Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
kawo ba idan Ahmad ya tambaya. Karfe goma saura
Ahmad ya shigo gidan daga Abuja, bayan Ramlah tayi welcoming dinsa ta kawo masa breakfast suna xaune
parlor yace "Jiddah ta je weekend gidan Umma halan?" Ramlah tace "Aa tana daki yanxu ma haka" Yace
"Islamiyyar fa?" Tace "She said she is having headache, bari in ce mata ka dawo" Daga haka ta mike ta
wuce dakin Jiddah, kwance ta ganta kan gado duk da tayi wanka ta shirya, Ramlah sae kallonta take ganin
kamar duk a tsorace take, Ramlah tace "Na xata bacci ma kike ai, baki karya ba fa, kuma Doctor ya dawo"
Jiddah ta mike xaune taki yarda suyi eye contact da Ramlah tace "Xan fito yanxu" Ramlah ta juya ta fita,
Jiddah ta sauka kan gadon ta dau Hijab dinta, sai da gabanta ya fadi jin kamshin da yake, ta ajiye ta bude
press ta dau wani sannan ta nufi kofa ta fita, xaunawa kasan carpet tayi ta gaishe da Ahmad ya amsa yace
"Ya ciwon kan?" Ta d'an yi murmushi tace "Yayi sauki yanxu, na sha magani" Yace "Maa sha Allah, kun
gama exams din?" Ta girgixa kai tace "Aa ranan Wednesday in sha Allah" Yace "Toh Allah ya taimaka" ta
amsa da Ameen, sannan ta mike ta wuce kitchen, Ramlah dae sae bin ta da ido take, tea kawai Jiddah ta
hada ta koma daki. Karfe sha biyu saura Ramlah ta shigo dakin Jiddah, Jiddah na xaune saman darduma
tana karatun qur'ani, Ta kai ayan karshe ta rufe Qur'anin ta d'an kalli Ramlah, ganin ta da mayafi tace "Fita
xa ku yi?" Ramlah tace "Ehh yana kiranki, kayayyakin ki Kuma na daya dakin fa na ajiye maki a ciki" Jiddah
tace "Aa ai ba nawa bane ni kadai" Mikewa tayi tunda dama da akwai Hijab a jikinta ta bi bayan Ramlah,
Ahmad na xaune parlor rike da car key dinsa yana kallonta yace "Are you going out with us now Jiddah?
Xan kai Captain airport" Jin sunan da ya kira sai da gaban Jiddah ya fadi sosai without thinking twice tace
"Aa karatu nake" Ramlah dai na tsaye bayan kujera tana kallonta, Ahmad yace "Tafiya xai yi fa, kuma xai
dau watanni bai dawo ba, kawai airport xa mu kai sa muyi sallama da shi mu dawo" Shiru tayi jin abinda
Ahmad yace, yana ci gaba da kallonta yace "Kije ki shirya mu tafi, ba komai ai, beside we are not staying
long" Bata kuma masa musu ba ta juya a hankali ta koma daki, Ramlah ta bi ta da kallo, Ahmad yana
murmushi yace "Why are u looking at her that way Baby?" Ramlah ta d'an yi murmushi bata ce masa
komai ba, Hijab kawai Jiddah ta canxa ta dau nikab dinta dake a goge ta saka hakan kadai ne xai iya sa ta bi
su kai Abuturrab airport, jakarta ta dauka ta rataye a shoulder sannan ta fito parlor, Dariya Ahmad yyi
ganinta yace "Tohh yau kuma nikab xa a sa kenan" Jiddah dai bata ce masa komai ba tayi murmushi daga
cikin nikab din, a haka duk suka fita gidan, back seat ta shiga... hira Ahmad da Ramlah ke yi har suka iso
kofar gidan Abuturrab, Ahmad ya dau wayarsa ya shiga kiransa, ba a dau lkci ba ya daga, Ahmad yace "I am
outside ka fito...." Abuturrab yace "Sai karfe biyu jirgin xai tashi xuwa lagos, I can't sit all day at the airport,
ka gane?" Ahmad yace "Ohk wai sai kun fara xuwa lagos dama?" Abuturrab yace "Yeaa, amma ba mu xa
