Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
ta ma rasa abinda xata ce har Hajja ta fita parlon, Ramlah tayi kasa da murya tace "Ko dai xaki
rakata don asirinmu ya rufu Jiddah??" Jiddah ta girgixa kai calmly tace "Ni baxan je gidan wannan matar
tasa ba wllh, dama dai bata nan ne, kuma ba gwara ta sa a kira mata shi ya xo ba, amma sai inyi ta wani
xuwa gidan mahaukaciyar a saboda me?? Baxan je ba" Ramlah sai kallon Jiddah take ganin yanda take
maganar kamar she have grudges with Aneesah, murmushi Ramlah tayi tace "Ki dai yi hakuri, idan ya so
kar ma ki shiga cikin gidan sai ki jira ta a waje" Jiddah tace "Na fa ce baxan je ba" Tashi tayi ta wuce daki
Ramlah ta bi ta da kallo, sai kuma ta mike ta isa window tana lekan waje taga ko Hajja ta fita compound
din, Tsaye ta ganta mai gadi na mata danne danne a waya alamar xai mata kira, Ramlah ta juya da sauri ta
koma....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
It’s S.SQAURE COLLECTION ANNIVERSARY YAYY🎊🎉
Jama’a gawata gagarumar sanarwa ku gyara zama kuji.
S.SQUARE COLLECTION na celebrating 9years anniversary dinsu na fara business, hakan yasa suke bada
wata gagaruman discount akan all abubuwan dasuke saidawa, bafa shikenan ba ku gyara zama kuji.
A shagon S.SQAURE COLLECTION zaki samu abubuwa da dama kaman haka;
Hadaddun dinkakkun Gowns wato dogayen riguna.
Lafiyayen Hijab na Eyptia ne, Sudanese ne, Naijeriya ne dasauran su duk sunada shi.
To ina masu baki achan achan irin mu gafa namu nan.
S.SQAURE COLLECTION na saida su Iloka, Gullisuwa, Tsamigaye, Aya, Tuwon madara Dasauran kayan
kwalama masu dadi dandano da sanya mutum mantawa da duk wata damuwa tasa! Hehehe badai kun
fara gajiya ba danfa ba anan kadai S.SQUARE COLLECTION suka tsaya ba.
Ina matan kamshi dasu Anty turare S.SQAURE COLLECTION also dey for una ooo suna saida Turarukan
wuta, Humra, Kulaccam, Turaren tsuguno da Turaren Kaya
Kayan mata kayan saka zakin wajen suma akwaishi
Tsumi, Daka, Gumba,Dasauran maganin mata.
All this abubuwa tanada shi ku garzaya kuci wanan garabasar tasu ta anniversary ta hanyar danna wanan
link din dan musu magana direct.
wa.me/+2347030037697
*Mg's skincare*
Sallah promo
15%discount💃
Hi sister's
Gafa dama tasamu kuhanzarta Kar ayi Babu kuduk meson siyan kayan mg's yahanzarta domin Kar ayi
babushi suna Bonanza na sallah Raba raba sannan sunkawo zafaffun Kaya masu matukar inganci fiye Dana
baya domin Karin jindadinku🥰Ina me fama da duk wani matsalan fata, pimples ne ko tabo,sunburn,acne
dama sauran matsaltsalun fata shin sister haske kikeso kiyi Amma bana bleaching ba? Shin kinshafa Maine
yabatamiki jiki kinkoma wata halitta daban kugarzaya@mg's skincare kujara products dinsu kuga abun
al'ajab domin sun shahara Kuma dayawa sunjaraba sundace karkice nagwada products dayawa baimin ba
sister kiyi kokari kinemi mg's products Koda soap ne Ina shaidamiki fatarki saita banbanta Dana sauran
Mata👌
Akwai soap 3k now 2500
Student package 7k now 6500
Beauty kit 11k nd now 10k🤗
Kuhanzarta kusiya naku domin promo din zaifara 1/7/22 Kuma products zaikoma normal price dinshi on
15/7/22 DNT miss out my people
Maiso yatuntubemu
08062991549,07046881166,07067210195,
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
💯 tested nd trusted
Natural/organic
Is time to join the glow gang my pupil
Show nd treat ur skin with some luv nd let ur skin do the talking
