Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
Rahama ta kara masu sallama ta tafi gun motarta, shi dai Abuturrab na xaune driver
seat ya kulle, Hajja ta bude bayan motar tana kallon Jiddah tace "Toh shiga" Jiddah ta shiga motar Hajja ma
ta shiga, Umma ta xaga xata shiga ta daya side din murya can kasa Hajja tace "Yanxu xata shigo duk ta
matsi mutane malam" Kamar kuwa Umma ta ji abinda Hajja ke cewa ta bude front seat kawai ta shiga, a
hankali Hajja tace "Toh Alhamdulillahi" Bayan sun d'an yi nisa Hajja tace "Yanxu ina muka nufa naga kana
ta wani xagaye xagaye Aliyu" Umma tace "Can gidana xa mu tafi" Hajja tace "Me?? Aje gidanki a kan me?
Anya kina tsoron Allah kuwa Ramlah ga dai gidan uwarsa a kai mata yarinya ta kula da ita tana yi nima ina
yi xaki wani ce a tafi gidanki? To ni nace gidan Usman xa mu kai ta, ai matar Aliyu ce ba matar wani ba,
mata kawai neman fitina yayi maki katutu, me xaki yi ma Jiddan wanda mu bamu iya ba, ni dai wllh kin cika
wahala, to gidan Usman xa a kai ta in ji ni, mata duk kin shanye yayarki sai yanda kika yi da ita kina ta
mulkanta yanda ranki ya so? To ni dai ba ruwana" Shi dai Abuturrab driving yake a hankali, Umma tace
"Idan kaje can bus stop din ka ajiye ni Aliyu" ya d'an kalleta yayi kasa da murya yace "No Umma u just have
to ignore her, don't take this personal, as if u don't know who she is" cike da damuwa Hajja tace "Toh wai
meye kake bata baki kamar warce aka yi ma laifi dai daga fadan gaskiya, ni fa ba wani abu nace ba, ko kaji
na xageta ne?" Umma tace "I said drop me Aliyu" yace "Then let me drop u home kawai, bai kamata kiyi
dropping a hanya ba" Ta kallesa tace "Ba ni nace maka haka ba" parking ya nemi waje yayi ganin how
serious she was ya juya yana kallonta ta bude motar ta sauka, sai duk Jiddah bata ji dadi ba taji kamar ta
sauka motar ta bi Umma, shi dai Abuturrab ya bi Umma da kallo har ta kulle motar tayi gaba, Hajja ta
sauke ajiyar xuciya tace "Toh ba shkkn ba... Yanxu da fada nayi mata ai baxata sauka ba, kaga yanxu da nayi
mata bayani cikin nutsuwa tayi wucewarta gida abunta baki alekum" Abuturrab bai tanka ta ba ya ci gaba
da driving dinsa, Hajja tace "Kai kuma sai wani cika kake kana batsewa kamar dai mu muka kashe maka
jariri Aliyu, toh kai arnene da baxa ka dau tawakalli ba, ita kanta warce d'an ya lalace a cikinta ma ta hakura
tana ta fara'a abunta tun a asibiti amma kai sai wani nukurci kake yi kana ba ma banxa ajiyar mu, a hakan
kake so Allah ya baka wani? Ai ba a ma Allah haka, da kasan xai baka ne?" Wani harara Abuturrab ya watsa
mata ta madubi, Jiddah ta d'an yi murmushi ta sunkuyar da kanta. Da daddare Jiddah na kwance kan
gadon Hajja bayan tayi wanka tayi shirin kwanciya, bude kofar dakin aka yi ta daga kai Abuturrab ya shigo
dakin ya kulle, ta mike xaune tana kallonsa har ya iso ya xauna gefenta ya kamo hannunta yace "How are
you feeling now?" Tace "Alhmdlh naji sauki" Gyada mata kai kawai yayi, da damuwa tace "Are u still sad"
ya kalleta amma bai ce komai ba, cikin lallashi tace "Kayi hakuri plss, Allah ya rubuta hakan xai faru... And
there is a reason for everything..." Ya d'an yi murmushi slowly yace "Sure wife" Ta rungumesa tace "Cheer
up pls dear" Ya marairaice mata yace "Xa ki samar mana wani da wuri plss???" Er dariya tayi tana shafa
