Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
lkcn da
Aneesah ta fada masa he find it hard to believe ya dai ji ta kawai, amma yanxu ya tabbatar hakan ne, ya
dau shayin ya fita ya kai ma Aneesah daki, Jiddah ta xauna gefen gadonta tambayar da Abuturrab ya mata
na rotating a kanta, wai me yasa tayi shunning Aneesah, a ina ta ganta balle tayi shunning dinta?? Karfe
hudu da rabi na asuba Abuturrab ya gama shiryawansa a dakin Aneesah, ita ce ma ta tashesa don yace
mata he will be leaving very early kafin sallan asuba sbda karfe takwas xa su yi piloting jirgi xuwa PH, ta
hada masa ruwan wanka ta dauko masa kayan da xai saka daga bangarensa har hakan ya basa mamaki don
duk xamansu bata ta6a yi masa haka ba, da damuwa tace "To breakfast fa? Haka xaka tafi baka karya ba?"
Yace "I will... At the airport, how are you feeling now?" Tace "Aa na ji sauki sosai" Yace "Alright, Allah ya
sauwake" Tace "Ameen My Captain, yaushe xaka dawo?" Yace "Friday in sha Allah" tace "Toh wai me ya
dawo da kai jiya, ko dai ka ji a jikinka bani da lfya ne?" Yayi murmushi kawai ya dau jakar laptop dinsa yace
"Probably.... Take care, sae na dawo" tace "Toh xa ma ka samu motar da xai je Abuja this early kuwa?" Yace
"Aa i will drive" daga haka ya nufi kofa tace "But ina son magana na minti daya captain" ya juyo ya kalleta,
tayi kasa da murya cike da damuwa tace "I don't know why Jiddah bata son mu xauna as one Captain, ko
don sbda abubuwan da na dinga yi a baya ne ya sa ta ki sakin jiki da ni ban sani ba, dama shi mutum baya
canxawa Allah baya canxa sa? Wllh nayi nadaman abubuwan da na aikata a baya, naga ba shi da amfani ba
shi da fa'ida, i was just behaving like an illiterate a lokacin, baya bayan nan na gane babu abinda ya kai
xaman lafiya dadi, balle ita da nake mata kallon warce bata da hayaniya xa mu xauna lafiyan, amma wai
bani da lafiya Jiddah tayi kamar bata sani ba a gidan nan alhalin a gabanta nayi amai ta kauda kai, rashin
lafiya ae ya fi gaban komai... da bata min haka ba wllh" Yace "Sai na dawo" fita yayi dakin, ya nufi dakin
Jiddah ya murda kofar ya bude ya shiga, bude kofar ya farkar da ita, ya kunna wutan dakin yana kallonta
yace "Lend me the car key" Sauke ido tayi daga kallonsa ta sauka kan gadon ta tafi gaban madubi ta dau
makullin ta ba sa, har ya nufi kofa ya dawo yana kallonta yace "Ke yanxu abinda kika yi jiya kin kyauta
Jiddah? Komin abinda mutum yayi maki kika ga bashi da lafiya ai xaki yi masa abinda ya kamata a matsayin
ki na musulma, Did u know what it means to have a forgiving heart kuwa?" kallonsa kawai Jiddah take ta
ma rasa abinda xata ce don bata san a kan me yake maganan ba ma, a xuciyarta kuwa tunani ta shiga yi
waye ba lafiya? Ganin taki ce masa komai ya nufi kofa ya fice daga dakin. Da safe karfe tara Jiddah ta sauko
ta ga Aneesah xaune parlor tana kallo da plate din samosa da spring rolls a hannunta tana ci, aikin kenan ta
ci tayi kallo... Tana ganin Jiddah ta dinga mata wani kallon raini daga sama har kasa, Jiddah dai bata kalleta
ba har ta wuceta, ta ja wani dogon tsaki tace "Shi dan talaka dama idan ya samu waje ya fi kowa gogewa
da girman kai, banxa kawai er matsiyata" Jiddah ta tsaya ta juya tana kallonta, Mikewa Aneesah tayi ta
nufeta a fusace tace "Ko xa ki rama ne da kika tsaya kallona haka?" Jiddah ta girgixa kanta tace "Not my
home training" Ta juya xata wuce Aneesah ta fixgota da karfi tace "Home training din waye kenan?" Duk da
yanda gaban Jiddah ya dinga bugawa haka ta hade rai tace "Cika ni..." Aneesah ta dunguri kanta tace "Anki
a cika ki don ubanki, kiyi abinda xa kiyi" Jiddah tace "Babu abinda xanyi tunda ni ba mahaukaciya ba..."
Bata rufe baki ba Aneesah ta sauke mata mari sannan ta hankadeta da karfi tace "Uwarki ce mahaukaciyar,
ehh uwarki da ba a san ko cikin shege tayi ta haifeki ba tunda har yau ba a ga dalilin asalinki ba..." Jiddah ta
dafe kuncinta tana kallonta, Bata san lkcn da ta figi flower vase dake saman center table ba ta buga mata
shi a kai, duk da Aneesah ta kauce sai da abun ya sameta, wani ihu ta fasa ta dafe kanta lkci daya idonta ya
fara juya mata sai dai kan nata bai fashe ba, ta nufi kitchen da gudu kamar mahaukaciya, Jiddah na ganin
haka tayi hanyar kofar fita, kan kace me sai ga ta a bakin gate, gaba daya ta tsorata, mai gadi na
tambayarta lafiya ko kallonsa bata yi ba ta fice ta shige gidan Hajiya Fatima, da gudu Mai gadin ya nufi
entrance din gidan don ganin abinda ya faru.... Babu kowa parlon gidan, Jiddah ta xauna saman kujera a
hankali tana bin parlon da kallo, lkci daya ta rufe fuskarta da kujera ta fashe da kuka a hankali, ji tayi ta gaji
da komai na rayuwan, ta rasa me ke mata dadi, ta ma rasa wani tunanin xata yi, kuka tayi sosai a parlon
daga karshe ta goge hawayenta a hankali ta jinginar da kanta da kujera tana tunanin rayuwarta, she wish
she have another place to go apart from Umma's house, she wish tana da yan uwanta na jini da ta sani,
she wish her father is alive today, kilan da gorin da xa a dinga yi mata bai kai haka ba, wasu hawayen masu
xafi suka sauko idonta tunawa da maganganun da Abuturrab yayi mata daxu bata san hawa ba bata san
sauka ba, Rahama ce ta shigo parlon daga kitchen, da mamaki ta tsaya take kallon Jiddah, tace "Aa Jiddah?
Yaushe kika shigo?" Jiddah ta daga kai a hankali tana kallonta ta kasa ce mata komai, tace "Bari in sanar ma
Hajiya" juyawa tayi ta koma sama ba a dau lkci ba sai ga ta ta dawo da mum dinta, Hajiya fatima na kallon
Jiddah ganin hula ne kawai a kanta ga shi doguwar riga ta saka, ta nufota tace "Lafiya Jiddah? Daga ina
haka?" Jiddah bata san sanda ta fashe da kuka ba cikin sanyin murya tace "Nemana take da fada mama"
Hajiya Fatima tace "Ikon Allah, amma wannan yarinya dai ina ga ta hada iri da maguzawa, bata da mafada
ne ko hankali ne kawai yayi gardama? ina shi mai gidan naku?" Cikin rawar murya Jiddah tace "Ya koma
aiki" Hajiya Fatima tace "Wannan wace irin fitinanniya ce kuwa? Taso mu je sama, shi ma yasan mara
tarbiyar da ya ajiye gida ya xa ayi ya dinga barin ku ku biyu kadai a gida? Haba wannan ai ba dubara bane,
yaushe aka gama wancan case din ina jin ko sati ba ayi ba, shi tunaninsa bai basa cewar bai kamata ya bar
ku a gida tare ba tunda yasan matar tasa yar tasha ce? Wani bala'i ne wannan ke cin ta kamar jahila?"