*WANAN NOVEL DIN NA KUDINE BIYA 500 zuwa 2029764071 first bank nafisa Nuhu sai a tura shaidar biya
zuwa ga lambar Nan 08033719070 ko katin mtn mutanen Niger Airtel Kika min SHARING bansanki ba Allah
Yana kallonki na barki dashi*
*Page 32*
Lubna
Sosai nake samun kulawa daga wajen mummy da zainab,ko tsinke basu bari na dauka,har mamakin
mummy nake yanda take san cikin jikina da nidai a tsakiya nake banji Ina so ba banji bana so ba, a yanzu
dana dan samu nutsuwa na fara tunanin sanaar daya Kamata nayi da kudin da ke wajena,dan mummy ta
dauka kayan order nawa ne bai iso ba har yanzu babban burina na nemi kudin da zan kula da kaina har da
Mimi da Kuma abinda zan Haifa dan banaso na dorawa mummy nauyin komai,har tayi tunanin na Kara
Mata hidima tayi tunanin na komawa Mahfuz, dan Koda Mahfuz ya karbesu nima zan dage wajen
hidimanta musu, daidai da sau daya ban taba Jin shaawar tunanin mahfuz har naji Ina San koma Masa ba
idan kuwa Zan tuna shi zanji kamar an sabunta kiyayarsa a raina tun ranar dayazo k'ofar gidanmu na hadu
dashi ban Kara marmarin fita ba,mummy data lura banasan maganarsa daina min tayi mmn Iman ce dai
idan tazo dole sai tamin maganarsa na Kuma rasa ya zanyi da ita haka zata ringa min waazi tana na
sausauta Masa ko dan Mimi da abinda ke cikina ita yanzu tausayin shi take ji bbn Iman daya bata labarin
halin da yake ciki idan taga na hade rai sai ta hakura da min maganarsa dan a yanzu nafi samun kwanciyar
hankali a gida bana so na tuna bakin cikin da mahfuz ya Sakani,da shawarar mmn Iman dana zainab nayi
amfani na fara dora kayan kitchen a status dina, ban canja layi ba na dai kulle layina ba Wanda ya Isa ya
Sameni a waya sai dai ni idan Ina raayi nakira mutum a waya,sai wani sabon Airtel din dana siya da ba
kowa ke dashi ba sai iya mmn Iman na Kuma roketa Kar ta fadawa kowa.
Da wanan na samu sauki nacin da mahfuz yakemin da text din da yake turamin ba adadi.
Kamar wasa daga Shiga grps da tallata kayan kitchen naga an fara biyoni ana so abin Dubu ashirin sai na
Kara Dubu biyu akai wani Kuma Dubu daya,idan dagaske ana so naga an turamin rabin kudin sai na siyo da
kudina, azo gida a karba ko na aika,Kamar wasa sanaar ta karbeni ta online na Kuma fara da kafar dama,da
wuya nayi posting abu ba'a nuna ana so ba wanan ya Kara d'auke min hankali naji bana cikin damuwa dan
canjika na shigomin a yanzu babban burina na sauka lafiya na Kai mahfuz hisba ya bani takardata kayana
Kuma mummy fir taki barina na kwaso a yanzu Ina zaune a Palo mummy na dakinta bansan mai takeyi ba
zainab na aiketa ta kwaso min wasu kayan kitchen da na siya inaso na aika kayan sokoto,dan har daga wani
garin ake min ciniki,ko a yanzu da nake zaune Ina ware kayayyakin mutane ne mmn Hidaya ta shigo
makociyarmu da sallama take na hade rai dan a yanzu Kuma ta fara isata da shigowa a rana sai ta shigo sau
biyu uku na Rasa uban Mai take nema ada ba ta damu da shigowa ba sai a yanzu da na fara tunanin gulma
yasa take shigowa Hadeeza ta koyamin hankali,a yanzu sam na daina yarda da mutane duk da ita wanan
din mun Dade da saninta amma a Yanzu dan Adam ba abin yarda bane ko ta shigo haka zata zauna tayi ta
kananan surutu zainab na biyeta har ta gaji ta tafi,dan ni tashi nake na bata waje,mummy ma daga gaisuwa
ba wani magana take mata ba ko da nayiwa mummy maganar ban yarda da ita ba nasan gulma ke kawota
murmushi kawai tamin tana ai indai nice yanzu ba abinda bazan ce ba ita yanzu tana min uzuri amma na
ringa sausatawa.
