Advertisements
Chapter 11 Reading Jeedderhh by Khaleesat Haiydar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jeedderhh by Khaleesat Haiydar

Author :  Khaleesat Haiydar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 108

30K to 33K   out of 321.7K words

baxai yiwu ba
kuma ki fitar min daga gida kada ma yasan kina nan in shiga uku" Hansai ta fashe da kuka tace "Amma dai
duk hatsin da yake kawo min ina dibar maka har rabin kwano wataran in kawo maka, har gawayi na sha
cika maka leda me kayau kayau in kawo maka, kuma matsala ta samu sai ka rufe ido kace xaka koreni,
cewa yayi fa xai kona gidanmu, idan na shashantar da batun ya babbake mu cikin dare fa?" Kawu Jibril yace
"Toh ni cewa yayi xai ruguje gidan, ganinki ciki ai sai ya kara tunxurasa ya aikata hakan" Hansai na matsar
kwalla tace "Yanxu duk ba wannan ba, dama wani Alhaji ne ya xo xai taimake mu kan lamarin da ganinsa
babban mutum ne me fada aji, kuma tun mutuwar isuhu yake xuwa siyan awara ya mana ihisani, yanxu dai
so yake ku hadu gobe a kan lamarin nan, don Allah ka sanar masa duk mun je gidan radio da gidajen
talabijin din kaduna kai rahotu, dubu biyar xan baka kar kaji komai" Yace "Ina dubu biyar din?" Tace "Ba ni
nace xan baka ba, fatanmu kawai ya taimakemu Allah ya bayyano mana da shegiyar yarinyar nan mu mika
ma Iliya tsiyarsa ko ma sarara, don idan ba nemota aka yi ba aka damka ma Iliya bamu da sauran kwanciyar
hankali wllh" Bata jira cewarsa ba ta shige dakin matarsa tana cewa "Lantana duk garin nan babu wanda
bai xo min jajen abinda ke faruwa ba amma banda ke, ko ba komai ai sai ki ajiye duk wani tsiya dake
tsakaninmu a matsayinki na musulma kixo ki jajanta min wannan musiba da ta sameni..."


✍🏻 Start ur payment for the book because i am almost and almost done with free pages kar
07087865788....
ku ji dippp an dakataπŸ’–


πŸ’–πŸ’– *Jiddatul Khair**πŸ’–πŸ’–




_By khaleesat Haiydar_✍🏻




10....


