya fito ya ga Abuturrab xaune balcony yace "Xan dawo before 7"
Da ido Abuturrab ya bi sa har ya wuce. Kamar yanda ya fada karfe bakwai ya dawo gidan, xaune ya tadda
Abuturrab a parlor ya jinginar da kansa jikin kujera, Ahmad ya xauna ya ajiye ledan hannunsa yace "Good
morning" Abuturrab yace "Afternoon duty ka koma yanxu" Ahmad na bude ledan da ya ajiye yace "I think
u are suffering from lack of sleep" Abuturrab ya dinga kallonsa yace "Wa ye xaka yi ma allura? Ni nace
maka bani da lafiya ne??" Ahmad ya kallesa yace "Aa baka ce min ba, but this will help" Abuturrab ya
gyara xama yace "You are wasting ur time, gwara ma kar kayi wasting alluranka, idan kuma ka hada sae ka
nemi wanda xaka yi ma" Ahmad bai tanka sa ba ya gama hada ruwan alluran, sannan yace "Kaga kar ka
6ata min lkci ka 6ata ma kanka lokaci Captain, how will a normal human being stay all through the night
without sleeping, sannan anjima yaje ya daga jirgi with over 300 passengers or less??" Abuturrab yace
"Wai kai nace maka banyi bacci bane, shkkn kuma mutum daga farkon dare har karshe sae yayi ta bacci?"
Ahmad yace "Duk kwararren likita ya ganka yasan baka bacci bawan Allah, don haka idan xaka daina
gardama ka daina...." Abuturrab yace "Ashe kai kwararren likita ne" Mikewa Ahmad yyi yace "You ur self
will feel relieved after the injection...." It took anoda 15mins to convince Abuturrab sannan ya yarda
Ahmad yyi masa alluran, in just less than 20mins ya kwanta nan kan doguwar kujera, Ahmad dake
watching dinsa yace "Da dai ka tashi ka shiga ciki baccin xae fi maka ma'ana" Tashi Abuturrab yyi ya wuce
bedroom dinsa, yyi rub da ciki saman gado.... Sae wajen takwas da minti goma Ahmad ya bar gidan bayan
ya ga Abuturrab yayi bacci. Sha biyu da rabi na rana Ahmad ya dawo gidan ya tadda Abuturrab yana bacci
har sannan, ya ajiye masa ledan takeaway din abincin da ya kawo masa, ya karasa yana kallonsa da kyau,
lkci daya Abuturrab ya bude ido, ya dafe forehead dinsa yace "What's the time, our flight is..." Da sauri ya
mike xaune yace "Karfe nawa?" Ahmad ya rungume hannu yace "This is after 12" Abuturrab ya xaro ido
yace "What????" Tashi yyi daga kan gadon yaji wani jiri ya debesa ya koma, Ahmad yace "Look, don't
deceive ur self nd ur Airline Captain, ka tura masu text yanxu cewar baka da lafiya" Abuturrab yace "Ni
nace maka bani da...." Rike cikinsa yyi da sauri, yace "I feel like throwing up" Ahmad ya karasa ya bude
masa bandakin, da kyar Abuturrab ya tashi ya shiga bathroom din. Karfe shidda suka iso train station na
rigasa, Salem na cikin mota yana jiransu, Ahmad ya bude front seat ya shiga, Abuturrab ya xauna bayan
motar ya jinginar da kansa da seat, Salem na kallonsa ta madubi yace "How are you feeling now?"
Abuturrab yace "Alhmdlh" Salem ya gaisa da Ahmad sannan ya tada motar suka bar station din. Da magrib
Aunty na tsaye kan Abuturrab dake kwance saman gadonsa with drip, tace "Ko wannan aikin naka ai ya isa
yyi weighing dinka down, aiki babu hutu kullum mutum na sararin samaniya" Shi dai bai ce mata komai ba,
tace "Toh Allah ya sauwake" daga haka ta juya ta nufi kofa ta fita, Aisha ce ta shigo dakin da cup din shayi
ta ajiye masa tace "Ya jikin yaya?" Yace "Ummi fa?" Tace "Tana can daki" bai kuma cewa komai ba ta ajiye
shayin ta fita. Umma ce xaune parlor tana kallon Ahmad da bai jima da shigowa gidsn ba, tace "Toh ya jikin
nasa yanxu?" Ahmad yace "A'a da sauki nayi masa allurori kuma na sa masa drip" Umma tace "Ikon Allah,
kuma yaya bata gaya min ba wllh, bari in kirata" Wayarta ta dauka ta shiga kiran yayarta, Bude kofar parlon
aka yi Jiddah ta shigo da sallama rike da qur'ani da takardunta, Ahmad ya amsa, ta karasa parlon ta duka
kasan carpet a hankali tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau Jiddah, har kun gama karatun?" Tace "Eh, ya Aunty
Ramlah?" Yace "Tana can gida ai, baku je bane?" Tayi murmushi tace "Aa bamu je ba" Umma