chest dinsa tace "Sai in ka bani da wuri ae, sai in samar mana da wuri" yayi kasa da murya yace "Yanxu
fa??" Xaro ido tayi dai dai nan aka bude kofar dakin, ta dinga kokarin kwace kanta amma ya ki saketa, Hajja
tace "Kun ga jaraba ko? Ni dama sai da na innata a raina kawai dai na bi son rai ne na laka ma matar
mutane maita, amma can kasan xuciyata ina tunanin kilan takuranka ne ma ya sa cikin nan ya lalace, banda
haka yarinya daga 6ari ko kwana biyu ba ayi ba ka xo ka sa ta gaba a daki ka makaleta, yanxu meye ma'anar
haka Aliyu? Ke kuma kin wani sakar masa jiki kamar kyanwa, ai kya bari ki murmure yanda ya kamata
tukunna dai ko" Tashi Abuturrab yayi daga kan gadon ya nufi kofa, Hajja ta bi sa da wani kallon takaici, can
tace "Tirrr, wannan ai jaraba ce kawai ba wani abu ba..." Jiddah dai ta koma ta kwanta ta ki yarda su hada
ido da Hajja, don sai ta ji kunya sosai... Washegari da safe Hajja na kada mata shayi me kauri Abuturrab ya
shigo dakin, ya xauna saman kujera yana kallon Hajja yace "Ina kwana" tace "Lafiya lau, basu baka
kumallon bane a can ka yo mana nan?" Yace "Aa, Abba ne ke kiranki" Tace "Usman din?" Yace "Ehh" ta
mike da sauri tana cewa "Dama nayi wani mugun mafarki a kansa wllh, shi sa yau da sassafe na fita na ba
mai gadi kudi yaje can anguwan da almajirai suke ayi min sadakan kosai na dubu daya" Abuturrab dake
kallonta yace "Mafarkin me kika yi?" Tace "Aa sai kace wata jahila xan xauna ina gaya maka mafarkin da
nayi bayan naji ance babu kyau, er benue fa nayi mafarki tana kokarin tura mun shi a teku ta basa apple
yana ci dadin apple na dibansa yana kakkanne ido, ni kuma sai gani na taho a guje ta bayanta kafin ta
turasa ni nayi maxa na turata cikin ruwan sai ruwa ya tafi da ita ta dinga kurma ihu da karfi, ni dai na kamo
hannun yaro na muka dawo gida" murmushi kawai Abuturrab ke yi Hajja ta fice daga dakin, Abuturrab ya
mike ya dau shayin Jiddah da warmer din masa da miya yace "Tashi mu je" Ta xaro ido tace "Ina?" Ya sha
kunu yana kallonta, mikewa tayi ya fita ta bi bayansa, bedroom dinsa ya tafi da ita bayan sun shiga ya kulle
kofar, ta marairaice masa tace "So kake in ji kunya don Allah?" Yace "Ehh shi nake so ki ji" Xaunawa tayi
saman carpet din dakin ta rasa ma me xata ce masa, ya ajiye mata shayinta da waina yace "Eat now"
Abincin ta fara ci yana kallonta, taji ya kira sunanta, ta kallesa, yace "Tell me how everything happen pls" Ta
ajiye wainan hannunta tace "Me yasa baxa ka cire wannan abun a ranka ba and move on pls?" Yace "Na
cire wife, just that i am still wondering what happened all of a sudden on that day, tunda lafiya muka rabu
da ke ai, and i even escorted you to the gate" Sai kuma ya jinginar da kansa da gado a hankali yace "I wish
na raka ki har cikin gidan may be hakan da bai faru ba" cikin sanyin murya tace "Ko da kai ko babu kai dole
hakan xai faru tunda Allah ya rubuta hakan" Yace "But pls tell me how it happen" Tayi shiru kamar baxata
ce komai ba, ganin yanda yake kallonta a hankali tace "I saw someone just like my father...." Abuturrab
yace "Ur father?" Ta gyada masa kai, yace "Where?" Ta sauke idonta tace "Gidan mama" Da mamaki yake
ta kallonta yace "U mean ur father?" lkci daya hawaye ya kawo idonta tana kallonsa cikin sanyin murya