Washegari da asuba bayan an idar da sllh Ahmad ya fito rike da karamar jakarsa, dakin Ummansa ya shiga
ya gaisheta tace "Da asuba xaka tafi Ahmad?" Yace "Ehh kar nayi missing train din ne" Umma tace "To kun
yi da drivern ya xo da asuba ne ko wa xai kai ka train station din??" Yace "Aa Abuturrab xai kai ni" Umma
tace "Abuturrab kuma? yana garin ne? Lafiya bai koma aiki ba" Ahmad yace "Ehh satin nan yana nan yace
min" Umma tace "Toh Allah ya tsare, kayi addu'a dai" Yace "Ameen Umma, in sha Allah" Har ya kai kofa
tace "Har xaka tafi gashi ka mance da drugs din nawa" Juyowa yayi da sauri yace "Oops, kiyi hakuri Umma
Abuturrab xai kawo maki anjima in sha Allah" Tace "Toh Allah ya kai mu, Allah ya kiyaye hanya" sallama ya
kara mata ya fita dakin, yana fita compound ya dau wayarsa ya shiga kiran Abuturrab, Abuturrab ya daga
yace "Gani na shigo layin yanxu" Ahmad yace "Alright" Sai da suka yi nisa Abuturrab ya d'an kalli Ahmad
yace "Medical report din da nace xaka min din fa?" Ahmad yace "Idan aka yi how will it reach you?"
Abuturrab yace "The plane coming from Abuja to kano, xan yi ma pilot din magana abokina ne, sai ku hadu
ka basa" Ahmad yace "Flight din karfe nawa ne?" Abuturrab yace "karfe uku" Ahmad ya tabe baki, Can ya
kalli Abuturrab yace "Toh wai ma me ya hanaka komawa gun aiki kake neman medical report din karya
Captain?" Abuturrab yace "That is none of ur interest, kai dai kawai kayi min medical report" Ahmad yace
"Toh baxa ayi ba" Abuturrab bai kuma ce masa komai ba har suka iso Station din, Ahmad yace "Yauwa pls
captain i will text some drugs now to you, na umma ne, xaka siya ka kai mata, i forgot to do so yesterday"
Abuturrab yace "A hakan xan siya magani in kai mata? Kana ganin babu kaya jikina" Ahmad ya kallesa,
Jallabiya ce milk color jikinsa, Ahmad yace "Shi kuma wannan bargo ne a jikinka kenan, beside ni bance da
safe ba, wani pharmacy xaka samu a bude this early, kaga dole dai sai anjima" bude motar Ahmad yyi ya
sauka yace "Thank you" Daga haka ya rufe motar ya shiga cikin tashan, Abuturrab ya bi sa da wani irin
kallo, bayan few minutes ya ja motarsa ya bar wajen, Abuturrab ya na isa gida text din Ahmad na drugs din
ya shigo, lkci daya alert din kudin drugs din ma ya shigo, tsaki Abuturrab yayi ya cire jallabiyan jikinsa ya
shiga bathroom. Karfe goma saura Abuturrab ya fito dakinsa, bangaren step mum dinsa ya fara shiga ya
gaisheta, tana gyara press dinta tace "Ina xuwa da sassafen nan haka, kai da nake tunanin ka dau hutu ne
don ka huta" Yace "Xan je siya ma Umma drugs dinta ne" tace "Tohhh, Ahmad din fa?" Yace "Ya koma gun
aiki" Tace "Toh nima ka siyo min Panadol night..." Yyi murmushi yace "Toh in sha Allah" Ya juya xai fita tace
"Captain shiru shiru kuma baka turo abun ba, kada a siye wajen ne fa" Yace "Ehh ina son in sanar ma
Ummi ne...." Da sauri tace "Sai ka sanar mata captain? Ina ce yanda ka dauketa haka ka daukeni?" Ya d'an
yi shiru, sai kuma yyi murmushi yace "Toh nawa ne kika ce?" Tace "1.7m" yace "Toh xan tura in sha Allah"
Tace "Yauwa ko kai fa, idan ka dawo anjima ka shigo da akwai wata maganan kuma" Yace "In sha Allah"
daga haka ya fita, bangaren Ummi ya shiga, waya ne kare kunnenta, hakan yasa ya jingina da kofa ya jira
har ta gama sannan ya risina ya gaisheta, tace "Lafiya lau..." yace "Jiya na shigo kin yi bacci" Tace "Ehh da
wuri na kwanta" Yace "Ohk, sai na dawo" Daga haka ya fita dakin ta bi sa da ido. Abuturrab na shiga mota
yayi ma Ahmad transfer din kudin da ya turo masa, sannan ya nufi wani babban pharmacy, ya siya duk
drugs din, bai mance na Stepmum dinsa ba, ita ma ya siya mata pack har uku na drug din da tace sannan
ya dau hanyar gidansu Ahmad, Sallama yyi bakin kofar parlon aka amsa masa sannan ya shiga, Umma na