mu yi piloting xuwa lagos din ba ai" Ahmad yace "But u should have told me that since" Abuturrab yace "Is
there anything wrong idan kun shigo kun jira for just few hours?" Ahmad yace "Alright then" Daga haka ya
katse wayar ya kalli Ramlah yace "Mu shiga ciki" Ramlah ta bude motar ta sauka, tuni mood din jiddah ya
canxa, amma bata jira ace ta sauka ba, kuma bata nuna hakan a fuskarta ba, ta bude motar ita ma ta sauka
ta rufe, Kalle kallen layin ta fara yi, ganin karamin kiosk can farkon shigowa layin ta kalli Ahmad tace "Yaya
xan d'an siyo abu a kantin can" Ya kalli inda ta nuna masa yace "Me xa ki siya" Tace "Yanxu xan amso in
dawo yaya" daga haka ta nufi kantin da sauri, su kuma suka shiga gidan, Aneesah tayi welcoming din
Ramlah kamar xata hadiyeta don fara'a, tuni ta cikasu da lemo da kayan ciye ciye irinsu cake, cin cin, da
alkaki da Chef Salma ke mata ta ajiye a gida sbda bak'i, Shi dai Abuturrab na xaune parlon yana danna
wayarsa, bayan few minutes Ramlah ta kalli Ahmad tace "Bata shigo ba har yanxu fa Yaya" sae a sannan
Abuturrab ya daga kansa, Ahmad ya mike ya nufi kofa, Abuturrab na kallon Ramlah yace "Who?" Ramlah
tace "Jiddah, tare muke, tace xata siya abu a kanti kuma har yanxu shiru" Bai kuma cewa komai ba,
Aneesah ta wani ta6e baki ta koma kitchen tana kas kas da chewing gum a ranta kuwa cewa tayi gwara dai
kam da bata shigo din ba don xata yi danasanin shigowa, abinci ta fiddo a deep freezer don dumama
masu, Bayan some minutes Ahmad ya dawo yace "Har gun mai kantin naje, ba abinda ta siya wajensa, kila
tafiyarta tayi" Ramlah ta dinga kallonsa, sae kuma tace "Toh ba waya kuma balle a kirata" Shi dai Abuturrab
danna wayarsa kawai yake amma duk yana jin su, Ahmad yace "Da akwai makulli wajenta ne?" Ramlah
tace "Eh akwai spare key, tun ranan da na bata da xan je gida" Ahmad yace "Ohk better" Aneesah ta fito
daga kitchen tana washe baki tace "Na daura girki bari yayi sai in xubo maku Sis Ramlah" Ramlah tace
"Ayya da ma baki yi bothering kanki ba Aunty, mun ci abinci daga gida kafin mu fito" Aneesah ta 6ata fuska
tace "Aa wllh, ke da ko girkina baki ta6a ci ba, yau dai kam sae kin ci" Ramlah tayi murmushi tace "Toh
shkkn Anty" Hira suke ta yi a parlon banda Abuturrab dake danne dannen waya, bayan kusan minti ashirin
da xuwansu Ahmad ya kalli Aneesah yace "Dauko min car key xanje laundry in amso kayana ynxu" Tana
kallonsa da mamaki tace "Amma kace delivery xa ayi maka ai, and babu wani kayan da xaka bukata a ciki,
ko ka manta ne" yace "Noo na tuna akwai wani rigan sanyi da xan dauka a ciki" Tace "Toh ka kira su kawo
maka mana dole sai kayi wahalan driving kuma" Mikewa yyi ya wuce sama, shi dai Ahmad idonsa na kan tv
yana kallon wani program da ake yi, sai ga Abuturrab ya sakko da makullin motarsa, Ahmad yace "Mu je
can din tare" Abuturrab ya kallesa yace "No, ba sai ka wani wahala ba kai da xaka kai ni airport, i will be
back soon" mikewa Ahmad yyi yace "Mu je can din, babu damuwa" Ta gefen ido Abuturrab ya kallesa,
Aneesah tace "Haba doctor ga abinci can nace ya kusa nuna kuma kace xaka fita, don Allah ka tsaya ka ci,
don Allah Dr" Abuturrab yace "Kaga dama kai ma baka ta6a cin abincin amarya ba, kawai ka tsaya ka ci...
So u can rate her" Yana fadin haka ya amshe makullin motar Ahmad yace "Ba sai na tsaya warming mota
ba, i will go with ur car, and i will be back in d next 20 mins" daga haka ya fice daga parlon, Aneesah kuwa
sai lallaba Ahmad take ya tsaya ya ci girkinta yau daya dai... Abuturrab na fita kofar gida ya shiga motar
Ahmad ya bar layin, tafiyar minti kusan talatin yayi ya iso layin....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
It’s S.SQAURE COLLECTION ANNIVERSARY YAYY🎊🎉
Jama’a gawata gagarumar sanarwa ku gyara zama kuji.
S.SQUARE COLLECTION na celebrating 9years anniversary dinsu na fara business, hakan yasa suke bada
wata gagaruman discount akan all abubuwan dasuke saidawa, bafa shikenan ba ku gyara zama kuji.
A shagon S.SQAURE COLLECTION zaki samu abubuwa da dama kaman haka;
Hadaddun dinkakkun Gowns wato dogayen riguna.
Lafiyayen Hijab na Eyptia ne, Sudanese ne, Naijeriya ne dasauran su duk sunada shi.
To ina masu baki achan achan irin mu gafa namu nan.
S.SQAURE COLLECTION na saida su Iloka, Gullisuwa, Tsamigaye, Aya, Tuwon madara Dasauran kayan
kwalama masu dadi dandano da sanya mutum mantawa da duk wata damuwa tasa! Hehehe badai kun
fara gajiya ba danfa ba anan kadai S.SQUARE COLLECTION suka tsaya ba.
Ina matan kamshi dasu Anty turare S.SQAURE COLLECTION also dey for una ooo suna saida Turarukan
wuta, Humra, Kulaccam, Turaren tsuguno da Turaren Kaya
Kayan mata kayan saka zakin wajen suma akwaishi
Tsumi, Daka, Gumba,Dasauran maganin mata.
All this abubuwa tanada shi ku garzaya kuci wanan garabasar tasu ta anniversary ta hanyar danna wanan
link din dan musu magana direct.
wa.me/+2347030037697
Parking yayi ya sauka yana kallon mai gadi dake xaune a waje, wanda har ya mike xai bude gate a
tunaninsa Ahmad ne sai ya ga akasin haka, suka gaisa Abuturrab ya shafa kansa yace "Suna ciki?" Yace "Aa
gaskiya basu jima da fita ba" Yace "Ba kowa a ciki yanxu?" Mai gadin yace "Babu kowa, ko awa daya basu yi
da fita ba Yallabai" Abuturrab ya tsaya kallonsa, Mai gadin na washe baki yace "Da na ga motar ma na xata
su ne ai" Abuturrab yace "Ohk, shkkn ba ma sai kace masu na xo ba... Sai anjima" Daga haka ya koma
motarsa ya shiga, a hankali yake driving din... Parking yayi ya jinginar da kansa da kujera, bayan few
seconds ya dau jotter a cikin motarsa da biro, ya cire pieces daya a ciki, kan steering ya ajiye takardan ya
fara rubutu a jiki, bayan some minutes ya gama rubuta abinda xai rubuta ya maida biron sannan ya linke
takardan gently, ya kashe motar ya sauka ya shiga cikin gidan, knocking yyi jin kofar a kulle, cikin minti
kadan Maimoon ta bude kofar, matsawa tayi tana kallonsa daga sama har kasa, lkci daya ya daure fuska, ta
xaro ido tace "Au, sannu da xuwa yaya" Da sauri ta juya ta koma parlon, Umma dake xaune Jiddah ma na
xaune kasa daga kusa da ita ta daga kai tana kallonsa, tunda Jiddah ta kallesa sau daya ta sunkuyar da
kanta, Ya karasa parlon ya xauna yana kallon Umma yace "Ina yini Umma" Tace "Lafiya lau, aka ce yau xaka
yi tafiyar?" Yace "Ehh in sha Allah..." Sai kuma ya shafa kansa yace "Naga ban xo mun yi sallama bane"
Umma tace "Bayan wanda mu ka yi a gidan Yaya?" Ya sunkuyar da kansa, Maimoon dai na tsaye sai
kallonsa take, idan ta kallesa sai ta kalli Jiddah da taki dago kanta sai wasa da fingers dinta take, Umma
tace "Toh ki kawo masa ruwa Maimoon" Maimoon tace "To Umma..." Har ta kai bakin kofar kitchen din ta
tsaya tana kallon Jiddah tace "Jiddoh xan xuba moringa din yanxu, ki xo ki gani" Jiddah ta d'an kalleta,
Umma tace "Ba kince kina son koya ba, ki tashi ki je" Mikewa Jiddah tayi ta wuce kitchen din, da gefen ido
ya bi ta da kallo a sace yanda Umma ma baxata sani ba, Umma tace "Amma daxu mun yi waya da Ahmad
yace xai je kai ka airport..." yace "Ehh Umma, xan koma yanxu.. nan da awa daya da rabi ne flight din"
Umma tace "Toh Allah ubangiji ya tsare, ya kai ku lafiya ya dawo da ku lfya" Yace "Ameen" Jiddah na
shigowa kitchen Maimoon ta kulle tana kallonta tace "Kawai sai naga yaya Aliyu, alhalin for almost 2 weeks
bai xo gidan nan ba" Jiddah ta hade rai tace "Toh me yasa kike gaya min?" Dariya Maimoon tayi har da tafe
hannu tace "Aa ni fa kawai hira nake maki wllh..." Jiddah ta juya xata fita Maimoon ta rikota tana dariya
tace "Ke wllh ni kawai jajantawa nake son mu yi da ke" Jiddah tace "Ki sakeni fita xan yi" Maimoon tace
"Dallah ki tsaya in hada miyan tukunna, to meye don nace kawai sai ga yaya Aliyu, au ni na ma xata Safiyya
ce nake maki wannan maganan, abinda mun saba gulman mu haka, amma ke kina so ki min wata fassara"
Jiddah dai bata ce komai ba sai kallon miyan dake saman gas take, Maimoon ta tafi ta dau ruwa da coke ta
daura kan tray ta dawo tana kallon Jiddah ta mika mata tace "Don Allah ki kai masa kar miyan ya kone" Da
sauri Jiddah ta matsa ta tafi gun miyan tace "Bar min miyan xan dinga dubawa kije ki dawo" Maimoon ta
hade rai tace "Kika san me xan ma miyan to?? Ni wllh wani lokacin kina bani mamaki, meye a ciki kawai dai
kije ki dungurar masa da tray din a gabansa ki taho, wllh ba don miyan ba ni da kaina xan kai, ai ni aka sa
ba ke ba" Maimoon ta d'an yi tsaki ta ajiye tray din tace "Haba, sai kace warce nace ki kai ma wani dodo
ruwan sha" Gun miyan ta tafi tana juyawa, sai kuma ta nufi kofa a tunanin Jiddah daukan ruwan xata yi ta
kai masa, sai taga bata dauka ba, Maimoon na fita parlor ta kullo kofar kitchen din tana kallon Umma tace
"Umma wai Aunty Malika na ta kiranki, kamar wayarki na daki koh?" Umma tace "Ta kira ki ne?" Maimoon
na d'an rawan baki tace "Haka dai tace min" Mikewa Umma tayi ta nufi hanyar dakinta tana cewa "To ai
wayar na daki" Maimoon ta koma kitchen da sauri tana ci gaba da juye juyen miya bayan gas din ma a
kashe yake tace "Kawai minti nawa kin kai ruwa kin dawo, idan ba dai da akwai wani abu a ranki da kike
boye ma mutane ba" Jiddah dai bata ce komai ba sai kallon tray din take, Maimoon banda satan kallonta
babu abinda take, daukan tray din Jiddah tayi daga karshe ta nufi kofa tana tafiya kamar bata son yi, ta
bude ta fita, sai da ta shigo parlor taga Umma bata nan, ta fara kalle kalle, yana ganin haka ya mike, ta
dungurar da ruwan kamar yanda Maimoon tace, xata juya yyi saurin kamo hannunta, ta juya ta marairaice
masa murya kasa kasa tace "Wllh xan maka ihu ka sakeni, ka daina min abun nn da kake yi bana so" jan
hancinta yayi har sai da ta ji xafi sannan ya saka mata takardan hannunsa a tafin hannunta yana kallon
kwayar idonta, fixge hannunta tayi daga rikon da yayi mata kusan a guje tayi hanyar dakin amma takardan
da ya bata na hannunta har sannan, ya bi ta da kallo kafin ya juya, ido hudu suka yi da Maimoon da ta d'an
bude kofar kitchen din tana lekosu, ai da sauri ta yi jamming kofar bayan sun hada ido, yayi hanyar kitchen
din, saura kadan ta tunkude miyan kan gas din bayan ya shigo kitchen din, sai xare katon idonta take tace
"Xa a xubo maka abincin ne Yaya?" Janyo hannunta yayi yace "Ba dai kin iya munafurci ba??" a gigice tace
"Don girman Allah kayi hakuri yaya, naje kulle kofa ne sai ka gan ni..." Bai saurareta ba ya bude kofar
kitchen din ya fita yana rike da hannunta.... Umma ce ta fito parlor tace "Au, tafiya yayi shashashan?" Babu
kowa parlon balle a bata amsa, Ta wuce dakinsu Jiddah taga Jiddah kadai a dakin tace "Aliyun ya tafi ne?"
