Advertisements
Chapter 89 Reading Jeedderhh by Khaleesat Haiydar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jeedderhh by Khaleesat Haiydar

Author :  Khaleesat Haiydar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   89 / 108

264K to 267K   out of 321.7K words

tace "Atoh shkkn, duk kai da mahaifiyarka xa
ku yi shaida ko gidan uban wa xa aje da kess din nan" Ali yayi ma Ummi sallama ya fita parlon, mikewa
Ummi tayi ta hade kan su Maimoon suka bar gidan tare da driver, bayan tafiyar su da mintuna kadan sai ga
Umma ta shigo babu ko sallama fuskar nan nata bbu yabo bbu fallasa ta jefar da jakanta saman kujera tace
"Me ke faruwa Hajja?" Hajja ta mike ta rushe da wani kuka tace "Hau sama ki gane ma idonki Ramlah, je ki
sama Ramlah..." Umma ta haura sama da sauri, tana arba da dakin Jiddah ta sauko tayi wani irin dariya
tace "Wllh wllh ban ga shegen da xai hanani daukan fansan abun nan ba, ban ga wanda ya isa hanani
daukan matakin da ya kamata ba, kuturin uba..." Tana kai wa nan ta figi jakanta ta nufi kofa kamar xata yi
tsuntsu tana huci, Hajja ta dau katon jakarta ta bi bayanta sum sum tace "Ni da nasan kan komai" Ummi ta
sauke boyayyen ajiyar xuciya ta kalli Abuturrab da kansa ke kasa tace "Aliyu" Dagowa yayi ya kalleta da
idanuwansa da suka koma kamar garwashi, shi dai ya san ba don mahaifiyarsa dake gidan nan yau ba babu
abinda xai hana shi yi ma Aneesah dukan tsiya wanda har sai ta suma, bai yi farin cikin kasancewar Ummi a
gidan ba wannan abun ya faru, Ummi tayi kasa da murya tace "Kayi hakuri Aliyu, kar ka yanke hukunci cikin
fushi, kuma ina umartanka duk hukuncin da xaka dauka banda saki...." ya marairaice mata yace "Ummi me
yasa xaki ce haka? To meye amfanin xama da ita Ummi? Wllh baxan iya ci gaba da xama da ita ba, ta fita
raina gaba daya, ko na xauna da ita ni nasan baxan kwatanta adalci tsakaninsu ba" Ummi tace "Xaka yi
Aliyu, now tell me meye amfanin sakin nata? Shkkn sbda saki abun banxa ne sai ku maida shi ado kai da
mahaifinka? Haba Aliyu, ni ban hanaka daukan duk matakin da xaka dauka ba amma kar ka saketa,
Alhmdlh abun ya tsaya iya kayan daki kuma ba komai ya ja tayi haka ba sai kishinka, da bata sonka kuma
baxata yi kishinka ba, kowacce mace da kalan nata kishin a xuciya, abinda tayi kuma yana nuni da how
frustrated she is, ba wai nace abu me kyau tayi ba Aliyu, dole dama xa a hukuntata, but plss do everything
except divorcing her, ko kadan bana son kalman nan ta saki, ban hanaka nuna mata bacin ranka ba amma
don Allah banda saki kayi hakuri ka ji, kaga ta dalilin wannan abinda ya faru kila Abban naka ya hakura ka
raba masu gida, sannan ina son tambayarka motar da ka siya su biyu ka siya ma ko yaya?" Ya kalli Ummi
yace "Kawai warce ta cancanci motar na siya ma Ummi" Ummi tayi shiru, sai kuma a hankali tace "Toh kai
ka tsokano bala'in kenan, wa yace maka ana haka? Idan Kyautatawa kake son yi ma daya a cikinsu sai dai
kayi shi a boye ba a sarari ba ai" Shiru yayi ba don maganan Umminsa na masa dadi ba, gashi baxai ta6a iya
cewa xai ce mata Aa ba, yanxu yana ji yana gani xata hanasa sakin Aneesah, jinginar da kansa yayi jikin
kujera yana jin xuciyarsa na tafarfasa, Ummi ta mike ta haura sama kofar dakin Aneesah ta tsaya ta
kwankwasa tace "Aneesah?" Sai da ta kwankwasa sau uku sannan Aneesah ta bude dakin, Ummi ta shiga
bedroom din nata ta kulle kofar tana kallonta, Aneesah ta koma ta ci gaba da xamanta a kan carpet