xaune parlon da Maman Abdallah dake xaune kasa Jiddah na gefenta alamar gaisheta suka shigo yi, daga
kai Jiddah tayi suka hada ido da shi ta sunkuyar da kanta, karasowa cikin parlon yyi ya xauna yace "Ina
kwana Umma" tace "Lafiya lau Aliyu, ashe kana garin" Kallonsa Jiddah tayi jin sunansa a karo na farko, ya
shafa kai yace "Ehh ina nan Umma, ya karfin jiki?" Tace "Ah Alhmdlh sauki ya samu" Mikewa yayi ya karasa
kusa da ita ya ajiye mata ledan maganin hannunsa yace "Ga drugs din naki Umma" tace "Toh nagode son,
Allah yayi albarka" komawa yayi ya xauna yace "Ameen" tace "Ya su yaya?" Yace "Suna lafiya..." Tace "Toh a
kawo maka breakfast?" Tana fadin haka ta mike, yace "Aa umma nayi breakfast a gida" Umma tace "Toh ga
awara da Maman Abdallah da mai sunan yaya suka yi da safe, u will like it" Ya d'an kalli Jiddah da kanta ke
kasa, Umma ta mike ta nufi kitchen, Abuturrab ya girgixa kai da sauri xai yi magana sai kuma yyi shiru ya
sauke boyayyen ajiyar xuciya, Maman Abdallah na kallonsa da fara'a tace "Ina kwama abokin Dakta" Babu
yabo babu fallasa yace "Lfya lau" Jiddah bata dago ba ita ma tace "Ina kwana" yace "Lafiya lau" Umma ta
fito kitchen, sai ga mai aiki rike da karamin tray me dauke da awara da sauce da pepper soup din naman
rago a rufe a wani warmer din, dinning ta kai ta ajiye, Umma na kallon Abuturrab tace "Gashi can a dining
area son" Ya d'an yi murmushi yace "Nagode Umma" Tace "Ko a kawo maka nan?" Ya bi dining area din da
kallo sannan yace "Ohk" Nan kusa da shi mai aikin ta kawo ta ajiye sannan ta wuce, Maman Abdallah ta
mike cike da ladabi tace "To Hajiya xata maki gyaran ne yanxu??" Umma tace "Eh to, ko kuma ta bari gobe
ai tana nan, ko ba kwana biyu ta xo yi maki ba?" Maman Abdallah tace "Tana nan tukun wllh Hajiya, don
bata ma sa ranan tafiya ba" Umma tace "Toh shkkn gobe sai tayi min gyaran" Maman Abdallah tace "Toh
shkkn Allah ya kai mu Hajiya" Mikewa tayi tana kallon Jiddah tace "Toh mu je gobe sai kiyi aikin ko" Umma
tace "To ki bar ta tayi kallo mana, tunda ke ba kallo kike ba" Maman Abdallah tayi dariya tace "Ehh kuma
haka ne, tunda xan je maki kasuwa yanxu, ina fita hijabi kawai xan sa in tafi dama" Umma tace "Toh ki bar
mata Abdallah ko baxai xauna ba" Maman Abdallah tace "Baxai xauna ba Hajiya, kiwuya ya gallabesa ai"
Umma tayi murmushi tace "Toh sai kun dawo" Ko kadan Jiddah bata so haka ba duk da ba wai tana da
niyyar bin ta kasuwan bane saboda tsoron kada wani da ya santa ya ganta a hanya amma xaman parlon ma
bata so, Umma na lura da ita taga alamar she isn't comfortable, hakan yasa tace "Ko kuma ku tafi kasuwan
kawai tare kada ta xauna shiru" Maman Abdallah da har ta nufi kofa tace "Dama tare nayi niyyar xa mu je,
da kika ce ta xauna tayi kallo ne yasa nima nace ta xauna Hajiya" Sosai gaban Jiddah ya fadi, Maman
Abdallah tace "Toh taso mu tafi kasuwan" Abuturrab dake xaune parlon yana sauraronsu yace "Tunda kallo
take yi ki bar ta tayi kallonta mana" Kallonsa Umma tayi da mamaki, that's very odd of him, shi mutanen
cikin gida ma baya shiga sabgarsu yayi masu magana balle wanda bai hada komai da su ba, Jiddah ta dago
kanta amma bata ce komai ba, Umma ta d'an yi murmushi tace "Toh tayi xamanta" Maman Abdallah ta fita
parlon bayan ta ce ma Umma sai ta dawo, Mikewa Umma tayi ta tafi kitchen sae gata ta dawo da karamin
flask da mug ta ajiye ma Abuturrab tace "Kilan ta manta ne bata kawo maka ba..." yayi murmushi yace
"Nagode Umma" Tace "Kana son madara?" Ya girgixa mata kai, tace "Yauwa nayi tunanin hakan, Ahmad
ma bai fiye shan madaran ba" Sama ta nufa tace "If u are done ina daki" Yace "Alright" Bayan few minutes
da tafiyarta ya daga kai ya kalli Jiddah, kanta na kasa tana wasa da hijab din jikinta maimakon kallon da aka
