Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
yi wani abun kamar warce bata ta6a shiga aji ba wllh Aneesah, ta
ya xaki gaya masa haka bayan ga chatting da mu ka yi dake daxu?" Aneesah ta xaro ido tace "OMG na
mance wllh..." Tsaki Chef Salmah tayi tace "Sai ki nemi yanda xaki gyara tunda kika bata, haba a gama
magana dake kawai ki shigo da wani salon da xai 6ata, ni dai gaya min inda xa a bar maki abubuwan idan
kun fita" Aneesah ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Kawai idan an kawo a xagaya a kai min ta kofar baya
kawai a ajiye i will stock dem all in the freezer idan mun dawo daga hospital din cikin dare" Chef salmah
tace "Ohk to, sai dai na shigo goben" Aneesah tace "Toh ki shigo da wuri don Allah gobe xa a kawo min
furnitures, i have to borrow ontop of wanda kika ara min fa wllh..." Chef salmah tace "Sai dai na shigo din,
kar ki wani damu" Daga haka suka yi sallama, Aneesah ta mike a hankali bayan ta ajiye wayar, wani kayan
ta sauya ta cika turare ta dau karamin veil dinta da handbag ta fito ta kulle rubabben dakin nata da makulli
tana ma kofar dakin Jiddah wani kallo, tun bayan da aka gama jera mata furnitures din ta koma dakin,
sauka downstairs tayi taga Abuturrab xaune alamar ita yake jira, bayan ta shigo parlon ya mike ya wuce
sama ta bi sa da kallo, dakin Jiddah ya bude ya ganta xaune saman darduma, ya xauna gefen gado yana
kallonta yace "Me xaki ci Baby?" Wani iri ta ji sunan, ta dai daga manyan idonta ta kallesa, yyi mata
murmushi yace "Yes tell me duk abinda kike so" a hankali tace "Anything" Ya d'an shafa kansa yace "Ohkk
xan je in siyo yanxu in dawo" a hankali tace "Allah ya tsare" Ya sakar mata murmushi yace "Ameen"
Sannan ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, ta kwantar da kanta jikin gadonta a hankali,
Aneesah na ganin saukowarsa parlor ta koma sama, ya bi ta da wani kallo yace "Kin san kina bata min lkci
kuwa?" Tace "One minute" tana haurawa sama dakin Jiddah ta bude ta shiga dakin tana tsaye daga bakin
kofa tana kalle kalle, Jiddah tayi mata kallon mamaki, Aneesah na murmushi tace "Pls ki d'an ara min body
spray dinki i couldn't get access to mine sbda yanayin dakin..." Jiddah ta nuna mata gaban mirror dinta, ta
tafi ta dau kala uku ta feshe jikinta da shi sannan ta juya ta kalleta tace "Thank you dear" Daga haka ta fita
Jiddah ta bi ta da kallo, Bayan few seconds ta mike ta nufi jikin window tana kallon waje, sai ga Abuturrab
ya nufi parking space din Aneesah na biye da shi a baya, yana shiga driver seat ta bude gaba ta shiga,
kallonsu take ko kiftawa babu har ya ja motar suka fita compound din, sauke idonta tayi ta nufi kofa ta sa
makulli ta bar makullin a jiki ta tafi ta kwanta gefen gado ta rufe har kanta da duvet. Sai da Abuturrab suka
6ata kusan 2 and a half hour a hospital din sbda series of test da aka yi ma Aneesah, ya so su wuce gobe ko
ita ta koma ta amshi result din ta ki yarda wai ita gwara a tsaya ya fito a bata magunguna ko xata iya bacci
yau, gaba daya hankalinsa na kan Jiddah sai kallon agogo yake, har karfe tara ya gota... wani kallo ya jefa