idanuwanta sunyi jajir ga yanyankewan da tayi a hannu bai fasa xuban jini ba, Ummi ta ja kujera ta xauna
tace "Me yasa kika aikata abinda kika aikata Aneesah" Kamar jira take ta fashe da wani matsanancin kuka
tace "Ummi tunda yayi auren nan yake walakanta ni yake ci min mutunci, ya fita harkata bai damu yayi
magana da ni ba, bai damu da halin da nake ciki ba, all he is after is his new wife..." kuka sosai take, Ummi
tace "Kuma a tunaninki fasa kayan dakin Jiddah da kika yi xae canxa komai ne?" Aneesah ta hade kai tana
kuka sosai, Ummi tace "Baki kyauta ba Aneesah, ko mahaukaci baxae aikata wannan abun da kika aikata
ba, yanxu meye amfanin hakan?" Aneesah dai kuka kawai take, Ummi tace "Yanxu baki tunanin abinda xae
je ya dawo wannan barnan da kika yi? Ko shi Aliyun kina ganin kyaleki xai yi da ba don ina gidan nan ba
yau? Balle warce Jiddah ke hannunta?" Shiru Aneesah tayi tana share idonta, Ummi tace "Tashi mu je
parlor" Tashi tayi ta dau hijab dinta ta saka tana hawaye ta bi bayan Ummi, suna saukowa downstairs, suka
shiga parlon, kafin Ummi tace komai ta durkusa gaban Abuturrab tana kuka sosai tace "Don Allah kayi
hakuri Captain, wllh sharrin shaidan ne, I don't know what came over me, kayi hakuri ka yafe min..." Ji yayi
kamar ya haureta yana jin wani mugun tsanarta a xuciyarsa, ko ganinta bai son yi a sight dinsa wllh, ganin
kallon da Ummi ke masa ya dake yace "I have nothing to say in here, tunda ba kayana kika yi ma haka ba, u
wait for the consequence from the owners" Aneesah ta kalli Ummi, Ummi tace "Tashi" mikewa tayi Ummi
ta dau handbag dinta suka nufi kofa Aneesah na biye da ita, Abuturrab ya bi Aneesah da wani mugun kallo
har suka fita, he just can't keep on staying with her as his wife, ya tsaneta har ransa. Ko minti sha biyar
basu yi da fita ba sae ga Umma da yan sanda Hajja na biye da su sae cewa take "Da kafinta ya kamata a xo
don shegiyar ta garkame kofa tun daxu, shi ae jijjige kofar baxata masa wahala ba tunda aikinsa ne" Umma
ko kallon Abuturrab bata yi ba ta nufi sama yan sanda mata biyu na biye da ita, bayan wasu mintuna suka
sauko Umma na masa wani kallo yace "Ina take?" Abuturrab yace "Ummi ta fita da ita" da mamaki Umma
tace "Ummi??" Hajja ta saki wani salati ta rike kanta tace "Amma daga tambadadde sae Hauwa, ta fita da
ita ta kai ta ina? Kun dai ga jaraba ko?? Wato yanda Hafsah ta dinga gallaza mata taki barin a dau mataki
haka take so a dinga yi ma Jiddah sbda bakin hali da mugunta? To wllh baxata sabu ba, to wa ma ya sani ko
ita ta saka Aneesar ta aikata abinda ta aikata tunda har xata iya fitar da ita daga gidan? Kai jama'a, wa
Hauwa take so ta burge a nan? Ita a dole ta Allah wai ko? to Allah ya wadaran naka ya lalace dai.." Umma
ta fice da yan sandan xuciyarta na tafarfasa, Hajja ta bi bayanta tana cewa "Na gaji da Hauwa wllh, na gaji
da halinta, to wai uban wa xata burge ne ban gane ba, da kyar idan bbu hadin bakinta a wannan tsiyar da
Aneesah ta tafka, wato gwara ta hade kai da Aneesah a cuci Jiddah, ai kuwa xan nuna mata ni er banxa ce
wllh" Mikewa Abuturrab yayi ya wuce sama rai babu dadi, ko kadan bai son ya kwana da auren Aneesah a
kansa yau, Umma ta sallami yan sandan ta nufi gidan yayarta tare da Hajja, har sannan xuciyarta na
tafarfasa, ai wllh Aneesah bata ci bilis ba, sae dai idan canxa sunanta aka yi daga Ramlah.....