tace "Yes, i saw someone just like him" Abuturrab yayi kasa da murya da damuwa yace "Amma ai baba ya
rasu Jiddah, wani baban kuma kike nufi" Ta fashe da kuka a hankali tace "Eh na san ya rasu, but they look
so much alike, ni nasan abinda nake fada ai, i saw my father's duplicate" Abuturrab yace "Ikon Allah, bak'o
su maman suka yi ne?" Tace "Nima ban sani ba, ina xaune parlon ya shigo and i was shock sbda nayi
tunanin Abbana ne a lkcn at first, kallon Abba na kawai nayi masa...." Abuturrab ya dinga kallonta a bit
confuse, knocking din kofar dakin aka yi, ya mike ya bude kofar, Jiddah ta goge idonta da sauri, Umma ya
gani tsaye bakin kofar ya gaisheta ta amsa ta shiga dakin tana kallon Jiddah tace "Ya jikin?" Jiddah ta
gaisheta ita ma sannan tace "Na ji sauki Umma" Umma tace "Toh maa sha Allah, sannu" juyawa tayi ta fita
Abuturrab ya bi bayanta cause he need to talk to her about this. Karfe sha biyu saura na safiyar Hajiya
Fatima ta iso gidan da Rahama bayan sun kira Abuturrab ya tura masu address din gidan, a lkcn da suka iso
gidan Jiddah na bacci a dakin Abuturrab, Hajja na kyalla ido taga Rahama da Hajiya Fatima ta bi su har
parlon Ummi, Umma sai wani hararanta take, Hajja na washe baki tana kallon Rahama tace "Ashe uwarki
ce wannan mata me kirki haka?" Rahama na murmushi tace "Ehh" Hajiya Fatima suka kara gaisawa da
Hajja cikin fara'a, Hajja tace "Ai ni na haifi Uban Aliyun, da yake dai ni ba mai shige shigen gidan yara bace
shi sa tun ranan da aka yi wannan yakin a gidan baki sake ganina ba, balle an saki fitinanniyar gidan, kinsan
fa halin banxa aka kamata tana yi dumu dumu, toh dai ba ruwana gwara ka rufa ma wani asiri kai ma Allah
ya rufa maka naka" Hajiya Fatima tace "Haka ne kam Baaba, kinga rashin xuwan da baki yi ne yasa bamu
sake haduwa ba don kuwa ina yawan leka masu duk bayan sati" Hajja tace "Oh oh dama nace Jiddah na
murmurewa idan ta koma gidan mijinta nima sai in tattara in koma can din in sa mata ido da kyau don
kada aje a samu wani cikin ya lalace a banxa, ai ba abu bane mai kyau er yarinya karama kamar ta cikin fari
ace ya lalace, kwata kwata ba kyau haka idan ba a saka ido a kanta ba tayi ta samun ciki yana xubewa
kenan, amma dai ni nasan da akwai wani abu a kasa ba banxa ba, da kyar idan wannan kishiyar tata ta
barta a haka, don kaf xuri'armu babu wanda ya ta6a 6ari mu dai" Hajiya Fatima na murmushi tace "Toh
Allah dai yayi mana mai kyau, ita kuma Allah ya bata wanda xai tsaya" Hajja tace "Ameen dai, to a kawo
masu abinci mana, me lemo da ruwa xai yi ma mutum???" Ganin su Mama xasu wuce bayan Azahar
Umma ta tafi dakin Abuturrab ta taso Jiddah ta fito su gaisa, Jiddah ta shigo parlon Ummi ta gaida su da
murmushi fuskarta, Hajiya Fatima tace "Ya jikin Jiddah?" Jiddah tace "Na ji sauki Mama" Hajiya Fatima tace
"Alhmdlh, Allah ya kara maki lafiya" Ummi na kallon Jiddah da ta rakube waje daya tace "Shiga ciki ki
kwanta to..." mikewa tayi ta shiga dakin Ummi, Hajiya Fatima ta sauke ajiyar xuciya tace "Tsautsayi dai
kawai, ni fa na shiga gidan nasu da safe yace tana bacci..." Da sauri Ummi ta dakatar da ita don kada ma
Hajja ta ji kan xancen tace "Allah sarki, Allah shi yasan dai dai ai Hajiya" Hajiya Fatima tace "Wllh abun ya