ma Aneesah da ko ajikinta sai chatting take a reception din, yace "Yanxu meye amfanin haka Aneesah kina
ganin karfe nawa yanxu kuwa?" Ta kallesa calmly tace "Kana da appointment da wani ne ko wata? Idan ma
matarka ta can gida kake tunani naga dai ba girkinta bane ai, so ko kwana muka yi a asibitin nan girki na
ne, lkci na ne... Sbda a ba a jikin ka ciwon yake ba shi yasa xaka axalxala haka kace mu tafi??" Dauke kansa
yayi, ta hararesa ta ci gaba da chatting dinta, har ranta taji dadin wannan dadewar da suka yi a asibitin, sai
kusan karfe tara da minti arba'in suka ga likita da test results din, magunguna kawai aka rubuta mata,
bayan likitan ya sanar masu malaria din ma babu yawa a jikinta, kila tana stressing kanta ne kawai, shi dai
Abuturrab fuskarsa a daure yake, ya mike ya amshi takardan da likitan ke basa na magungunan, Aneesah
ta mike ta bi bayansa ranta fess, sai da Abuturrab ya siya mata duk drugs din a pharmacy din hospital din
sannan suka fita, wani eatry ya tsaya yayi masu take away sannan ya dau hanyar gida, ba su suka shiga
gidan ba sai kusan karfe goma da minti goma, Yana sauka motar bai tsaya ta fito ba ya kulle side dinsa yayi
wucewarsa ciki yana rike da ledan abincin, ta bi sa da wani kallo ta kulle motar tana murmushi ta bi
bayansa, dakin Jiddah ya nufa direct, ya murda ya ji a kulle knocking yayi nan ma no respond, juyawa yayi
ya tafi part dinsa, Aneesah ta tsaya bakin kofar Jiddah tana kwankwasa tace "Jiddah, are u asleep, mun
dawo ki bude ki amshi abincinki" Tana tsaye tana ta kiran Jiddah tana cewa sun dawo ga abincinta har ya
dawo rike da spare key yana ganinta ya hade rai, ya sa makullin jikin kofar amma yaki buduwa sbda makulli
na jiki ta ciki, Aneesah tace "Then probably she isn't hungry tunda ta kulle kofa don wanda ke jin yunwa xai
jira har sanda aka kawo masa abinci" Tana fadin haka ta wuce dakinta, Abuturrab ya koma bangarensa,
kasa cin abincin yayi shi ma, shayin ma da yake sha da daddare bai sha ba, yana kwance saman gadonsa
karfe sha biyu saura bayan ya kashe wutan dakin Aneesah ta shigo sanye da kayan baccinta, rufe idonsa
yayi as if sleeping, tsaff sai da jera duk abubuwan da Chef salmah ta bada a kawo mata a deep freezer
dinta, tun daga soups kala uku, da stew me yawa, sannan ga danyen samosa da su spring rolls duk ta ajiye
su a ciki, har da lafiyayyen jollof rice, da fried rice... kulle kofar dakin tayi bayan ta shiga ta tafi ta kwanta
daga gefensa, duk da kamshinta da ya cikasa da abinda ya soma ji lkci daya, haka yayi ignoring yyi feigning
bacci. Da ya farka cikin dare sai yaji hankalinsa ya tashi sbda wnn turaren Aneesahn amma ko kusa da ita
xuciyarsa bai yarje masa yaje ba, amma wani lkcn cikin bacci sai ya ga kamar Jiddah ce a side din nasa sai
yyi saurin kawar da thought din, dab da asuba yaji ta matso kusa da shi a hankali sbda dakin yyi sanyi
tunda Ac a kunne yake, ya lumshe idonsa ya kai hannu ya ta6ata, Aneesah bata ta6a xaton bayan duk
abinda Abuturrab yayi a wnn lkcn baxai kusanceta ba, infact mara lafiya ne kadai xai iya hakuri a wnn lkcn,