Nasan zata iya girmana duk da na hade rai ciki ciki na amsa sallamar da murmushi ta samu waje ta zauna
tana "Ke kadai ce a gidan Lubna"
"Gashi kuwa kin gani kike sake tambaya"
Dan shigowar ta biyu kenan na cigaba da raba kayyakin mutane ko dagowa banyi na kalleta ba da tana da
hankali daga yanda na hade rai ya Kamata ta gane bana maraba da shigowar ta gidan
"Ina Aunty"?
Kamar bazan kulata ba nace mata tana daki.
"Ina Mimi"?
Na bawa banza ajiyarta dan daga mimi zainab zata tambaya
Haka ta cigaba da zama ganin ba kulata zanyi ba taja bakinta ta tsuke na gama abinda zanyi na zuba su a
leda na manna sunayen da lambobin wayanda Suka siya na ajiye a gefe na mike na bar Mata palon,har ga
Allah ta isheni inaga ta kusa kawoni wuya sai na fito mata a mutum zata daina sintirin shigowa.
Koda na Shiga d'aki wayata na dauka na kunna data a yanzu grps din kasuwanci yafi yawa a wayata,sai
daidaikun kawayena da muke chat dasu zancen duniya baya buya duk sunji labarin ina gida,amma sabida
su tabbatar sai cemin suke zasu zo gidana ni kuwa na nace musu a yanzu bana tare da mahfuz bana Jin
kunyar kowa yasan mun rabu dan nasan ko na boye ko ban b'oye ba dai sai anji labari,daga Mai jimami sai
Mai cemin aure hakuri akeyi,anan wasu har da bani labarin halin da suke ciki suma da hakurin kawai
suke,daga marowaci,sai mafadaci nidai sai nake ganin da haka halin mahfuz din yake Zan iya zama ai amma
mazinaci ne shi da bazan iya cigaba da zama dashi ba.
Hira muka dan tab'a dasu har zan sauka naga anyi min magana da wani lamba Ina dubawa naga matar
yayan mahfuz ce mmn Nadeeya da hoton nadeeya nagane itace gaisawa mukayi dan munyi zaman
mutunci da ita ba laifi itace ta fara fadamin halin Ammi bayan mun gaisa tace "Lubna yanzu dan Allah
bazaki yi hakuri ki dawo ko dan Mimi ba"
"Dan Allah karkimin maganar dawowa rabuwarmu yafi alheri ya su Nadeeya"?
Dan Sam banasan ma a ringa min maganar komawa
"Suna nan kalau Ashe cikine dake danaje gida gaida Ammi nake Jin labari"
Sam banso ma Suka san Ina da ciki ba mummy tayi subutar baki ta fadawa mahfuz
"Eee cikine dani"
"Dan Allah lubna kiyi hakuri ki dawo,wlh ya gane kuransa duk da bamu San Mai ya hadaku ba amma wlh
mahfuz yaji jiki bakiga yanda ya rame ba naji labarin ma kudin da aka kai na aurensa dole Ammi ta masa
baso yake ba"
Sai naji gabana ya yanke ya Fadi "Au kudin aure ya kai dama"?
"Eeee sati biyu da suka wuce naji labarin awajen Abban nadeeya sam bamuji Dadi ba har shi kansa mahfuz
din dama ki hakura lubna ki dawo dakinki dan Allah wlh mahfuz na kaunarki ko dan Mimi da abinda ke
cikin ki"
"Wacce ya kaiwa kudin"?
"Wlh bansani ba nadai ji labarin an Kai kudin Aurensa Ammi Kamar ta zuba ruwa a kasa ta Sha"
Bansan zanji na damu ba sai gashi naji wani irin abu ya tsayamin a Raina har jikina na dan rawa na kashe
data na sauka.
Na Rasa tunanin da ya Kamata nayi ko ni aka tambayeni Mai ya jefani cikin bakin ciki ba sani nayi ba na
tsinci kaina da hawaye da lissafa wata na nawa yanzu a gida wata na uku a gida cikina wata biyar,a cikin
wata uku har Mahfuz ya Kai kudin aure dama nasan duk abinan da yakeyi na munafirci ne,daga lokacin da
yaji Ina da ciki na dauka zai cigaba da sintirin zuwa ko dan cikin jikina amma ko a jikinsa,yanzu ya riga da ya
gama dani ya ajiyeni zai je ya auri Hadeeza daya fifita a kaina akanta ya wulakantani yake Kuma san ya
nunawa duniya zai iya rayuwa batare dani ba wata uku da rabuwar mu har ya Kai kudi,sam bansan lokacin
da Mummy ta shigo ba sai data zauna a gefena naji tace "Ke lafiyarki kuwa"?