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




FZ BEAUTY SUPPLEMENTS
Dealer in all kind of dietary supplements such for skin whitening, skin glowing, weight gain, slimming, flat
tummy, infection killers, dark spots removers, fertility booster, Hips boosters, Breast firming and Enlarging,
Teeth whitening, eye, joint, stretch marks, and for marital pleasure. All supplement are available for
wholesale and retail. For more information contact FZ via wa.me/2348143821028

FZ Beauty Supplements
Dealer ce ta supplement masu qara fito da kyaun mace ko namiji, hadi da qarama garkuwar jiki kuzari.
Muna sayarda Supplemnt kamar na qarin duwawu, akwai wanda zaya taimaka wurin dawoda martabar
Nono, akwai na rage qiba da tumbi, akwai na rakwainuwa, akwai na tada komada, akwai masu saka hasken
fata da qyalli, akwai na infection, akwai na saka hasken ido da hakori sannan akwai na gyaran turaka. Muna
maraba da mai sayen daya ko sari. Wa.me/2348143821028



Ummi dake xaune parlor ta daga kai tana kallon Umma da Hajja da suka shigo parlon babu ko sallama
kamar an jefo su, Umma tace "Yaya na je can gidan na samu labari kin tafi da yarinyar nan Aneesah" Ummi
tace "Ehh ya aka yi?" Umma tace "Ban gane ya aka yi ba Yaya, kin kuwa je sama kin ga abinda ta aikata ma
kayan Jiddah?" Ummi tace "Na je, Allah kuma ya tsayar a nan Ramlah" Umma tace "Ba xancen kinje bane
yaya, dukiya ce ta walakanta haka fa?? Ba sato kudin wanda ya siya mata kayan yayi ba" Ummi tace "Toh ya
kike son ince Ramlah tunda dai abinda ya faru ya riga da ya faru sai ayi addu'an Allah ya tsare na gaba, ko
da abinda kike son ince da ya wuce wannan? shi mai gidan ne xai dau hukuncin da ya dace amma ba mu
ba, iyaka idan mun ga baxai yi adalci ba sai muyi involving kanmu" Hajja da ta kankance ido tana ta kallon
Ummi tace "Tabdii, ashe haka kike ban sani ba Hauwa? Ashe haka kike? Tun ranan alhamis nake ta baxa ido
Usman ya dawo in yi masa kaca kaca akan maganaganun da Hafsah ta min ranan a gidan Aliyu, sannan in
nuna iko na da isata ya rabu da ita na har abada don ta ci min mutunci ta xageni ta min rashin da'a, shine
kiri kiri yanxu kike nuna ma Jiddah bakin ciki kin je kin dauko kishiyarta mahaukaciya da tayi mata
axababben ta'adi kin xo kin boyeta, kawai muka kwashi kafa muka je da yan sanda kika kunyata mu a
gabansu?" Ummi tace "Hajja shi fa duniyar nan da muke ciki d'an hakuri ne, wata rana sai labari, sai a ga
kamar ba ayi ba wllh, meye riba don ka xuba ido an ci ma sa'ar er ka mace mutunci, 'ya yan nan fa muna
da su ta ko ina, kishin nan kuma halitta ce a xuciya sai dai na wani ya fi na wani, ko ince wani yayi na jahilci,
sannan abinda Aliyu yayi bai kyauta ba wllh in dai xancen gaskiya xa ayi, idan xai kyautata ma amaryarsa
don wani dalili na daban sai yayi sa cikin sirri ba a sarari ba, to what was he expecting dama idan ba tashin
hankali ba a gidan nasa yau, ke kuma Ramlah halan har yanxu yan sanda basu gaji da ganin fuskarki bane a
yankin nan? Komai kice yan sanda abu da xa ayi solving cikin gida sai ki kwasa ki kai ma yan sanda? Who
does that for God sake?" Hajja ta rike kai tace "Huhuhu Allah ya wadaran naka ya lalace, na kara tsoron
Hauwa, na tsorata da lamarinta!! waiiiiii Allah" Umma dake ta kallon Ummi babu ko kiftawa tace "Fine and