tsaya min har yanxu a rai, ji nayi ta kwala ihu kawai..." Hajja ta gyara xama tace "Ta kwala ihu a ina?" Hajiya
Fatima tace "A parlor na" Hajja ta hangame baki tace "Wai a parlonki cikin ya lalace dama?" Hajiya Fatima
tace "Ehh wllh Baaba shi yasa abun ya dameni" Umma tayi saurin cewa "Aa babu xancen saka damuwa a
rai Hajiya, sai kace ba musulmai ba, Aa mu kam mun yarda da kaddara wllh, ai ko ba a parlon ki ba tunda
Allah ya kaddara sai cikin nan ya xube dole xai xube ko ma a ina ne, in ma dakina, dakin Ummi, ko ma
dakin Hajja" Hajja dai aka rasa abun cewa, sai kallon kowa take ta gefen ido, Hajiya Fatima tace "Haka ne
kam, Allah yayi mana me kyau" Umma tace "Amma kun yi wani bako a ranan da ya sameta a parlon naki
ko?" Hajiya Fatima tayi shiru, sai kuma ta kalli Umma tace "Mai gidana ne, dawowarsa kenan ma daga
Abuja" Umma tace "Ikon Allah... To ce ma Aliyun tayi taga yana kama da babanta ne...." Hajiya Fatima ta
gwalo ido tace "Babanta, amma ai tace min babanta ya rasu" Umma tace "Kwarai ya rasu, amma tace wai
suna kama sosai" Hajiya Fatima ta kalli Rahama da ta saki baki ita ma, Hajja tace "Me kama da babanta
kuma??" Hajiya Fatima tace "Toh ni kam na rasa ma me xance kuma" Ummi tayi murmushi tace "Ai kam
abun da mamaki, kuma dama irin haka na faruwa ai sai ka ga wani wanda ke kama da wani naka da ka
sani" Hajja tace "Aa to ko dai uban nata mutuwan karya yayi masu, wato ya gaji da wahalan su da talauci a
hayi" Umma da ta bude baki ta kalli Hajja tace "Toh sai kuma aka yi yaya?" Hajja tace "Atoh, ya gudu mana,
so nawa muke samun irin wannan labarin daga karshe ace ai ya gudu birni ya auri wata mai kudi sun
hayayyafa, ku ka san ko haka yayi shi ma" Salati Ummi ta dinga yi a ranta, Umma kuma ta dinga ma Hajja
wani irin kallo, ita kam Hajiya Fatima sai kirkiran murmushi take, Hajja tace "Xancen gaskiya fa, idan kuwa
har sun tabbata ya mutu din to duk yanda aka yi wanda ta gani din d'an uwan ubanta ne, tunda ba daga
sama ta fado ba... ayi mutum ace bai da dangi ko daya" Hajiya Fatima da kanta ya gama daurewa don ita
dai a iya saninta duk familyn mijinta ta sansu na kauye na birni da ma wa enda suke wasu kasashen, ta
dinga kallon Hajja ta ma rasa abun cewa, Hajja tace "Da xa a samu hoton shi uban nata da aka ce ya rasu
sai a kai ma mijin ki ya gani kawai" Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace "Ina ga hakan xai fi, idan anyi hakan
kilan Jiddan xata fi samun nutsuwa ta kara sakawa a ranta cewar ba mahaifinta bane kawai me kama da shi
ne" Hajja tace "Toh ba shkkn ba, amma idan nayi magana a dinga min kallon ta6a66iya, kawai abinda xa ayi
kenan yanxu a samo hoton ubanta mu kai ma mijinki shi kuma mu ji me xai ce, sannan idan kin lura er ki na
da wannan nakasan na gefen kumatu ita ma jiddah na da shi, wannan lotsewan nan" Hajiya Fatima dai tayi
shiru, Hajja tace "kawai abinda xa ayi kenan" Sai wajen karfe biyu da rabi Hajiya Fatima da er ta suka bar
gidan, amma gaba daya a sanyaye take da wannan lamari har Allah Allah take ta tafi ta sanar ma mijinta
dake gari har lkcn. Abuturrab na kallon Umma yace "Xan gane gidan, wancan lkcn ma ai da Hajiya Fatimar
muka je" Umma tayi shiru, sai kuma tace "Toh Allah ya kyauta, xuwa bayan la'asar sai mu tafi can din,