Kamar Ina jiran kiris na fashe da kuka
Mamaki yasa ta zuba min ido cikin bakin ciki nace "Wlh mummy na tsani mahfuz,wata uku da rabuwarmu
har ya Kai kudin aure bai damu ma da abinda yamin ba ashe hanya yake nema da zamu rabu sabida yaje ya
auri karuwarsa mummy shiyasa na dage bana San cikin nan dan shi zai cigaba da rayuwarsa ne na Kare da
raino na gama Shan wahala ya dawo ya karbi yayansa"
"Lubna kenan toh yanzu mai yasaka ki kuka har da damuwa da auren da zaiyi bayan bakya San shi a ganina
murna ya Kamata kiyi tunda bakya San shi sabida me zaki damu dan zaiyi aure,kece Kika tsane shi tunda
kin tsane shi kowa ma ya tsane shi kenan Kar yayi Aure kenan tunda kince bazaki koma Masa ba sai yayi ta
zama haka ni a ganina ba abin damuwa bane wanan abin kiji dadine tunda kila auren da zaiyi zai saka ya
manta dake ya hakura ya baki takardarki cikin sauki idan Kuma kinsan har yanzu kina San shi sai a nemo shi
a daidaita ku ki koma"
"Wlh bana San shi ba kishinsa nake ba bakin ciki nakeji da cutar daya min mummy yana so ya nunawa
duniya dama ba sona yake ba daga rabuwar mu zai sake aure?ko shekara ba muyi da rabuwa ba wata uku
kacal,mummy tunda yazo Kika fada Masa Ina da ciki idan mai hankaline ai ya Kamata ya ringa zuwa Yana
Jin lafiyar abinda ke cikina amma bai Kara zuwa ba Ashe aurene agabansa"
"Nidai bangane miki ba Kam gashi dai karara dai kina Sansa da kishinsa Amma kin dage ke bakya San shi,
zuwan mai zaiyi bayan wulakanci kike masa bama fitowa zakiyi ba sabida me zaizo Ina ganin ikon Allah a
wajenki.
Yana kirana a waya ya tambayeki da lafiyar Mimi da abin cikinki yace min idan akwai wata matsala a fada
masa dan keda zainab ba sauraransa kuke ba ya kikeso yayi kuma"?
Lura nayi mummy magana take fadamin raina na kara b'aci hakane yasa ban sake magana ba a madadin
mummy ta nuna rashin Jin dadinta sai naga kamar ma goyon bayan auren da zaiyi yake yanzu Hadeeza ta
samu abinda takeso shima ya kasa rabuwa da ita zai aureta
A ranar da bakin ciki na kwana Ina Kara Jin tsanar mahfuz a raina ni nasan ba wacce zai kaiwa kudi sai
Hadeeza.
Mummy kuwa ta sakoni a gaba da lokaci bai kure ba idan Ina san mijina zata iya kiransa yazo kila ya fasa
auren kar na cuci kaina na saka Mata kuka akan ba San sa nake ba wulakanci daya min yasa nake Jin
haushi.
Mahfuz
Damuwar da yake ciki yafi na baya dan har ga Allah baya jin zai iya auren Hadeeza data saka shi a tsaka
mai wuya,a kullum tunanin yanda zai fasa auren yake Yana gudun Lubna taji labari ta tsane shi, duk da
rokon Ammi da yayi akan bayaso kowa yasan da maganar Kai kudin,sai data zaga ko'ina ta ce ya kai kudin
aure Kamar ya fasa kuka,Yana San kara zuwa yaga lubna amma bashida kwarin gwiwa zuwa sai yake ganin
kamar zata ji labari tunda har Hadeeza tasan komai akansu zata iya duk abinda zata yi dan lubna taji labari
ko dan ta Kara rabasu,abinda dai yake gudun yasan lubna taji labari zatayi tunanin a san ransa zaiyi auren,
tunani na neman kwantar dashi ya rasa Mai ke masa dadi a yanzu ba abinda yakeso sama da Wanda zai iya
fahimtar halin da yake ciki ya taimaka Masa da shawara ba Kuma kowa zai iya bashi shawara nagartattu ba
sai Abdul da yayi fushi dashi da har gobe idan ya kirashi a waya baya d'auka daga lokacin dayaji labarin duk
abinda ya faru yama ki yarda ya saurareshi balle har ya taimaka Masa da shawarwari,gefe guda Kuma haka
Hadeeza ta sako shi a gaba da waya da ko kadan baya d'auka,dan ko tunata yayi wani irin bakin ciki ke
rufeshi bayajin zai iya zama da ita idan ya auretan ba abinda ke ransa sama da ana daura musu aure ya
kaita asibitin ana zubar da cikin take zai saketa saki uku.