good, daga yanxu duk wani abu da ya shafi gidan Aliyu dama na cire hannuna in sha Allah" Ummi tace "Aa
gwara ki cire wllh da wannan sintirin gidan yan sandan dai, don wannan ba yi bane... kullum ana ganin yan
sanda na kai komo a gidansa, babu saiti ne abun?" Umma tace "Ai sai ki tsaya ki saurareni yaya, ban gama
ba" Ko kallonta Ummi bata yi ba, Umma tace "Amma kinga a kan lamarin Jiddah? Wllh babi wanda ya isa
ya sa in cire hannuna, sai inda karfina ya kare ba sani ba sabo, kuma wallahil azeem sai an biya aika aikan
nan da yar iskar tayi mata a daki, babu ruwana da wanda xai biya, kawai abinda na sani a mayar ma yarinya
da dakinta yanda yake, kuma wllh baxata koma gidan ba sai an canxa mata kayan dakinta dai dai da yanda
nayi mata" Hajja tace "Lallai... Toh da fa, ai babu tantama Hauwa ta aiki Nanisa tayi aika aikan da tayi, ko
rantsuwa nayi baxan yi kaffara ba, sannan Usman na dawo xan basa shawaran ya dawo da matarsa Hafsah
tun dai kishiyar abar dadi ce, kowa sai yayi ta fama da na shi" Ummi tayi murmushi tace "Kowa fa da
halinsa yake xaune Hajja, ni wllh bana mata bakin cikin dawowa dakinta, karya ce ke karewa ba dai gaskiya
ba..." Kwafa Hajja tayi ta nufi dakinta, Umma kuma ta fice daga gidan gaba daya.... Abuturrab na xaune
parlor tun bayan fitar su Umma, gaba daya good mood dinsa yau ya baci, hukuncin da xai ma Aneesah
kawai yake tunani, ga shi Ummi ta hanasa hukunci me kankat wato saki, abubuwan da ta dinga masa tun
farkon aurensu ne ke dawo masa da yanda ya sameta ba virgin ba, and he hate himself for everything, he
hate himself for being silent for that long babu wani hukunci da ya dace da ita banda ya rabu da ita na har
abada don ba canxa halinta xata yi ba, ba daina abubuwan da take yi xata yi ba, babu abinda yake basa
mamaki irin yanda ya iya xama da ita for this long duk da mugun kazantarta, a yanda ya ba ma tsafta
muhimmanci a rayuwarsa bai ci ace ya iya ci gaba da xama da Aneesah ba, kai bai ma ta6a xaton xai iya
rayuwa a inda kazanta yake ba, duk wa ennan tunanin suka hadu suka sa yaji inaa baxai iya rayuwa da ita a
matsayin mata ba, banda he was impatient tun xamansu na farko da Jiddah ya gano me tsafta ce sosai, bai
ta6a dawowa ya tarar da gidan ko jikinta ba dai dai ba, komai ya gwada mata a rananta na farko a gidan
yayi sinking a kanta, bude kofar parlon aka yi ya daga kai da sauri Umma ta shigo da Maimoon da wasu yan
mata biyu, ko kallonsa bata yi ba ta wuce sama su Maimoon na biye da ita, Maimoon sai boye hannunta
take cikin Hijab dinta, Abuturrab ya bi su da kallo har suka haura sama, next thing da ya fara ji shine fashe
fashe da tarwatse tarwatse a sama, ya jinginar da kansa da kujera sai kuma yayi murmushi, shi dai ko
motsawa bai yi ba har suka sauko kasa bayan minti talatin, Umma ta nufi kofa kamar boss su Maimoon na
biye da ita a baya, ko da wasa Maimoon bata yarda ta kalli inda Abuturrab yake ba, ya bi su da ido har suka
fita sannan ya mike ya haura sama, dakin Aneesah da ya gani a wangale ya nufa, ya tsaya bakin kofa yana
kallon yanda suka yi kwatsa kwatsa da dakin don har ya fi na Jiddah muni, har akwatunanta sai da suka