barta tayi a parlon, ya bude flask din gabansa ya xuba ruwan Lipton cikin mug, wanda ya xuba ko rabin
mug din bai yi ba, sae kamshi ruwan shayin ke yi, Calmly yace "Baki da wani damuwa a inda kike?" Ta dago
ta kallesa sannan ta girgixa kai, bayan few seconds a hankali tace "Sai dai Baabarmu xa tayi ta nemana a
gida" Kallonta yayi a takaice yace "Toh a mayar da ke wajenta kenan?" Shiru tayi tana kallonsa, can ta
sauke idonta cikin sanyin murya tace "Iliyan xai iya sake biyo ni, ita ma xata iya kai ni wajensa" Abuturrab
ya hade rai yace "Shine kuma xaki ce min Baabarki xata nemeki?" Bata ce komai ba, ya fara shan shayin
hannunsa a hankali, tv ya dinga kallo kafin murya can kasa yace "Amma idan aka sauya maki shi wanda xai
aureki yanxu da wani daban xaki amince da auren?" Kallonsa take babu ko kiftawa, yace "Ko baxa ki
amince ba?" a sanyaye tace "Toh ai ban san waye shi ba" yace "Toh ni nasan sa" Tace "Toh in dai baya
shaye shaye" Ya dinga kallonta sannan yace "Kina dai son kiyi aure kenan dama?" Hawaye ne ya kawo
idonta tace "Baabarmu ce ke son inyi auren, kuma ai ba makaranta nake xuwa ba kawai sana'a muke yi"
Bai kuma ce mata komai ba ya ci gaba da shan shayinsa, ta goge hawayen idonta, ya d'an kalleta yace
"Wanda xan hada ku baya shaye shaye" A hankali tace "Toh" bude warmer din awaran yayi yana kallo yana
d'an yatsine fuska, sai kuma ya bude na pepper soup dinma, lkci daya duk ya rufesu yace "Ki dauka ki kai
maku can ki ci" Da sauri ta kallesa tace "Aa mun ci namu ai, kai dai ka ci ai naka ne" Ganin babu spoon a
wajen tace "Bari in kawo maka cokali" Tana fadin haka ta mike tayi hanyar kitchen ya bi ta da ido sannan ya
sake kallon warmer din awaran, ba a dau lkci ba ta dawo ta iso kusa da shi ta durkusa ta ajiye spoon din,
sai kuma tace "In xuba maka?" Bata jira yace komai ba ta fara dibar masa awaran a plate sannan ta mika
masa, calmly yace "Kwashe su nace baxan ci ba" Sauke idonta tayi a hankali sannan ta juye ta mayar cikin
warmer din ta dau tray din ta mike ta wuce kitchen. Tana fitowa ta nufi kofa xata fita ya bi ta fa kallo yace
"Kee, ina xaki?" Ta juyo tace "Xan xauna a waje ne" Authoritatively yace "Dawo nan ki xauna" a hankali ta
dawo parlon ta koma ta rakube inda take xaune da farko ta xauna, ya ci gaba da shan shayinsa har ya gama
ya ajiye mug din ya kalli agogo dake nuna sha biyu saura, mikewa yayi ya nufi kofa ya fita parlon, sai da ya
shiga motarsa sannan ya kira Umma yace mata ya tafi. Yana cikin driving wayarsa ya fara ring, kallon wayar
yayi ganin me kiransa ya nemi suitable place yayi parking sannan ya daga wayar, Daga daya bangaren aka
ce "Captain da kansa barka da wuni..." Abuturrab yace "Ya kake Mu'axxam?" Mu'axxam yace "Alhmdlh
Oga, Kayi scarce kawai wannan satin, daxu nake tambayarka Umar ke cewa ai baka shigo ba satin nan baka
jin dadi" Abuturrab yace "Ehh ina kaduna" Mu'axxam yace "Toh ya jikin Captain!" Abuturrab yace
"Alhmdlh" Mu'axxam yace "To maa sha Allah ranka shi dade" Abuturrab ya jinginar da kansa da kujeran
motarsa a hankali yace "Kana ji na Mu'axxam?" Mu'axxam yace "Ina jin ka Oga" Abuturrab yace "Kana da
mata ne?" Mu'axxam yayi dariya yace "Aa tukunna dai Oga Allah bai kawo lkcn ba" Abuturrab ya gyara
xamansa yace "Ohk, wata yarinya na sama maka ko hakan yayi maka?" Mu'axxam yace "Ikon Allah, Oga ai
baxa ka min xabin da xai cutar da ni ba nasani wllh" Abuturrab yace "To kar ka damu, in sha Allah xan maka
duk wani abu da ya kamata na auren tunda nasan kilan ba wai ka shirya bane yanxu ae" Mu'axxam yace
"Allah sarki Oga, amma wllh nayi farin ciki da wannan labarin naka, naji dadi sosai, dama tuntuni nake son
yin auren amma babu halin yi sbda kasan komai yanxu tsada, shi kansa auren tsada, duk da iyayen nawa
sun ma riga mu gidan gaskiya sai kanni da yayyi, da dangi, amma ginin da nake yi a kauyenmu shi ke cinye
min kudi wllh...." Abuturrab yace "Babu damuwa, Allah xai rufa asiri, amma xuwa ranan alhamis ko
Juma'ah ka dau leave din kwana biyu ka xo kaduna, a nan yarinyar take, but before then ma xa mu yi
magana" Mu'axxam yace "In sha Allahu kuwa Oga, Allah ubangiji ya saka maka da alkhairi, ya biya maka
bukatunka na alkhairi, ya ji kan iyaye da kakanni, wllh nayi farin ciki sosai Oga" Abuturrab yace "Maa sha
Allah, xa mu yi magana" Daga haka ya katse wayar, wani ajiyar xuciya ya sauke... this is now almost settled
saura mutanen Hayi kuma yanxu, tada motar yayi ya ci gaba da driving din nasa. Kawu Jibril sai muxurai
yake daga inda yake xaune jin abinda Abuturrab ke cewa, Hansai ta marairaice tana wuri wuri da ido tace
"Ni kuwa Alhaji sai nake ga fa kamar idan mun koma gun 'yan sandan nan maganar nan babba xata xama,
Iliya fa bai bari mun yi baccin kirki ba daren jiya a gidan nan, ni har na sadakar jiya xan mutu, saboda ka
sanar min da xuwanka yasa na koma can gida karfe goma nayi ta jiranka sai gashi ka xo bayan azahar
sannan na kawo ka wajen kawun nawa" Abuturrab yace "Ae baraxanar da yake maku ne dalilin da yasa xa
aje police station din yanxu ba wani abu ba..." Abokin Kawu Jibril dake xaune tare da su yace "Ni da xa aji
ta nawa kawai a tafi wajen me unguwar yankin nan gaba daya, naga yana fada aji, idan abun ya gagaresa
shi sai mu koma gun 'yan sanda don gaskiya wannan yaro Iliya d'an iska ne wllh, iyayensa ma ba isa suka yi
da shi ba balle wani, amma gwara a fara sako mai anguwa a lamarin nan sannan ya kai mana gaban
hukuma koko ya ku ka ga?" Hansai tace "Wallahi haka ma yafi, mu je aji ta bakin me anguwan tukunna"
Kallonsu kawai Abuturrab yake with surprise, su fa ko damuwa da 6atan yarinyar basa yi, damuwarsu da
tashin hankalinsu Iliya da ya sako su gaba, Kawu Jibril yace "Ko ya kace Alhaji??" D'an murmushi yayi yace
"Ehh hakan yayi, aje wajen nasa" Hansai ta mike tana gyara takurarren mayafinta tace "Ba sai mun sha
wahalan neman abun hawa ba da motarsa ya xo babba ce duk xata kwashe mu" Abuturrab bai ce komai ba
ya mike shi ma duk suka bi bayansa xuwa kofar gida, sai bayan da suka shiga motar, Hansai tace "Ita Jiddah
ganinta me sauki ne wllh, nasan tsoro ne yasa ta buya wani gun, amma ko ni daya sai in samota ai, bari dai
a gama da tantirin nan" Ta madubi Abuturrab ya kalleta yace "Kinsan inda take kenan?" Da sauri Hansai
tace "Aa amma nasan tana nan cikin hayi babu inda xata, kasanta da shige shige da yawace yawace tunda
ba jin magana take ba, baxata rasa wanda xai boyeta ba na kwanakin nan kam" Abuturrab bai kuma cewa
komai ba har dai suka isa gidan mai unguwar, xuwansu ya sa shi fitowa xuwa kan tabarmansa dake
shimfide a waje da wasu dattijai uku ke xaune, Bayan an gaisa Kawu Jibril yace "Toh gashi dai mun xo
gareka mai unguwa...." Sanin kawun nata bai iya magana ba yasa Hansai ta amshe bayan ta maka masa
harara, ta marairaice tace "Mai unguwa muna cikin tashin hankali da fargaba wallahi, don a gaskiya bamu
da wani tsaro xaman mu a hayi" Mai Anguwa yace "Ikon Allah, me ke faruwa? Har kin fita takaba ne
Hansai?" Hansai ta sinne kai taki basa amsansa na karshe, Nan dai ta kwashe duk abinda ke faruwa karya
da gaskiya ta sanar masa tana matsar kwalla da kyar, kallonta kawai Abuturrab ke yi da mamaki don
maganganu da yawa ta canxa a kan yanda shi ta gaya masa, Mai Anguwa na jinjina kai yace "Ikon Allah Iliya
dai guda, d'an gidan Malam Kabiru?" Hansai na shessheka tace "Shi wllh" Yace "Toh yanxu ke kin tabbata
yarinyar na nan cikin garin nan, don lafiyarta shine babban abin dubawa yanxu..." Hansai tayi saurin cewa
"Tana nan anguwar wllh Mai anguwa, ai nasan babu inda

11 / 108