A cikin wanan halin aka tura su Lagos wani aiki shi da wani Abba,tafiyar nan da zasuyi ya jefashi cikin
farinciki dan Kano ta Masa zafi gefe guda Kuma Yana murna zaije wajen Abdul kila ya samu ya shawo kansa
idan yaga har lagos yaje.
Da haka ranar tafiyar tazo Suka tafi a jirgi,sam basu samu wani zama ba sabida aikin da suka je bai samu
kansa ba sai da aka kwana uku kafin ya samu zuwa wajen Abdul.
Ya dauka zai hade rai daya ganshi ko ya canza Masa fuska sai ya samu akasin haka dan Abdul rungumeshi
yayi cikin tsananin farincikin ganinsa sai Kuma daya cika shi ya had'e rai Yana "Na manta fada muke dakai"
"Abokina Ina bukatar taimakon ka ka daina fushi dani dan Allah iya rama da bakin da na Kara ya Isa yasa ka
gane halin da nake ciki"
Abdul har a ransa yaji tausayin mahfuz.
Sai da yayi wanka ya siyo musu abinci Suka ci Suka koshi mahfuz ya tankwashe kafarsa cikin tsananin
damuwa kamar zaiyi kuka ya kwashe komai ya fada Masa da tsaka mai wuyan da ya shiga na tilasta masa
auren da Hadeeza ke san Yi har cikinsa da lubna ke d'auke dashi ya Kara da "Abokina na rasa yanda zanyi
da rayuwata yarinya nan ta zame min masifa da balai ta danna min tarko bansan yanda Zan fita ba"
"Mahfuz sai a yanzu na tabbatar da bakada wayo da lissafi ko na sile biyar, Kai a yanzu dan tace ma tana da
ciki zata tona ma asiri shine ka yarda zaka aureta har duk girmanka a haka ayi maka wayo?yarinya da take
runs maza sunfi hamsin da take muamalla dasu tazo tace ma ciki gareta Kuma naka ne sai ka yarda?idan
ma cikin naka ne kai sai ka yarda ka aureta macen da take bin maza ko karene zai Bata kudi zata iya binsa
wlh duk abinan mahfuz Kai ka jefa kanka a ciki abinka Sam ba class kana da mace irin lubna kaje kana bin
Hadeeza mai ka gani a jikin ta Banda rufewar Ido,har ta ringa rinjiyarka ko gudun cuta bakayi a gaskiya
kunyar lubna nakeji laifinka ya shafeni dan na Sha k'ok'arin kiranta a waya bana samun ta alamun tayi
blocking dina,kayi kuskure mahfuz,mai hakuri bai iya fushi ba nasan nima kaina laifinka ya shafeni ba lailai
yanzu na mata magana ta yarda dani ba zata dauka bakinmu daya da Kai"
"Ka taimaka min Abdul dan Allah a yanzu bansan ya zanyi ba har ga Allah bana san auren yarinya nan
burina kawai na yakice aurenta na cigaba da bawa lubna hakuri dan wlh a yanzu ko mutuwa Hadeeza
zatayi bazan Kara fadawa tarkonta ba"
"Yaushe zaku koma"?
"Gobe idan Allah ya kaimu"
"Tom ba damuwa jibi zanzo idan Allah ya yarda zanyi iya k'ok'arina Allah ya bamu ikon shawo kan lubna"
"Ngd abokina"
Daga nan suka hau hira a ranar kusan raba dare sukayi suna hira Abdul har sake gwada Kiran Lubna yayi stil
wayarta bata Shiga uku washegari karfe hud'u na yamma ya rakasu airport Suka tafi.
Lubna
Sabida mummy na danne bakin cikin da nake ji game da auren da akace mahfuz zaiyi banji a raina
kishinsa nake ba illa wulakanci da nake ganin yamin da cin fuska har gwara naji wata ya aura da ya auri
Hadeeza dan Hadeeza taci galaba akaina kenan.
Haka na daure duk da mummy ta sakoni gaba akan kishi ke dawainiya dani na watsar da makamai na ta
Kira mahfuz sai da na dage Mata ni ba Sansa nake ba ta kyalleni.
A Palo muke