Jiddah tace "Ina daki ban sani ba" Umma tace "Toh ga shi ki amso min kati na dubu daya a waje" Jiddah ta
d'an xaro ido amma bata ce komai ba ta amshi kudin gabanta na faduwa, Umma na fita dakin ta saka hijab
dinta ta fita ita ma, duk jikinta a sanyaye ta fita compound, tana isa gate ta leka waje ta ga motar Ahmad
instead, amma Abuturrab ne a ciki Maimoon na tsaye daga window din kusa da shi ta daddage tana cewa
"Ni dai wllh ka tura yanxu kafin ka tafi yaya, haka kawai idan ka je ka manta bayan na sanka da mantuwa,
kawai bari in kira maka account number din ai yana kai na" Ko kallonsu Jiddah bata sake yi ba ta nufi kantin
da xata amso kati, Abuturrab na danna wayarsa yace "Call the account number" tana washe baki ta shiga
kira masa account number dinta har ta gama, snn ta fara kallon wayarta dake hannunta tana murmushi,
cikin few seconds sai ga alert, ta duba da sauri taga dubu hamsin, wani tsalle ta doka tana tafe hannu
sannan tayi masa blow din kisses tace "Nagode sosai yayana, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara maka
budi, Allah ya kai mana kai lafiya ya dawo da kai lafiya" Komawa baya tayi ganin ya tada motarsa tana daga
masa hannu har ya bar layin, baki har kunne ta shige cikin gida, Jiddah ma ta shiga gidan don duk tana
kallon abinda Maimoon take a titi.... Dakin Umma jiddah ta tafi ta kai mata katin sannan ta fito ta shiga
nasu dakin, gaban madubi ta tafi ta dau takardan da ta ajiye bayan ta shigo dakin daxu, daukan takardan
tayi ta shiga warwarewa, haka kawai ta ji gabanta na faduwa, ganin ta kusa gama budesa ta rufe idonta, sai
da ta warware gaba daya sannan ta bude idonta a hankali tana kallon content din takardan gabanta na
faduwa, "Ni ba matarsa ba, ni ba muharramarsa ba... amma yake min wasu abubuwa da bai dace ba a
addininmu, bayan duk wani da yasan karatun addinin nan namu yasan haramcin yin abinda yake yi, ya
kuma san hukuncin wanda ya aikata hakan, kullum tunanina wanda xan kai ma kararsa... ya takura ni, ya
takura ma rayuwata bayan kuma ya sakeni kowa kuma ya shaida ya sakeni....." Boldly daga kasan rubutun
aka rubuta "Ur mentality Jidderh!!! And I know u might be questioning my fate, amma ki saka a ranki ba
dai dai kike da sauran yan matan da ke gaban iyayensu ba yanxu, you ain't of the same level with them...
abu kadan xa ki yi Allah yayi fushi da ke! ... no doubt na fi ki sanin addininmu, limit ur interaction with
MALE, limit ur going out, and by so doing, u are respecting ur religion" Jiddah ta karanta content din
takardan nan yayi sau biyar amma ba abinda ta gane, da ta dauko hanyar ganewa sai abun ya ruguje kan ta
kai karshe, a hankali ta linke takardan ta yaga, sai da tayi masa pieces sannan ta tafi ta bude window ta
watsar, Maimoon ta shigo dakin ta ajiye wayarta gaban mirror tace "Ke bikin kawar nan tawa fa sati me
xuwa ne, ina ta son in kira Aunty Ramlah ince ta baki waya in gaya maki muna da biki, kuma ba karamin
casu xa ayi ba, hope kun gama exams before then?" Jiddah ta