faffasa, ga show glass dinta me shegen tsada da aka kawo mata kwanan nan shima duk sun hallaka shi, ya
fi minti biyar tsaye kafin ya juya a hankali ya bar bakin kofar, yana tunanin dama haka auren mata biyun
yake? Shi ya xata a film kawai irin haka ke faruwa, so even in reality, reality din ma a gidansa, ya sauke wani
ajiyar xuciya shi dai baxai ce ya ji haushin su Umma ba ko kadan that serves Aneesah right, downstairs ya
koma ya ci gaba da xamansa a nan. Throughout ranan a dakin Ummi Aneesah ta yini, haka nan kawai taji
hankalinta ya kwanta sosai, ko ba komai ta samu saukin abinda xuciyarta ke mata tun shekaranjiya, ganin
idon Ummi ya sa duk aka kira sallah kafin a ajiye mic a masallaci xata tashi taje tayi alwala a bandaki, da
yake kafin su dawo gidan sai da Ummi ta kai ta chemist aka duba mata yankewan da tayi aka yi mata
alluran tetanus sannan aka bata drugs shi sa ta samu saukin xafin wajajen da ta yanke, rabon da ta ci abinci
har ta manta sai yanxu a dakin Ummi da aka kawo mata tuwo me xafi da miyar kubewa, ramar da tayi was
so obvious shi yasa Ummi ta sake tausaya mata don a hakikanin gaskiya kishiya ko ma wace iri ce babu
dadi kai ko da kishiyar rana daya ce, balle wnn irin bambanci da Abuturrab ya nuna kiri kiri ai sai mutum ya
hadiyi xuciya ya mutu, Aneesah ta gama cin tuwon ta ajiye plate da bowl din gefe ta tafi bandaki ta wanke
bakinta ta fito ta xauna saman darduma, ita fa bata ji tayi regretting abinda ta aikata ma dakin Jiddah ba,
da son samu ne har da motar ya kamata ta hada a lkcn, ta share hawayen da ya kawo idonta duk da
xuciyarta ya rage xafin da yake mata amma har sannan bai dawo dai dai ba, duk son da take ma Abuturrab
xai walakantata ya ci mata fuska haka dama... tana son kiran Aunty da yan uwanta amma bbu dama tunda
bata taho da wayarta ba, bude kofar dakin aka yi ta daga kai, suna hada ido ya wani daure fuska ya juya ya
fice daga dakin don bai san tana ciki ba da baxai shigo baz ta bi sa da kallo. Main parlor ya koma ya xauna
sai ga Ummi ta fito daga bangaren Abba wanda ko minti talatin bai yi da dawowa gidan ba, ya gaisheta ta
amsa tana kallonsa, mikewa yayi yace "Abba ya dawo ne?" Tace "Ehh" parlon ya nufa ya shiga ya gaida
Abban nasa, yana xaune cikin parlon Hajja ta shigo, Abba ya gaisheta da ladabi yace "Dama yanxu xan
shigo ai dakin naki Hajja" Hajja tace "Aa ba ruwana ni ba sai ka shigo ba, ni da abu ya tsaya min a rai ba
gashi na taho da kaina ba" xaunawa tayi parlon tace "Toh abubuwan da suka faru dai yau Usman da a
Masar ne kai da kake tushen komai xa a daure, abubuwan da suka faru yau kam sai godiyan Allah waiiii, Aa
ban ta6a ganin haka ba ko a pim" Abba dai kallonta yake ta yi, Hajja tace "Toh ba dai komai bari Ramlah ta
iso na sa yara sun kira min ita daxu so nake ayi komai gaban idonta, tun da na dawo Masar abubuwa ke ta
faruwa a garin nan, wanda lkcn da nake bauchi babu haka wllh" Abba ya sauke ajiyar xuciya yana kallon
Abuturrab yace "Do u have any idea of what happened?" Hajja tace "Aa ba sai ka juya masa yare ba, ni nan
xan maka bayanin komai tunda a kan ido na aka yi, amma sai Ramlah ta iso, to amma kafin ta iso ina son
kayi kiran Hafsah ta xo, nasan ai tana garin, kayi kiranta ta xo gidan nan" Kallonta kawai Abba yake, Hajja ta
kalli Abuturrab

89 / 108