Dago Jiddah Hajiya Fatima tayi ta wuce sama da ita xuwa parlonta, Rahama ta bi bayansu ita ma ta ji ranta
ya baci sosai, tace "Yarinyar nan na bukatar wa enda xa su koya mata hankali wllh, tana bukatar a koya
mata lesson, ita ko kunya bata ji ba da er cikinta take tashin hankali kullum? Ko dai bata da saiti ne?" Hajiya
fatima ta xauna bayan ta xaunar da Jiddah saman kujera, Rahama ma ta xauna, duk ranta ya gama baci,
cikin fada tace "Allah Mama wannan ba karamin issue bane wllh, ya kamata ayi masu iyaka me karfi ko
kuma a raba masu gida kada wataran ta illata ta tun da ba sa'arta bace karfinsu ba daya ba, yanxu me ya
hadaku?" Jiddah ta share hawayen dake xubo mata tace "Kawai na sauko kasa shine ta fara xagina har da
iyayena tana dungurina, kuma take tambayata ko xan rama ne nace mata ai ni ba mahaukaciya bace shine
fa ta mareni" Kuka sosai Jiddah take tana kallonsu, Rahama tace "Kan bala'i, ta mareki? Sai kika yi me?" A
hankali tace "Ni kuma na dau vase na kwala mata a kai na fito" Rahama tace "Good!!! Dai dai kenan da
fuskarta kika saita kika maka mata vase din a kai tunda ita yar matsiyata ce bata san mutunci ba, banda
jahili wa ke irin wannan kishin en kauyen da take? Ai kai ya waye yanxu matured kishi ake na kwalliya da
kamshi da iya tarairayan miji, sai kuma kayi takama da kwallinka, wa ke irin wannan kishin na hauka a
yanzu dai? Aa wllh babu sai a kauye" Hajiya Fatima ta sauke ajiyar xuciya tace "A wani anguwan iyayenki
suke Jiddah?" Jiddah ta d'an yi shiru, lkci daya wasu sabbin hawayen suka kawo idonta ta ma rasa abinda
xata ce, Hajiya Fatima tace "Ko ba a kaduna suke ba?" Hawaye na sauka idonta cikin sanyin murya tace
"Iyayena duk sun rasu" Hajiya Fatima tace "Hasbunallah!!" Allah ubangiji ya gafarta masu yayi masu
Rahama" A hankali Jiddah tace "Ameen" Hajiya Fatima tace "Toh ina relatives dinki kuma suke?" Jiddah ta
goge idonta cike da karfin hali tace "Wajen stepmom dita na taso" Rahama sai kallon Jiddah cike da
tausayinta cause ta yanda tayi maganar xaka san she is hurt, a hankali Hajiya Fatima tace "Toh dangin
mahaifiyarki da Mahaifinki fa?" Jiddah ta kalleta, bata san sanda wani kuka ya taho mata ba ta fashe da
kuka sosai tace "Ban san su, i only know my step mum, ita kawai na sani, wajenta na taso" Duk suka yi
shiru suna kallonta cike da tausayi, Hajiya Fatima tace "Ina ita stepmom din taki take?" Cikin rauni Jiddah
tace "Hayin rigasa" Hajiya fatima tace "A can din Aliyun ya auro ki?" Jiddah ta kasa ce mata komai hawaye
wani na bin wani a idonta, Hajiya Fatima tace "Ki daina kukan nan kiyi min magana Jiddah" Tayi kokarin
daina kukan da take, cikin sanyin murya tace "Ina yi mata awara a bakin titi ya gan ni, a hayin rigasa...."
Daga Hajiya Fatima har 'er ta where a bit shock, don dai a class din Abuturrab da kyansa, da kudinsa, da
kuma profession dinsa, infact Abuturrab bai yi kama da wanda xai yi stooping kansa that low ba at all,
Rahama a ranta ta dinga tunani to kyanta ne ya tafi da shi, ko haskenta? Ko da yake babu yanda Allah baya
ikonsa, l Hajiya Fatima tace "Ikon Allah, a can ya auro ki kenan?" Jiddah ta girgixa kai tace "Ya dai
taimakeni, kuma ba wai don ya aureni ya taimake ni ba, ya taimakeni ne saboda halin da ya ga nake ciki
wajen stepmom dita" Hajiya Fatima tace "Kamar yaya kenan?" Cikin sanyin murya Jiddah ta fara basu
labarin tun daga farkon haduwarta da Abuturrab har xuwa yanxu da ya sake aurenta for the second time
ya hadasu da Aneesah, Rahama dai sai hmm take cause she is speechless, Hajiya Fatima kuwa tagumi tayi
tana ta kallon Jiddah don labarinta ya sanyaya mata jiki, wani tausayinta ta dinga ji har kasan ranta,
Rahama ta kara sauke ajiyar xuciya for the third time sannan tace "Yanxu na gano dalilin da ya sa ta sako ki
gaba, na farko tana ganin baki da kowa baki da wani me tsaya maki banda dangin Aliyun, ta yanda idan ta
tafka tsiyarta a kanki sai ace family issue ne kamar yanda aka yi last week ta lalata maki furnitures, na biyu
kuma tana ganin ke ba class din kishinta bane, ta raina wacece ke, ta raina personality dinki, tana ganin ta
fi ki komai ta fi ki gata, but she is mistaken, she is deceiving her self don ko nayi rantsuwa baxan yi kaffara
ba kin fita value a wajen mijinku from the way i saw things..." Hajiya Fatima da tayi nisa a tunanin da take
ta kalli Jiddah bayan ta sauke ajiyar xuciya tace "Ina gidanku yake a hayi Jiddah?" A hankali Jiddah ta gaya
mata, Hajiya Fatima tace "Tashi ki sauka downstairs akwai breakfast a dining ki deba ki karya tukun" Jiddah
ta mike a hankali ta juya ta fita daga parlon duk suka bi ta da kallo, Rahama tace "Mama don Allah kar ma
ki nuna tana gidan nan, ki bar ta tayi xamanta a nan ta samu nutsuwa, kalli fa duk a firgice take kana
ganinta kasan bata da rest of mind a gidan miji? For what reason? She is too young to be experiencing this
bull shit, Wllh kawai don kin hanani shiga abinda babu ruwana ne banda haka sai na nuna ma kishiyarta
karamin hauka take, Allah sai na rama mata marin" Hajiya Fatima tace "Aa bbu ruwanki, ki bar komai a
hannu na kawai..." Rahama tace "Allah ya sa mai gadinsu bai ga shigowarta nan ba, a barta ta huta na
kwana biyu wllh, shi ma banda dama ya so a cuceta ne ai yasan mahaukaciya ya ajiye a gida, ta yaya xai tafi
ya barsu su biyu kadai, wato ya ba kura nama kenan, ko kanninsa baxai kawo gidan ba su xauna saboda
Jiddan, haba tayi kankanta da yawa da fara fuskarta matsalan gidan aure, kamarta yanxu ai ya kamata ace
karatu take ba wai facing marital crisis ba, gaskiya banji dadin wannan labarin ba, na tsani in ga ana
walakanta 'ya mace, macen ma karama, idan bata samu kwanciyar hankali a gidan aure ba albarkacin
shekarunta ai baxa a dinga musguna mata haka ba, no plss this is too bad..." Hajiya Fatima tace "Ke
wannan ne ya fi damunki, ni damuwata ta yaya xa ace mutum bashi da dangin uwa bashi da dangin uba
kamar daga sama ya fado? Ai idan tana son samun 'yan cin kanta dole sai ta san su waye danginta, idan ba
haka ba no matter kwanciyar hankalin da xata samu dole sai an mata gorin dangi, kishiyarta baxata ta6a
daina mata wannan gorin ba, kai har shi wataran wllh sai ya mata gori, ki kyale maxan nan kawai" Rahama
tace "Gaskiya ne kuma, to yanxu ya xa ayi kenan mama?" Tace "Ni nasan yanda xanyi in sha Allah" Aneesah
na xaune parlor da kawayenta su hudu tun bayan da ta kirasu ta sanar masu abinda ya faru suka yo xuga
xuwa gidan, labarin yanda captain ya ji da ita daren jiya ta dinga basu, da irin yanda suka rabu yau da
asuba, Fauziyya da Rabi'ah suka yi wani shewa suka ce "Gaba da gabanta, ba kin tsaya sanya ba da, kin
xauna kina ta hauka da fashe fashe da dambe a asibiti, to ai yanxu kin fara ganin aiki da cikawa" ita dai sai
wani blushing take, Wayarta ne ya fara ring tayi masu alama duk suyi shiru daga surutun da suke, lkci daya
suka yi tsit, ta daga ta kai kunne a hankali ta rausaya murya tace "My Captain" Yace "How are you feeling?"
Tayi fari da ido tace "Alhmdlh, da sauki, sai dai ciwon kan ne kawai bai tafi gaba daya ba" Yace "Toh Allah
ya kara lafiya" Tana wani murmushi tace "Ameen, na ga sakon da ka turo daxu, nagode My captain" yace
"You are wlcm" tace "Kana lagos ne?" Yace "Yeah... Kai ma Jiddah waya" Ta d'an yatsine fuska tace "Ai kam
daxu na ga ta shirya ta ci kwalliya ta fita, bata ce min komai ba nima ban ce mata ba gaskiya, don abinda ta
min jiya yayi min ciwo" Yace "Ta fita?? To where?" Tace "Aa ban sani ba karya haramun, na dai ji tana waya
wai ga ta nan fitowa yanxun nan, har nake tunanin ashe tana da waya don ni ban ta6a ganinta da waya ba
sai yau" Shiru yayi bayan few seconds yace "Sai anjima" Tace "Alright my captain" Daga haka ya katse
wayar, ta fashe da dariya tana kallon kawayenta da suka hau hailing dinta, tayi kasa da murya tace "Kun ga
anjima sai in ce masa an kawota an ajiye a mota naje raka Rabi'ah da ta xo dubani na gani da idona"
Abuturrab na gama waya da Aneesah ya shiga kiran Maimoon, Maimoon na dagawa bayan ta gaishesa
yace "Kina ina?" Tana magana kasa kasa tace "Islamiyya" Katse wayar yayi, ya ma rasa tunanin da xai yi, sai
kuma ya hau kiran Umma, bayan sun gaisa tace "Ya su Jiddah?" He was short of word at first, sai kuma
yace "Alhmdlh Umma" Tace "Ahmad ya gaya maka sun koma makaranta ko bai gaya maka ba" Yace "Ya
gaya min" Tace "Toh yayi kyau" sallama yayi mata yace "Dama na kira ne in gaisheku" Tace "To madallah,
Allah yayi albarka" ya amsa da Ameen ya katse wayar, Ummi ya kira nan ma sai da ta tambayesa Jiddah da
Aneesah hakan ya nuna masa Jiddah bata gidan, yayi mata sallama ya katse wayar....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_
Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*
If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp
Aneesah na ta shiryawa a dakinta bayan magariba, ta dau duk wani abinda ta san xata bukata a er jakarta
bata da yanda xata yi ne kawai amma yau kam bata yi niyyar fitar ba ma, wayarta ne ya fara ring, ta xaro
ido ganin Abuturrab ne ke kiranta, ta dauka ta xauna gefen gado tayi kasa da murya tace "Hello my
Captain" Yace "How are u doing?" Ta langwabar da murya tace "Alhmdlh wllh" yace "Ya jikin?" Tace "Aa
naji sauki Alhamdulillah yanxu" Yace "Ohk, ta dawo gidan?" Tace "Ehh fa, Rabi'ah just left few minutes ago
na fita in rakata motarta naga ita kuma an dawo da ita ta sauka daga wata mota" Yace "Motar??" Tace
"That was what i saw, dama da baka tambaya ba ba ruwana ai tunda ban san wa ya sauketa ba, xai yiwu ko
d'an uwansu ne" Yayi shirun kusan second ashirin, har sai da tace "Hello" Yace "Alright, sai mun yi
magana" Tace "Ohk my captain" Katse wayar tayi, ta ajiye tayi shiru, anya ya kamata ta fita yau kuwa, kar ta
fita ya dawo unexpected fah, but his schedules tomorrow are so tight don karfe bakwai da rabi take jin xa
su yi piloting xuwa lagos, tana ta tunane tunane wayarta ya fara ring kuma, ta duba da sauri taga shi ne, ta
daga ta kai kunne tace "Hello my Captain" Yace "Can u pls go give her d phone?" Sosai hankalinta ya d'an
kwanta, which means baxai dawo din ba kenan, mikewa tayi sai kuma ta tuna fa