haka kawai yaji xuciyarsa ya kasa yin hakan abun ya fita kansa lkci daya, ganin ya juya mata baya ta rikesa
murya can kasa tace "Meye haka Captain?" Juyowa yayi, yayi kissing forehead dinta yace "I am only after
the romance, nothing more" Daga haka ya mike ya shige bandaki ta bi sa da kallon mamaki. Yana dawowa
masallaci da asuba ya murda kofar dakin Jiddah dake a kulle still, ya kwankwasa kofar ya tsaya for almost 3
mins bata bude ba, yayi kasa da murya yace "Meye haka pls Jiddah? Why are u doing this?" Bayan few
seconds ya kara kwankwasawa bata bude ba, juyawa yayi ya koma part dinsa, shiryawa kawai yayi don
gaba daya yaji ransa ya baci, Aneesah ma na bacci ko sallah bata yi ba ya dau jakar laptop dinsa da komai,
snn ya buga gefen gadon yace "Na tafi...." Ta mike xaune tana murxa ido duk da haushinsa da take ji tace
"Da wuri haka?" Yace "Yea i will be driving to kano, plss and pls Aneesah i want nothing but peace, i am
begging u, kinga kece babba i am expecting nothing sai kwanciyar hankali har in dawo" Tayi wani
murmushi tace "In sha Allah Captain baxa ka samu akasin haka ba, Allah ya tsare" Juyawa yayi ya fita ta
mike da sauri bayan ta ji fitarsa gaba daya daga parlonsa, lekawa tayi taga ko xai tsaya kofar dakin Jiddah
amma sai ta ga otherwise don sauka kawai yayi downstairs bai ko kalli kofar dakin ba, tayi wani murmushi
ta juya ta koma ta ci gaba da baccinta, Jiddah na xaune kan darduma ta ji ya kunna motarsa, mikewa tayi a
hankali ta isa jikin window tana kallon compound din, booth taga ya rufe bayan ya saka jakarsa ya nufi
driver seat ya shiga yana gama warming motar mai gadi ya bude masa gate ya fita, Jiddah ta sauke idonta
sannan ta juya ta koma gefen gadonta ta kwanta a hankali.
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
FZ BEAUTY SUPPLEMENTS
Dealer in all kind of dietary supplements such for skin whitening, skin glowing, weight gain, slimming, flat
tummy, infection killers, dark spots removers, fertility booster, Hips boosters, Breast firming and Enlarging,
Teeth whitening, eye, joint, stretch marks, and for marital pleasure. All supplement are available for
wholesale and retail. For more information contact FZ via wa.me/2348143821028
FZ Beauty Supplements
Dealer ce ta supplement masu qara fito da kyaun mace ko namiji, hadi da qarama garkuwar jiki kuzari.
Muna sayarda Supplemnt kamar na qarin duwawu, akwai wanda zaya taimaka wurin dawoda martabar
Nono, akwai na rage qiba da tumbi, akwai na rakwainuwa, akwai na tada komada, akwai masu saka hasken
fata da qyalli, akwai na infection, akwai na saka hasken ido da hakori sannan akwai na gyaran turaka. Muna
maraba da mai sayen daya ko sari. Wa.me/2348143821028
Karfe goma saura Jiddah ta bude kofar dakinta a hankali ta dalilin yunwan da taji ya dameta, tun da taga
fitan Abuturrab daxu da sassafe ta tsorata da gidan kuma, material ne a jikinta na doguwa riga sai hulan da
ta rufe gashinta da shi, ta fito daga dakin ta kulle kofar without making any sound tana satan kallon kofar
dakin Aneesah dake can karshe duk tunaninta tana ciki, ta fara sauka downstairs shi ma bata yarda tayi