nasan ita matar uban ai baxata rasa hoton marigayin mijin nata ba" Abuturrab yace "Haka ne, amma fa
tana fita bara sai dare ake samunta a gida" Umma ta rike ha6a tace "Bara kuma? Allah me hikima, bara
take yi?" Yace "Ehh" Umma tayi shiru sai kuma tace "Kar a biye halinta Aliyu, idan da taimakon da muka ga
xa mu iya rendering mata we should do so, ta ci albarkacin Jiddah" Abuturrab ya girgixa kai yace "Bani da
wannan halin Umma" Umma bata kuma ce masa komai ba, ya mike yace "In kina nan har magrib din sai
mu tafi can gidan, idan kin koma gida kuma sai in je in daukeki a can gidan mu tafi" Tace "Shkkn" Bayan
magrib Abuturrab ya tafi can gidan Umma ya dauketa xuwa can gidan Hansai, yau kam bai yi mistake din
xuwa anguwan ba nose mask ba, tunda yayi parking Umma ke kallon layin da gidan yake, suka sauka daga
motar ya nuna mata gidan, Umma ta shiga ciki ya tsaya daga waje ya ki shiga, da ya tuna irin abubuwan da
Hansai ta dinga ma Jiddah a hayi da irin axabar da ta dinga gana mata tana amfani da ita tana making kudi
shi kansa dubi irin karyan da ta dinga lafta masa ya bata kudinsa yayi dubu dari biyar sai yaji wani bacin rai
ya xo masa, and he believes the situation she is right now serves her right, don haka ko digon tausayinta
baya ji wllh, Umma na shiga dakin ta rasa wajen xama ga wani doyi da dakin yake, Hansai dake xaune kan
darduma da wani rubabben fitila da ya d'an haske dakin ta amsa sallamarta cikin sanyin murya sai kuma ta
mike ta shimfida mata buhun cement a kasa tace "Sannu" Umma ta daure ta xauna tace "Yauwa nagode...
ya gida?" A hankali tace "Lafiya lau" Umma ta kunna wayarta ta ajiye sai kallon Hansai take ganin yanda
idanuwanta suka wani kumbura tace "Amma in ji dai lafiya baiwar Allah" Kamar jira take ta fashe da kuka
tace "Yau kwana uku Allah yayi ma 'ya ta rasuwa..." Sai ta dinga rusa kuka, Umma tace "Hasbunallah,
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya gafarta mata" cikin kuka Hansai tace "Ameen" Umma ta girgixa kai
tace "Nasan baki san ni ba, ni ce uwar rikon Jiddah sannan kuma kanwar uwar mijinta" Hansai ta dinga
kallon Umma sai kuma ta sunkuyar da kai, Umma tace "Na xo neman wata alfarma ne a wajenki" Cikin
rawar murya Hansai tace "Ina jin ki Hajiya, Allah ya sa bai fi karfina ba, ni ma kuma ina son rokon wata
alfarka a gareki" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "In sha Allah" a hankali Hansai tace "Toh wacce
alfarman kike so wajena Hajiya?" Umma tace "Hoton mahaifin Jiddah xaki bamu idan har kina da shi don
Allah" Hansai ta goge idonta tace "Baxa a rasa ba" Tana fadin haka ta mike ta bude Ghana must go da ta
ciro hoton kakar Jiddah da mahaifiyarta, ta dubo hoton mahaifin Jiddah wajen kala shidda ta ajiye ma
Umma har da wanda yake saurayi, Umma ta dau hotunan tace "Toh nagode kwarai da gaske, ki fadi ta ki
alfarman..." Hansai ta xauna a sanyaye tace "Alfarma daya nake so Hajiya don Allah a bar ni inyi xumunci
da Jiddah, ko da sau daya ne a shekara in dinga ganinta xanyi farin ciki wllh, nasan na xalunceta na ci
amanarta da na mahaifanta amma na roketa yafiya kuma tace ta yafe min yau wata hudu kenan tun
xuwansu gidan nan, in ci albarkacin ubanta kada a rabani da ita don girman Allah" Hawaye kawai take tana
shessheka, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh