Advertisements
Chapter 33 Reading Jeedderhh by Khaleesat Haiydar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jeedderhh by Khaleesat Haiydar

Author :  Khaleesat Haiydar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   33 / 108

96K to 99K   out of 321.7K words

parlon, durkusawa tayi nan parlor ta
fara kuka kamar an aikota, kallon hanyar kitchen din yayi yaji muryar Aunty tana cewa "Sai yanxu na ke
sake yarda cewar da gangan yayi komai da ya faru, har sabida ke xai walakanta min Aneesah, to in dai nice
wllh xai sha mamaki, ba mu xai kawo ma gayyar tsiya family ba..." Karasawa yayi gun Jiddah ya dagota,
kuka kawai take ya kakkabe jikinta ya kama hannunta suka fita parlon, nan balcony ta saka takalminta
sannan suka fita compound xuwa gun motarsa, har suka bar layin kuka take kamar xata shide, ya hade rai
yace "Ya isheki haka nan, me yasa baki tsaya kitchen din kin mata kukan sosai ba?" Bata ce komai ba ta
hade kanta da gwiwa tana shessheka, har suka isa gida hawaye na xuba idonta, bayan yyi parking yana
kallonta yace "Baki ji ki daina kukan ba?" Ta dago kai cikin rawan murya tace "Ce min tayi wai muna yin
iskanci fa" Ya dinga kallonta kafin yace "Da wa ku ke yin iskancin" Cikin kuka tace "Wai kai" Dauke kai yayi
da farko, can ya juyo yace "Ai ban san wani irin iskanci take nufi ba" Tana hawaye tace "Tace iskanci muke
yi da kai a gida" Ya buda ido sosai yace "Toh fa, ni iskancin da na sani shine ace mutum bashi da kirki ko
baya jin maganan mutane..." Da sauri Jiddah tace "Ba shi bane" Yana kallonta yace "Toh wanne ne?" Cikin
rawar murya tace "Kilan ta xata kana ta6a ni" kallonta ya dinga yi, can ya kai hannunsa ya kamo nata yana
caressing dinsa gently yace "Haka take tunani?" Da sauri Jiddah ta janye hannunta ta saida kukan tana
kallonsa, ya daga kafada yace "Don an kama hannun mutum shine iskanci?" Ta girgixa kai tace "Tayi
tunanin muna kwana a daki daya" Yace "A kano ba a daki daya muka kwana ba? Sai ace wannan iskanci
ne" wasu hawayen suka sauko mata tace "Aa ba haka ba" Yace "Toh ya ne?" Tana goge idonta tace "Tana
tunanin muna kwana waje daya" Yace "Toh me ake yi idan an kwana waje daya da ake kiransa da iskanci"
Kin cewa komai tayi, ya bude motar ya sauka, ya nufi cikin gidan, bude motar tayi ita ma ta bi bayansa tana
goge idonta, Tun da ta shiga dakinta bata fito ba har bayan isha, ita iskancin da Aunty tace take yi ne ya
tsaya mata har da ce mata karuwa, wanka kawai tayi tasa rigar baccinta ta shige cikin duvet da ta tuna sai
taji hawaye ya taho mata. Karfe tara ya bude kofar dakinta, duk da tana ji bata motsa ba, ya isa inda take
ya bude bargon, suka hada ido hawaye ya gani idonta, yace "Ohk kukan kike yi har yanxu kenan" ta gyada
masa kai wasu hawayen na taruwa idonta, yace "Saboda ance kina iskanci kike kuka har yanxu" ta mike
xaune ta hade kanta da gwiwa tace "Toh ni ae ban ta6a iskanci da kowa ba" yana kallonta yace "Toh ae
gwara kawai kiyi ki san kinyi ko?" ta dago kanta da sauri tana kallonsa, ya rungume hannunsa shi ma yana
kallonta, tace "Inyi iskanci fa kace" yace "Ehh, ko hakan xai sa abun ya daina damunki, kinga kinsan kinyi
kenan ko an fada baxai maki ciwo ba" Ta wani ja gefe daya ta hade rai tace "Allah ya kiyaye ni ba yar iska