making any sound ba, sosai gabanta ya fadi ganin Aneesah xaune parlon tana sanye da rigar bacci har
sannan, ta daura kafa daya kan daya tana cin cake tana danna wayarta, xuciyar Jiddah ya dinga bugawa ta
karasa cikin parlon tana tafiya a hankali, duk da yanda ta dinga avoiding su hada ido sai da suka hada idon
da ita, daburcewa tayi, bata san lkcn da tace "Ina kwana" Aneesah tayi mata wani kallon daga sama har
kasa, ta ja wani tsaki ta ci gaba da cin cake din hannunta tana danna waya, Jiddah ta sauke idonta ta nufi
kitchen duk jikinta yayi sanyi, kulle kitchen din tayi ta turo baki ta jingina da kofar, sai taji haushin kanta
gaisheta da tayi, to amma ai bata ma san sanda ta gaisheta ba, bin kitchen din ta dinga yi da kallo, duk da
babu wani plate da aka bata amma kitchen din na bukatar gyara, rabon da ayi masa komai tun jiya da safe
da ta yi, ta ta6e baki ta shiga store ta dau indomie guda daya a kwalli sannan ta fito, sai da ta fara daura
kwai a kan wuta, tana tsaye har ya dahu, sannan ta fara girka indomie din, bata jima a kitchen din ba ta
gama, ta juye indomie din a plate sannan ta rufe da wani plate ta dau fork ta bude kofar kitchen din ta fito,
sosai gabanta ya fadi ganin wasu manyan mata har hudu a parlon tare da Aneesah duk sun cika parlon da
muryarsu kamar ganga, da yake ta rufe kofar kitchen din shi yasa bata jiyo su ba tun daxu, tana fitowa
parlor duk suka yi shiru, duk da ba kallonsu take ba amma jikinta ya bata duk ita suke kallo, har wani
hardewa take tana tafiya da sauri, Chef salmah ce da Rabi'ah sai Suhaila da Fauziyya, duk kawayen
Aneesah ne kuma sa'aninta da suka yi karatu tare a Abuja kana ganinsu ka ga gogaggun yan matan Abuja,
Aneesah kadai ce ta dace tayi aure cikinsu, sauran duk gantalinsu kawai suke, kuma yawanci duk babu
warce iyayenta ke nan kaduna kawai xamansu suke a garin, Chef Salmah da Rabi'ah ma su biyu kadai ke
xaune gidan iyayen Rabi'ah dake Unguwan sarki, dukkansu suka bi Jiddah da kallo, Rabi'ah ta kalli Aneesah
da wani expression tace "Wait... wai wannan er yarinyar ce kishiyar taki?" Aneesah ta kyabe baki tace "Wai
ba" Wani dariya suka yi gaba daya har da kyakyatawa, Chef salmah tace "Kuturin uba!!! Yo ai wannam
karamar alhaki ce Aneesah, ni wllh duk tunanina sa'ar mu ce aka kawo maki xa ku gwabza, yanxu da
wannan er cikin naki aka hada ki kishi? To kiyi kishi da ita kice kinyi kishi da wa Aneesah?? Wllh ni duk sai
naji raina ya baci, me aka yi aka yi wnn yarinyar, dubeta fa duk a tsorace kamar zomo...." Jiddah dake jin su
ta nufi stairs ko juyowa bata yi ba tana jin kamar xata fadi sbda hardewar da take, Suhaila ta rike ha6a tace
"Ikon Allah, yo minti nawa xa a 6ata wajen gamawa da wnn er yarinyar? Ni har kin ban kunya wllh
Aneesah, ni fa na xata wata uwar mata ce ashe wai wnn kwailar aka kawo maki gida kika bi kika daga
hankali kika bi kika ishemu a group" wani tsaki ta ja, Fauziyya ma ta ja tsakin tace "Wllh kwana uku yayi
kadan idan ban sa xaman gidana ya gagareta ba shegiya nake, look how meek she is, wannan ai kamar kin
samu er wanke wanke ne da share share, ya wuce ma ki aiketa ta amso maki kati ko cingam a kofar gida??"