bace" Dariya ta basa, amma bai yi ba, yace "Amma ko jiya kin kama hannuna ai" da sauri ta juyo a tsorace
tace "Ni??" Yace "Ehh" ta hade rai ta hararesa tace "Ni ban ta6a haka ba wllh" karasawa yayi daya side din
da take yace "Ni kike harara haka?" Saukowa tayi da sauri ganin ynda ya hade rai tace "Ni ban harareka ba
wllh" Ya fixgo hannunta tana ganin haka ta rufe fuskarta a jikinsa tace "Don Allah kayi hakuri ni ban harare
ka ba" daga sama har kasa yake kallonta, ya d'an rufe ido sae kuma ya rungumeta tightly to himself yace
"Yanxu me ake kiran wannan?" Kwace kanta take son yi amma ta kasa yana jin ynda xuciyarta ke bugawa
kamar yanda nasa ma ke bugawa, lkci daya kuma ya saketa, ta juya da sauri ta bar wajen, a mugun tsorace
ta juyo tana kallonsa, ba tare da ya kalleta ba yace "Kinga maganar Aunty ya fito, don haka idan tace kina
iskanci kada ki sake damun kanki tunda gashi har rungumeni kika yi ynxu, ko bayan wannan akwai wani
abu da ake kira iskanci?" Juya masa baya tayi xuciyarta na bugawa sosai, daga sama har kasa ya dinga
kallonta, riga ne da wando red color na bacci a jikinta rigar ce kadai barrier din skin dinta, dauke idonsa yyi
ya nufi kofa ba tare da ya kalleta ba yace "Ki sakko kasa ki dau abincin ki, kuma kar ki yrda in dawo baki
sakko ba" daga haka ya fita, ta bi sa da kallo har sannan xuciyarta na bugawa, bayan kusa minti goma sbda
tsoron kada ya dawo kamar yanda yace, ta dau Hijab dinta a sanyaye ta saka har kasa sannan ta sauka,
kanta a kasa ta shigo parlon, ta durkusa jikin kujera taki kallonsa a hankali tace "Ni ba yunwa nake ji ba,
naci abinci a can gidan" Yace "Koh?" Bata ce komai ba, kuma bata dago kanta ba, ganin ya mike ita ma ta
mike da sauri tana kallonsa, da alamar ta tsorata da shi, dariya ta basa amma ya fuske yace "Ohk, da ni
mijinki ne haka xaki dinga yi idan na ta6a ki??" Ta kasa ce masa komai, yace "Ki bani amsa" Ba tare da ta
kallesa ba tace "Toh ai kai ba mijina bane" Kallonta kawai yake yi, can yace "Toh amma mijin na ki baxa ki
dinga yi masa haka ba ko" A takaice tace "Nima ban sani ba" yace "Dauki abincin ki" tace "Na koshi" yace
"To tafi" juyawa tayi ta wuce sama, ya bi ta da kallo, xaunawa yyi ya jinginar da kansa jikin kujera, daga
karshe ya dau wayarsa ya kashe wutan parlon ya wuce sama xuwa bangarensa ya kwanta, Aneesah ya
shiga kira, sai da ya kusa katsewa ta daga amma bata ce komai ba, yyi lumshe ido yyi kasa da murya yace "I
know i did what is uncalled for, but... I hope u aren't among d set of pple that believe ban saketa ba ko?"
Tace "How will i believe you Aliyu bayan abinda ka min a kanta jiya?" Ya kwantar da murya yace "What if
na auroki kika shigo gidan kika gani ma idonki cewar ba matata bace?" Tace "Then i will believe u 100%"
Yace "Ranan juma'ah daurin auren Ahmad, kafin uncles dinmu su koma xa a kawo gaisuwa da kudin saka
ranan gidanku ranan lahadi in sha Allah" Kamar xata yi kuka tace "Are you for real Aliyu?" Yace "Sure" Farin
cikin da Aneesah tayi a lkcn baya misaltuwa, lkci daya duk ta mance abinda Aliyu yayi mata jiya, amidst d
joy yace "I am missing you seriously, vid call?" Tace "Sure, amma kar ka wani kashe wuta" yace "I have to"
bai jira cewarta ba ya katse wayar ya kashe switch din dake kusa da gado sannan ya shiga kiranta vid call....
Washegari Abuturrab na dawowa masallaci ko azkar bai tsaya yayi ba ya dawo gida a stairs suka kusa cin
karo da Jiddah xata sauka kitchen, da sauri ta juya masa baya don bata sa hijab ba, bata yi xaton
shigowarsa a lkcn ba, ta koma sama da sauri ta shiga dakinta, bangarensa ya nufa ya shiga daki ya kashe
wuta ya kwanta. Kiran Ummi ne ya tashesa wajen karfe takwas da rabi, ya jawo wayar a hankali ya daga
coz she's been calling him since yesterday har ma da Aunty, ya kai kunne hade da sallama, Ummi tace
"Don walakanci Jiya ka dawo ka tafi da Jiddah babu sallama??" Ya mike xaune da sauri yace "Ummi yau xan
kawota dama, bak'i nayi a gida..." ummi tace "Good!!!Abbanka na nemanka, kuma ka taho tare da Jiddar,
ba jiran ka xai yi ba, karfe goma xai fita yace" Daga haka ta katse wayar, sosai ya ji gabansa ya fadi, Abba
calling him for what? Kallon agogo ya sake yi sannan ya ajiye wayar ya lumshe idonsa yana jin xuciyarsa na
bugawa, bayan minti goma ya mike ya shiga bathroom. Tara da minti goma ya fito daga bangarensa cikin
kananun kaya, ya tsaya bakin kofar jiddah for some seconds kafin ya bude kofar a hankali, gyaran daki ya
sameta tana yi, ta sunkuyar da kai, ganin ta shirya yace "Dauko hijab din ki" Daga haka ya juya ya fita,
karasa gyaran dakin tayi sannan ta sa hijab din ta fito. Throughout the ride hankalinsa baya jikinsa, sai da
yaga sun kusa gidan ya kalleta rasa abinda xae ce mata yyi har suka shiga gidan, parlon Abba ya nufa direct
tana biye da shi a baya, yana sallama aka yi masa izinin shigowa, shi ya fara shiga sannan ta shiga, Aunty na
xaune parlon tare da Ummi da Umma, kamar dai xuwansu ake jira, ya ji gabansa ya fadi sosai, xaunawa yyi
kasa, jiddah ta xauna side dinsa a hankali, ita ta fara gaishesu cikin sanyin murya sannan shi ma ya
gaishesu, Abba gaisuwanta kawai ya amsa, yana kallon Abuturrab babu yabo babu fallasa yace "For how
long have u divorced her Aliyu??"


Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last
bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd
getting rid of any skin problems

Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta
samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar
rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata
masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda
zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada

Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240
Abuturrab ya buda ido sosai yana kallon Abbansa gabansa na faduwa yace "Divorce kuma Abba?? Why will
i do so bayan kayi instructing dina kar inyi haka? Ni ban saketa ba Abba ga ta ka tambayeta, idan na saketa
ae baxa mu xauna tare ba.. " Ba Aunty da ta bude baki tana kallonsa ba, har Jiddah kallonsa take da
mamaki, Ummi dai wani direction din daban take kallo, Umma kam duk jikinta a sanyaye yake jin batun
nan da ya tasheta da sassafe, Abba kansa ya kasa cewa komai, Aunty ta saki salati tace "Yaushe ka fara
karya Abuturrab? Yaushe ka dawo makaryaci? Bakina da naka kace min ka saki yarinyar nan tun ranan da
ku ka tare shine xaka karyata ni yanxu a nan?" Ya girgixa kai a hankali yace "Ban karyata ki ba Aunty, kawai
na gaya maki haka ne saboda hankalinki ya kwanta tunda naga baki son auren, amma ni ban saketa ba,
bana son abinda xai sa ki dinga damun kanki shi yasa na fada maki haka" Bude baki tayi tana kallonsa, yayi
kasa da murya yace "Abba ga ta nan ku tambayeta ni ban saketa ba, I'm saying nothing but the truth"
Jiddah ta sunkuyar da kanta daga kallon da take masa duk jikinta yayi sanyi, Abba kam ya ma rasa abun
cewa, Can Ummi na kallon Jiddah tace "Jiddah" dago kai Jiddah tayi ta kalleta, Ummi tace "Ki fada min
gaskiya Jiddah, Aliyu mijinki ne a yanxu ko ba mijin ki bane?" Gabanta ya dinga faduwa taji hawaye ya
kawo idonta, Abuturrab ya gyara xamansa shi ma gabansa na faduwa sai dai bai kalleta ba, a hankali tace
"Mijina ne Ummi" Aunty taji kamar ta rusa ihu a wajen lkci daya idonta yayi jajir, Abuturrab ya sauke wani
boyayyen ajiyar xuciyar relieve, Abba yace "Shkkn, Allah ya rufa asiri, u can leave now Aliyu" Abuturrab ya
mike ba tare da ya kallesu ba yayi masu sallama, ita ma ta tashi ta sallamesu sannan ta bi bayansa tana
goge hawayen idonta, Umma ta bi su da kallo xuciyarta na kokwanton amsan da Jiddah ta ba yar uwarta,
this isn't joking matter, she needs to investigate deep into this issue... Aunty ma ta bi su da wani kallo sai
kawai ta saki kuka kamar warce aka sanar ma sakon mutuwa, ita Abuturrab xai yaudara, ita xai karyata, ita
xai watsa ma kasa a ido, ita xai kunyata gaban kowa?? Ko minti daya Abuturrab bai kara a a gidan nasu ba
ya wuce da Jiddah, bai ce mata komai ba ita ma haka har suka iso gida bayan ya siyo masu abinci a hanya,
parking yyi a compound dinsa, sai da ya sauka sannan ita ma ta sauka motar, ya mika mata ledan abincinta
yana kallonta, kin amsa tayi hakan yasa yyi wucewarsa ciki da ledan ya bar ta tsaye a wajen, xaunawa yyi
kan kujera a parlor ya jinginar da kansa da kujeran ya sauke ajiyar xuciya feeling relieved, sai bayan kusan
minti sha biyar ta shigo parlon, xata wuce sama yace "Xo nan" Ta ki tsayawa har ta wuce, ya bude baki
yana bin ta da kallo. Through out ranan jiddah na daki shi kuma yana downstairs, bai bi ta kanta ba har
after isha, bayan ya dawo mosque ya dai ga alamar tayi making tea a kitchen, yana haurawa sama ya tsaya
kofar dakinta sai kuma ya bude slowly, xaune ya ganta idonta yyi ja, ya kulle kofar dakin yana kallonta, yace
"An maki wani abu ne kike ma mutane kuka tun safe?" Ta ki kallonsa, a d'an tsawace yace "Ba magana
nake maki ba?" Ta juya masa baya, rungume hannu yyi yana kallonta, can yace "Kuka kike saboda kina
tunanin kinyi musu karya?" Ta juyo tana kallonsa cikin rawan murya tace "Ehh mana, me yasa xa ka masu
karya??" Yace "Ohh da na masu sai nace ke ma kiyi masu??" Kallonsa ta dinga yi ko kiftawa babu, ya karasa
ya tsaya gabanta yana kallonta da kyau yace "Ni ai ban aike ki kiyi masu karya ba... sannan akwai wani abu
na musamman da ke sa mutane su yarda cewar mata da mijinta ne ke rayuwa a cikin gida? akwai wani
abun da xanyi da xai tabbatar da cewar ni da ke mata da miji ne? Ko bana ciyar da ke yanda miji ke ciyar da
matarsa ne? Ban baki sutura ba? ban baki wajen kwana ba? ban baki kariya ba? Ina ce duk wannan shine
abinda miji ke ma matarsa? Ko akwai wani abu daban da ban sani ba ki sanar da ni nima in maki don
xaman namu yayi kama da na mata da miji a daina xargin mu..." ta dauke kanta tace "Idan mun yaudari
mutane ai Allah shi yasan gaskiya, kuma ai kai ma kasan ni ba matarka bace nima kuma nasan kai ba mijina
bane" Kallonta kawai yake yace "Toh meye shaidan hakan?" Tace "Ai kai ma kasani, meyasa baxa ka fada
masu gaskiya ba, sannan ni ka bani takardan in ajiye wajena tunda baka aikeni inyi karya ba" durkusawa yyi
yana kallonta yace "Haba?" Tace "Ehh" yace "Toh ko dai in fara maki abinda masu aure ke yi, kilan hakan
xai sa ki fara rage tunanin ai ni ba mijin ki bane, infact mancewa ma xaki yi cewar babu aure tsakaninmu,
takarda kuma da kika ce... Mu je in baki ki ajiye wajen ki" mikewa yayi still yana kallonta, ta k'i tashi, ya
hade rai yace "Mu je ki amsa nace" mikewa tayi a hankali, ya nufi kofa ta bi bayansa xuwa bangarensa,
suna isa ta tsaya bakin kofar babban parlon, ganin bata shigo ba yace "A bakin kofa xan baki takardan?"
Shigowa parlon tayi taga ya nufi bedroom dinsa yana isa ya tsaya bakin kofa ganin bata karaso ba yace
"Shigowa xa kiyi ai malama" daga haka ya shiga cikin dakin, a hankali ta bi bayansa tana shiga ya kulle
kofar, ta makale jikin bango tana kallonsa, sanyi sosai ne a dakin sbda Ac dake aiki, ya nufi gaban mirrow ya
dau diary dinsa ya bude sai ga takarda well folded ya ciro a ciki yana kallonta ya mika mata yace "Gashi" Ta
sauke kanta kasa kamar baxata je ba sai kuma ta karasa ta sa hannu xata amshi takardan ya fixgota, kara
tayi a tsorace ta fara kokarin kwace kanta, yace "Saboda ina tsoronki xan baki? And.. ina ruwanki da rashin
auren dake tsakaninmu, ci kika rasa ko sha??" Gaba daya a tsorace take, kamar xata yi kuka tace "Kayi
hakuri don Allah...." Yace "Baxan yi ba" a hankali ta daga kai ta kallesa, saketa yyi ya tafi gaban madubi ya
ajiye takardan sannan yace "Idan kin isa ki dauka ki fita" Yana fadin haka ya nufi kofa ya bude ya fita ta bi
sa da kallo har ya kulle kofar, a hankali ta isa gaban madubin ta dau takardan ta warware tana dubawa,
takardan ne kuwa, in accord to the content of d paper, he is no longer her husband, duba diary din tayi
taga ba a ciki ya falli takardan da yayi rubutun ba, wajen mirror din ta dinga dubawa nan taga takardan da
ya cira a ciki, ita ma ta cira sannan ta mayar da sauri ta ajiye, linkewa tayi yanda ya linke na rubutun ta ajiye
gaban madubin sannnan ta dau wanda rubutu ke jiki tana tunanin inda xata boye, kana ganinta kasan a
tsorace take, hularta ta saka hannu ciki taji gashinta is very oily, ta sake ciran wani sabon takardan ta
nannade na rubutun a ciki sannan ta tusa a cikin hulan ta koma inda take tsaye ta tsaya, bayan kusan minti
goma sai ga shi ya shigo, sunkuyar da kanta tayi cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri baxan sake cewa ka
bani ba kuma" Bai ko kalleta ba, ya ajiye sauran bottle water din hannunsa, sannan yace "Aa ki dauka dai,
gashi can gaban madubin" Ta girgixa masa kai kawai, gun takardan ya nufa gabanta ya dinga faduwa tana
kallonsa ko kiftawa babu, ya dauka, bata jira taga me xai yi ba har ta juya xata fita da gudu taji yace "Gashi
ki tafi da shi" Juyowa tayi tana xare ido taga yana mika mata takardan, kallonta kawai yake, yace "Amsa
nace" Ta karasa a hankali ta sa hannu xata amsa ya murda kunnenta yace "Tahowa kika yi xa ki amsa
kenan" Bata fuska tayi bata dai ce komai ba, lkci daya taga yana bude takardan da gudu ta nufi kofa ta fice
daga dakin ya bi ta da kallo ganin babu komai a jikin takardan, mamaki

33 / 108