Duk suka kyalkyale da dariya, Rabi'ah tace "Toh ke yanxu Aneesah fasa kayan daki shine iya abinda xaki iya
yi ki burge kenan? Is that all u can do? Haba wannan ai karamar alhaki ce" Aneesah tayi wani dariya tana
jinjina kai tace "You guys are only being faster than ur shadows" Jiddah dai tuni ta shiga dakinta ta saka
key, gaba daya ta tsorata da su, on a serious note Chef salmah tace "Kinsan Allah Aneesah lamarinki ya
kunyata ni wllh, na xata xan xo in ga er 35 ne, wai ashe a kan wnn da kilan bata wuce 18 ba kika daga
hankalinki haka" Aneesah tayi kasa da murya tace "I think i told u all yanda abubuwa suka dinga faruwa
tun ma kafin ta tare, da rashin mutuncin da na dinga yi, yanxu abu kadan captain yake jira inyi shi yasa ku
ka gan ni a yanda ku ka gan ni, shi yasa ku ka ga nayi shiru, wllh ba don mahaifiyarsa fa ranan da nayi ma
kayanta aika aikan nan saki na yayi niyyar yi don har ya dauko takardan ta hanasa, banda haka ni dai
kunsan ba kanwar lasa bace, kawai ku bar ni in ci gaba da bin su da ido for the mean time, ko kun ta6a
ganin mutumin da bai kama dahir ba yana iskanci? Ai yanxu sai dai kawai in bi komai a hankali, domin
kuwa a wuyar captain nake yanxu, nasan kuma babu wanda yake jin haushi sama da ni a duniyar nan, sarai
na sani" Rabi'ah tace "Toh Allah ya kyauta, idan an kawo kayan mun gama gyare gyaren da xa mu yi sai mu
tafi inda xa mu je kawai since akwai lkci, ni fa shi sa har yau ku ka ga naki amsa ma Alhaji Salisu, so kawai
nake sai na gama duk abinda ya kamata tun daga waje, ta yanda ina shiga gidan komai ya dawo hannuna
baxan iya wahala ba gaskiya, don haka sai na shirya tsaf anyi duk abinda ya kamata sannan xan basa izini
ya turo" Fauziyya tace "Kina da gaskiyar ki wllh, wa xai xauna? Yan iskan uwayen gidan nan da jira kawai
suke Allah ya kawoka su nuna maka takama da isa, to wllh ba ayi matar nan ba, shi sa muke shiri sosai kafin
mu shiga...." Aneesah dai sai wani murmushi take tana girgixa kafa, jin ringing din wayarta ta mike ta isa
gun wayar dake caji da sauri ta dauka ganin me kiran ta daga ta kai kunne, a d'an fusace tace "Ni ban ga
wani alert ba har yanxu wllh, haba abu tun jiya dae kamar xa a turo min miliyan goma, gashi sbda rashin
cikon kudin ba a turo min kayan ba har yanxu" Ta kyabe baki tace "Toh ina jira ni dai..." daga haka ta katse
wayar, Fauziyya tace "Yanxu da mun xo karfe takwas da rabi haka xa mu yi ta xama kaya basu iso ba"
Aneesah tace "Toh ba sai an samu cikon kudin ba sannan xa su iso Fauziyya, kun san fa na canxa furnitures
din daga wanda na tura maku a group, wannan ya fi shi tsada, daga baya company din suka turo min
wannan naga ya fi kwanta min kawai na xa6e sa" Sai karfe sha biyu motar kayan Aneesah suka iso gidan,
kamar dai yanda aka yi na Jiddah ita ma haka sai da suka sauke sababbin kayan snn suka dinga fitar da
fasassun waje suna lodawa a babban motar, kafin karfe uku masu kawo kayan duk suka shirya mata
furnitures din sannan suka wuce... Suna xaxxaune da kawayenta a dakin bayan an gyara ya dawo fess, sai
ya6a furnitures din suke, ita kuwa sai murmushi take tana bin dakin da kallo don ya fi nata na da kyau,
miliyan 1.5 tayi kayan dakin, Babu warce ke da alamar tashi tayi sallan axahar cikinsu, Aneesah ta fita tayi
masu rechauffe din jollof din dake freezer ta kawo masu dakin da drinks da ruwan gora, ko wacce ta sauko
kasa xa a ci abinci. Sai wajen karfe biyar da rabi suka shirya ta rakasu bakin motar Rabi'ah dake kofar gida,
Chef salmah tayi wani dariyan yan da6a tace "Sha kuruminki aminiya, mota kamar Aliyu ya siya maki
wanda ya take wancan na garage, ke dai Allah ya bamu nasara kawai.... Mu ne fa!!" Rabi'ah tace "Banda
ma tana ta mana xurfin ciki ai da ba a kai ga haka ba wllh, ni duk a xatona don taga tayi aure ne ta wani fita
harkanmu take shan kamshi shi sa nima na sakata a kwadon shara, kawai na sha iskanci ne tsabagensa
take mana, ashe tana nan tana ta kunsar takaicin d'a namiji, ni da na maida maza kamar rigar sawa ta, in
cire sanda na ga dama in mayar, ga dai su da yawa a gari kamar ledan pure water,